Showing 24001 words to 27000 words out of 124070 words

Chapter 9 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

328

son kawa

Kan giwa ya ce" kin daina abota da ni ? Tunda momy ta rasu wanene abokinki ?

Ta kawar da kanta ta ce" ai kulun kana wajen aiki, bakada lokaci, baka kaini shopping, baka rakani saloon, baka kaini shan ice cream, baka zama na baka labari

Ya dan kauda kansa Inda da gefen ido yake dan hangen yarinyar nan tayi kamar ace mata kak ta fita da gudu, ya ce" to ba ga su Djamila ba ?

Ta girgiza kanta ta ce" bana son fita da su

ya ce " why ? Matana ne fa, idan baki fita da su ba, idan baki zauna da su ba, da wa zaki zauna ne ? Baby karki daga min hankali plz

ta shashabe fuska ta ce" momy tana cewa, u are my father, idan basa nan komai nake SO kai zaka yi min, kaine Baban yayana kuma abana, i beg u my dad, my big broth, my Freind ka barni wajenta na zauna da ita, haka kawai da grandma ta ban labarinta naji ina son ta, so plz karka hadani zama da matanka my yaya
ta karashe tana dan matso kwalar karfi da yaji

Kan giwa ya kawar da kansa a hankali ya furta oh shuiiiiit ! Baby>?&? @&,

mikewa yayi daga bakin gadon da ya zauna ya shiga karewa dakin kalo a hankali har ya sauke idannuwansa a fuskar Nuriyah dake kalon kasa tamkar ta nitse, dalilin yannayin shigarta, da kuma mugun tsoronsa, wani sashi na zuciyarta na matukar mamakin yanda aka yi har *Kan Giwa* yake irin wannan maganar mai tsayi cikin lalashi, sai yau ta yarda da maganar Bilkiss cewar irin son da yakewa kanwar nan tasa tamkar ransa

gabanta ne yayi wata mahaukaciyar faduwa daidai lokacin da ya dago habarta idanuwanta suka shiga nasa suka yi tsamo tsamo, ji tayi tamkar ta fada kogi gaba dayanta, nunfashinta ya shiga fita da sauri da sauri, kwayar idanuwanta suka shiga shokii suna sama suna kasa, wasu yan guntayen hawaye suka zubo mata a tare, ta nemi yawun bakinta ta rasa domin sun kafe kaf

Cikin kakausar murya ya rike habarta gam ya kuma dan zaro mata ido ya ce" tabuwar lafiyar kanwata daidai da daukewar nunfashinki na kaiwa karen daji ya cinye namanki na kawo kasusuwanki na daka su da hannuna, na nunka albashinki linki uku dan ki kular min da kanwata, wato na cireki a aikin hajiya daga yau zaki kula da baby, idan kika kuskure nayi miki alkawarin karar da danginki gaba daya kafin na zagayo kanki, sai na tabatar baki bar tarihi ba a gidan duniya

Yana gama fadar haka ya cikata ya mike Inda ya bi dan ruwan dake gangarowa daga kasan wandonta, ya danyi kwafa ya fice a dakin Inda ta juyo ta tsurawa Murja ido wace take murmushi tana kokarin komawa tayi konciyarta

Wani irin kuka nuriyah ta fashe da shi Inda ta dora hannu a kai tana dan jujuyawa

Murja ta diro ta nufota tana ta tambayarta lafiya, mai ke damunta, sannan idannuwanta suka hasko mata fitsarin da ya gudu a saman tyls din dakin, murja ta zaro ido ta ce" lah, fitsari kika yi ?


