Showing 9001 words to 12000 words out of 132946 words

Chapter 4 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1155

Kilishi ta narka ma?udan kuWaWe na gaske wajen siyan tsadaddun kayan gyaran jikin da zasu karbi fatar Amina, ta yadda a waje kowa zai sanya ta cikin layin nutsuwa da kwanciyar hankali da kallo daya, yadda komai zurfin da zuciyarta zata yi babu mai iya gano hakan don za'a shagala da kallon canjawar fatarta maimakon damuwarta, gashi kuwa hakan ya fara aiki har akan mahaifinta da ya kawo ta duniyar nan, wai sau nawa ne zata fada? Kilishi mugun ice ce da gaske!

Sai kawai tayi wani murmushi a hankali sannan ta gyada kanta tace.

"Haka ne."

Shima ya gyada nasa kan.

"Sai dai mu bisu da addu'ar dorewar zaman lafiya.

"Tabbas kuwa."

Amman ta sake fada tana jin wani abu kamar raha na ratsa zuciyarta, tana ?ara yarda cewa mata duniya ne, Allah ya basu damar juya namiji duk girma da tsufansa a tafin hannunsu, kawai da yawa ne basa amfanin da danarsu.

"Mun yi waya da Kawu Mallam yanzu, yace za'a rako su Maryam din anjima, tunda kike ta kallo na a hanya na san abinda kike so kice in tambayo miki kenan."

Ta girgiza kanta.

"Ni ban aike ka ba, idan zasu kara kwana ma ba zan damu ba."

Kice zaki iya bacci babu Hafsatu a gidan nan?" Ya tambaya

"Kafin in same ta fa?"

"Kina da Amina."

Sai kawai ta mike tana dariya, ta Wauki tsintsiyarta ta fita. Alhaji Sulaiman ya bita da kallo yana jin zuciyarta wani iri, kamar bai gama yarda da kalamanta ba, amma kuma babu yadda zaiyi, matarsa daban ce a cikin mata ya sani, halayenta wani abu ne da ba zai taba iya kwatanta su ba, juma abinda bai sani ba shi e matarsa iri daya ce da kowacce mace, natan ne kawai basa gane cewar nutsuwar zuciyarsu a kowanne fanni na rayuwarsu taba zaune cikin ?wa?walwar su.

Awanni biyu bayan hakan ya baro cikin gidan, Ya fito ya nufi titi don tafiya ga sana'arsa.

Daidai lokacin da Awwalu dake zaune cikin motarsa a can gefen layin ya tada motar shima yabi bayansa.


****

*A wannan safiyar.*

Ma'aruf ya tako cikin gidan a hankali, hannunsa daya na sanye cikin wandon shaddar dake jikinsa kalar ruwan toka yayin da Wayan ke rike da wayar dake kare a kunnensa, kayan jikinsa kalar ruwan ?asa ne wanda ta haska cikin safiyar, ?afafunsa na tahowa cikin falon a hankali yayin da yake saurarar bayanin da Faruk ke yi masa a cikin wayar.

"Mutumin nan sh*ge ne B, ?arfe biyun dare ya kira ni wai shi daga sannan yake amsa waya, wallahi har na zata yan fashi ne suka shigo mana."

Yayi murmushi kaWan.

"Baka da hankali Faruk dan fashin ne zai fara kiranka a waya ya gaya maka cewa gashi nan zai shigo tukunna? ka gaya min yaya kuka yi dashi kawai?"

"Yes, ya karba. But sai mun bashi wani abu tukunna, kuma ka san shi cash yake baukata, kuma gayen yana da matsala wallahi don yace dole yau yake bukatar kuWin, shi yasa tun farko ni raina bai kwanta da mu saka shi cikin al'amarin nan ba."

Ma'aruf ya girgiza kansa.

"Kar ka damu, zanje na ciro kuWi anjima sai ya gaya mana inda zamu same shi."

"Shikenan, I will talk to him zuwa yamman, zan gaya maka."

Da haka wayar tasu ta kare, daidai lokacin da Ma'aruf ya shiga hanyar koridon zuwa kitchen, inda ?arar motsin kwanuka ke tabbatar masa da cewar tana ciki.

