Showing 12001 words to 15000 words out of 132946 words

Chapter 5 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1157

fada, ilai kuwa kafin ya gama tunanin yaji da wannan shakakkiyar muryar tata ta sake cewa.

"Hajiya ce tace in gaya maka tana nemanka."

Wai wa ya gaya mata cewar Sunan Mamah Hajiya ne ma?

Ya ja tsaki kafin yace.

"Ina zuwa."

Shirun da yaji bayan wasu sakanni yasa ya fahimci cewa ta tafi, don haka ya kara jan wani tsakin kafin ya jawo wayarsa a gefe, karfe sha Waya da rabi na safe, laifin me aka cewa Mamahn ya sake yi da zata turo a tashe shi da sassafen nan? Missed call Win Haro ya gani har guda tara don ya saka wayar a silent, gayen bashi da hankali wani lokacin.

Yana shirin sake maida wayar ya ajiye sai ga shigowar wani kiran nasa na goma. Ya Wauka ya ?ara a kunnensa.

"Ina ka shiga ne J? Ka bar gari ne?"

"Yes, ina gida."

"Dole ka baro Abuja yau Jawad, don na gano hanyar da zamu lalata yarinyar nan?"

Ba shiri Jawad ya mi?e zaune yana sake rike wayar a kunnensa, kusan bakinsa na rawa yace.

"Me ka samo? Me zamu yi?"

Daga cikin wayar Haron ya ?yal?yale da dariyar shakiyancinsa kafin yace.

"Ma'aruf Mansoor Bakori!"

**

_Me kuke tunani ya zama karshen hatsarin nan shekaru goma da suka wuce?_

_Wace mafita kuke tunanin Amina ta samo?_

_Ga dai Awwalu can na bin Baba..._

_Me ya Haro yake nufi da sunan Ma'aruf a matsayin hanyar da zasu hukunta Ru?ayya?_

