Showing 90001 words to 93000 words out of 124070 words

Chapter 31 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

344

kallon lebenta dake dan rawa wanda sai yanzu ya ga man leben da aka shafa masa sai walwali yake yi abinsa walwalwalwal yana dura masa ashar, to in ba dura ashar ba gaba daya gani ya yi zai tsole shi ne walahi

Yawun bakinta ta hadiye a hankali ta sake kure nasa leben da kallo itama dan ta karra karantar furucin bakinsa dake sanyayar mata da gaban jiki yana fada mata kalaman da yake fadi dan ya nutsar da ita ba zai yi mata komai ba dan ta kunace masa waje haka sannan hannayensu sun hadu

A hankali ya ce" kina son zuwa ki siyo goron?"
(Kai jama'a =? ?) daga shi har Hajia da ita din tambayar ta masu wani iri, dan shi din da kansa da ya yi tambayar sai da ya yi ya fahimci ya yita ne dan yana so ya bata damar yin abinda take so ba tare da ta yi kuka ba, ita kuma tama rasa me zata ce, Hajia baba kuwa farin ciki ya dada mamaye zuciyarta tana mutsu mustsu da hannunta dan bata so ya cika nasa duda ta kage aman ta danawa bawan Allah tarko dole ta jure

A hankali ta gyada kanta tana sake kallonsa kamar ta afka masa take ji, gashi bayanta har ya fara amsawa na gajiyar dukowar da ta yi

Kansa ya gyada din shima a hankali ya ce" Nuriyah"

Aa sake duban idannuwansa sai kuma ta maido kan lebunnansa tana kallo
Kan Giwa ya kuma fadin" Kin san bakya son duka ko?"

Da sauri ta gyada kanta tana kallonsa da son ta fashe da kula da tsoron sunnan dukan, hakan ya sa ya ce" Ki amsani mana "

Nuriyah ta bude bakinta tana yin kasa kasa da kallonta dan idannuwanta da suka ciko da kwalah ta budi bakin ta ce" Bana son duka sir".......hakan ya sa hawayen nata zuba a saman kumatunta

Hawayen ya bi da kallo da tarin mamakin rauninta da saurin kukanta, yaya aka yi yawancin matan da ya sani bai sansu da irin wannan ba? Kai asalima baby kadai ya sani nada saurin kuka a duniya sai ga wata babyn nan itama yar uwarta, sai yake ji du baya son hawayen har cen kasan zuciyarsa, baya son kukan yarinyar nan kwata kwata , ba kuma haushi bane kukan nata ke bashi, jine yake yi idan tana kukan tamkar ya rushe da shi shima ko zai ji sauki a zuciyarsa ( da mun shiga uku)

Cijewa ya yi ya ce" Idan kuka je siyan goron, daga cikin mota Baby ta fita ta siyo ta dawo a dawo da ku yanzu grand parents dinki zasu zo, ai zaki so ki fara ganninsu ko?"

Yanzunma amsashi ta yi da eh, dan haka sai ya samu kansa da samun boyayiyar ajiyar zuciya na jin relief a zuciyarsa ya dan wara hannunsa hakan ya sa hannun Hajia ya bude domin dama ba wai ba zai iya budewar bane, ya zare kudin ya sakawa Nuriyah a hannunta yana kallonta a hankali ya ce" Share hawayen naki"

Hawayenta ta kai hannunta a hankali ta share tana sasauke ajiyar zuciya ta sake duban fuskarsa a daidai lokacin da idan ba gizo idannuwanta ke yi mata ba fararan hakoransa ne ta gani na yan sekwani ya mata murmushin da zata iya rantsewa da Allah bata taba gannin murmushin namiji da kyau irin nasa ba, sai kuma ta juya da sauri tana sake yafa mayafin Lafayarta ta kai dubanta wajen iyayenta, wa'inda a dagowarta suka cire kawunnansu a bangarensu suka juyar kmar basu ga komai ba, haka kuma ta saci kallon wajen mazan, sai ta ga Abanta kadai ke kallonta watau mijin mamanta fuskarsa dauke da murmushi sauran suma basa kallonta, dan haka ta sakar masa murmushin itama ta karasa wajen Murjanatu da ta yi mutuwar zaune ta kama hannunta tana fadin" Mu je"