Nuriyah ta bi fitsarin da kalo ta juyo ta ce" ::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(23)*



*Yar Gatan yayanta* ND *Yar Baba* ina mugun yinku, irin Lodi lodi din nan



Yana fita daga falon ya dan daga kafa ya isa bangarensa

Yana shiga ya nufi dakin da yake tarewarsa da Isabel,

Hangota yayi kamar yanda yayi tunani tayi daydaya saman bed din nan ta saka ?couteurs sai bin wakar rihana take tana irin rawarta

A hankali ya kashe fitilar dakin sannan ya karasa gareta har jikinsa na kyarma


Murja karama ta kusan minti talatin zaune dan guard din kofar dakin sun tabatar mata cewar yana ciki, hakan ya sa ta zauna ta tana jiransa ya fito ta lalaba shi dan ya barsu su tafi gidan su kawarta


Karar bude dakin hutunsa taji, hakan ya sa ta dan dago da kanta, sai dai gannin da tayi sai da tayi dan daman da bata zo ba

Saurin sada kanta tayi kasa daidai lokacin da suka yi ido hudu da big broth dinta sun fito da yarinyar da shi da bakinsa ya ce mata kawarsa ce, ta dan sha karamin wandonta da yar rigarta

Gannin Murja bai Hanna Isabel ci gaba da dan narkewa *Kan giwa* ba , inda shi kuwa wata irin kunyar kanwar tasa da dana sani suka lulube shi,

Bai taba yin tirr da wannan rayuwar ba sa? a yau, kanwarsa ta kama shi a haka duda yana iya yi mata na yan duniya dan kuwa bata kamashi turmi da tabarya ba , aman wannan bama zai yiwu ba yayi mata karya ta biyu

A hankali ya cewa Isabel" ki gane, masu tsafta ke shigar jet dina, su Abana da Su hajiya, dan haka ki je kawai ki ciri ticket mayi waya

Isabel ta dan lumshe idannuwanta ta ce" ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?please h?ros, karka yi min irin yanda ka saba, i beg u, idan nayi kiranka ka daga


Dan daga mata kai kawai yayi yana kokarin karasawa kusan Murja ,

A hankali ya zauna yana dan tsayar da idannuwansa kyam a fuskarta

Idannuwanta ta dago wa'inda hawaye suka gama wankewa , ta saka su kyam a cikin na yayanta Wanda tafi so du duniya,

Wani irin karfi ne ya zo mata inda ta kale shi ido cikin ido ta ce" *Yau da nice a cikin irin rayuwar Isabel shin ya zaka yi yaya!? Ina nufin idan nice nake bin maza?*
......... Bata kai karshen ayarta ba ya dauketa da mari,
Gigitancen marin da ya dauke jin ta na wucin gadi, Wanda nan da nan ya fito reras a fuskarta ya kwonta, Wanda ya kwonce mata nadin fuskarta

Cikin bacin rai ya nunata da yatsa ya ce" Ashe bakida hankali? sa'anki ne ni da zaki kali cikin kwayar idonna ki kawo min maganar banza? , shin kin ji mai bakinki yake furtawa Baby? Du dan iskan da ya taba yatsar hannunki walahi walahi sai na harbe shi, shin soyayar da nake Nuna maki ne yayi yawa har kike kokarin sangarce min ki raina ni? Kin Mance wanene ni

Murja da gaba daya jikinta ke kirma, wani irin tsoronsa da bata taba ji ba a yau ya darsun mata, sannan a yau ta yarda da maganar mutane dake cewa idan ransa ya baci baya ji baya gani, aman ina abinda yayi shi, shi yayi ta, mahaifa guda suka kwonta, ta san du abinda zai yi bazai kasheta ba, sai dai ta daku,

Da kyar ta kara dago da idannuwanta da suka yi mata nauyi ta kuma zuba masa su ta ce" ni ban isa na raina yayana Abana ba, du irin soyayar da ka Nuna min bata kai wajen da zan raina Wanda ya raine ni ba, sai dai kuma ni nan koda yayana zai dauke numfashina da bindiga sai na tsaya tsayin daka nayi magana a irin abinda na san zai cutar da shi, yayana shine exemple din rayuwana, karka manta aya ce *DU ABINDA KAYIWA YAR WANI TO ZA'A YIWA TAKA*