_After all this, what do you think about the love Birds??_

_I'm here singing Confession Song by Omah lay..._

_Ku shirya ganin wasu Confessions Win daga MMB...=??_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*03*

~~~~~~~

_The best part is, I wasn't looking when I found you._ _- Unknown_

**

*Shekaru goma da suka wuce.*

Lokacin da aka shigo da gawar, lokacin da gidan ya sake hargitsewa da tarin jana'ar dake da ta shigowa da kuma masu kuka da salatin da muryarsu ke Wagawa, lokacin Hajiya Maimuna ta bude fuskar gawar danta da aka shimfude a falon Baffa, hannunta ya rike zanin atamfarta da aka nannaWo shi a jiki, danshin jinin dake jikin atamfar ya a ratsawa har tsakiyar kanta, a lokacin ne kuma abinda ya faru tsakaninta dashi jiya ya dawo cikin kanta.

"Mimi...

Muryarsa lokacin da ya shigo cikin gidan ta ratsa kunnuwanta a jiyan. Tun da yayi sallama da Ladi ta bude masa ?ofar yake kwala kiran har ya shigo gidan, a lokacin tana kitchen, ta jiyo shi tana ta amsawa ama shi bai jiyo ta ba gashi babu kowa a gidan, don safiya ce dukkan yammatan gidan sun tafi makaranta, don haka tana jinsa sai da ya zagaye kusan kowanne daki a gidan yana kiran sunanta a yadda shi kadai yake gaya mata wato Mimi, kafin ya dangana da kitchen din.

Kuma shirun da tayi bayan ya buWe kofar kitchen Win ya saka ta juyowa daga tukin tuwon da take yi. Ya tsaye ri?e da hannun ?ofar kawai yana kallonta, ta manta rabon da ta ganshi da manyan kaya, kullum cikin kananun kaya yake sune shigarsa a kodayaushe, don shekara wajen biyar ya shafe a Cairo yana karatu don haka dasu ya saba.

Amma yanzu da ya dawo gida kuma ya karbi aikin kamfanin Bakori wani abu da yake burinsa kuma mafarkinsa tun yana yaro, sai ya zama dole manyan kayan su zasu zama kayansa.

Jamal yafi kowa kyau a gidan, hakan wani abu ne da ba sai an lissafa ba, tun daga kan yayanta har zuwa na Kilishi babu wanda yake ko kama dashi, tun yana yaro mutane da yawa na cewa ma ba ita ta haife shi ba duk da cewar itama fara ce, amma baya kama da ita kuma baya kama da kowa banda hancinsa da wasu suka ce yana shige da na Baffa don na Baffan ma dogo ne kamar nasan, akwai lokacin da yana shekara bakwai har sai da jama'a suka sa mata kokonto a ranta game dashi itama ta shiga tunanin ko anyi mata canjansa a asibiti ne sai da Baffa ya dakatar da ita tukunna.

"Raina yana ta tashi har nayi zaton ko bakya gidan ne, muryarsa mai zurfi ta fada yana kllonta,.

"Allah ya sawwake maka, ta ina rai yake tashi Jamal?"

Ta faWa tana dariya kafin ta juya.
Ya karaso ciki ya tsaya a kusa da ita yana kallon tukunyar dake jan gas din da take tuka tuwon da ita.

"Mimi kice min wannan miyar waken ce?"

Ya tambaya sanin cewar ta gaya masa tana da miyar tun jiya.

"Itace dai yanzu zan dauko ta daga freezer, kawai tashi nayi yau ina sha'awar tuwon."

"Alhamdlilah." Ya fada yana zura hannunsa cikin gashin kansa.

"Dama banci komai ba wallahi, ina tashi naga wai yaran nan dankali aka soya musu."
Shi baya son duk wadannan kayan cimar na zamani, abu kadan yake ci a cikinsu yafi son abincin gargajiya duk kuwa da zamansa a kasar waje, bama shi kadai ba kusan duka yayanta haka suke, har Ma'aruf idan bata manta ba.

A lokacin ne ya zaro wasu kudi daga cikin aljihunsa ya ajiye a gabanta, gaban flask din da ta gama kwashe tuwon a ciki, kuma ganin yawan kudin shi ya tsayar da ita cak daga karasa abinda taje yi.

"Baffa ne yace in kawo miki."

Ya fada da sautin muryarsa da ya canja a yanzu, tana iya tuna yadda wani irin daci ya mamaye kirjinta a lokaci guda kafin ta yi kokarin ture hakan, hannunta ya kai kudin tana fadin "Allah ya saja da alkhairi', amma sai Jamal yasa nasa ya dafe nata kafin ta dauka.

"Kudin cefane ne ko?" Ya tambaya, muryarsa na shaida irin bacin ran dake cikinta, bata amsa ba ya cigaba.

