Showing 114001 words to 117000 words out of 132946 words

Chapter 39 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1141

garinsu ba, amma zata kiyasta cewa yana cikin kwatankwacin matsalarta ne a lokacin, ko ma wadda tafi tata.

Kuma ta tabbata abinda ke gabansa shi yasa shi barinta a lokacin, idan ba haka ba ta sani,ta san Jawad ta fahimci galinsa a dan kankanin lokacin da ta sanshi, baya fadin abu sai idan har da gaske yake kuma ya tabbatar dashi har cikin zuciyarsa don idan ya fada Win, to babu wani kuma a duniya da ya isa ya canja ra'ayinsa, ko a bakin Hajiya Mardiyya tasha jin tana bawa kannensa hakuri akan su hakura da wani abu, tace ko ita tsoro sa take yi idan ransa ya baci.

"Malama idan baki da kudi gwara ki koma gida, alkur'anin Allah babu wanda zai dauke ki har Sameru kyauta a wannan tashar..."

Wannan mutumin ya sske fada a lokacin da ya gama rubuta sunaye ya shiga haWa kan yan canjin da aka tattara masa, a lokacin kuma wani mutumi ya ?araso ya biya nasa kudin aka gama cika mitar,direban ya zagayo ya karbi kudinsa ya cire kamashon tasha sannan ya shiga ya tada motar.

Sai kafafunta suka matsa daga wajen ta koma gefe, gefe kusa da wasu kanti da kuma rumfuna ta tsaya, tana kallo motar ta juya ta fita ta nufi hanyar fita, idonta ya koma kan jerin motocin da akace mata sune ke nufar garin da take son zuwa, mutane na ta hada-hada a wajen ana lodi da kuma jera kaya yayin da masu karbar kudi ke yi.

Bata da ko sisi, bata ma san inda zata same su ba, amma al?awari ne ta yiwa kanta cewa ba zata sake komawa cikin Yakura a yanzu ba, watakila watarana zata dawo ko don ziyartar kabarin mahaifiyarta, amma a yanzu ta yarda cewa babu abinda zao sake maida kafafuwanta wannan gidan.

Tunanin Jawad ya sake haskawa a cikin kanta,ta san zai dawo zai neme ta, amma rashin samun nata da zaiyi bai dame tasosai akan tunanin samawa kanta ?anci da take son yi ba.

_"Babu abinda zanyi miki Zainab, wallahi babu abinda zanyi miki, I just want to feel you close to me... So nake kawai in dinga jinki a kusa dani. Shi yasa na tambayeki idan zaki aure ni saboda zan je har wajen iyayenki ne in nemi aurenki, babu ruwana idan ma akwai wanda suka tsara zasu baki Zainab, ko shari'a zan iya yi da kowa idan akace za'a hana ni aurenki..."_

Abinda ya fada mata kenan da yabayin fuskarsa dake tabbatar mata da kowacce kalma? da yake fada a lokacin, don haka ta yarda idan har da gske yana son ta, zai nemo ta a duk ind take tunda ta san va zata yi nisan da hakan zai gagare shi ba.

Tana yawan son korewa kanta nauyi a kodayaushe, ta yarda babu wani ingantaccen abu da rauni ke samawa mutum a duniyar nan, don haka ba zata bari rauninta ya rinjaye ta wajen zama jiran Jawd ba, idan har ta mike da kafafunta, ta tafi wajen da zai tabbatar da darajarta tun kafin yazo da ma bayan yazo din, abubuwa zasu canja daga kalar yadda suke tafiya a baya, shi kansa zai san cewa bai same ta ne a wani hali na rashin gata da madafa ba.

"Har yanzu kina nan?"

Mutumin nan ya fada bayan ya dawo zai wuce, hannunsa babu littafin nan a yanzu. Ya ja ya tsaya a gabanta sannan ya gyada kai.

"Lallai da gaske kike, hala mutuwa akayi muku a can din ko?"

Kalmar mutuwa ta sake dawo mata da zagayen halin da take ciki, sai kawai idanunta suka ciko da kwalla sannan t ja hancinta kadan kafin ta gyada kanta. Sai shima ya girgiza nasa kan.