Tabas yaya kaima bawa ne, baka fi kowa ba a wajen Wanda ya karbi maman mu wato mai duka, sannan du dukiyar mu, du isarmu , du kyanmu, du tsaron mu , Aya sai ta kasance a kanmu, duda yanzu baka haihu ba yayana aman kanada ni, Wace ka kilace, kake karewa,


Idannuwa ya zubawa kanwar tasa , Wanda yake cike da matukar mamakinta, sai yau ya gabe tabas ta girma, ashe girman nata har ya kai nan, a hankali ya ce" ke da ita ba daya bane, ita ba musulma bace, ita ta banzatar da kanta, dalilin kudi ba Wanda bazata kula ba


Murja ta ce" idan ita ba musulma bace ai kai musulmi ne sannan a adinin mu anyi hani da ka mayar da matar da ba taka ba ta zamto tamkar taka, sannan yaya Allah bai ce ba Wace ta banzatar da kanta KO Wace take gidan su a kamilance, shi dai yayi hani da hakan ne sannan ya fada za'ai maka, mai zai Hana ka aureta, idan har ita kake ra'ayi?

Zuwa wannan lokacin ya gama ficewa a nutsuwarsa hakan ya sa ya nunawa Murja karama hanyar ciki sannan ya Nuna mata waje ya ce" ya isa haka, kina iya shiga KO ki tafi, kaina bazai ci gaba da dauka ba


A hankali ta dan gyada kanta ta juya ta tafi inda ya koma jagab ya fada saman kujerar yana furta" Yar Allah, ka yafe min, ka shirye ni, ka nisanta ni da *ZINA*


Tana fita da kyar ta karasa dakinsu ita da NuRIYAH, ta fada saman bed din ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,

Tana cikin wannan halin *Nuriyah* ta shigo dauke da tea , idannuwa ta zaro ta ajiye flask din ta nufi bed din da gudu tana fadi " Ya Allah, mai yake faruwa haka? Bai yarda ba KO? To idan bai yarda ba kuma sai ayi irin kukan nan hajiya? Dan Allah kiyi hakuri

Murja ta dora kanta a cinyar Nuriyah, tana ajiyar zuciya

Idannuwan Nuriyah suka sauka a fuskar Murja, ta zaro ido jikinta na kyarma ta fashe da kukan itama, sannan ta ce" innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, ke kanwarsa Wace ake ikirarin irin son da yake miki yayi miki haka , ina da ni banza, na san du ranar da na kauce kawai kasheni zai yi

Du irin halin da murja ke ciki sai da taji kamar tayi dariya gannin irin yanda Nuriyah ta tsure kamar ita aka daka, ta lumshe idannuwanta tana sakin ajiyar zuciya sannan tana sauraron kukan Nuriya har baci yayi awon gaba da ita,

Itama Nuriyar a nan ta bingira tayi bacinta tana ta ajiyar zuciya>?#?>?&? @&



Wasa wasa yau kwana na hudu, *Kan Giwa* bai ga autarsu ba, hakan na matukar damunsa, sai dai ya ganta ta computersa, kwata kwata ta daina neman shi dan ta Ganshi ma,

Sannan marin da yayi mata sai ta cewa su hajiya ai bugewa tayi,aman hajiya hassana ta tsareta sai da ta fada mata dalili dan kuwa bata yarda cewar bugewar ne tayi ba

Sosai taji ba dadi a ranta , sannan ta gargadin yartata da su dukufa da adu'ar Allah ya yaye masa, dan kuwa du yanda kaso da shiryuwa sai ka hada da rokon Allah ya yarje maka,

A yau asabar tun karfe takwas ya farka yana dakon son gannin kanwarsa, idannuwansa ya sauke kan Djamila da ta kwana a bangarensa sai baci take, KO wanka bata yi ba bale sallah, ya dan girgiza kai ya shiga dan bubuga kafarta hade da Kiran sunanta

