Showing 39001 words to 42000 words out of 124070 words

Chapter 14 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

347

kadan dan ta gaishe shi muryarta a sanyaye ainun da tsoron da ya cika mata ciki ta shiga gaishe shin

Shirun da ya dauki wajen ba amsa ne ya saka mutanen dake wajen bayan su sake dubansa, sai dai gannin Kan Giwa na yi mata irin kallon nan nasa na son karantar abu ko mutun ya sa Da sauri Murja ta ce" Nuriyah dan daga muryarki kadan bai jiki ba fa"

Nuriyah idannuwanta na cika da kwallah ta dubeta muryarta na rawa ta ce" Auta haka nake magana ba da gangan na yi ba"

Tausayinta ne ya kamata, domin kwarai gaskiya ta fada ita din mai sanyin magana ce sosai da sosai, da yawancin lokuta har akan ce mata kissa ce irin ta mata masu classs, sai dai idan ka zauna da ita zaka gane haka muryarta take da sanyi, saima ta karra sanyayawa idan tana hali na rudanin zuciya ko tsoro

Ita dinma jikinta a sanyayen ta dubi Kan Giwa da siga irin nata da take tunkararsa koda ransa a bace ne ta ce" Yayanah, da mura ne ta tashi yau sosai ka yi hakuri dan Allah"

Kamar an kwaci fuskarsa haka ya maida dubansa kan Murjanatu
Ya yi mata kallo na yan sekwani kafin ya dauke idannuwan nasa a hankali ya mike daga zaunen da yake ya juya barin da Nadia ke tsaye tana cika tana batsewa da yaren turanci ya umarceta kan ta dauko masa abincinsa ta kawo masa dakinsa sannan ya wuce ya yi tafiyarsa dakin nasa dan ranar hutawa yake yi na zai fita ba sai ko gobe

Sai da ta je ta hada komai tana ta tunanin kar ta saka abinda zai bata masa rai ko kwatankwacin hakan domin su ba su suke saka masa abinci ba hakan ya sa basu san me da me yake so ba da adadin abincin da yake iya ci ba

Tana tura yar kurar da ake dora abincin ta karaso kusa da su kasa kasa sosai ta ce" Kanaina haka kuka zabarwa kanku? Kun taba gannin KAN GIWA ya ci abinci a daki? Sanadiyar wannan yarinyar yau har ya kaurace wajen cin abincinsa na shekara da shekaru? Ku sake tunani kan lamarinku gaskiya"

Da ido suka rakata babu wanda ya ce da ita ufan har ta shige babar kofar dakin Kan Giwa

Kasa kasa sosai RISLAN ya ce" Me yake faruwa ne Baby?"

Auta ta sauke ajiyar Zuciya tana dage kafadunta ta ce" Ni kaina ban san meye damuwar matan nan ba, dan tun jiya suke abubuwa tamkar zararu , a tunaninsu Nuriyah ta zo wajen nan ne dan ta zama barazana a cikinsu, a ganninsu tana iya zamtowa daya daga cikinsu shi yada gaba daya suka haukace suke neman haukata zaman lafiyar kowa, domin kowace cikinsu abin fada take nema"

Da mamaki shinfide saman fuskarsa ya kalli NURIYAH dake ta murzar hannu dan du a takure take ya kalli Murjanatu ya dauki yaren turenci ya ce" Me kike nufi, kina nufin tsabar basu da hankali sunna tunanin Yayanmu zai iya yim soyaya da Nuriyah?"

Itama da wani mamakin da ya shinfidu a saman fuskarta tana kallonsa ta ce" Ban gane sunna tunanin zai iya yi ba yaya? Kamar kana gannin bata kai matsayin ba?"