"Allah ya jikan musulmi, ai kuwa kya so tafiya... Kuma zan taimake ki tunda haka ne."

Ba shiri ta dago ta kalle shi da idanunta da har a lokacin suke rine da kuka, ya sake gyada masa kana alamun ya tabvatar da hakan.

"Akwai shugabanmu anan wajen, wallahi ba wani abu zai yi miki ba, kawai dai taimakon juna zaku yi ki sami abinda kike so, ke fiye da hakan ma zai baki a yau din nan, babu wanda zai sani kuma babu wanda zai ganki."

Wani abu ya doka a kirjinta da jin hakam,don tsaf ta fahimci inda zancen nasa ya dosa, ta zare idanunsa akanta tana? kallonsa cike da tashin hankalin da shi bai fahimta ba ya cigaba da cewa.

"Kuma walkahi ma ni a duk wadanda nake kai masa babu irinki, duk yan kauyen nan ne dake kawo tallan kaya cikin tashar nan, to suma baki fa abinda suke samu ba balle kuma ke... Ai ina gaya miki sa'ar da zaki raka yau..."

"Kayi hakuri Malam, amma? ba zsn iya abinda kake nufi ba."

Muryarta ta fito a hankali tana katsse shi, kuma dukda hayaniyar cikin tashar yaji abinda ta fada da yake hankalinsa na kanta.

Zainab ta juya zuwa batanta inda wajen yake da rumfa daga gefen wani shagon container ta cire takalmanta ta zauna tana jin yadda hakoran bakinta suka kasa tsayawa waje guda sakamakon kukan da yake shirin kubce mata tana danne shi, mutumin ya kalle ta daga inda yake tsaye, takaicin asarar kudin da yake hangen zai samu a wajen shugaban nasa na bi ta kan zuciyarsa.

Har zai juya yaji ba zai iya dannewa ba, don ba karya yayi mata ba, shi dai ta hanyarsa ya sani cewa bai taba kaiwa Alhajin wata mace kamar ta ba, fatarta kadai? wata kala ce dake tsakanin fari da kuma ruwan ?asa, wata kala mai Wauke da kuma daukar hankali, bata da shahararren kyan da a lokaci guda zaka gane shi, amma ?irar jikinta kaWai da yake gani tun daga cikin hijabin, ya sani ba kowacce mace take haka ba.

Don haka a lokaci guda ya canja shawara, shawarar daya san tunaninta ba zai iya kufce masa ba.

Bai sake cewa komsi ba ya juya ya tafi kuma sai a lokacin ?wallar dake tare a idanun Zainab ta ganganro kan kumatunta, bata taba yiwa kanta wannan fatan ba, bata taba fatan za'ayi ranar da zata zubar da mutuncinta don biyan wata bukatar ba... Zata gwammace ta koma inda ta fito da tayi wani abu makamancin hakan, a hankali ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta biyu tana kokarin goge hawayen.

Banda Jawad babu namijin da ya taba rike ta a duniya, kuma shi nasa daban ne, baya kallonta da niyyar komai, yawanci fushinsa ne ma ke sawa ya rike ta, fushinsa da take mutukar jin tsoro a lokacin, amma a kwanakin nan musamman tahowar da suka yi, idan ta kalle shi a wannan yanayin, sai taji kamar ta rungume fuskar sa a jikinta tsawon lokacin da ba zai kara ganin komai ba bayan ita...

_"...zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni."_

Wani abu tsaya a makogwaronta a lokacin da ta tuno hakan, Jawad bai sani bane amma halayen rayuwa sun sa tun a yanzu ta fara koya...

"Baiwar Allah..."

Muryar wata mace dattijuwa ta sa ta dago da kanta bayan wucewar wani lokaci, fara ce, farin da bata sani ba idan na gaske ne ko kuma wanda ta samawa kanta, fuskarta dauke da fara'ar da ta sa a lokaci guda tasa bayan hannunts ta goge hawayen dake kan fuskarta.

"Ance min taimakon kudin mota kike nema ko?"

Ta sake tambaya da wani murmushin, kuma kafin ta bata amsa ta cigaba.

"Gidan abinci ne dani anan baya, kuma almajiran dake min wanke wanke bai zo ba yau, idan zaki yi in biya ki kinga sai ki samu kuWin motar ko?"