Wutsil ta bingiro ta Mike tana zare ido, ta ce" lafiya, du a firgice take dan kuwa tashin karfe takwas ba nata bane

Ya dan kawar da Kansa dan da yar salebar baci a gefen bakinta ya ce" ki je ki tsaftace jikinki kiyi sallah>?&? @&


Ta dan juya ta ce" ohk tohm

Tana shiga bayin ya yaye blanket din gadon ya dauko suturarsa shada kalar ash mai duhu , ta sha simple dinki anyi Riga iya gwuiwa da wando,
Haka ya zira ya dauki turare yayiwa kansa wankansa sannan ya juya ya fice

Bai zame ko'ina ba sai kofar dakin Nuriyah, yana isa ya dan dakata yana tunanin yanzu haka suna baci kar aje ya tashe su

Har ya juya kawai ya juyo ya murda abin budewar sai ganninsu yayi sun bayana *Nuriyah* a zaune a kasa, Murja a sama da kumb suna yar kokawa ala tilas sai tayi mata kitso, ita kuwa tana ihun zafi bata so

Shirun da taji Murja tayi ne ya Sakata dago da kanta dan wani fitinanen kanshi ya kaiwa hancinta ziyara, kanshin mutumen da take jimawa a sujada tana rokon Allah ya saba kiwonsu,

Gabanta ne ya mugun fadi inda ta Mike tana kirma ta ce"""""""""
*KAN GIWA**>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(24)*



*d' manal dinah=؋?* ina kaunarki kamar yadda kike kaunata. Ina son ki kamar one alive kamar two alive kamar three alive kamar four alive kamar five alive =?
?=?
?=?
?=?
?=?
? muna tare iya wuya insha allah ke ta daban ce da saura ina mungun yinki Lodi lodi din nan



Mikewa Nuriyah tayi tana kirma ta ce" *KaKAN GIWA* ne

Kan Giwa ya dan kaleta yayi Saurin kawar da kansa domin yar doguwar riga ce Wace da kyar ta dan fice gwuiwar ta, domin suna gama sallah suka yi wanka kuma sai suka shiga kitso, sosai rigar tayi mata kyau sannan har dan dagewa ta kara daga baya dalilin mazaunanta da suke da tudu da fadi

Ganin yanayinta ya sa murja wurga mata baban hijabi dan a zaman da take da Nuriyah da kyar ta saba da ita kanta macen ma bale a gaban namiji

Karba tayi ta saka ta dan zauna tana kikifta ido

Sai a sannan Kan Giwa ya dan sauke ajiyar zuciya, ya nufi kanwarsa gadan gadan Wace ta dan hade rai tana kalon kasa

Yana isa ya dan zauna a gefenta , a hankali ya kamo hannunta yana dan murzawa ya ce" fushi kike yiwa yayanki?

Murja ta dan girgiza kai batai magana b?, sannan ita kanta sai ta ji ta kasa sakewa da shi, du a tsorace take tana gudun ya kara mata wani marin,

Juyo da furkarta yayi, inda a hankali ya dan taba wajen da ya mareta , abinka da farin mutun bai baje ba gaba daya, ya danyi duhu kadan, a hankali ya furta" i'm sorry dear, nayi laifi na daki autata,bazan kuma b?

Murja ta dago idannuwanta da suka cika da hawaye tana bude baki kawai sai ta barke da kuka tun karfinta

Sai da ya barta tayi ta huce har tana sauke ajiyar zuciya inda ya kafe Nuriyah da kalo Wanda shi Kansa bai san yayi hakan ba,

Can ya ce" yanzu dai ai na baki hakuri KO? Mai kike nayi miki da zaki huce?

Murja ta tsagaita kukanta ta ce" ka dena abinda na tarda a gidanka yayana, ka aureta idan bazaka iya rabuwa da ita b?

Bai san lokacin da bakinsa ya ce" bazan iya aurenta b?, dan ina bukatar macen da zata baiwa yayana tarbiya , sannan ina son kasancewa da ita dan ita kawai take iya daukan lalurata, matana basa iya gamsar da ni!