Murjanatu ta mike ta bita har kamar zata kifa inda yake bin tafiyarta da kallo har ta bude bayan motr ta shige ta rufe kafin ya sauke ajiyar zuciya a daidai lokacin da abanta ya yi wani murmushin a zuciyarsa yana ayan' CauCau haihuwa mai dadi , ashe Kan Giwa zai ce min Baba?'

Bai cire dubansa a kansu ba sai da suka bacewa ganninsa kafin ya juyo ya sake duban hannunsa da na Hajia dake rike da junna raf kamar wani abin, dan haka da sauri ya yarfe yana juyowa barinta ya ce" Meye?" Domin sai wani duba da tsararen murmushi take kashe shi da shi

Hajia ta tabe baki ta ce" Menene kuwa mijin ba indiya, ka ga Ka yiwa matarkan cen fada ta daiana hararar wajen da nake zaune, wa bilahilazi zan kwada mata marin da zata kusan summa!"

Da bakin mai fadin matin, da hannun da zai yi marin ya kalla, sai kuma ya juya wajen wace za'a maran, gaba dayansu ya ga irin yadda fuskokinsu suka yi kicin kicin tamkar an turro masu da sakon mutuwa, haka kuma gaskiyar hajia kamar wa'inda suke hararansu, to aman me suka masu da zasu harare su? Bayan wannan su din ai ba saanin su amshi harara daga wajensu bane ko?
Tsatsaresu da ya yi da ido ya saka su cire nasu duban a kansa Nadia rai bace da yaren turanci ta ce" Tunda kike da Kan Giwa ya taba yi maki magana a hankali haka Djamilartttttt? Wai mema ya cewa yarinyar cen da ta tafi da katon takashi kamar bayan mota"

Djamilarrt da ta kasa zama waje daya tana ta abu kamar ta sha yaji ta daki cinyarta da ciwon abin ta ce" ko me ya fada mata ba shine damuwana ba irin yadda ya bi duwawunta da kallo, kin san fa oganmu da son abin nan kamar mate, kar dai yace zai so yarinyar nan karama bayan ka'idarsa baya ra'ayin karamar mace?"



*Karashensa sabon salo*


Na

SAJIDA


Page.
5?? 3??




A hankali Nadia ta ce" Kina nufin , zai iya sonta, har ya kai ga kwoncia da ita?"

Djamilarrt ta tabe baki ta ce" So ne wo, ko ba so ne ba wo, na tabata soldier oga yanzu haka ya gama daukan caji wo, Allah ya sa yau ba nice da shi ba?"

Gaba daya Nadia sai ta rasa abinda zata ce, ta sake juyawa ta zuba masa ido tana kallonsa, ta kula sam Djamilarttt ba'ai mata haalitar kishi ba a zuciyarta, domin kuwa wannan abin da take yi ta tabata idan yace auren yarinyar cen zai yi bata da damuwa da haka, shi yasa bata gabanta dan ta tabata ba son mijinta take yi ba, kudi ya fi mata mijinta daraja, domin da kudinta ne ta ga zai bace da ta tada wajen nan da ihu da karkade karkaden zani, aman yanzun mijinta ne ya bi yar aiki da kallon nan ta nuna oho? Dama zuciyarta cike da takaicin mutanen da aka zo tarba da su kamar wasu mutane masu mahimmanci a rayuwarsa, sai kuma wannan? Walahi ba zai taba yiwuwa ba, ba zai yiwu ba

Mikewa ta yi ta yi gaba ta nufi cen hanyar da idan suka dawo ta nan zasu biyu ta yi tsaye tana gadin wajen
____________________________________