Babu shawara ta biyu tunanin Zainab ya amince da hakan, bata ga aibun hakan ba, bata ga komai ba... Don hausawa sun ce wanda yake ruwa aka mi?a masa takobi kamawa zai yi, ?afafunta suka mike a daidai lokacin da nasa suka ?araso wajen.

*

"Kace ta san sunan garin ko?"

Jawad ya tambaya a cikin gudun? da motar ke yi, gudun da suke yi daga gefen titi wajen da babu komai sai kasar dake tashi a baya da zarar sun wuce.

Nura dake zaune a gefe ya gyada kansa.

"Ta sani, haka Baban ya gaya min cewa ai tun da daWewa ta san sunan garin.

"Kuma ka tabbata babu wata tasha da ake zuwa garin sai wannan da zamu je?"

Ya sake tambaya yana zura hannunsa a cikin gashin kansa.

Nura ya sake gyada kansa.

"Ita kadai ce a kusa yallabai, ita kadai ce wadda zata iya zuwa, kuma gashi ma Isa ya tabbatar mana da cewar ya ganta akan hanya..."

Jawad ya cije lebbensa na kasa, hannunsa ya sake danne sitiyarin motar da babu shiri suka kara figa da gudu,? Abdallah Wan wan Hajiya Salamatu wanda bata yarda da tafiyar Jawad ba sai da ta turo shi ya biyo shi yayi magana daga inda yake zaune a bayan motar.

"Easy mana bro,zamu isa yanzu ai Insha Allah."

Jawad ya girgiza kansa.

"A kowanne lokaci mota tashi take yi a tasha zamu iya sabanin ko kuma minti daya ne Abdallah. Tun yaushe ta fita, tun safe fa yace badu ganta ba."

Nura ya gyada kansa.

"Amma ai da tazarar tafiya,ta dauki lokaci kafin ta isa na san sannan kuma bata da kudi a? hannunta, sai da kowa ya caje kudinsa a gidan yau duka bata dauki ko sisi ba, kaga kafin tayi abinda zata samu kudin mota shima wani lokacin ne don haka za..."

"Me zata yi ta samu kudi?!"

Ba shiri Jawad ya katse shi yana daga muryarsa, kafin ya juyo da fuskarsa yana kallonsa.

"Me zata yi ta samu kudi a cikin tasha Nura? "

Kafin Nuran ya amsa, wayar Abdallah tayi ?ara a hannunsa ya dauka ya kara a kunnensa da sallamar da Jawad ya riga ya san ko wacece, Hajiya Salamatu... Don tun daga lokacin da suka sauka daga jirgi a Kaduna suka je gidan abokinsa suka Wauko motarsa da ya bari a can, ta kira shi da kuma Abdallah fiye da sau goma, sai da ta fahimci shi yake tu?in motar sannan ta koma kira Abdallahn.

Zai rantse da Allah a lokacin da ya gaya mata cewa zai taho Kaduna a yau, kalar tashin hankalin da ya sauka a idanunta iri Waya ne da wanda ya gani a idanun Hajiya Mardiyya kafin tahowarsa... Tsoro ne karara da kuma taraddadin rasa shi, wani abu da ya kara bashi tabbaci na cewar da gaske ita mahaifiyarsa ce Uwa wadda babu makamanciyarta a duniya, tunda a kwana daya rak da ta san shi har zata iya tarayya da halin da wadda ta raine shi tsawon shekaru ta shiga wajen tunanin rasa shi.

Har hannunta ya ri?e ya gaya mata cewa zai dawo su tafi can Abujan tare kamar yadda ta tsara har ma da wasu ?anuwanta, tana gaya masa cewa akwai tarin wasu yanuwan nata da zaau zo wajensa a yau daga Gombe shima yana gaya mata cewa baya fatan abinda zai kaishi ya Wauke shi tsawon wani lokaci.

Bai gaya mata ba, bai gaya mata abinda zaizo yi ba kamar yadda shima Abdallahn bai gaya masa komai ba, kawai ya tsinci labarin ne bayan sun dauko Nura a cikin irin maganganun da suke yi na zuwa nemanta.