A tare suka dago ido suka zuba masa , Wanda ya ankarar da shi da wa'inda yake maganar, b? shiri ya mike tsaye a hankali ya ce " oh shuiiiit! , baby ki bar maganar nan plz

Murja ta dan murza idannuwanta ta ce " i'm sorry yayana, bazan iya barin maganar nan b? fa, i'm 22 old, shekaruna sun isa suyi magana a kan lamarin yayana,

Ta danyi Jim ta ce" to ka kara aure, ka nemi wata matar ka kara

Kan Giwa ya lumshe idannuwansa ya ce" na kare zuwa wajen mace KO yar gidan waye da zumar na zo neman aurenta, nayi na farko, nayi na biyu, ban karu da hakan b?, zan duba KO a wajen aikin mu ne na samu daidai ni, domin na kare da auren yarinya ta kawo min raini, duba da Nadiya shekara biyu na bata, djamila kuwa har hudu, kinga kawai zan ga sa'ata na aura may be ita zata iya da ni

Murja ta danyi murmushi ta ce" Allah ya dafa mana yayana

Ya dago da kansa ya kali Nuriyah still bata daina kalonsu da mamaki ba ya ce" ke kalon fa? Kin wani tsareni da ido?

Da Sauri ta sada kanta kasa tana kifta ido a ranta tana cewa wani abin sai yayan boko, to in b? boko ta ratsaka ba taya zakayi irin maganar nan da yayanka? Tap

Muryarshi ta katseta lokacin da ya ce" ki tashi mu tafi na kaiki ganin kayan kawar taki

Murja tayi dan tsale ta ce" yeah , Nuriyah tashi maza mu shirya mu tafi

Kan Giwa ya danyi kwafa ya ce" minti ashirin na baki baby , bara na gaishe da tsofafin nan

Yana fita cikin gudu gudu Sauri Sauri suka shiga kintsawa inda Murja ta dage sai da ta shafawa Nuriyah hoda ta saka mata Jan baki kalar lebe mai haske, ta caje mata gira dan ta ki amincewa ta zana mata, kashin idonta ta saka mata maskara dan kuwa abin hodar ya sa yayi farifari,

Sosai tayi kyau na ban mamaki daidai ta saka abayar da Murja ta ciro a yau baka ce har kasa Wace itama tana Sakata kawai sai ta bi lafiyar mazaunanta tayi slim a jikinta

Murja ta kare mata kalo ta ce" Nuriyah, b? daga kayan bane yake saka jikinki yin kyau haka, yannayin halitarki ce, Allah ya tsara maki abinki yayi miki kyautar kayanki, Allah ya baki mijin da zai iya kulawa da ke ya daukaka wannan halita



Nuriyah ta danyi murmushi a ranta ta amsa da amin ya Allah,

Suka fito bayan sun saka takalma ita Murja mai tsayi ita kuwa mai dan tsayi kowace sai baza kanshi take


Suna shiga falon Hajiya Hassana ta dan dakata murzawa Hajiya murja kafafuwanta da take tana dan kalon Nuriyah, Haka kawai yarinyar sai ta ringa irin tafiyar yar uwarta, KO dan itama tanada mazaunai ne kamar na yar uwarta ,

Dan sauke ajiyar zuciya tayi lokacin da suke gaishe da jama'ar falon

Hajiya hassana ta dan nisa ta ce" Babyna ga abincinku fa, ku tafi ku ci

Murja ta ce" momyna, bana jin yunwa ni dai, shin ina big broth ne? Yace shi zai kaimu gidan su freind muyi mata barka


Hajiya murja ta ce" lale yar g?ta, da nice na isa ma, kuma ya yarda harda y'ata?

Murja ta ce" sosai, suka nufi kofa dan tarda shi


Suna isa suka tarar da mazan ma'aikatan du sun tsatsaya kowane a nitse harda Mubarack,
Shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login