Showing 39001 words to 42000 words out of 132946 words

Chapter 14 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1118

kashe Jamal ba kuma na san shima ya san hakan, da zai dawo nayi imanin zai gaya maka hakan, zai gaya maka cewa ya san ba laifinka bane."

"Laifin waye Doll? Har yanzu na kasa gane laifin waye, ko zai dawo Win ta yaya zai yarda dani?..."

"Zaka sani insha Allah, nayi imanin idan ka cigaba da nema zaka sani, Allah ba azzalumin bawansa bane Ma'aruf, ya sani cewa ko su waye sun cuce ja kuma sun hargitsa rayuwarka, zai maka sakayya ta hanyar tona musu asiri insha Allah."

Maganar ta fito tare da tahowar wani hawayen mai dumi daga idanunta, sai kawai ya sake sunkuyo da fuskarsa kan goshinta yayi kissing idanun nata duka biyu yayin da ta rufe su.

"Insha Allah Doll, fatan da nake yi kenan a kodayaushe."

Wasu hawayen suka sake biyo bayan na baya suka fito masu Wumin gaske. Abinda ta sani kawai a wannan lokacin shine idan har da sa hannun Hajiya Kilishi a mutuwar Jamal, to tabbas kuwa Ma'aruf ya kusa samun amsar sa.

***

*?arfe tara da rabi.*

Tunda suka tashi take iya kokarinta wajen ganin tayi komai kamar yadda suka saba, yau asabar ce don haka ta san vabu inda zai je, wajen karfe takwas ta fito ta sake yin wanka sannan ta shiga aikinta, tana jiyo shi daga daki yana ta waya kuma bayan taje kai masa daya wayarsa da ya bari a falo wadda ake ta kira, ta ganshi ya fito da system har guda biyu yana ta faman dube-dube. Basu yi wata magana sosai ba amma yayi mata murmushi fiye da yadda zata kirga a iya safiyar kawai.

Ta kammala hada breakfast din tana dauraye kwanukan da tayi amfani dashi ne lokacin da ihun Hamida ya ziyarci kunnenta, ta tashi tana ta kiran sunan Mary.

Ta fahimci Mary ce ?ar aikinta da kullum suke tare, kuma takaicin da ya kasa barin zuciyarta shine na yadda sunan arniyar ya zauna a bakinta, ko mahaifiyarta bata kira sama da ita, yanzu ma ace yaro ya tashi daga bacci babu kiran sunan Allah sai wata arniya... Da sannu zata canja mata hakan a hankali.

Kuma ko da ta isa dakin har ta sauko daga gadon tana shirin fitowa, don a bakin kofa ta tarar da ita. Kuma cikin siga da dabararta sai da ta sa ta fadi addu'ar tashi daga bacci kafin su wuce zuwa bandaki inda tayi mata brush da wanka gabadaya.

Bayan sun fito ta shirya ta cikin wata ?ar doguwar rigarta mai kyau pink colour sannan suka fito falo,inda anan suka tarar da Ma'aruf har ya fito shima ya Webo kayan breakfast din da kansa zuwa falo ya zuba yana ci.

Yana ganinta ya fara bata hakuri cewa yunwa yake ji shi yasa ya kasa jiransu, Hamida ta makalkale shi tana gaya masa cewa tayi mafarki da Unicorn, wani shirmen mafarkinta irin cartoon din da kullum take gani.

Wannan lokacin yayi dadi a zuciyar Amina ba kadan ba, sai take ganin yadda yarinyar ta dada sawa gidan ya zama lively a tsakaninsu, har wayar Ma'aruf Win ta dauke lokacin da Faruk da wani Josh ke ta kira babu kakkautawa, sai da ya ro?e ta da Allah ya gaya mata cewar wani suke nema da yayi musu satar wasu tarin kudi masu yawa a kwanciyar nan da yayi na kwana biyu kawai sannan zancen ya dake ta da wani irin yanayi ta bashi wayoyin.

Ya fita zuwa barandar waje duk da suna jin dukkan abinda yake cewa, kuma ko kafin ya dawo Hamida tasa ta canja mata daga tashar CNN din da yake kallo zuwa Disney Junior dinta, ita kuma ta kwashe kayan nan zuwa kitchen ta shiga karasa wanke wankenta da bata gama ba.