"Tunda Baffa ya bani kudin nan bake binsa da kallo, baice min komai ba amma na fahimci baya miki magana tun last week, kuma na tambaye shi amma bai bani amsa ba, bana son inyi komai akan zargi Mimi, ki gaya min abinda nake tunani haka ne?"

"Jamal..." Ta fada tana kallonsa.

"Dan Allah." Yayi saurin katse ta.

"Ki gaya min gaskiya, ki san gyarawa zanyi, kin san ba zanyi abinda bai dace ba."

Wucewar wasu sakanni kafin ta gyaWa kanta a hankali tana cigaba da kallonsa.

"Akan zancen zuwa hutun su Munaya ne a Abuja, yace bai yarda ba kuma suna son zuwa, shine nayi masa maganar cewa ta kanaya suje din, amma sai bai fahimta ba, sai laifin ya dawo kaina, yace sun fara girma sun fara raina maganganunsa ni kuma ina nS u sun fara zagaye zuciyarta, taba ganin ma'anar kowacce kalma da suka sha fada mata, .

Sai gashi lwata-kwata awannin da hakan ya faru basu karfin na kwana guda ba, yace in dai
Ina raye... Kamar wani abu a lokacin na gaya masa cewar zai iya rasa ran nasa da wuri.

Tana jin kukan su Shukra da sauran jama'ar gidan daga wajen falon, tana jin tashin kukan kowanne a cikinsu yayin da mazan dake wurin ke ?o?arin basu baki, don an hana kowa shigowa a wannan lokacin, Baffa yace babu wanda zai ga gawar a wannan yanayin sai an shirya shi tukunna, itama ta shigo ne don ita mahaifiyarsa ce, babu wanda zai iya kallon idonta yace ba zata ganshi ba.

Idanunta na kallon gawar da tayi kaca-kaca da jini, kirjinsa ya dagargaje, ance bishiyar da suka daka shi ta soke don a saitinsa take, kuma har a yanzu ma akwai wasu kananun itacenta da suka hade da jikinsa da aka kasa cire su, jini yana malalowa a hankali har yanzu daga jikin gawar yana jika kayanta a lokacin, don tana tsugunne a gabansa, sanye da wani tsadadden leshinta da tayi shirin zuwa biki dashi a ranar.

Tana jin yadda danshin jinin nan ke ji?a kayanta, yana gaya mata cewa jinin Jamal ne, Wanta guda na farko a duniya, Wan dake mutukar sonta fiye da komai a duniya, Wan da tun yana karaminsa zuciyarta ke cin buri akansa, wannan kyakkyawan Jamal Win da kowa ke yabawa, kyakkyawan Wan da take alfahari dashi a kowacce, a yanzu vabu wannan kyan, babu kamanninsa ma ko kadan, dogon hancinsa ne kawai ake iya ganewa a cikin kumburar da fuskarsa tayi ba. A cikin kunnenta muryarsa kawai take ji yana ce mata...

_Zafi nake jin Mimi, ko'ina a jikina ciwo yake yi..._

Haka yake ce mata duk lokacin da bashi da lafiya a makaranta idan suka yi waya.

"Limamin ya iso."

Taji wani a cikin mazan dake bayanta yana faWa, sannan taji muryar Baba Usman yana cewa.

"An kira waya yanzu, ance an shiga da Ma'aruf din tiyata, likitocin sun ce anyi sa'a babu internal bleeding."

Sannan taji wani a cikin mutanen na tambayar su waye a wajensa.

"Mami ta tafi tun dazu."

Amsar da ta fito daga bakin wani, itace a amsar da tun a wannan lokacin ta bawa Hajiya Maimuna wani tabbaci na cewar shikenan tayi biyu babu.... babu Jamal Win kuma babu Ma'aruf din! Don bata jin bayan addu'a tana da wani sauran fata a duniyar nan na dawowar Ma'aruf wajenta.

***

*Present Day.*

Tun da Munaya ta shigo tace da Hajiya Maimuna wai Ma'aruf ne ke zaune a falo yana jiranta hannayenta ke rawa wajen shiryawa, karfe goma sha Waya na safiya a lokacin sai kallon agogo take tana karawa.

A tarin shekarun da lissafinta ba zai iya ta tancewa ba, ta manta yaushe rabon da ta sanya idanunta a cikin na Ma'aruf din a wannan lokacin, iyakarta dashi bayan tsawon wasu kwanaki ne da zai shigo ya gaishe ta kawai, zuciyarta ta daWe da ha?ura dashi game da wasu abubuwa da ta san cewar hakan ne ya kamata, ta dade da Waga kasan ruhinta ta binne dukkan wasu al'amuransa, shi yasa har a yanzu dukkan maganganun ?anuwanta game da hakan basa damunta sosai.