"Wai nice zaki boyewa maganar nan tsakaninki da Allah ? Abinda ya ringa fada maki a hankali nake so ki fada min haba yar uwata?" Murjanatu ta sake fada tana ta sake yiwa Nuriyah naci dan so take yo zargin da ta fara yi ya tabata, to ita kuwa idan haka ne ina zata saka ranta yau dan dadi? Tabdijan, wayo dadi sai ya kasheta

Nuriyah da leda mai dauke da goron ke hannunta ta dafe kuncinta tana kallonta ta ce" Ya Allah, baby nace maki ba komai bane ko? Ni kam na rasa gane kanki"

Murjanatu ta tabe baki tana hararanta ta ce" Karma ki fadi"

Nuriyah ta saka yar dariya , dama ja mata rai take yi dan ta ga ta damu da son jin gulmar ta budi bakinta zata fada mata kennan suka ji motar ta tsaya, dan haka suka waiga a tare dan gannin har sun iso wajen ajiye motocin ne? Domin sun ga lokacin da suka shiga a?roport din

Idannuwansu su dukansu a kanta suke a lokacin da ta saka fari kal din hannunta ta bude bayan motar ta dafe marfin da hannunta fuskarta a daure tana kallon Nuriyah ta ce" Ke fito nan ina son magana da ke"

Cikin Nuriyah sai da ya murda mata , ba wai maganar ce bata gane ba, ta gane maganar yannayin matr ogan ce ke neman tsoratata

Murjanatu na kallonta ta ce" Aunty lafia dai? Ki shigo mana sai ki ganta daga ciki ana wucewa ana kallon........."

"Dakata ke sarkin iyayi ba da ke nake ba, ke zaki fito a motar nan ko sai na tsintsinka maki mari?" Ta fada a zafafen da ya ankarar da sojan dake tare da su har ya bude ya fito yana kallonsu baki daya dan yana son fahimtar abinda yake faruwa, da ladabi ya dan zagaya da kyau ya ce" Madame, lafiya dai ko?"

A zafafe ta juyo ta dauke shi da idannuwanta ta watsar rai bace ta ce" Kai me hadinka da shiga hurumina ne? Ka koma ka zauna har na gama abinda nake son yi dan ka san matar oganka nake na fi karfin cece kuce da kai!"

Kansa ya cire a kanta da yadda take daga murya tana zazaro idannuwanta harda dukan kirjinta, karara masifa ke cinya wanda ya gama gane tana iya kofa masa mari a bishi da sorry dan ba abinda zai iya yi a kan hakan, dan haka sai ya dan hade fuska ya ce" Sorry Madame ki gafara daga nan na mayar da su domin umarnin boss ne yadda na kaisu na maido masa su lafiya"

"Ka mayar masa da su lafiya? Sai ka mayar masa da su lafiyan na gani , nonsence cikin ni da su sai ka duba ka zabi wace ta fi mahimmanci a duniyar Ogan naka!" Ta karashe da karajin da ya dan fara sakawa masu shige da fice dan kallonsu, wasu a motocinsu, wasu a baburansu, wasu a kafa

A hankali ta damki hannun Murjanatu domin jikinta rawa yake yi bilhaki, a daidai lokacin ne shi kuma ya daga kafarsa ya sheka da gudu dan karasawa wajen ogan nasa ya sanar masa domin tana da gaskiya bai san wa zai zaba a ciki ba, kanwar ogan ko matarsa, kowace ya zaba zai iya janyowa kansa matsala, uwa uba babu wace ya isa ya kama da karfi ya sakata yin abinda bata yi niya ba, yana zuwa sun mimike sun zasu nufi ciki domin jirgi ya dauka har pasinger sunna ta fitowa ta wata doguwar hanyar da kake iya tarban wanda ka zo tarba, tunda ya ganshi a kafa ba motar da ya saka shi rakiya da idannuwansa sai ya tsame a cikinsu ya basu damar shiga da nunin yana zuwa kafin ya tarbe shi ya ji abinda yake faruwa
Kwarai ya yi mamakin hakan, dan haka ya nufi wajen hankalinsa kwonce ba da wani gagawa ko gudu ba