A lokacin Ma'aruf ya shigo cikin kitchen din, ya karaso har inda take sannan ya rungumeta ta a hankali cikin hannayensa.

"Hey Angel."

Ya faWa a cikin wuyanta, a lokaci guda numfashinta ya katse a kirjinta kafin tayi? kokarin saita kanta zuwa tambayar dake bakinta.

"Me yasa zaka fita yau weekend?"

Tayi tambayar don taji sanda yake gayawa Faruk cewa gashi nan zuwa. Taji yayi murmushi a cikin wuyan nata kafin ya lalubi daidai kunnenta yace a hankali.

"Saboda babu yadda zanyi Doll, dole ne muyi abin nan da gaggawa mu samo mutumin nan, babu wanda ya san abinda ya faru a kamfanin har yanzu, ni da Faruk da kuna Josh ne kawai, sai wadanxan mutanen daya kamfanin. Kuma bana son ayi dadewar da dole zancen zai fita balle har Baffa ya sani... Idan hakan ta faru rayuwata zata sake taSuwa ne na sani."

Tana jin yadda jikinta ke yi kamar ya kama da wuta, sannan tana jin murmushin da yake yi a jikinta alamun yana jin dadin rikita tan da yake yi, kuma kafin daya daga cikinsu ya sake cewa wani abu, sallamar Samirah da kuma Munaya daga falo ta shiga kunnensu.

Ba shiri tayi kokarin matsawa amma yaki sakinta.

"Su Samira ne suka zo..."

Ya gyada kansa.

"Naji su, me za'ayi?"

Ya tambaya da gaske, hannusa daya na kokarin kwance dankwalin kanta, babu shiri tasa nata hannun duka biyu ta dam?e shi sannan ta juyo tana kallonsa.

"You are busy ka manta kace fita zaka yi yanzu, suma kuma yanzu zasu shigo nema na har nan."

Ya girgiza kansa yana ?ara jawo ta jikinsa.

"Na fasa, I want this busy yanzu more than anything."

Ya fadi hakan idanunta na kan kofa don daga yadda take jin Samirah na kiran sunanta ta san yanzu zata shigo, sai kawai taji ya shiga kissing gefen kumatun ta yana jawo hankalinta daga kofar zuwa kansa.

"Dan Allah ka tafi kar su shigo." Muryar ta ta fito kamar zata yi kuka.

Ya janye fuskarsa baya sannan murmushi mai kama da dariya kafin yace.

"Yanzu kike shirin roko na kar in fita yanzu kuma kina korata saboda waWannan yaran, wai laifi muke yi ne ko me?"

Girgiza kai kawai take tana kallonsa cike da roko, kuma kafin ta iya cewa wani abun muryar Samirah ta doso kitchen din tana fadin.

"Matar gidan tana nan ne..."

Ai bata san lokacin da tasa dukkan karfinta ba ta fita daga hannun Ma'aruf ta dawo gaba ta tsaya da sauri tana kokarin daukan wasu kwalayen sugan data juye a jar ta bar kwalayen anan kan worktable din dake tsakiya, kuma kafin Samiran ta shigo tana jin sanda ya juyo shima ya sake tsayawa a daidai bayanta sannan kafin tayi tunanin komai ya sunkuyo daidai gefen kunnenta yace.

"Kina nufin in zuge miki zip din rigar? Dama wancan karon da na taya ki din nan kamar ba daidai muka yi ba ko?...."

Bakinta ya faWi har ?asa yayin da numfashinta ya dauke a lokaci guda, sai kawsi ya kyalkyale da wata dariya a hankali sannan yayi gaba ya wuce ta zuwa hanyar kofa, kuma sai da yaje daidai kofar sannan ya juyo yace.

"Na tafi inda kika kore ni, kiji dasu, amma akwai lokacin da bakin ki ma bai isa yayi magana ba."

Yana fadin haka ya kifta mata idonsa daya yana murmushi sannan ya fita daidai lokacin da taji Samirah bna cewa.

"Ashe kaima kana nan Yaya..."

Sai kawai ta saki wani numfashi a hankali sannan bakinta ya tale da murmurshin da ta kasa tsaida shi.

