Showing 15001 words to 18000 words out of 124070 words

Chapter 6 - NEMAN NA KAINA HAUSA NOVEL

23 Dec 2025

355

tayi murmushi tace " Dan nema, y'ata dai sai dai hangen nesa
Du Wanda ya nemi ya shiga lamarinta zan hada shi da kan giwa,

Rislan ya ce" kai wannan tsohuwar to shi Yaya kan giwan ma ai ya nemi Aure kuma ya samu Yana zaune da su dan haka kinga ba zai hanani raya sunna ba

Hajiya tayi kwafa ta kawar da kanta tana Jin haushin bodyguard din da suka shiga dayar motar dan su rakata, domin ? yau Elhaj Yana busy tare da kangiwa da kuma mahaifinsa Karibullah



su Wanene family *KAN GIWA*?



*KAN GIWA* kiranyan da yan ta'ada suka yiwa Ibrahim Karibullah Ibrahim,

Ibrahim karibullah Ibrahim ya kasance D'? na uku sannan Wanda ya rayu kafin kannansa uku da suka biyo baya Yaya ? wajen Karibullah da Sedina

Karibullah ya kasance hamshakin mai kudi, wato ya riki matsayin ministan kudi a Japon inda ya hadu da matarsa yar gidan Elhaj sulaimankhan menistan ?ducation na kasar indiya,
Sedina ta kasance ba'indiya shi kuwa Karibullah bafulatanin usul,
sosai Karibullah ya sha fama kafin mahaifin Sedina da mahaifiyarta su yarda su hada su aure bayan rigingimu da tashin hankali aka yanka masa sadaki ya biya ba tare da dar ba domin kuwa shi SO yake domin Allah,
bayan auren Sedina da Karibullah, ta samu ciki har sau uku Yana zubewa, ? na hudun ne Allah ya bata d'? namiji Wanda aka saka masa sannan *Ibrahim* wato ya ci sannan mahaifin Karibullah,
Sedina ita kadai mahaifinta suka malaka, ta je wanka gida wani dare tana shayar da yaronta sai mahaifinta ya shiga bayi dan yayi wanka, abinka da ajali bayan ya cika bahon wankan da ruwa irin Wanda yake aiki da wutar lantarkin nan ashe ya manta bai rufe wajen jona ruwan ya zama na zafi ba, Yana saka kafarsa ta kama shi,
Cikin firgici ya saki inalilahi wa'ina ilaihi raj'une, hakan da mahaifiyar Sedina ta ji ya saka ta fada bayin da gudu dan ganin abinda ke damun mijinta, tana shiga itama ta kama shi da niyar ta warto shi sai gawarsu aka tarar

sosai Sedina ta shiga tashin hankali, inda Hajiya Murjanatu da Elhaj Ibrahim Da Elhaj karibullah suka tare gaba daya ? gidan su Sedina dan tayata jimamin rashin iyayenta da tayi

Wata rana suna zaune, jujun mahaifinta ya Zo da takardun du abinda ya malaka wa'inda du sunnayenta ne ? jiki, da kuma irin dukiyar da ya tara ? cikin acount dinsa na banki ya kawo shaidar komai ya baiwa Sedina, Inda baiwar Allah ta tatara komai ta mikawa mijinta tana share hawaye ta ce" Banida kowa sai kai, ka haneni aikin gwomnati domin ka tsaya ? lamarina, ba abinda na nema na rasa ? nan gidan duniya, wannan arziki bansan ya zanyi da shi ba, kamar yanda na baka ragamar rayuwana haka na damka maka na dukiyar mu, ? mayar da komai da sunnan mai sunan Aba kafin ya girma, koda na kuma haihuwar wasun na san zaka kula dan ganin kansu ya hadu

sosai Hajiya Murjanatu take zubar da hawaye tana kara rarashin Sedina

tundaga wannan rana hajiya murjanatu take kula da lamarin Sedina koda ciwon kai take tana tsaye sai taga ta warke hankalinta yake kwonci