Zamansa ya gyara yana ajiye wayarsa da kyau ya ce" Baby kin fa san sarai me nake nufi, NURIYAH fa idanma ta fiki bai fi ta baki shekara biyu ba, kin kuma san waye yayanmu, a tsarin macen da yake iya duba babu ta kasa da shekara talatin, bama wannan ba ni kar ku min haka bana so, duda ta dakatar da ni ta nuna min cewa ni din na fi karfin soyaya da ita lokaci na bata, na bata dama ta sake hutashe da tunaninta, na mata tanadin lokacinmu, na tabata idan na zaburo zata dubeni , gaskiya idan matan nan nasa zasu takura mata ne ta koma cen har su Hajia su dawo"

Zata iya cewa kwata kwata ita lamarin dan uwan nata bai wani shigeta ba, dan hakane ta ki tofawa a kan hakan, ko dan yayan kawarta ya nuna yana son Nuriyar ne? Ita gaskiya gaba daya gani take yi Yah Rislan yaro ne sosai a kan lamarin Nuriyah, ko me yasa ? Oho..........a sanyaye ta sake rike hannun Nuriyah tana kallonta ta ce" Ni bama wannan ba duka, gaba daya bama wannan ba Brother, Wannan tsoro da baya baya da Nuriyah ke yi a gabansu baki dayansu na damuna, dan Allah me yasa zaki ringa jin tsoronsu ne? Mutane ne kamarki, bale a yanzu da suka sako ki a gaba burinsu su saka ki gaza daukan rigimarsu, me zai hanna ki yi gwa da gwa da su ne?"

Da mamaki itama Nuriyar take kallonta a nutse ta ce" Auta, na yi gwa da gwa da su wa kike magana?"

Murjanatu ta ce" Da ita Nadiar da Djamilar"

Nuriyah ta yi murmushi tana sauke ajiyar zuciya ta ce" Ni a wa?"

Daga Rislan har ita kallonta suke kafin Rislan cike da shaukin yarinyar ya ce" Ke a mutun dan Adam mai daraja"

Nuriyah ta kalleshi a karo na farko ido cikin ido tun fitowarta domin tun dazun tana ta murza hannayenta ne dan ta samu jikinta ya daina rawar gannin Kan GIWA da matarsa a wajen , tana ta son koyawa kanta yadda zata rayu da su ba tare da ta wahaltu sosai ba, domin wajen nan dai nasu ne, ya zama dole haduwa da ita da su a kowani irin lokaci

Murmushi ta yi tana janye idannuwaan a cikin nasa a nutse ta ce" Tabas dan Adam yana da daraja, shine halita mafi daraja a cikin halitu, haka kuma a cikin y'ayan Adam akoy sarakai, akoy iyayen gida kuma akoy y'ayan gida, kamar ma'aikata ce, zaka yiwa wanda yake gaba da kai biyaya koda kuwa ka girme shi a shekaru ne, bale aiki irin nawa
Ban taba aikin aikatau ba sai a wannan karron, ban san yaya wasu gidajen suke ba aman nakan ji daidaiku a wajen saide saidenmu ana kwatanta irin rashin adalcin wasu iyayen gidan, Auta da yaya RISLAN da an zo gidan nan zan iya cewa hankalina ya kwonta sosai na kuma samu nutsuwar da har nake ji a yanzu idan na fita zan yi ta gararamba a kan titi ne ina bin waje waje, shi yasa nake so ku taya ni, dan Allah ku tayani yiwa iyayen gidana biyaya, kar ku ringa saka min abu a kaina duda ba mahaukaciya nake ba aman zuciya bata da kashi yau da gobe kuma sai Allah, idan ku kun aikata irin haka kun tsira ni na san sai dai a tsireni domin haka din rashin da'a ne, rashin kunya ne, rashin godiyar Allah ne, a gaskiya ina alfahari da tsoronsu da nake ji dan ko ba komai tsoron nan nasu da nake zai sa na kiyaye dokokinsu in sha Allah " ta karashe tana ta sauke ajiyar zuciya dan harga Allah abinda take da muradi su yi mata kennan, ba su ringa daidaita kansu kai tsaye da ita a kowani lokaci ba, kai ita da za'a ware mata aikinta a wannan bangarenma kamar yadda take da shi a dayan bangaren da ta godewa Allah, da kuma matansa ko a leke ba zasu kuma ganninta ba dan idan ta buya sai an nemeta