Da gaske yake abinda ya faWa mata jiya cewa tana ?ara ?awata duniyarsa, don duk da har yanzu bata gama sakin jikinta dashi ba, ya sani cewa shigowarta cikin rayuwarsa ya fara samun wata nutsuwa da shi kansa baya gane mata, abinda kawai ya sani shine abinda yaji tun daga ranar da ya fara ganinta shi yake jan ragamar sa akanta.

Tsakanin jiya da yau kaWai yana jin sunyi sabon dashi da Ru?ayya basu sami hakan a Wan kankanin lokaci ba, ya nuna mata cewar da gaske yake wajen gyara alakarta dashi, kuma hakan bai bashi wuya ba don da gaske ne yarinyar bata da matsala, tana da hankalin da bai san da me zai kwatanta shi ba, tana da hankalin da ya fahimta sosai a cikin dukkan amsoshin da ta bashi don sunyi hira sosai a jiya, yayi mata tarin tambayoyin daya fahimci kusan rayuwarta gabadaya a dun?ule.

A lokacin ne kuma ta juyo ta kalle shi, hannunta daya rike da plate din da take wankewa a cikin sink, lbakinta yayi masa murmushin nan nata dake tafiya har cikin zuciyarsa. Wani abu daya lissafa shi cikin nasarorinsa na kwanakin nan kenan, yana gaya masa cewa da gaske yayi kokarin da ya fara rusa wasu abubuwan dake tsakaninsu, shi yasa a jiya ya daure yayi mata tambayar da yake fatan amsar da zai samu amsa daga gare ta, amsar da yake fatan ta zama abu na karshe da zai cire duk wani hijabi a tsakaninsu.

"Sannu da zuwa" Muryarta ta fito a hankali.

Bayan asuba ya sake fita wajen ?arfe bakwai na safe, ya tafi can yamadawa inda ya halarci janaizar wani abokin Baffa da ya rasu a daren jiya, da Baffan suka yi waya a jiyan ya gaya masa cewa yaje ya wakilce su shi da Baba Usman tunda basa gari, sai gobe ne suke shirin dawowa daga Kadunan.

Don haka can ya tafi kuma har bayan an kai mutumin sai da ya sake komawa gidan don bai shiga ciki yayi musu gaisuwa ba, ya san matarsa guda Waya, don a shekarun baya kafin ya auri Rukayya daga ita har mijin nata sunyi kokarin hada shi da wata ?ar su Nafisa, kuma shima saboda hankalinta ya so yarinyar a lokacin amma sai naci da kuma dagiyar Rukayya ya tsallake nasu.

Yanzu ma da yaje yaga yarinyar, tana zaune a gefen mahaifiyar tata ri?e da wani yaro mai kama da ita sak wanda hakan ya shaida masa cewar tayi aurenta itama, kuma sunji mutukar dadi na ganin nasa, don bai san me yasa ba kai tsaye yake iya fahimtar farin ciki da kuma yabawa a fuskar mutane, kamar yadda a jiya ya fahimci daWin da Amina taji a lokacin da yake godiya da kuma yabawa girkin da tayi masa.

Ya karaso cikia hankali sanda da ta kashen famfon tana rike da kofi na karshe a hannu ta.

Ya tsaya a gabanta.

"Anyi jana'izar?" Ta tambaya bayan ta kalle shi ta sunkuyar da kanta. Ya daga nasa kan kafin ya amsa.

"Anyi tun Wazu, makabartar babu nisa da gidansa." "

Yaga kamar ta hadiye wani abu a makogwaronta kafin tace.

"Allah ya jikansa."

"Ameen."

Ya amsa yana cigaba da kallonta, kuma abinda yake gani a fuskar tata bai tafi ba, don da alama mutuwar ta Wan taSa ta duk da bata san mutumin ba, yaga hakan a fuskarta tun daga lokacin da ya gaya mata inda zai je da safe bayan ya shiga dakinta ya same ta zaune akan dardumar ta har a lokacin.

Kayan dake jikinta a yanzu wata doguwar riga ge ta atamfa Green, kuma akwai wani abu a cikin kalar rigar da yayi mata kyau yake kunna wani abu kamar wuta daga ?asan zuciyarsa tun sanda ta shigo kitchen din.