***

*Karfe goma sha Waya.*

?arar ?wankwasa kofar ta karaWe gidan gabadaya, Amina ta taho da sauri daga cikin daki inda ta bar Hamidah na ?o?arin taje girarta a gaban mudubi, yarinyar na son kwalliya da alama, don ko Wazu da ta raka ta toilet tayi fitsari tana kallonta lokacin da take gyara hularta a jikin mudubin jikin sink.

Allah ya sani a yanzu tana jin son yarinyar nan yana ?aruwa a cikin ranta, kwana biyu kawai amma duk sanda ta kalle ta da waWannan idanun nata irin na Ma'aruf sak, sai taji wani abu na yawo a cikin ?irjinta, don ita kanta yarinyar ta ?ara sakewa da ita sosai.

Tafiyarta a hankali saboda yadda take jin jikinta ta karaso bakin ?ofar, kuma haka kurum sai taji gabanta ya faWi, taji farin cikin da ta tashi dashi a yau na yayewa, taji zuciyarta tayi fayau yayin da jikinta yayi shafal a lokaci guda kamar fallen takarda.

Sai kawai ta karanto hasbunallahu wa ni'imal wakil sau uku sannan ta bude kofar daidai lokacin da aka ?ara kwankwansawa.

Kuma a lokaci guda idanunta ya shiga na cikin Hajiya Kilishi dake tsaye a wajen.

***

"Me tace?"

Muryar Amma ta tambaya a cikin wayar da Amina ke yi awanni biyu bayan hakan. A hankali taji wani abu na zarcew cikin ma?ogwaronta yayin da idonta ke kallon Hamida da tayi bacci a cinyarta.

Kalba take yi mata a cikin gashinta mai tsananin laushi amma kuma babu yawa, laushinsa ne kawai irin na Ma'aruf amma bai yo yawan nasa ba, saura guda daya su gama don haka ta daWe da yin baccin don tun a farko tayi abinta.

"Me ya kawo ta Amina?"

Amman ta sake tambaya jin tayi shiru, tun dazu suke wayar, tun dazu Amman ta kira take shaida mata cewa ashe a airplane su Hafsa suka sa mata wayar tun jiya shi yasa bata same ta ba, kuma bayan ta kashe ta sake kira ne ta shiga zayyano en mata zuwan Hamida da kuma layar da ta gani a cikin kayanta.

"Kinyi daidai wajen ?ona layar,don nsyi imanin idan har ba da sunanki aka yi ba to da nasa ne, don da alama asirin kusa ne,sai yana tare da mai shi sannan zai ci, suna da tasu manufar tabbas, amma nafi danganta hakan da cewar kome take son taui ita mahaifiyar yarinyar, shi yasa suke son su jawo hankalinsa kanta ko kuma ke su kore ki, amma bamu da tabbas, don haka ki dage da addu'a, ki kuma cigaba da kiyaye dukkan wani abu a gidan.

Zasu zo, ni na tabbata zasu zo miki don asirin bai fara ci ba tukunna, ki zuba ido kawai ki saurari zuwansu, wannan matsalar mai sauki ce don nasu tunanin bashi da fadi don haka a lokaci kankani zaki gama dasu.

Amma yarinyar, ki cigaba da rike ta da wannan kulawar da na sanki da ita Amina, Kilishi ba zata kawo miki ita a banza ba amma tunda bata ce komai ba mu saurare ta tukunna, wanda kafin nan ki cigaba da rike ta da zuciya daya don wannan ba karamar kofa bace da zaki ?ara bude wata darajar taki a zuciyarsa, kar ki manta kullum ina gaya miki takamar kowacce mace a duniyar nan zuciyar mijinta ce, samun nasararki akan Kilishi dama duk wani abu da zai biyo baya ba zai kai darajar kyautata rayuwar aurenki ba."

Da wannan suka kammala zancen Hamida da kuma batun layar nan, sannan Amman ta shiga bata labarin cewa Hajiya Kilishi ta turo da wasu mutane an dauki Baba da Aminu zuwa wajen da za'a fara musu fafutukar visa don kaishi asibiti a india kamar yadda ta shaida musu.

"Suna nan suna ta yabonta Amina, Babanku da ?anuwansa har ma dasu Asma'u (?annenta) kowa yana ta sambarka, basu? san cewar umarninki bane Amina, don wannan bashi da maraba da cewar umarnin hakan kika bata, umarnin da ita kanta bata sani ba."