Da wannan suka je suka karya suma sannan suka fice gaba dayansu suka nufi cen bayan gidan Rislan na ta jajen gobe gobe zai tafi shi kam ko kwana biyu ba za'a bashi ba, yar uwar nata tsokanarsa irin na mutun da mabiyi, Nuriyah kuwa na dan murmusawa idan halin hakan ya kama

A cikin dakin KAN GIWA

Tunda ta fara magana da irin kalaman dakew fita daga bakinta ya cire dubansa irin na kureta da idannuwan nan ya kawar gefe guda ya kurawa lalausan kafet mai gashisshika ido yana kallo bai ce mata ufan ba har sai da ta dire bayaninta sannan ya sake juyowa a karro na biyu yana kallon hannayen nata da take maganaa da su zuwa bakinta dake furucinsa

Dan murmushi mai ciwo ya yi sosai yana kallonta ya ce" Tabas na san aure ba iya sex ya tsaya ba, domin nakan ji magidanci na shaukin maganar cewa yau ko me madame ta dafa? Nakan ji magidanci yana cewa ya ajiye madame a saloon, ko da ya zo lokaci zuwa lokaci sai na ga waya ta yi haske wai ace madame ce.......... ni da kaina ina son na ga dayan abin nan da na rasa gane menene shi na sanshi......sai dai abin takaicin Sex dinma da ake min kallon shi na sani a duniya bani da shi yadda nake so?"

Nadia ta kure shi da kallon tsoron irin kalamansa na yau, domin da da ne zai wartota ne ya danneta a saman gadon ya amshi abinda yake so
A raunane ta ce" Baby (>?z?), yanzun du irin kokarin da nake yi a saman bed bai kai godiya ba? Kana ganni ina iya bata lokaci mai tsayi ina romancng din dukkan wani lungu da sako na jikinka, bai isa ya saka ka samu nutsuwa da ni ba?"

Jin kansa na neman sarawa ya mike ya nufi bayi yana fadin" Kina iya tafiya"

Da kallo ta raka shi har ya shige cikin bayin sannan ta sauke ajiyar zuciya tana zarro ido da kallon abincin da ta zuba masa bai ci ba gashi har karfe goma sha biyu na neman yi na rana bayan Kan Giwa ba dai yiwa abinci uzuri ba
Marfinsa ta saka ta rufe ta juya ta fice a dakin
Abu daya tal ta sani tare da mijinta shine idan ransa ya baci baya so kowa ya zauna masa a tare da shi, shi yasa ba zata takura masa ba, ita ta kwana gidan sauki, da ta masa maganar me yasa rayuwarsa sai da sex zai rayu da iya gaskiyarta take, ace rayuwa Namiji sai ya sasakeka? Shi ba zai iya hakura da Romance ba? Romance ai shine soyayar, aman sai ta rasa daj me yake son sai ya yi, har fada yake yi yau kwanansa uku rabonsa da mace, ko ina Izabel dinma ta yi?

A bangarensa kuwa a bayin ruwan sanyi ya samu ya runga wanke fuskarsa da shi
Tamkar wanda wani abu ya ciyo shi mai mugun daci ya saka hannunsa da karfi ya daki gilasss din dake jikin bangon haka kuma tashi daya zuciyarsa na tafarfasa

Idannuwansa ya rintse, domin gilass din ya fashe ne harma ya shigar masa bayan hannu hana ya sa jinni ya fara dan bata wajen a hankali a hankali

