Showing 129001 words to 132000 words out of 132946 words

Chapter 44 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1132

da cewar zai mayar dashi can hida Kano inda shi da kansa zai dinga jagorantar komai... A yanzu kusan an gama komai ma kokarin samun masu siyan ginin kawai ake yi... Kuma sai ya zama fitar ma ta kara taimaka masa wajen sake warwarewa don ta sani akwai tarin abubuwan da a zaman gidan kadai zasu cigaba da tuno masa da Kilishi da kuma dukkanin abinda ya faru, amma bai taSa maganarta ba tunda ya farka, ko da Baffa ko kuma da Baba Usman Win da suke waya a kullum.

Sannan bayan tahowarsu Munaya ta gaya mata cewa cikin abinda bai fi sati hudu ba wata guda n canja tsarin gidan bakiWaya, Baffa ya saka an rushe bangaren Hajiya Kilishi, an haWe gidan baki Waya a waje Waya kuma ta kofa guda saboda su Samirah dama dukkanin al'ummar gidan da tabbas ganin Sangaren nata zai dinga tuna musu da ita a kodayaushe.

Don ko a lokacin da yayi general meeting tun kafin tahowarsu, ba ga ?an gidan kadai ba har da sauran yanuwa na da kuma na Hajiya Maimuna akan abubuwan da suka faru, yayi ta jaddada cewa dole ne kowa ya cire ta daga cikin zuciyarta saboda trin laifuka da kuma cutarwar duk da cewa an Soye wasu da yawa saboda Inna Danejo dake fama da rikicewar tsufa tun daga wannan daren da al'amarin ya faru.

A zahiri yanzu rayuwa ta fara komawa daidai, abubuwa suna tafiya kusan a daidai ga kowa don Baffa yana iya bakin kokarinsa wajen ganin ya daidaita rayuwar tasu ta koma kamar da, amma a cikin zuciyoyin kowa Amina ta sani cewa dole akwai wannnan digon bakin ciki da ba zai taba gogewa ba musaman ga su Samirah ?a?anta, wanda ko sau daya Baffa bai bari sunje sun ganta a can kurkukun da aka daure ta ba...

Munaya tace mata wasu daga cikin yanuwansa sunyi kokarin tausar sa akan hakan, amma babu wanda ya san cewa yayi nasa fushin sai a lokacin, don Ishaq ya kira ya zauna a gabansu sannan yace ya zama shaida zai yi shari'a da duk wanda ya ?ara kawo masa magana makamanciyar wannan. Shikenan! Sai zancen ya mutu ko su Samirah basu kara yunkurin hakan ba.

Gobe itace ranar da Ma'aruf ya yanke shawarar komawarsu, bata sani ba ma idan ya gama da zancen asibitin nan, amma ya tabbatar mata cewar zasu koma gida don tun jiya shi da Ishaq suka gama tsara komai, don haka itama tun a jiyan da kuma yau da safe ta gama shirya dukanin kayansu, akwati guda uku ne sai kuma wata jakar dake Wauke da yan kanan tarkacenta, ta tattare komai nasu hatta kayan da zasu saka ta fito dasu, na jikinsu idan sun cire ne kawai zata sama musu waje.

Kuma bata san me yasa ba haka kurum tun jiyan take jin wani iri don haka a yanzu da Amman tayi mata wannan tambayar sai kawai ta sake jin jikinta ya mutu, ta haWiye yawu a ma?ogwaronta kafin ta gyada kanta a hankali.

"Insha Allah Amma ba abinda zai faru, yaji sauki da gaske, kuma idan mun dawo Win ma zai ?ara tafiya can asibitin da ake duba shi kafin ma ya koma aiki insha Allah."

Daga cikin wayar, Amma ta yi tata ajiyar zuciyar? a hankali.

"Shikenan, Allah ya kawo ku lafiya, Allah ya ?ara sauki. Maganar da nake son mu yi akan yadda zamanki zai cigaba a gidan nan ne... Na gaya miki Kilishi ba itace matsalarki ta ?arshe a duniya ba, zama yau da gobe tare da kowa a duniyar nan dole yana bukatar hakuri don watarana ma baka san lokacin da zaka batawa wani ba, kina gani ko sanda kina nan a tsakaninku yanuwa ma kuna samun sabani balle kuma a gidan surukai.