Direban kuwa ji yake kamar ya ja motar haka dan ya kula yarinyar ta tsorata, watau Nuriyah, domin du maganar nan da ake yi bata ce komai ba, hasalima ta shige jikin Murjanatu tana ta son boye fuskarta dan bata son duka

Hannunta ta saka ta finciko na Nuriyah ta janyota waje da karfi wanda sanadiyar hakan har takalmanta ta zubar a nan kasa, kaffafuwanta suka taka kwaltar dake malale mai zafin rana duda yama ta yi

Janta ta yi da karfi, Murjanatu ta bale itama da gudu ta nufi inda ta yi da ita daidai lokacin da ta hankadata da karfi rai bace tana sake ruruko idannuwanta ta nunata da hannunta yatsotsinta a hade ta ce" meye hadinki da mijina? Me yake fada maki a cen? Me da me kika cewa mijina na ga yana murmushi har ya biki da kallo"

Gana daya Nuriyah sai ta rasa me zata cewa wannan baiwar Allah, itama idannuwanta a wajen tana kallonta tana kuma kallon Murjanatu da ta karaso da gudu da takalman nuriyar ta shiga tsakani tana fadin" subahanalah, aunty wai meye haka? Me hadinta da yaya kuwa aikenmu ya yi fa, , Ke Nuriyah saka takalmanki mu tafi!"

Murjanatu bata taba sannin wannan lange langen baindiyar nada karfi ba sai yau domin saka hannu ta yi ta warce hannunta ta mayar gefe ta sake durfafar Nuriyah wace ta kwala kara hadi da fancakalar da goron ta saki lafayar tana baya baya da saurin gaske tana girgiza kanta tana fadin" Aa aa aunty walahi ni babu hadina da shi , aikenmu ya yi kar ki dokan takalmi mai tsini a kaina......"

Hannunta ya saka nasa ya rike gannin batama san inda take saka kafafuwanta ba, sanann ya sauke dubansa a kan Nadia da mamakinta, ashe Nadia bata da hankali? Yake ayanawa a cen kasan zuciyarsa, a gaban mutane take shirin aikata me? Me kennan?

Hannun Nuriyah ya ja ya nufi wajen motar da ita, hakan ya sake harzula zuciyar Nadia tana kallonsa ta fashe da kuka ta kirayi sunnansa,

Dakatawa ya yi ya juyo yana kallonta

Da sauri ta karaso tana kallonsa ido cikin ido hawayenta na zuba a fuskarta ta ce" Me kennan? Me kake yi haka?"

Sake kallonta yake yi kafin ya mata alamu na tambayar a ina?

Da hannunta ta nuna masa hannunsa dake rike da na Nuriyah sannan ta ce" yaya zaka rike hannunta a gaban mutane kamar wata budurwarka wace kake so a cikin zuciyarka ne? Yaya zaka ringa yi mata magana a hankali kana nuna carrng a kanta ne? Me yasa kake yi mata magana a hankali kana mata murmushi ne? "

Dukkan abubuwan da ta fada sai yanzu ya yi tsai yana ta auna a yaushe ya aikata haka? Sai kuma daya bayan daya yake gannin amshoshin a idannuwansa da lokutan da ya aikata haka din

A hankali ya sake janye Nuriyah gannin Nadia na son sake wartota , samun kansa ya yi da maidata bayansa ya zamto yana gaban Nadiar a tsaye yana fuskantarta

Nadia ta dago idannuwanta da suka yi mata jajajir ta ce" Khalb, ka miko min ita na matse mata wuya ta yadda zata fita a harkarka, ka mikon ita na mata maganar kar na kuma gannin tana tafia a gabanka tana juya maka duwawu"

Kunya da tsoro ne suka kama Nuriyah, da sauri ta rintse idannuwanta tana rukunkume jikinta hadi da janyo lafayarta
Muryarsa a saukake yana kallon Nadia ya ce" Me ya sa?"