"Bamu karasa ba har yanzu Aunty muna hanyar..."

Abdallah ya faWa a cikin wayar yana dawo da hankalin Jawad kan halin da suke ci kuma a sannan ne suka fara hango tashar, daga can saman wani waje da ya danyi tudu alamar tsanuni ne a wajen tunda hayar tana da hawa da sauka da yawa.

Ya cije lebbensa na kasa hannunsa ya sake danne kan motar a lokacin da Abdallah ke cewa.

"Insha Allah Aunty, insha Allah za'a ganta..."

Ya sauke wayar sannan ya shiga sake tambayar Nura sunan wajen da kuma tazararsa da cikin garin Kaduna, sai dai Jawad baya ko jinsu idanunsa dama duk wani abu mai motsi a jikinsa sun tafi ne ga bakin tashar nan, baya ko damuwa da gudun da yake yi ganin ya fara shigowa cikin mutane.

Tayoyin motar suka tsaya tun kafin ya ?arasa kofar tashar, kuma ya fito a lokaci guda da motar ta tsaya yana rufe kofar motar, su Nura suka biyo bayansa suka nufi ciki gabadaya, tarin mutane da kuma hayaniyar dake faruwa a ciki ta cika kunnen Jawad kota wanne bangare, wata yarinya ya fara hangowa dauke da kaya, kammaninta suka koma ba Zainab sak a idanunsa.

Har ya fara tafiya sai ya hangi wata irinta itama daga wani gefen, ya ga wata da goyo sannan ya ga fuskoki da yawa daga cikin wata mota duk irin nata, sai kawai ya ja ya tsaya, ya tsaya daidai lokacin da Nura ke tambayar wani inda ake samun motocin Sameru.

"Wallahi maigida nima matafiyi ne ban sani ba, sai dai ko ku gwada tambayar wancan na ganshi da rigar ?an union."

Yana faWa yana nuna wani ma'aikaci dake aiki daga can gefe, kuma Nuran ne kadai ya tafi yana ganin kwatancen da mutumin yayi masa tun daga can, kuma tun daga can Win ya gane, don haka kafin ma Nuran ya dawo ya riga yayi cikin tashar Abdallah na binsa a baya.

Mutum biyu suka samu akan wata mota dake kan layi kuma duk irin tambayar da suka yi musu kai tsaye suka nuna cewa basu ga yarinya mai makamancin kwatancen da suke yi ba.

"Amma bari a kira Sani, sune a wajen da safe, watakila bakuwar taku da safe tazo."

Dayan ya fada yana yin gaba zuwa wani gini daga gefe. Dayan ya kalli Jawad sosai yace.

"YallaSai wallahi kar ku saka rai, tashar nan sai mutum dari su zo a kasa da minti goma,wani ko fuskarsa ba zaka kalla ba zaka karbi kudinsa ka tambayi sunansa... Da ka rubuta shikenan kai dashi har abada, to ta yaya za'a iya gane wata yarinya?...."

Bai ?arasa maganarsa ba sai ga daya ya dawo tare da mutumin da aka kira da Sanin, yana tsayawa tun kafin ma Jawad ko Nuran su ce wani abu ya tambaya.

"Yallabai farin hijabi ne a jikinta..."

Jawad ya daga kansa da sauri yace.

"Ofcourse bata da tsawo sosai..."

Sanin ya daga kansa shima.

"Ai bata je ko'ina ba, bata hau mota ba, tazo inaga kamar bata da kudi ne saai kuna ta tafi. To bayan hakan kuma sai na ganta a zaune a wajen shagon Ashiru, amma wallahi tun Wazu ne, ban sani ba yanzu ko za'a same ta..."

"Ina ne wajen? Nuna mana wajen kawai..."
Cewar Nura.

Mutumin ya shige gaba, dukkaninsu suka bi shi a baya zuwa daya bangaren tashar wajen da ake lodin motocin dake karasawa cikin Kadunan, Jaji zuwa Kawo.

Kuma Ashirun da Sanin ya ambata shi suka fara gani a wajen yana Waukan sunayen wasu mutane a cikin mota. Basu san me Sanin yace dashi ba, don shi ya fara ?arasawa kafin su, idon Jawad na kan Ashirun a lokacin da yake gyada kansa yana nuna wata hanya da ke gefe don haka bai ko ?arasa wajensu ba ya yi hanyar.