Don haka dole ne ki cigaba da yin taka tsan-tsan wajen kyautatawa kowannensu da kuma Wauke kai akan abinda bai shafe ki ba, wadannan abubuwan guda biyu Amina sune abinda mata da yawa suke kuskurensu shi yasa ba ga surukansu kadai ba har a wajen miji suna samun matsala, idan kin dawo zamu sake yin magana insha Allah."

Amina ta gyaWa kanta alamun ta fahimta ta kuma rike kamar dukkan sauran maganganun mahaifiyar tata kafin ta amsa.

"insha'Allah Amma, insha Allah."

"Kice muna gaishe shi, sai goben idan zaku taho kya kira mu."

"Toh zai ji insha Allah."

Har Amman na shirin katse wayar tayi saurin sake magana.

"Maryam tana kusa dake? Zan tambaye ta wani abu ne..."

"A'a bata nan amma ga Adam nan, bari ya kai mata."

"Toh Allah ya bamu alkhairi."

Amman ta amsa kafin ta mika wayar a hannun Adam dake zaune yana game a wayar Aminu, ya mike da sauri zuwa tsakar gida inda Maryam Win ke kitchen tana sake zubawa su Hafsa da suka tsira mata idanu? abinci tana faWin kar su shigar mata daki su bata mata.

Ta karSi wayar bayan hakan sannan suka shiga tasu hirar akan wasu Winkunan kaya da ta barwa Maryam Win ta kai mata kafin tafiyarsu, Winkunan da take sa ran su zata yi amfani dasu a bikin Munaya da Ishaq wanda aka saka rana watanni biyu masu zuwa... Watakila lokacin da zata haihu da kwanaki kaWan. Ko can gidan a yanzu shirye-shiryen kawai da ake yi kenan, shine babban abinda ke dan dauke hankalinsu daga al'amarin da ya faru, musamnan su Samirah da Munsyan ke gaya mata cewa suma sun kara sakewa sosai a yanzu.

Aminu ya shigo kafin su ?arasa eayar da Maryam, yana shirin fita zuwa wajen aikinsa da ya cigaba da zuwa sakamakon saukin da kafarsa tayi. ya karSi wayar daga hannun Maryam suka shiga tasu hirar kamar kodayaushe yana gaya mata cewa ya cika akwati na uku ya buWe na huWu da kayan Baby.

***

Daga kan matattakalar benen dake saukowa cikin falon gidan, Ma'aruf ya sauko, kafafunsa na biyo matattakalar a hankali yayin da yanayin hasken falon ke shaida masa yanayin tafiyar da lokaci yayi don har ya kammala shiryawa da komai bai kalli agogo ba tunda wayarsa ma a falon ya barta tun jiya.

Iskar dake faman kadawa a falon kasancewar bude windows da akayi ta shoga kada shi kotawanne Sangare yayin da idonsa ya sauka akan Amina dake tsaye daga can wajen kitchen tana zuba fulawa a cikin wani kwano.

Numfashinsa ya tsaya a kirjinsa a lokaci guda ganin kayan daje jikinta, rigarsa ce... Wata loose T-shirt dinsa da yawanci idan zaiyi ball yake saka ta... Fara ce ?al, ta tattare dogwayen hannunta zuwa can sama, kanta babu dankwali yayin da girman cikinta ya fito sosai a saman rigar... Kafafunta, wadannan siraran kafafun nata da a yanzu suka kumbura ?aWan suna yawo ta kasan dan karamin wandon da ta saka wanda bai kai gwiwa ba.

Ba wai yau ya fara ganinta da irin wannan shigar ba, kusan kullum ne, amma kusan kullum din sai zuciyarsa ta cika da wani irin abu mara misaltuwar da yake ganin kamar idan ya kira shi da sunan farin ciki kaWai bai yi masa adalci ba... a lissafinsa itace duniyarsa a yanzu, ita kadai ce wani abu da har cikin ransa yake ganinta a cikin rayuwarsa a matsayin wani abu da yake so har cikin zuciyarsa ba wani abu da ya karba a matsayin maye gurbi ko kuma don babu yadda zai yi ba.

Yana sonta ta sani, yana sonta saboda kyawawan halayenta, yana sonta saboda kyautatawar ta, sannan yana sonta saboda taimakonta wanda a kullum a kodayaushe yake ?ara ganinsa... Musamman a yanzu da? yake ganin wata irin kulawarta wadda duk yadda zuciyarsa ke da tauri a yanzu kai tsaye take wucewa tana taSowa har can ?arshe.