"Har kinyi breaskfast?" Muryarsa ta tambaya da wani irin amonta mai sanyi yana katse shirun dake son faruwa.

Ta girgiza kanta a hankali sanin cewa kofin hannunta yake kallo.

"A'a, nayi amfani dashi ne."

Ya zaro wayarsa daga aljihu ya kalli lokaci.

?arfe goma har da kwata.

"Dama ba kya cin abinci da wuri?"

Ta sake girgiza kanta.

"A'a ya danganta kawai."

Sai taji yayi wani abu kamar murmushi kuma kafin ta Wago ta kalle shi ya sunkuyo da fuskarsa kusa da tata yace.

"Ya danganta da lokacin da na dauka a waje kina jirana kafin na dawo?"

Wani irin abu ya lullubeta a lokaci guda tun daga kai har ?afa, ta dago ta kalle shi idonsa yana kanta kamar yadda ta sani.

"Ki gaya min gakskiya dan Allah ba zan fadawa kowa ba... kawai ce miki zanyi nagode." Ya roje ta a hankali.

Bata san lokacin da tayi wani guntun murmushi ba sannan ta daga kanta sau daya tana cigaba da kallonsa.

Wani abu da yasa a lokaci guda Ma'aruf yaji wasu abubuwa kamar chemical concoctions na zubewa a cikin zuciyarsa.

"Now I feel like posting it on my Facebook wall."

(Naji kuma yanzu kamar inje in rubuta a shafi na na Facebook.) Ya fada muryarsa can ?asa.

Sai kawai tayi wani murmushin mai fadi sannan ta juya, ta nufi wajen da take ajiye kofunan a kitchen din ta ajiye na hannunta sannan ta debo wasu containers da ta juye su Madara da Milo a ciki ta juyo, ya jingina da gefen sink Win har yanzu yana kallonta, kamar yana son yace wani abu.

"Sauran kayan suna falo."

Ta fada tana nufin sauran kayan breakfast din, kuma da haka ta taho zata wuce ta gabansa, amma kamar yadda zuciyarta ta ayyana mata zai faru, sai ya tsayar da ita, ya riko hannunta ya dawo da ita gabansa.

"Baki bani amsata ta jiya ba Amina."

Kai tsaye ya fada yana karbar kayan hannunta ya ajiye su akan sink din.

Sai ta kasa kallonsa wannan karon, ya riko hannunta Waya sannan muryarsa ta cigaba da magana a hankali.

"yunda na tashi da safe tunanin da nake yi kenan har naje na dawo, ko aikina da tarin mutane ke karkashina baya damuna kamar yadda a yanzu jiran abinda zaki ce ya dame ni, I always have the last and final say a kamfaninmu, but zuciyata bata damuwa da abinda zan fada kamar yadda a yanzu ta damu da abinda zaki fada min, so Please save me from this boredom and just say it now. Na gaya miki ko a yaya amsarki tazo zan karbe ta a hakan ba tare da wani tunani ba, I just want to hear your mind out." ( So nake kawai inji abinda yake a zuciyarki.)

A lokaci guda Amina taji makogwaronta ya bushe, taji tana shakar wata busashshiyar iska tana wucewa har cikin cikinta yayin da maganganun da ya fada mata jiyan ke dawowa cikin kanta.

"Amina ban san tunanin ki gane dani ba har yanzu, auren mu daban ne da irin wanda kowa yake yi, ban taba ganinki ba sai a ranar da kika zama matata kuma na san kema haka, kowanne mu bai san yaya Waya yake ba balle halayensa har aka haWa rayuwarmu tare, bamu da wannan sanin ko kuma fahimtar junar da mutane da yawa ke samu kafin aure.

Sai a yanzu ne muke fara gina tubalin da muka baro a baya, kuma ba zan boye miki ba I think I have started falling in love with you since from day one da na ganki a cikin gidan nan, ban san me yasa ba I just did... Kuma a yanzu da na ?ara sanin ki nake sanin komai game dake Amina, zuciyata ta bani tabbacin cewa da gaske ne ina son ki ba tunani nake yi ba, zuciyata tana godewa Allah a kodayaushe da ya zamo kece wacce Mami ta zaba min a matsayin matata.