"Tazo Wazu Amma."

Kai tsaye bakinta ya fadi hakan, don a wannan lokacin ta kasa daurewa tarin hargitsin da kuma ruWanin dake cikin kanta.

"Me tace?"

Sune kalmomi biyu da Amman ta furta wanda taji su a cikin ranta kamar baron da aka cika da ?asa mai nauyi yake rike a hannunta kuma tana shirin hawa tudu dashi, don bata san ma ta inda zata fara ba, bata san ta inda zata fara dauko zancen ba, amma shirun wayar dake tafiya yana shaida mata jiran sauraren da Amma ke yi tasa ta hadiye abinda ke bakinta sannan tace.

"Akan Hamidan ne."

Amma bata ce komai ba har ta ?ara haWiye wani abun a cikin ma?ogwaro??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nta sannan ta cigaba.

"Kamar yadda kika fada tace bata kawo min ita a banza ba, bata tsallake kowa tace ni zan rike ta ba sai don tana da dalili, dalilinta kuma shine bata bukatar yarinyar ta zauna a cikakkiyar mutum, ta gaya min da farko tayi niyyar a kawar da ita ma gabadaya, amma kuma sai taga cewa gwara ta bar Ma'aruf da wani abu ko guda daya ne a rayuwarsa bayan ta tafi.

Bata gaya min inda zata je ba, amma tace daga ni har ita mun kusa barin rayuwar Ma'aruf don ta kusa kammala burin da ta shigo dashi gidan, burin da yasa tayi fafutukar auren Baffa tun a shekarun baya, don haka tace min ko bayan bata nan bata son ya zama akwai wani abu mafi soyuwa a rayuwar Ma'aruf sama da ita.

Tafi son ya zama zuciyarsa na tunawa da ita da matsayin da yafi na kowa a wajensa, don ta gaya min cewar tafiyar da zata yi ma zata tafi ne ba tare da sirrinta Waya ya fita ba, zata tafi ne ta barsu suna begenta har karshen rayuwarta don hakan shine babban burinta kuma ta riga ta tsara yadda zai kasance tuntuni, kawai tana jiran kammala cike abinda ke gabanta ne.

Don haka ta gaya min cewa tana so ta makantar da Hamida ne ta kuma gurgunta ta ta yadda ba Ma'aruf kadai ba, babu wani mahaluki da zai kalle ta da daraja a duniyar nan kuma zata yi haka ne ta hanyata, ta gaya min da hannu na zanyi hakan Amma."

Muryarta ta kai ?arshe da tsananin rawar da take fitowa kamar kuka ne ke shirin kwace mata,amma kuma duk da haka sai taji kamar ta Wauke wani dutse ne daga kirjinta, nauyin maganganun da ta furta na barinta kamar yadda iska ke Wiban yashi.

Kuma shirun da ya ratsa a cikin wayar, mai tsawo ne, tsawon da ba zata iya tantance shi ba don har sai da Hamida ta motsa a cinyarta ta gyara kwanciyar ta, daga bangaren layin gidan wayar kuwa, ta san bakinsu na ta washewa na ganin adadin cinikin da suke yi dasu, kuma abinda Amman ta furta bayan tsawon wannan lokacin shine.

"Alkawarin me tayi miki wannan karon?"

Ta shaki wata busashshiyar iska a cikin hancinta kafin tace.

"Na'am Amma?" Alamun bata gane ba.

"Alkawarin me tayi miki idan har hakan ya cika?"

Ta gane yanzu, amma bata gane me yasa shine abu na farko da Amman ta tambaya ba, amma duk da haka sai ta hadiye mamakinta sannan muryarta ta fito.

"Tace zata canja muku gida sannan ke da Baba zaku je aikin hajji wannan shekarar."

Sai kawai ta jiyo murmushin Amman kafin tace.

"Ashe ina da rabo a wadanda Allah ya kira zuwa dakinsa wannan shekarar Amina."

"Amma ban gane ba..."

"Kar ki damu zaki gane komai Amina, abinda zan gaya miki a yanzu kawai shine cewa babu abinda zai faru, babu abinda zai sami yarinyar nan, amma kuma a idanun Kilishi komai zai faru, zaki cika mata wannan aikin nata sannan kuma zata kaimu Makkan har da wannan canjin na gida ma!"