Kuma bai san me yasa ba lokacin da al'amarin ya faru, lokacin da komai ya faru, bai sani ba idan wani a cikin yanuwansa ko ma Hajiya Maimuna sun kalle ta da wani tunani, amma shi bai ko tuna ba sai daga baya, bai tuna ma cewa ta shigo rayuwarsa ne ta hanayar matar da a yanzu bai san a wane irin mizani zuciyarsa ke tunaninta ba. Idan ya kalle ta kawai a kullum kuma a kowanne hali baya tuna komai sai cewa itace waje mafi girman da yake samun nutsuwar zuciya.

Lokacin da ta juya dauko wani jug din ruwa a gefe, lokacin idonta ya kai kansa, ta kalle shi a lokaci guda da murmushi ta subuce a fuskarta.

"Wani yasha bacci yau..."

Ta fada a lokacin da ya karasa saukowa daga kan stairs din, ta cire hannunta daga cikin fulawar ta ware su tana murmushi sannan ta ?araso da sauri ta rungume shi, ta rungume shi sosai ta yadda har sai da kafafunta suka Waga daga kasa kamar ?ar ?aramar yarinya.

"You miss me this much?"
(Kinyi missing dina har haka?)

Muryarsa ta fito a hankali dab da kunnenta, sai ta dawo baya a hankali tana sauka akan kafafunta sannan tace.

"Nayi missing dinka fiye da haka Sugar.."

Yayi murmushin da fuskarsa tayi mata kyau yana kokarin cije lebbensa.

"Really? Kamar yaya kenan?"

"Kamar cikin malala gashin tinkiya..."

Ta fada tana kama kuncinsa kamar karamin yawo.

Dariyar da yayi ta jefa kansa zuwa baya.

"I can't beleive kina hada ni da tinkiya Babygim.."

Yadda ya fadi abin ya saka ta dariya itama kafin tace.

"Kawai fa salon magana ne, ni na isa nace maka haka, you are the most adorable person to me a duniyar nan yanzu Sugar."

"Mhmmm, Baki ce masha Allah ba..."

Ya fada yana daga gira guda. Ta sake yin wata dariyar sosai kafin tace.

"Dama ana cewa maza Masha Allah ne?"

"Su ba mutane bane?"

Sai ta cije nata lebben yanzu har yanzu daya hannunta akan kafadarsa daya kuma tana rike da gefen fuskarsa kafin tace.

"Idan mazan suna so a gaya musu, su fara fadawa matan tukunna, especially in sun yi kwalliya ba wani dogon turanci ba..."

"Ni ai ba sai na fada ba Babydoll, saboda ni mijinki ne, nawa hanyoyin daban suke ma bayan wannan dogon turancin."

"Really?"

Ta tambaya tana daga duka girarta biyu bayan murmushin da take yi. Sai kawai ya sake sunkuyo da kansa dab da fuskarta sannan a hankali yace.

"Ko in nuna miki? Kinga sai mu ?ara da photocopy a ciki kafin printed one din nan ya fito?"

Ba shiri bakinta ya buWe sannan idanunta suka zare a lokaci guda. Ta cire hannunta dake gefen fuskarsa ta naushe shi sannan ta juya tana fadin.

"You're soooo Bad Ma'aruf Muhammad Bakori!"

Ta maida hannunta cikin kwanon fulawar daidai lokacin da ya zagaye duka nasa biyu a kugunta yana rungume dan karamin cikin nata da ba zaka yarda ya kai watanni har takwas ba. A kusa da kunnenta sosai ya shiga magana.

"Zan fita wajen su Khalid ne yace wasu mutane sunyi masa magana zadu je su ga ginin, kinga idan mun daidaita dasu komai zaifi sauki dama ina nan, idan kuma ba haka ba Khalid din shi zai ?arasa komai bayan na tafi."

Sai ta gyada kanta a hankali yayin da Waya hannunta ke zuba ruwa a cikin fulawar tana kara cakuda siraran yatsunta a ciki.

"Zai iya shi kadai? Kuma ka yarda dashi?"

Ta tambaya, tana cigaba da sbinda take yi,daga bayan nata, nasa udanuna a tsaye akan sbinda take yi Win yace.