Saboda da bake bace Amina da labarin zai canja, ko sau Waya kar kiyi tunanin cewa da kowacce mace aka kawo cikin gidan nan zan karSe ta kamar yadda na karSe ki. Na san me nake so Amina na san abinda bana so, kuma ina da tsarina a kowanne Sangare.

Don haka kema ina son inji tunaninki game dani, bana son in matsa miki da komai Amina, idan zamu gyara alakarmu mu cire komai a tsakaninmu ina so ya zama da yardar dukkaninmu ne, bana so ya zama don ni ina so ke kuma ya zane miki dole, so nake mu ajiye duk wani tunani a gefe tare mu karSi junanmu da zuciya daya, I want us to ignite our hearts together and get lost because we wanted to, shi yasa a jigawa nace miki not there, not then, sai lokacin da zuciyarki ta amince kuma kika bani dama Amina."

Allah yaso a jiyan da yake fada mata hakan cikin duhu ne, lokacin da bai nemi shawarar ta ba ya shigo dakinta bayan ta barshi a falo yana kallon zancen wata siyasar America, tayi masa sallama da cewar sai da safe zata je ta kwanta, kuma ya amsa mata suka yi sallamar Allah ya tashe su lafiya, sai gashi minti goma bayan hakan ya shigo dakin bayan yaje ya canja kayansa zuwa na bacci.

Ta rufe idanunta alamun bacci take yi har sanda taji ya hawo gadon, amma lokacin da babu zato taji ya naWe hannunsa daya waist dinta kafin ya jawo ta cikin jikinsa a hankali, babu shiri ta bude idanunta tana kallonsa, kuma a lokacin ne ya gaya mata wannan maganar, a yanzu kuma da safiyar Allahn nan yake neman amsarta.

Kuma abinda take ji a yanzu ya wuce duk yadda zata iya fassara shi, yadda ya rike hannayenta duka biyu kadai tana jinta ne kamar wani kwan fitila da ya kama tar! Sannan tana jinta kamar tana shawagi a iska, kuma cikin hakan ne taji lokacin da ya saje cewa

"Duk abinda zaki fada ina son kiyi considering cewa ba kowa ne zai baki irin wannan damar ba Amina, Allah ina da kirki sosai."

Bata san lokacin da wani murmushi mai kama da dariya ya subuce a bakinta, yace ya bata damar da zata fadi ra'ayinta amma kuma ya fara yiwa kansa campaign tun bata ma ce komai ba. Sai ta dago tana kallonsa sanda shima yake murmushin. Shima ya sani ai, amsarta ba zata canja daga abinda yake fata ba, ya riga ya gama daure ta da jikyoyinta, kamar ya sace zuciyarta tun a farkon zamansu ya kulle ta a wani keji, kuma bai bude ta ba sai da ta gama sabawa dashi ta yadda a yanzu da ya baya mu?ullin da kanta don ta bude kanta ya san ba inda zata iya zuwa... Dole da ta fito ta tashi zata dawo ne ta faWo cikin hannayensa.

Don Allah ya sani ko ba ita ba, bata ga macen da zata iya kallon Ma'aruf a wannan lokacin tare da kyawawan halayensa tace bata son sa ba, idan kuwa har an samu yo tabbas ko waceve za'a iya jeranta ta cikin masu karancin sa'a a duniya.

Don haka a wannan lokacin Amina ta daure dukkan wani tunani a zuciyarta, ta ture komai gefe, a karo na farko a rayuwarta tayi wani abu kai tsaye da zuciyarta ta gaya mata ba tare da tunanin komai ba, don a wannan lokacin ta ma manta kowa Win kuma ta manta komai, babu wani kokonto a ranta ko kuma tunanin hakan bai dace ba, abinda ta sani kawai shine Ma'aruf ya tambaye ta abinda ke zuciyarsa ne kuma zata fada masa gaskiyar zuciyar tata.