Hauhawa kirjinsa yake yi da wani dacin , sosai ya gama hawa sama a tsaka tsakiyar tashin hankalin da yake ji tun daga cikin zuciyarsa ...........wannan shine gaba kura baya sayaki! .......ZINA bashi, matansa sakarkaru, idan azumin ya dauka yana shan ruwan yake tashi da feeling!, Ya subahannalah! Ya kai hannayensa ya dafe kansa yana jimkewa
Bai taba jin daci irin na yau ba
Bai kuma taba yarda cewa eh idanma akoy son zuciyarsa na bin matayen banza to fa akoy sakaci na iyalinsa
Bai kuma sake yarda cewar rainin hankali ne ya masu yawa ba har sai da ya auna su sauran matan dake iyawa da shi ai suma mutane ne ba injinna ba

Da dacin rai ya fito ya fice ya nufi bangaren da kayan motsa jikinsa suke ya rufe ya shiga motsa jikinsa, ga yinwa na dan tsikararsa da sauransu

A wannan ranar a nan ya wuni cirrr, idan lokacin sallah ya yi ne yake ficewa ya je masalaci ya salata ya dawo, a cikinsa kuwa banda madarar dake cikin frij din da ya ringa sha kadan kadan baya taba komai, yana ta auna lamarin rayuwarsa ne
Shi dai ya san a harkar jikinsa akoy wa'inda suka dame shi suka shanye a nacin abin nan, ya kuma san babu abinda ke rikita kwonciyar hankalin namiji irin ya kasamce a irin bukatuwar nan ya kumarasa.....to wai yana da tambayama a wajen mutanen dake dukan kirji su budi bakunnansu su ce " *DAN ME ZA'A TAKURA DA MAGANAR SEX BAYAN SOYAYA BA A NAN TAKE BA, ANA KUMA IYA RAYUWA DA SOYAYA A ZUCIYA BA TARE DA AN YI SEX BA*!" Neman amsarsa shine a fayace masa dala dala maganar nan dan ya gane mahaukaci ya yita ko mai hankali????????? A fada masa ta yadda zai rayu da mace igiya na zame masa karfe a wando ba zai taba ba sai dai ya kalla dan shi so ai so ne babu tabe tabe?






*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
3?? 1??





Yana dawowa daga sallar isha'i ya wuce direct cikin gidan ya zarce dakinsa domin a lokacin su Nuriya na kicin ita da Murjanatu sunna girkin da suka saka kansu wanda Nuriyah ke cikin nishadin gannin sunna girki da kansu, dambun nama suke yiwa Rislan da ya nuna yana so mai yawa da zai yi guzurinsa dan komawa makaranta

Yana shiha dakinsa wanka ya shige ya yi sosai sannan ya fito daure da tawul dinsa ya nufi wajen da ya bar wayoyinsa
Kiran da ya tarar sai da ya saka shi dan zarro ido ya mayar da wayar nan ya ajiyeta bai maidawa kowa kiran ba , ciki kuwa harda Hajia Murjanatu domin yau din nan harda ita ya wuni jin haushi a zuciyarsa dan du ita ta karra saka masa kyamatar zinna a zuciyarsa haka kawai ita da mijinta da d'anta !

Da wuri ya samu waje ya kwonta, abincin nan da aka kawo masa yana nan wajensa , sannan dakin bai samu arzikin tsintsiya ba, shi du ba ta hakan ba yake hannunsa ya yi kaba sosai ya fara kumbura haka kuma jikinsa yanna jin da zafi zafi dan haka ya kwonta ya rufa rufff ya shiga neman barci

A bangaren sai da suka gama komai suka juye a abin tsanewa suka rufe rufff dan kar wani abu ya fada sannan suka rufe kicin din suka shige dakinsu da nasu abincin, falon sai kanshin soyayan dambun naman yake basu saka turaren wuta ba, dan gudun fitinanun matan nan da tunda safe basu kuma gannin kowace a falon ba, su a tunaninsuma ko sun fita ne, sai dai ai basu wuce su ba basu ji karar fitarsu ba, kawai kowace na dakinta tana fama da wayar asara, babu wace ta nemi wajen da mijinta yake, hasalima a wunnin ranar idan sun daga waya dan kiran cikin gidan dan su yi oder irin abincin da suke iya ci ne kawai a kuma kawo masu har bangarensu