"Lawyer ne, abokin Ishaq, kuma gidnsa bashi da nisa da aibitin, saboda haka mai siyan wajen kawai zai samo, jiya muka samu wani kamfani NHC da suka siya duka kayayyakin aikin dake cikin asibitin har sun biya kudin, sannan na gaya miki na gama biyan staffs Win duka tun shekaranjiya so kin ga kusan babu abinda ya rage kenan..."

Daya hannunta ya kara ruwa a cikin fulawar yayin da iskar da ake yi har yanzu ke cigaba da kada su kotawanne Sangare kamshin damina da kuma sanyinta? na cika gidan. Tace.

"Allah ya taimaka komai ya faru da wuri,? Allah yasa hakan ne mafi alkhairi."

Addu'ar tayi masa dadin da har sai da yayi murmushi kafin ya amsa.

"Ameen."

Sai kuma fuskarsa ta koma daidai a lokaci guda, ya kusan hade ransa ma kafin yace.

"Wai meye wannan kike yi?"

Ta dan juyo da kanta ta kalle shi da murmushi jin muryarsa ta canja.

"Fanke..."

Fatar bakinta ta motsa yayin da sautin ya fito a hankali.

"Fanke?" Ya tambaya cikin rashin fahimta karara.

"Fanke da na sani na mutuwa? Me za'ayi dashi?"

Amina ta kyalkyale da dariya ba shiri tana juyar da kanta. Sai kawai ya sake ta sannan ya juyo da ita sosai tana fuskantar sa.

"Seriously da gaske nake, me zaki yi da fanke? Ba sai anyi mutiwa aje raba shi ranar sadaka ba?"

"Sugar waya gaya maka? Koyaushe fa anayi... Har yara ana yiwa su je dashi makaranta sannan mutane suna cinsa as breakfast ma, me yasa sai anyi mutuwa za'aci?"

Yanayin fuskarsa ya nuna alamun ya dan fahimta a lokaci guda, amma duk da haka hannunsa na rike da itan yace.

"Ke me zaki yi dashi?"

"Ci zanyi, kawai na tashi ne naji ina sha'awarsa."

"Me yasa baki ce in taho miki dashi ba? Me yasa sai kin wahalar da kanki?"

Ya tambaya a hankali yana cigaba da kallonta... Sai ta karasa matsowa cikin jikinsa ta mayar da hannayenta saman kafadarsa kamar dazu sannan a hankali tace.

"Saboda nafi son inci wanda nayi da hannuna Sugar, ka daina damun kanka aiki baya wahalar damu, we are strong!" (Muna da karfi.)

Kalmar 'Mu' din da ta furta ta shiga har cikin zuciyar sa a lokaci guda, sai ya sake rike ta a jikinsa yana tallafo ta da duka hannayensa biyu.

"Jamal is strong Babydoll, don haka insha Allah haka little one dinsa ma zai zama..."

A lokaci guda kumatunta suka yi murmushin da take yi a kodayaushe ya fadi hakan, don tun daga ranar da suka ga gender Win Babyn ya tabbatar mata da sunansa... Jamal.

Fuskar Kilishi ta gifta a cikin kanta a lokacin maganganun da ta faWa mata suna haskawa a cikin kanta.

_"...na san ba zan iya hana Ma'aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma kuma ba zan lazimci wani abu ciki ba don babu shi ko kaWan a cikin lissafina!"_

Murmushin da bata shirya masa ba ya kufce mata, a lokacin ta faWa ne kamar ita ke da iko a komai, kamar ita ke da ?addarar su a tafin hannunta, kamar babu abinda ya isa ya giftawa wannan umarnin nata, sai gashi a yanzu tana duniyar, da lafiyarta da komai, amma bata da ikon ko da ganinsu balle har ta san me suke ciki ko kuma tayi gadarar zartar da wani hukuncin...

Sai ta gyaWa kanta sau biyu tana cigaba da murmushi kafin muryarta ta fito a hankali tana kallonsa, a hankalin da ko da akwai wani a kusa dasu ba kallai bane yaji abinda tace.

"Insha Allah."

Idanunsa suka cigaba da kallonsa tana nazarin tarin abubuwan dake kara canjawa a hankali a hankali game dashi din. Gashin kansa ya taru sosai sai dai har yanzu bai kai na baya ba, ya taje shi sosai yana ?yalli, don har yanzu da laushinsa, yadin jikinsa kalar dark blue ya kara fito da hasken da fatarsa ta kara yi a kwanakin sakamakon hutun da ya samu akan rayuwarsa ta baya.