Bayan shekaru goma sha bakwai da haihuwar Ibrahim Kan giwa Sedina ta kuma haihuwar Yaya uku, Inda ta samu Sulaimankhan, ta samu Rislan, sai yar auta wace aka saka Mata Murjannatu sannan mahaifiyar Karibullah,
? daidai wannan lokacin arzikin karibullah ya kara habaka duba da irin yanda kasuwancin yafi karbarsa sai kawai ya ajiye aikin gomnatin ya tatara iyalansa suka juyo gida Nigeria inda aka baro Ibrahim kan giwa ? makarantar sojoji wace tun yanada shekara bakwai yake can

Sedina na rainon yayanta cikin ingantaciyar tarbiya, domin du irin arzikin su Bata taba yarda da sangarta su ba duda tana iya yinta dan ganin tarbiyar UmI ( Murjannutu) Bata lalace ba, dan kuwa nuna mata Soyaya Suke Fiye da tunaninta,

Shekarar Ibrahim Ashirin Da biyar A makarantar sojoji ta kasar Japon, inda aka yaye su cikin ikon Allah Karibullah ya samu hanya aka kawo Ibrahim Nigeria dan ya kama aiki

Zuwan Ibrahim baifi wata ba miyagun mutane suka yi masa sunan kan GIWA, dalilin irin yanda suke shan fama da shi, ? zuwansa ya rufe manya mayan masu fada ? ji da suke taka doka ? Nigeria sannan Banban palas kan giwa suka ginata ? kano inda babu ne kawai babu,

Matan Ibrahim kan giwa biyu, da Ba'indiya mai suna *NAdiya* sai yar Ibo mai suna *Djamila*

Ibrahim ya kasance irin mazan da ake Kira kerare, wato Ibrahim ? tsaye yake sandan, dogo ne har can kakarfa, aikin soja ya saka farinsa ya dan disashe aman du da haka farine mai dan duhu, jikin Ibrahim tun daga kan kirjinsa har kwabrin kafarsa wani irin sanka sanka irin na maza masu Cin karfen nan aman shi hakan bai sa ya gajarce ba sai ma kara tsayuwa da yayi
Idannuwan Ibrahim basuda irin girman nan, tsaka Tsaki Ne KO don lumshe su da yake ne sai ka rantse cikinsu babu fari wato si kwayar idannuwan nan tamkar jajaye ne aka yi masa sai bakin dake tsakiya
Kamanun Ibrahim sun sha banban da na yan uwansa dan kuwa su yan hutu ne shi kuwa Dan filin daga ne
Sosai mata suke ra'ayin kasancewa da Ibrahim koda ? dare daya ne, inda Ibrahim du yanda yakeda mata biyu aman yanada bin mata dan Allah yayi masa halitar sha'awa ? tare da shi sannan matansa kowace bata iya masa dan su hutu kawai suka iya, shi suka sani hakan ya sa yakeda budurwa banasaria wace kowa ya san shi da ita aman ya kasa aurenta kasancewarta ba musulma ba kuma batada ra'ayin musulunci

Ibrahim *Kan giwa* baya Daukan raini hakan kuwa KO kai wanene, mace daya ke tsaya ta Luka masa zaki yayi dan murmushi ya kada kai sai Hajiya Murja wace yake sonta tamkar ransa,

Bayan shekara guda da yan watanni Allah ya karbi ran Sedina inda wannan family ta shiga rudani da tashin hankali tunba Mujannatu da Karibullah ba dan kuwa sun jima kafin ? samo kansu

Bayan rasuwarta sai hajiya murjanatu ta zagine dan ganin rayuwar yan jikokinta ta inganta cikin ikon Allah bayan rasuwar da shekara biyar karibullah yayi Aure inda ya auri wata Yar gidan amininsa mai sunna Hasana Inda jininsu ya hadu da Murjannatu take kula da yayansa cikin kauna da zuciya daya

Haka rayuwana gidan *Kan Giwa* ta kasance Yana cikin gidan aman sai ayi wata ba'a ganshi ba dan kofar boye gareshi ta cam?ra yake kalon kowa sai yar kakarsa da idan ya sha kwana zai tarda ita KO ita idan tayi missing dinsa zata wanke kafa ta tarda shi gefensa tayi ta mita...