Cike da nishadi da farin ciki yan matan suka gama cin abincinsu bayan sun gama yin wanka da sallah da komai, sannan Murjanatu ta turawa mamanta vidio call a daidai lokacin da summa suka gama cin nasu abincin sunna dan taba hirar yama don tserayar awanin dake tsakani ya saka bambancin lokacin tsakanin kasashen

Idannuwanta ta zubawa fuskar Nuriyah a lokacin da take yar dariya dan Hajia na mata tsokana kamar jikarta ta jinninta

Ajiyar zuciya ta sauke ta maida dubanta kan mijinta da shima ya kurawa yannayinta ido

Idannuwan nata ta sake cirewa a kansa ta maida kan Nuriyah, watau yarinyar harda gura gura gareta a harshenta irin na gidansu sai dai a gidan nasu yar uwarta bata gura gura, itace mai gura gura da mahaifinsu da mahaifiyarsu

Tabatan da Hajia ta yi da kula tana fadin" Maman takwara lafiya?" Ya sakata sauke ajiyar zuciyar da sai da kowa ya kalleta

A hankali Murja auta ta ce" Mamanah baki da lafiya ne?"

Dan murmushi ta yi wanda kumatunta suka lotsa tana shafa gaban goshinta ta ce" Lafiyata kalau autana, ina yayanku ne? Ina fata ya ci abinci kuma kun kula da baku dauki magana ba ko?"

Murjanatu ta gyada kanta duda bata da masaniya a kan maganar cin abincinsa, sai dai a tunaninta ai mata ne tare da shi har biyu wa'inda take tunanin Saboda su yanzun yama tsaneta ne, domin tun jiya zuwa yau wani iri take ganninsa ita dai kuma du laifinsu ne , dan haka ta bada amsa da eh

Mama ta yi murmushi a sanyaye ta ce" Nuriyah ?"

Nuriyah dake bayan Murjanatu ta duko da girmamawa da Murmushi ta amsa tana kallon Maman,
Mama ta lumshe idannuwanta zuciyarta na dokawa a sanyaye ta ce" Allah ya maki albarka"

Sai da NURIYAH ta ji wani irin abu na tsirga mata jikinta gaba daya, muryarta a sanyaye ainun ta dago sosai tana kallon fuskar matar ta ce" Amen ya Allah Mamah"

Mama ta sake lumshe idannuwanta ta mike da sauri ta yi ciki hakan ya sa Hajia rakata da kallon mamaki da tunanin abinda yake damunta, inda Aba ya mike ya bi bayanta dan yannayinta ya saka shi a cikin tunanin ba lafiya ba

Yana shiga ya ganta tsaye gaban madubi ta sada kanta ta rungume hannayenta biyu a kirjinta , hakan ya sa ya karasa yana kallonta a nutse ya furta" Maman Auta me yake damunki ne haka?"

Juyowa ta yi a hankali tana sauke dubanta a saman fuskarsa, raurau din da ta yi ne ta kasa rike hawayen da ya cika mata idannuwanta har suka samu damar biyowa gurbin idannuwanta a hankali sunna zarya a saman kumatunta
Hankalinsa ne ya fara tashi yana dubanta ya ce" Yar uwarki ko? Aman me ya saka ta fado maki a rai kai tsaye haka bayan kikan jima koma nace tunda kika dauki shawarar Mama cewa kuka ba shine magani ba ki yi ta yin adu'a kina fadawa ubangiji sannan ki ringa yawaita sadaka in sha Allahu ko me ya faru da ita zaki ji shine yau kuma zaki yi halin?"

Hannayenta ta hade ta shiga murzawa tana fadin" Ba zaka gane ba Aban Babana (Kan Giwa), ni da kaina na rasa gane cakulewar tunanina a kan lamarin yarinyar cen, ka ga dai bata kama da yar uwata sam, aman kuma wasu irin abubuwa ke karra fuzgata a kanta, da zarar na ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login