Shi kansa bai yi zato ba sanda ta tattaro dukkan dauriyarta a hankali ta ?ara tsawonta kaWan ta hanyar mi?ewa kan kafafunta sannan ta kai fuskarta daidai kunnensa, muryarta ta fito ne a hankali da kalaman da ita kanta sai a wannan lokacin taji su.

"You re the piece of me I didn t know was missing untill now."

(Kaine wani Sangare na da ni kaina ban san bani dashi ba sai yanzu.)

Ta sauke ?afafunta a hankali tana kallon fuskarsa dake Wauke da tsananin mamakin da ita kanta take jin yana lulluSe ta, taga yadda ya haWiye wani abu a cikin ma?ogwaronsa kafin ya gyaWa kansa a hankali.

"Nagode Amina, insha Allah ba zan taSa sawa kiyi dana sanin sanina a rayuwarki ba, zan kare dukkan hakkokin ki da Allah ya rataya min a wuya na, ba zan taba cutar dake ba, ina da tabo mai girma a cikin rayuwata, ina da abubuwa da yawa da ba zaki so saninsu ba, I'm a mess just like I told you, amma idan kika bani dama nayi miki alkawarin komai zai tafi daidai Insha Allah."

Kuma bai bari ta sake ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wani tunani ba ya haWe tazarar dake tsakaninsu, ya rungume ta a jikinsa da wata irin shiga da taji kamar yana son kange ta ne daga dukkan wani hargitsi na duniyar nan, wani abu daya dawo da ragowar hankalinta jikinta yana tuna mata da zagayen halin da take ciki, fuskar Amma da kuma ta Hajiya Kilishi ta haska cikin kanta a lokaci guda, dukkanninsu suna kallonta da jiranyen da ta san yana zagaye da ita, sai dai Ma'aruf bai bar hakan yayi nisa ba lokacin da ya sake ri?e ta a jikinsa sannan a hankali ya lalubo kunnenta ya raWa a cikin kunnenta.

"Thank you so much Doll, I was dying to do this..."

Kuma bai Sata lokacin wani tunani ba, lokacin da ya dawo da fuskarsa saitin tata sannan ya hade dukkan wata tazara tsakaninsu, his lips were rough and urgent, sannan tana iya jin dukkan wani sakon da yake bata a cikin hakan, kuma cikin wannan sakon ne Amina ta samarwa kanta mafita itama, wata mafita da a lokaci guda ta haska a cikin kanta, wata mafita da zata jefi tsuntsu biyu da dutse Waya!

Tsuntsu biyu, ba guda daya ba!

*****

Aka kwankwatsa kofar Wakin sau daya, biyu, uku....

"Who the hell is that?"

Muryar Jamal ta daka tsawa daga ciki yayin da yake naWe cikin bargon makeken gadonsa.

Zainab, ?ar aikin gidan dake tsaye cikin uniform dinta na masu aikin gidan ta zabura kaWan tayi baya saboda yadda muryar ta firgita ta, ta saba a lokuta da yawa irin haka idan tazo dama da sigar da take samun amsar sa kenan, amma ta kasa sabawa har yanzu, ta kasa sabawa tun sanda ta fara aiki a gidan.

"Hajiya ce tace in gaya maka tana nemanka."

Ta fada da karfi kaWan yadda zai jiyo ta. Jamal yaja tsaki yana shafa kansa da duka hannayensa duka biyu. Ya tsani yarinyar nan, ya tsane ta har cikin ransa, matan mahaifinsa uku ne, suna da ma'aikata fiye da hamsin a gidan kuma kusan rabinsu arna ne, idan ma akwai musulman to babu bahaushe ko Waya a cikinsu.

Don haka ya rasa dalilin da yasa mahaifiyarsa ita kadai ta fita zakka ta Wauki irinta aiki, shi baya hausa ma tare da ?an aiki amma akan yarinyar nan ya fara. Kuma tun daga ranar da ya fara ganinta a Sangaren mahaifiyar tasa, sanda suka ci karo ta zuba masa miyar data dauko a kwanon hannunta yaji ya tsane ta har cikin zuciyarsa.

Har ya buWe baki zai bata amsa ya tuna ko yayi turancin ma sai yazo ya fassara, don haka zata cigaba da tsaiwa a wajen tana kara maimaita masa abinda ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login