"Idan kika cigaba da kallo na haka, ba lallai ne in iya fita ba Babydoll...."

Muryarsa ta fito a hankali yana cigaba da kallonta, sai kawai ta cije lebbenta tana murmushi sannan ta yi Wage a hankali ta kai fuskarta dab da kunnensa.

"Kayi zaman ka kawai, idan nayi fanken nan sai mu siyar,? kaga may be ma mu samu fiye da kudin asibitin nan... Naga alama ?an gayu basu san fanke ba."

Yayi murmushi sosai yana kallonta.

"Ki rufa min asiri Babygym, ni da nake neman kudin da zan gina miki irin wannan gidan, naga alama kina son shi da yawa..."

Idanunta ya zare a lokaci guda...

"Ni bance ba, ni bance ba Sugar, ka rufa min asiri dan Allah..."

Yadda ta fada tsakaninta da Allah ya bashi dariya sosai, sai kawai yayi baya da kansa kafin ya sake kallonta sosai.

"I'm madly in love with you Amina.."

Ya faWa yana lumshe idanunwansa. Ta sake yin dage akan kafafunta a hankali tana wasa da yatsunta dake sarke da wuyansa.

"Madly? Madly dai? wanda na sani?"

Muryarta ta fito kamar wani fiffiken dake fadowa kasa a hankali.

"Idan baki gane ba Babydoll, zan iya yi miki bayani, kin san babu wanda ya san ?warewata anan kamar ke..."

Ba shiri Amina ta kyalkyale da dariyar da tana yin baya zuwa gefe, hannunta ya dauko wani mug kalar ba?i an rubuta 'Pa' a jikinsa ta tsiyayo masa ruwan tea Win data haWa a wani flask sannan ta mi?a masa.

"Mutane suna can suna jiranka Pa...."

Da murmushi ya karSa ya jan kujera a gefensa ya zauna, yana gaya mata wallahi da gaske yaje, zai bata mamaki tunda har bata yarda dashi, yana bayanin tana murmushi tana juyowa tana kallonsa.

?arar wayarsa? ce ta katse shi, yasa hannu a aljihu ya Wauko ta, nambar Maryam ?anwarta da ya gani ta tabbatar masa da waye tun kafin ma ya Wauka.

"Dadddddyyyy!!"

Muryar Hamida ta faWa da ?arfi daga cikin wayar, ba shiri Amina ta taho da sauri ta karSa tun kafin ma ya amsa tana tambayarta yadda take, makarantarsu da kuma gaya mata cewa gobe zasu dawo.... Dama a dazun nauyin Amma ne yasa basu gaisa ba, kafin kuma tace Maryam din ta hada ta da ita sai Aminu ya karbi wayar.

Daga inda Ma'aruf ke tsaye yana kokarin karasa shanye tea Win dake hannunsa ya cigaba da kallonta yana murmushi...

Amina itace rabin rayuwarsa a yanzu ya yarda, itace nutsuwarsa dama dukkan wani fatan samun nasarar sa... Kulawar da yake samu tare da ita, wani abu ne da bashi da inda zai je ya samu idan ba a wajen nata ba.

Komai mu?addari ne daga ubangiji ya yarda!? lokacin da ya amince da aurenta, yayi ne saboda Jamal, saboda ya san alakarsa da ita a lokacin da yaga sunanta har ma da adireshin ta, sai gashi daga baya ya fahimci cewa wannan sunan na wata Aminan ce daban da itama take a wannan unguwar ta gadon kaya, wata Amina ce daban da suka yi makaranta tare a wajen sauran takardunsa na wajen Hajiya Maimuna da bai san dasu ba sai a lokacin da Amina ta haddasa kusancinsu...

Allah ya sani bai san tarin alkhairin da zai lissafa? da ya samu ta dalilinta ba tun daga lokacin da ta shigo cikin rayuwarsa zuwa yanzu, kamar tana tafiya ne da wani haske a kafafunta dama hannayenta ta yadda duk inda ta taka ko kuma abinda ta taSa sai ta haskaka shi.

Ita kaWai, ita kaWai ce abinda idan ya tuna cewar ta hanyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login