Ci gaban labari
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(14)*




A hankali ta kai zaune saman kujerar coiffeuse din dakin da take kwana, tana zama ta dauko tisubala ta konce daurin dan kwalin dake kanta, da kyar take tsifar kan nata domin kitson har ya bace sosai ? cikin juna,

? hankali take dan shafa jelar kitson tana tuno ranar da innarta tayi mata shi Inda take cewa Inna ki daina kitsewa har tsinnin kinga fa kafin na kunce shi na kan sha fama,
Sai innarta tayi murmushi tace " Nuriyah kitson naki duka hudu ne, ni ga tsufa bana iya yi miki fiye da hakan ke kuwa kin nace da bazaki je wajen lami tayi maki ba, shi kuwa gashin nan naki masha Allah idan ban kitse har tsinin ba bakya gannin santsinsa bazai jima ba zai warware da kansa

Murmushi ne ya subuce mata ? hankali ta furta "Innata

Firgigit ta zabura cike da tsoro tana kalon wayar dake mane da bango sai ruri take tana neman agaji har wata yar jar wuta na dan haskawa tana daukewa,

Tsayuwa tayi jikinta na kyarma ta kasa daga wayar dan ita bata ma san da ita ? dakin ba, tun tana yi har tayi shiru da alamar ta tsinke

Ajiyar zuciya take kokarin saki Inda ta kuma daukan wata tsuwar, ai Bata san sanda ta mika hannu ta daga jikinta na Bari tayi tsai tana sauraron lokacin da aka ce"Nuriyah ki Zo na dawo

tamkar an farkar da ita daga baci ta ce" Toh Hajiya,

sai taji dif alamun an kashe, tayi tsai tana mamakin kenan da gaske ne, wata rana sabiu ya taba nuna mata wata wakar indiya da taga ? ciki akoy irin wannan wayar ashe da gaske kana iya jiyo muryar mutun, ta sauke ajiyar zuciya tana mamakin Hajiya, nan da nan sai anyi Kiran mutun ? waya ? Wata zuciyar ta ce mata kin manta ba unguwar yawa gidan laka kike ba, su ? nan wannan ai ba wani abin bane, ta kuma sauke ajiyar zuciya tana kalon madubin dakin ? fili ta furta " ? gaskiya bazan jima ina irin wannan shigar ba, dan kuwa ni musulma ce, sannan ban Zo nan dan na cutar da su ba

tana wannan maganar tana dan tafiya ne cikin nutsuwa Inda ta cunkushe gashin nata dake dan bugawar warin ruwa

Tana karasowa ta duka kasa tana gaishe su

Hajiya ta amsa da fara'arta sannan cikin yaren turanci ta ce" Emy, ki kaita a gyara mata kanta, da kuma faratunan ta, ina SO ta ringa yin irin aikin gida, koda baki akayi ta basu ruwa da komai

wace akayi Kira da Emy da alamar Christa ce ta amsa da" to, sannan tayi gaba Nuriyah na biye da ita ? baya

Suna juya baya Rislan ya bita da ido yanai mata kalon kurullah, ? hankali ya juyo ya ce" gaskiya ? bar tunanin saka min mata aiki, raina Yana iya baci

Hajiya Murjannatu ta kama baki tayi salati ta ce" gidanku, nace gidanku Rislanu, toh dan ubanka baka Isa ba, bazan baka ita din ba, dan haka ka fitar min ? ido na rufe dan nema

rislan ya ce" idan ita ta zabeni ai sai ki hanna, dan kinga ina wanni lalabaki, to sa? ta soni

Hajiya Murjannatu ta rike baki ta ce" to da Ubanka kake, KO dan Ubanka ka saki ka rabin min yarinya na hadaka da mai tataka ka ? gidan nan ai kafi kowa sannin halayensa

Rislan ya rage murya kasa kasa ya ce" ni fa ba lalata na nema ba, maganar Aure nake, kuma shima yayan ai yanzu ya san na girma bazai min irin na da ba, waima ke da kike kalonsa da budurwa wace ba musulma ba, ba kuma ra'ayin Aure yake ransu ba aman sai ki dage ? kan dan alhaki, to Nuriyah sai ta SO ni

Yana gama fadar haka ya mike yayi gaba abinsa Inda ya bar yar kakarsa cikin tashin hankali, *Kan giwa* mutun ne har mutun sai dai ta rasa ya zata yi ta raba shi da wannan yarinyar, ta rasa wata masifa yake tsinta ? wajenta bayan ga mata zuka zuka ? tare da shi, ta rasa gane kansa, wannan abin na daga mata hankali, shin mai zasu cewa ubangiji na sake da amanar da suka yi, suna yi iya yinsu aman abin yaci tura, ban ban abin haushin ma matansa Sam basu damu ba, KO mai hakan ke nufi ?