Sai dai duk da dauriyarta, ta sani cewa bata isa ta canja cewar ita uwa ce ba, bata isa ta daure wannan kewar da zuciyarta ke ciki shekara da shekaru game dashi ba. Basu saba ba, Wawainiyarsa kaWan ta sani, abinda take gayawa kanta kenan a kullum wajen tausar kanta, amma ta sani cewar babu wani abu a duniyar nan da zai yi daidai da dawainiyar rainon cikinsa da kuma haihuwar sa da tayi, shi yasa har abada a duniya uwa Waya ce, kuma babu girman wani abu da ya isa ya canja matsayinta.

A zaune a falon kuwa ta same shi baysn ta fito, hannunsa rike da wani dan karamin kwano mai kyau, yayin da idonsa ke manne da Tvn dake nuna tashar CNN.

Ya juyo ya kalle ta daidai lokacin da ta karaso hannunta yana danna buttun Win tsayawa jikin keken tayar.

"Barka da yamma."

Muryarsa ta gaishe ta ba tare da wata inkiya ba kamar yadda yake yi kullum, kuma a wannan lokacin dai taji hakan bai dame ta ba kamar yadda take ji a baya, ganinsa kadai a wannan lokacin ma ya isa ya mamaye dukkan tarin abubuwan da take lissafawa a kansa.

"Barkanmu dai, kun tashi lafiya?"

Ta amsa farin cikin dake zuciyarta na nunawa akan fuskarta.

"Lafiya kalau, ya ?arfin jiki?"

"Alhamdulilhi mun gode Allah."

Har yanzu idanunsa na ?asa bai dago ya kalle ta ba, kuma tayi zaton iya abinda zaice kenan kamar yadda suka saba a kodayaushe, amma sai kawai taga ya dago ya kalle ta sannan yace.

"Kwanaki Baffa yace mun Abdurrahim ya kusa dawowa ko?"

Ba shiri ta daga kanta da murmushi.

"Eh, nan da sati biyu insha Allah."

"Ashe har ya tsayar da rana, the last time da muka yi magana yace mun bai saka rana ba tukunna."

Mamaki ya dhiga cinye ta a yadda take zaune, amma sai ta daure tace

"Yanzu ya kammala komai ai, don ma baya son taro ne amma ni da nayi niyyar wasu suje masa convocation din."

Sai ya gyada kansa.

"Haka yace mun nima, har Ishaq ma ya tambaye shi amma sai yace masa wai ba wani abu za'ayi ba."

Ta sake yin murmushi.

"Rigimarsa tafi shi ai, nace masa ko kewar mu baya yi."

Shima murmushin yayi ba tare da ya sake magana ba, yana tausayin kannin nasa ya sani, duk sanda suke magana ta hanyar text idan ya tuna cewar ba zai taba iya kiransa ba yana jin wani iri a ransa. Wani iri kamar yadda yake ji a yanzu da yake zaune gaban mahaifiyar tasa yana hira da ita, hirar da ba zai iya tara shekarun da aka rufa kafin ta iya tuna lokaci na karshe da suka zauna irin haka ba.

Kai tsaye yaji wani Sangare na zuciyarsa ya shiga godewa Amina da tayi sanadin zuwan nasa, don yadda ta kalli idanunsa ta ro?e shi da Allah ya san ba zai taba iya kin ce mata A'a ba.

Kuma a wannan lokacin ba kallon Hajiya Maimunan yake yi ba amma sai jikinsa ya bashi cewa robar dake hannunsa take kallo, kuma yaji shigowar sako a cikin wayar dake aljihunsa, ya san Faruq ne, shi yake jiransa don haduwarsu da Yakubu ( mutumin da zasu tura nemo musu Mr. Okafor.)

Don haka sai yayi saurin tasowa ya miko mata robar dake hannun nasa.

"Wai zogale ne na bayan gidan ta tsinko ta dafa shine tace in kawo miki Munaya tace mata kina so."

Yadda shiru ke ratsawa waje a lokaci guda ya kashe ?arar komai haka Hajiya Maimuna taji a cikin kanta lokacin da ta karbi robar, kalaman suka shiga cikin kanta amma suka tsaya cak! Ta riga ta fahimci wa yaje nufi da itan ba sai ya fassara ba, amma hakan wani abu ne da bata taba tunanin faruwarsa a cikin lissafinta ba.

Ta kalli robar ta sake kallonta, ba wani abu ne mai yawa ba, amma wannan lokacin tana jin kamar nauyin zogalen nan daje ciki yafi girman dukkan wata kadara da take shi, kwalla ta cika ramin idanunta a lokaci guda, don haka bata Wago ba sai kawai ta daga kanta a hankali.

"Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi Ma'aruf, Allah ya ?ara haWa kanku, Allah ya baku zaman lafiya, ya kade dukkan sharrin da zai shiga tsakaninku, Allah ya baku zuri'a dayyiba."