Ya isa daidai jikin wani shago lokacin da idonsa ya hango masa ita a lokaci gudataa mikewa da aamun zata bi wata farar mata dake tsaye a gabanta tana yi mata murmushi.

Ta juya bayanta tana fuskantar matar, bata ga tahowarsa ba balle ta ganshi, don haka bai jira komai ba ya ?arasa da taku biyu ya riko hannunta, yatsunsa suka lankwasa a tsakanin nata tun kafin ta juyo a lokaci guda da ta kalle shi, ta kalle shi da idanunta a zare da tsananin tsoron da cikin sakanni biyu kawai ya juye zuwa mamaki.

"Jawad...??"

Bakinta ya furta a hankali yayin da zuciyarta ta buga sau Waya, ta buga da wani sauti da ta tabbatar da cewar dukkan sauran mutanen dake zagayensu sun ji shi. Ba shiri idanunta suka cika da shekin kwallar da bata san ta ina ta fito ba, mamaki take idan shi din ne ko kuma mafarki take yi... Don tunaninta ya kasa bata cewa zai iya zuwa ya same ta a wannan wajen kuma a wannan lokacin.

Sai dai babu wani bata lokaci, yayi abinda ya tabbatar mata da cewar da gaske shi din ne ba wani ba, da gaske Jawad din da ta sani ne...

Hannayensa duka biyu suka zagaye jikinta, ya rungume ta a cikinsu, ya rungume ta a kirjinsa, ya rungume ta a gaban tarin mutanen dake wajen ba tare da tunanin komai ko kuma abinda za'ace ba..

Sai kawai ?wallar da ta cika idanunta ta zubo kan fuskarta, ta riga ta sani komai ya zo ?arshe, wahalar da take tunani ta yanke tun kafin ma ta fara, shikenan tayi sallama wa dukkanin wahalarta!

***

*03:15 am.*

Tana tsaye daga jikin tagar dakin, hannayenta duka biyu dafe da gilashin da aka rufe yagar wanda ta manna fuskarsa a jiki yayin da idanunta ke tsaye ?yam! Akan wanda ke kwance a akan gadon dakin, ance mata Ma'aruf ne, kowa yace mata shine, amma fiye da minti goma da take tsaye a wajen babu wani abu a kwakwalar ta da yatuna mata cewar Ma'aruf din da ta san shi take kallo.

Fuskarsa a kumbure take idan ka dauke katuwar robar zukar numfashin da aka manna a fuskarsa da kuma gashin kansa da aka aske, wannan sumar... Wannan sumar ta Ma'aruf da kullum take tare da hannaensa, yanayin yadda yake cusa su a ciki kadai Kala-kala ne ta yadda ta kan fahmci wani abun da yake nufi idan yayi tun ma kafin ya furta.

Don haka gabaWaya kamanninsa sun canja ta yadda ko ba'ayi wa mutum bayanin rashin lafiyar dake damunsa ba shi da kansa zai kintata tun daga harafan dake rubuce Saro-Saro akan gilasan wajen da launin ja... ICU.

Wani abu ya wuce ta makogwaronta lokacin da ta tuna da san da ta farka ta riski labarin komai... fuskar Amma ta fara gani kafin komai, tana zaune daga kujerar dake gefen gadon da take kwance, hannunta rike da wani carbin ta kalar yalo, wani carbi da a cikin su gabaWaya babu wanda zai iya fadar adadin shekarun da suka san shi a hannunta, dashi take lazimi kulum, a kowacce safiya da kuma yammar Allah.

Ta rufe idanunta a hankali sannan ta sake????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
bude shi tana kara kallon Ammar da kanta ke sunkuye tana addu'o'in ta, yanayin sai ya koma mata iri Waya sak da wani lokaci a can baya, lokacin da Maryam bata da lafiya, lokacin da suke zaman jinyarta a asibiti, haka Amma ke zama a gaban gadonta da wannan carbin tana lazimi.

Fahimtar cewa yau itace ba Maryam din ba ya dawo mata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login