A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ta lalubo wayarta ta dannawa *Kan Giwa* kira

Sai da tayi Kira ya kai sau biyar sannan ya daga muryarsa tamkar ya tashi daga baci ya ce" Ya akayi ?

Hajiya ta share hawayenta muryarta na rawa yanda da ka ji zaka fahimci ? cikin tashin hankali take ta ce" Ibrahim

Da sauri *Kan giwa*, ya ture hannun Isabel ya mike tsaye ya ce" mai ke faruwa Hajiya ?

Yana maganar ne Yana kokarin kuna computersa ya dano bangaren Hajiya Murjannatu Inda ya hangota zaune tana dan share hawaye cikin sauri ya ce" kukan mai kike ? Wa ya mutu ? Mai kike SO ? Wa ya taba ki ? >??>??


Hajiya murja ta ce" Ba komai, ina son karshen satin nan kaci abincin dare ? gefena da kai da iyalinka

Jikin Ibrahim ya mutu murus ya ce" bakya Jin dadin jikinki ne ? Mai yake damunki ? Wani abin kike SO ?

Hajiya zuwa wannan lokacin ranta ya kara jagulewa ta Mike ta nufi daidai camerar dake haska masa su dan ta san tabas Yana kalonta ta dago kanta ta watsa harara sannan ta ce" Laifi ne dan na bukaci ranar asabar ku halarci gidana da kai da iyalinka baki daya ? Na'am ? Tana gama fadin haka dif ta kashe ta fada falonta ta nufi dakinta dan ta samu nutsuwar zuciyarta

Ajiyar zuciya ya sauke Inda ya lumshe idannuwansa Yana Jin yanda Isabel ke shafar kirjinsa, du masifarsa kawai sai ya kasa biye mata harma ya dakatar da ita ya fada bayinsa yana tunanin abinda ya dagula lisafin hajiyarsa

Nan da nan Ya kara shiga wanni yanayin damuwa du ya juye Yana ta tunanin wannan lamari


Bayan kwana biyu Da sasafe ta gama shiryawarta tana gama saka rigarta Kiran Hajiya ya shigo ? wayar dakin Inda take ce mata ta duba cikin sif din nan gefen dama akoy irin dogayen riguna ta saka guda dan yau juma'ace su je tare harda elhaj


Murmushi tayi lokacin da take karbar wannan sako ta ce" to

Harda dan tsalenta da ta buda gefen kayan hausa ba na aiki ba, Inda ta shiga ruwa ido tana ta jera adu'o'i tana mamakin kayan nan, ? hankali ta dauko wata doguwar bakar Riga , tana zazage Linkin da ta sha dogon farin wando da yar Riga kamar shimi suka fado daga ciki, ? hankali ta furta masha Allah lokacin da tayi arba da duwatsun gaban rigar, ta kara zazaga hannayen dogaye ne sun matse daga karshen tsintsiyar hannun,

Adu'ar saka sabin kaya tayi Inda ta warware wandan ta saka shi, Allah ya taimaketa mai jayuwa ne dan haka bai Bata wahala wajen saman ba, ta dora abayarta ? sama ta kara gyara zaman chouchounta dan tana gudun cirewa ta kasa daure kan, ? hankali take yana dan kwalin nan tayi masa tamkar na larabawan nan ta juya tana kalon madubi ? hankali ta mika hannunta tana taba fuskarta ta ce" komai na son gyara



Komai Bata shafawa fuskarta ba, kafarta kadai ta dan shafawa mai sama sama ta saka takalminta plat ta fito cikin nutsuwa

Cikin sauri sauri Ta sauko ta nufi motocin dan kuwa har sun fifito ana saka kayan dake dauke da wainar sadaka,

Har kasa ta zube tana gaishe su, ? tare suka amsa Elhaj Ibrahim ya ce" ina direban ?