Mami tasha yi masa addu'a, kala-kala ma, har da wadanda idan ta fada zai kara kallontasau biyu kafin ya amsa, amma Allah ya sani ya dade baiji addu'ar da ta shiga har cikin zuciyarsa ta tabo wani abu da bai san da zamansa ba irin wannan. Kalaman Mami daban ne da irin wadannan, yawanci addu'arta tana tsayawa akansa ne kadai babu wani a gefe da ya shafe shi, don haka tmya sani tun bayan lokacin daurin aure sa da Baffa da kuma Baba Usman suka yi musu makamanciyar wannan addu'ar, zai lissafa wannan a karo na biyu da yaji irin wannan addu'ar daga bakin wani.

Makogwaronsa ya bushe a lokaci guda, amma yayi kokarin hadiyr wani abu a hankali kafin ya amsa sannan ya tsugunnna yana yi mata sallama, bai kara iya kallonta ba itama kuma baya jin ta sake kallon nasa, don wata?ila suna raba abu iri Waya ne a zuciyarsu daga shi har itan.

Kuma karo na farko a wannan ranar bayan ya shiga wajen Hajiya Kilishi yaji haka kurum baya son dadewa don ransa bai gana daidaita ba har a lokacin, yaji hirar da take yi masa ba fahimta yake yi sosai ba, don haka yayi mata sallama ya fito, sai dai kafin ya bar cikin dakinsai da yayi mata wata tambaya dake yawo a cikin kansa tun bayan lokacin sa Amina ta bashi robar zogalen nan.

"Mami kina son zogale kuwa?"

Ta kalle shi kamar tana son gano wani abun kafin tayi murmushi tace.

"Haba ka manta ne Mai gaskiya, amma bana son zogale tun asali."

Sai ya gyaWa kansa kawai sannan ya ?ara yi mata sallama.

_"Dan Allah zaka mi?awa Hajiya wannan? Zogale ne na bayan gidan nan tsinko na dafa, Munaya tace min Hajiya tana so, amma Mami ita bai dame ta ba."_

Haka ta gaya masa lokacin da ta tsaya a gabansa rike da robar tana ta juya ta a hannunta. Wani abu ne ya faru smdashi bai gama gabe masa ba har yanzu, ya san dai kawai ba laifi suka yiwa Mamin ba amma kuma duk da haka yana jin wani iri.

Ya zaro wayarsa ya duba bayan ya shiga mota, sakon da ya shigo dazu ba daga Faruk bane, daga mutane kamfanin RTL ne da suka yi dasu akan cewar gobe zasu je shi da wasu daga cikin board trustees Winsu su karbo kudin da suka siya dilolin kaya a hannunsu, haka kurum wanna karon ya yanke shawar cewa baza su karbi kudi ta account ba gwara su karbi cash kawai, tunda an cuce su wancan karon kuma har yanzu basu gama da gano matsalar ba.

Sakon yana bayani ne kan wajen da zasu hadun da kuma lokaci da sauran abubuwa, ya kashe wayar ya tada motar daidai lokacin da kiran Faruk ke shigowa, ya san ya riga shi isa wajen kenan kuma yanzu zai dame shi, don haka ya danna motar ya nufi hanyar titi daidai lokacin da idonsa ya kai kan robar zobo mai sanyin da Amina ta ajiye masa daga kasan dashboard din motar wajen da akayi musamman don ajiye roba dama.

Babu shiri wani murmushi ya subuce a bakinsa, yana da plan dama tarin tsaruka na ydda zai saita rayuwarsa tare da tmyarinyar nan, don tabbas ya gama yarda cewa ita din alkhairi ce a rayuwarsa, kuma mafi dadin abin shine ya same ta ne a lokacin da ba nema yake ba.

Ani abu da alokacin bai sani ba shine kwance a cikin zobon nan, sinadiri kwayoyin maganin Hajiya Kilishi ne ke yawo tun daga sama har kasa.


****

*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*

A cikin ?aton falon, baka jin komai sai ?arar A.cn dake hurawa ta kowanne bangare na falon, akwai manya-manyan royal chairs set uku da aka rarraba falon zuwa waje uku dasu. Jamal yana zaune daga kuherun gefe masu kalar ruwan madara, gajeran wando ne a jikinsa kuma wata t-shirt kalar ruwan kasa, a gabansa wani tebur ne da aka cima da kayan abincin safiya, hannunsa na rike da kofin mug yana kuSar shayin ciki yayin da mahaifiyarsa dake gefe Hajiya Mardiyya ke kallonsa tana sake maimaita maganganun da ba jinsu yake yi ba.

"Yanzu Babana ko don wadannan makiran matan mahaifin naka ba zaka saurare ni ko sau daya a rayuwarka ba? Kana ganin irin banbancin da ake nuna mana a gidan nan, kuma da nayi magana sai kace dani ba zaka yi ba babu kyau, bayan shi kansa mahaifin naku ai ya san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login