Nadia ta ce" Me yasa me , me yasa ba zaka miko min ita ba?"

Kan Giwa ya tabe baki wai wani a miko mata ita kamar yarta, ya ce" aa ba na miko maki ita ba, ai ba ke kika haifeta ba, tana tsoronki ne dan kina da sunnana a rabe a jikinki, ina son sanin Me yasa zaki hannata tafia a gabana?"

Daga ita har Nuriyar ido suka dago suka kallonsa da shi

Bakin Nadia har hardewa yake yi tana dubansa taa ce" Tambayana kake yi me yasa zan hanata tafia a gabanka irin haka? Huby kana sane da abinda kake fada min kuwa? Nice fa matarka?"

Lebensa ya cije cike da karra jin rakaicin abinda take fadi, da irin tarzomar da ta tada kamar wata marar ilimi a wajen nan a gaban yarensa, me ta yi kennan? Ta san darajar da ya zuba masu su iyalinsa kuwa? A kan me zata wulakantar da kanta haka kawai dan wani shirme nata? Dan haka ya sake fuskantarta dan ya ga karshen nata haukan yaa ce" Eh bana so ki hanna ta?"

Wani abu mai nauyi ke sake hawa saman kirjinta, da kyar ta iya budar bakinta tana kallonsa ta ce" Me yasa? Kana sha'awarta ne ? Ko sonta kake yi? "

Shima yanzun maganar tata sai ta bashi kunya sosai da nauyi fiye da kima, danma Baby bata kusa sai ya ji da sauki sauki, aman duda haka sai ya samu kansa da aauna maganar a leben bakinsa da cikin zuciyarsa

Alamun da ya ji tana jan lafayarta ga dukkan alamu tana son tafiyarta ne dan irin yadda jikinta yake rawa ta lafayarta da ya take yake ganewa

Sai da ya sake riko fitsarariyar zuciyarsa ya ce" Akoy haramun a ciki, ko auren coci na yi da ke?"

Idannuwan Nadia har shigewa suke yi dan birkicewa tana dubansa ta ce" Haramun ne, haramun dinka ne gaba daya, Mu'Azam ka rasa me zaka ce min dan ka kuntata min sai wannan? Idan laifi na yi maka ai sai ka horani ta wani fannin, ba wannan ba, ka manta da kanka kake cewa mace idan bata kai shekara talatin ba bata isa a dubeta a matsayin wace zata iya kwonciya da namiji ba? Yarinya ce karama? Sannan ka manta a lokacin da na so mu kwonta da kai kafin aurenmu ka nuna min ba kyau a adininka na yi hakuri a daura mana aure aurena kake son yi? Ko kuma ka manta wannan din kaskantaciya ce mai aikinka ce?, Mema ta fini da shi da zata birgeka?"


Yanzun kam kasa rike kukanta ta yi dan abubuwan nan sun girmami tunaninta
Fashewa ta yi da kuka tana jan abinta muryarta na rawa ta ce" Sir dan Girman Allah ka daga min na tafi gida, dan Allah ta yi hakuri, kaima ka yi hakuri, wallahi wallahi ba abinda take tunani bane na fada mata aikenmu ka yi, sir dan Allah ka daga min"

"Ka daga mata lafayar mana mai gida?" Muryar Hajia ta saka shi rintse idannuwansa ya juyo a hankali hakan ya sa ta rike lafayar tata da sauri ta juya da gudu wajen da Murja take tsaye jikin motarsu tana hawayen itama

Hajia ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Sun karaso har sun nufi gida shine na ce su je ni tare da jikikina nake a motarmu, shine na taho mu tafi, sai kun zo"

Daga haka ta juya ta nufi motar ta shiga itama direban ya ja su

Rai bace ya juyo kirjinsa na dokawa ya damki hannunta ya janyota gabansa har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login