Muryar Rislan ta katse su lokacin da ya fito ya sha shadarsa marun Yana dan jefa ky din Yana cafewa yace" ni zan tuka mu, su kuwa bodyguard din sai suyi mota biyu daya gaba daya baya

Hajiya murjannatu ta ce" dayar ma da Yaya nake hakurinta bale har biyu, ni ba matar shugaban kasa ba, ni ba kakar shugaban kasa ba, aman ace ? falona kawai na Isa na rawata ba kato ? bayana, kuma kai kana kalo Elhaj bazaka hanna ba

Elhaj Ibrahim ya DAnYi kasakai ya ce" idan mun Dawo zanyi magana

Ta turo Bakinta ta ce" nifa yanzu na tsufa a daina yi min wayo,

Elhaj Ibrahim yayi murmushi Yana kalon lokacin da aka bude mata ta shiga tana mitarta,

Shima bayan ya shiga Inda Nuriyah da Rislan suke gaba ya tada ya kama hanya

A hankali rislan ya dan kali gefen Nuriyah ya ce" Nuriyah !!!!

A tare suka kalo wajensa suka tsura masa ido dan Jin mai zai ce


Nima idon na zuba masa dan jiyo muku da wace kuma ya zo=?3?>??>??>??>??>??>??>??
*>?&? @&>?&? @&>?&? @& NEMAN NA KAINA>?&? @&>?&? @&>?&? @&*


Marubuciya: *SAJIDA*


*P+


*(15)*

Rislan ya ce" zaki zama Kawata ?

Nuriyah ta zaro ido tana kalonsa

Yayi murmushi ya kara cewa" kinsan kinada kyau ?

Daidai wannan lokacin tsoronta ya ninku, ta sada kanta kasa tana wasa da yan yatsunta ? ranta tana fadin wannan wani irin mutun ne

Elhaj Ibrahim yayi murmushi ya kawar da kansa gefe Yana kalon bakin titi, Inda Hajiya Murjannatu taki kawar da kanta ta tsura ido tana karantar halayen Nuriyah

Rislan ya ce" Nuriyah

Ta kuma dukar da kanta kasa tana tunanin shi wannan wani irin mutun ne, abota da mace, macen ma kaskantaciya kamar ita

Maganar Hajiya Murjannatu ce ta katse ma Rislan tasa Inda ta dan kebe bakinta gefe ta ce" insha Allah gobe ne zamu ci diner da iyalan Kan Giwa da shi

Elhaj Ibrahim ya dan juyo ya kaleta Yana dan kara gyara zaman gilas din fuskarsa mai kara masa karfin gani ya ce" masha Allah, ya samu lokaci KO ?

Ta kawar da kanta gefe ta ce" Aban karibullah, mai yasa baka son takurawa yaron nan ne ? Kaga fa irin halin da ya saka kansa ? ciki, yanzu fisabillilahi idan ya mutu ? wannan rayuwar wani irin makoma zai tarar ? Aban karibullah, ka hanene ni magana, aman kayi hakuri ni na gayato shi da iyalansa

Elhaj Ibrahim yayi shiru Yana nazarin matarsa, ita dai ta manyata duda shekara goma sha biyu ya bata aman yaci ace ? shekarunta ta daina yawan saka damuwa ? ranta, har zaiyi magana sai ya ja bakinsa yayi shiru ? hankali jikin tsufa ya kama ya fito Inda bodyguard dinsa ya mika masa sandarsa fara ya shiga dan dogarawa Yana tafiya Yana sadaka, hakama matarsa da su Rislan da Nuriyah


Sosai Rislan ke yiwa rayuwar Nuriyah katsalandan har suka gama suka juya gida, Inda daidai wannan lokacin ta fara yiwa abin dariyarsa murmushi aman bata furta komai
dan ita ganni take wannan mutumin bai santa ba da bai nemi irin hakan ba, da bai kirata da sunan aminiya kawa wai da wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login