"Amma..."

"Kar ki ce komai a yanzu, bar ni kawai da tunani na har zuwa lokacin da zata kawo miki umarnin farko na abinda zaki yi. Yanzu ki gaya min ta tambaye ki wani abu game dashi a yau din?"

Amina ta haWiye tarin kalamai da kuma rudanin da bata san adadinsu ba a cikin kanta sanin cewa tunda Amman ta faWi haka babu wani bayanin da zata kara samu daga Amman a yanzu. Kuma abinda ta fada yanzu ta san shi din da take nufi Ma'aruf be, don bata taba kiran sunansa saboda haka sai kawai ta Waga kanta kamar tana kallonta sannan tace.

"Eh ta tambaye ni inda ya tafi kasancewar yau asabar."

"Sai kuma me?"

"Na gaya mata cewar suna bincike ne shi da abokin aikinsa game da wani abu da ya faru a kamfanin su."

"Me ya faru?"

"Yace min wani mutumi suke nema da yayi musu satar wasu tarin kudi masu yawa a kwaciyar nan da yayi na kwana biyu kawai."

Murmushin da Amma tayi wannan karon ya amsa sosai a vikin kunnen Amina kafin tace.

"Kin fahimta? Kin fahimci wannan ne aikin da Kilishi tace miki tana son yi a wajen aikinsa wanda tace miki bata bukatarsa a sannan?"

Ta gyada kanta da sauri.

"Na gane Amma nima na fahimta, shi yasa da ta tambaye ni na gaya mata gaskiya din nsji abinda zata ce, amma kuma abinda ta fada din ban gane masa ba."

"Me tace?"

Ta sake maimaita kalma biyun nan na Wazu. Amina ta gyara zaman wayar zuwa Waya kunnenta kafin tace.

"Dariya kawai tayi, tace wai ai da sun daina wahalar da kansu abinda suke nema yana wajen da ba zai taba fitowa ba, kuma sai da nayi tunanin sannan na gano cewa wajenta take nufi tunda ba zata taba faWa ba."

Amma ta sake yin shiru na wucewar wasu lokutan kafin muryarta ta sake fitowa.

"Me suka samo su game da mutumin?"

"Ban sani ba dai duka amma naji kamar suna waya da wani yana gaya masa cewa an kwatanta musu siffarsa ne kawai"

"Bani minti biyar, ina zuwa Amina."

Abinda ta fada kenan sannan ta kashe wayar ba tare da ta jira komai ba.

Amina ta rike wayar a hannunta, tana sake niya dukkan maganganun nasu kafin a hankali kuma tunaninta ya tsaya kan abu guda daya da bata shaidawa Amman, wannan abun da tun a farko ta boye mata na zancen cewa Kilishi bata yarda da wani zance na samun ciki a wajenta ba, a yau ma ta sake maimaita mata cewar ta cigaba da yin taka tsantsan da zuciyarta akan Ma'aruf, ta kawo ta ne don tayi mata aiki ba don ta zama matarsa ba.

Kalaman da suka kara sata jin wani abu na sauka a zuciyarta yana kara gaya mata cewa wannan yakinta ne, ta ?yale Amma a ciki ta nunawa Kilishi nata kalar kissar da lulluSin da bata isa ta yaye ba.

Da wannan tunanin, zuciyarta ta koma wajen jiran da Amman tace tayi,? fiye da komai zata so su fara samun mafita kamar yadda tayi alkawari wa rayuwar Ma'aruf, komai ya tsaya cak akanta, hatta hanyenta dake rawa a yanzu sun daina, ta kasa ko sake taba kan Hamida balle ta karasa kalbar dake jiranta, jira kawai take yi yayin da idanunta kallon wucewar lokaci a agogon wayar.

Minti goma bayan hakan wayar ta shiga gurzawa a hannunta da ?arfin vibration din dake jikinta, kuma ba tare da ta jira komai ba, ta danna wajen amsa kira ta kara ta a kunnenta.

"Amina..."

Muryar Amman ta fito da wani irin yanayi da ta kasa fassara shi.

"Na'am.." ta amsa a hankali tana jin yadda nauyin da take murna da tafiyarsa a Wazu ya sake dawowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login