Showing 72001 words to 75000 words out of 132946 words

Chapter 25 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1120

gabanta idanunsa na kare mata kallo.

"Me ya same ki?"

Shine abinda ya fara faWa kafin ?amshin turarensa ya zagaye ta, kuma duk da rikicewar da take ciki, sai da amon muryar tasa yasa taji wani abu kamar tayi kewarsa tsakanin jiya da yau din kawai, don haka gaisuwar da take da niyyar yi bata fito ba, sai kawai ta girgiza kanta tace.

"Babu komai zazzaSi kawai nake yi... Na, na warke ma, kawai ban fito bane yau shi yasa ban kawo maka abincin ba...."

Bayanin da ta fara cikin rawar murya ya katse a lokaci guda da Jawad yasa hannunsa akan wuyanta, sanyin fatarsa ya ratsa har cikin kanta, jikinta ya tsaya cak, numfashinta ya ?ame a cikin wuyanta, ya sake motsa hannun nasa yana ?ara zura yatsunsa cikin wuyanta...

"Wane magani kika sha?"

Muryarsa ta sake tambaya, tana kokarin dawo da ita cikin haiyacinta, sai kawai ta haWiye wani abu a makogwaron ta a hankali sannan ta girgiza masa kai, bai dauke hannun nasa ba ya cigaba da kallon ta da idanusa daue kara rikita ta sannan yace.

"Maamah ta san baki da lafiya?"

So take yi ta tashi amma ko yaya bata son yin motsin kar hijabin jikinta ya zame, rigar dake jikinta yar ?arama ce, irin ta bacci da ?anwarsa ta bata, da ita ta kwana sai da taji sanyi da asuba sannan ta jawo hijabin ta lulluSa, don haka sai ta sake girgiza kanta a hankali idanunta na kallon kasa.

Kamar ba zai Wauke hannun nasa ba sai kuma ya cire shi a hankali m, tana jin yadda yatsun nasa ke barin fatar ta.

"Taso mu tafi."

Ya fada yana mi?ewa kuma maimaikon ya juya sai ya tsaya akanta yana kallonta, kallon da yasa ba shiri ta mike tana kokarin riko hijabin nata kotawanne bangaren amma saboda yadda jikinta yake rawa kafarta ta take shi garin mikewa ba tare da ta sani ya kuwa tafi kasa gabadayansa.

Zuciyar Jawad ta buga a lokaci guda da idanunsa suka gane masa kayan jikin nata, sai kawai ya juya da sauri gabaWayansa yayin da ta koma ta zauna da sauri tana ?o?arin sake tattaro hijabin nata.

"Idan kin shirya ina waje."

Ya fadi hakan ba tare da ya sake juyowa ba sannan ya nufi hanyar fita, tana ji wadanda suka tsaye daga waje na yi masa a sauka lafiya, amma tsabar kunya, takaici da kuma rawar da jikinta yake yi ta kasa ko Wagowa.

Kuma fitarsa ke da wuya, abinda take jira ya faru, sauran matan nan suka shigo suka zagaye ta, masu shewa irin tasu ta ?abilu nayi masu tsokanarta nayi, har da masu cewa ta fada musu kalar asirin da take amfani dashi suma su samu.

Zuciyarta ta sake matsewa da takaicin maganganun su, tana jin cewa da zata iya asirin, da zata samu asirin da wanda zai canja rayuwarta gabadaya zata yi, wanda zai canja rayuwarta tun daga tushe ba a rana tsaka ba.


***

"Me yasa lokacin da suka fita baki zo kin gaya min ba?"

Hajiya Mardiyya ta tambaya tana kallon wata yar aikinta dake tsugunne a gabanta.

"Ai Hajiya na zata tafiya zasu yi, don tace min yau zata koma garinsu shi yasa nayi tunanin gida kawai za'a kaita."

Ta faWa cikin harshen turancinta na Pidgin, Hajiya Mardiyya tayi shiru tana kallonta ba?tare da ta san me zata ce ba, sai kawai ta tashi ta mike daga falon, ta nufi cikin dakinta inda ta bar wayarta akan mudubi.

Dole ne ta takawa Jawad birki, bai isa ya tozarta ta a idanun duniya ba, bayan sun gama shawara da ?ar uwarta akan ta ha?ura da yarinyar kawai ta maida ita garin su tun abubuwa basu Saci ba, sai kuma yazo ya fara shirin warware tufkar da take yi? Me yasa yake son rikito da duniyarta ne a kodayaushe? Me yasa ko sau Waya a rayuwarsa ba zai taSa bata matsayinta na mahaifiyarsa ba?

Hannunta ya kai kan wayar tana jin zuciyarta na fitar da zafin? da sanyin A.cn dakin bai isa ys kore shi ba, kuma kai tsaye hannunta ya danna nambar Jawad a cikin wajen kira sannan ta kara a kunnenta, tana jin karar bugun dake shiga cikin kunnenta kamar ba za'a Wauka ba...

"Assalamu alaikum Maamah..."

Muryasa ta shiga kunnenta a gabar da saka rai da tsinkewar kiran.

"Wa'alaikum salam... Jawad kana ina?"

"Ina asibiti." Ya bata amsa kai tsaye.

"Kai da wa?"

"Ni da Zainab, bata da lafiya Maamah kin sani?"

Wani takaici ya taso ya? kara lullube zuciyar Hajiya Mardiyya, ashe da gaske ne daukanta yayi suka fita har asibiti, da taji muryarsa bayan ya Wauka sai taji kamar zai ce mata yana office ne ko kuma wani waje daban.

"Jawad a wani hurumin zaka Wauki yarinya ka kaita asibiti? Ni ban san bata da lafiya bane sai kai?"

Hannunsa ne ya tsaya daga ?o?arin karbar receipt din da wata cashier ke kokarin miko masa bai karba din ba kawai ya tsaya yana sauraren mahaifiyar tasa a lokacin da ta cigaba da cewa.

"Bata gaya maka cewa yau zata koma garinsu bane? Ko bata gaya maka iyayenta sun aiko suna nemanta bane ko kuma kai baka da aikin da zaka tafi yi ne?"

A hankali idanunsa suka juya yana hango Zainab din da ya bari daga can kan wasu kujeru na jira, dogon hijabi ne sanye a jikinta, kalar ruwan hoda, fitilun wajen sun haska fuskarta tar da kuma manyan idanuwanta dake ta zarewa tana kalle kallen mutane da kuma abubuwan asibiti, kamar koyaushe, kamar duk lokacin da zai ganta wani abu ya motsa a zuciyarsa, sai kawai ya girgiza kansa sannan yace.

"Bata gaya min ba Maamah, abinda na sani kawai shine bata da lafiya yau don haka a ?yale ta, idan ta warke ni da kaina sai in kaita ta gaishe su..."

"Ba dawowa zata yi ba Jawad, aure iyayenta zasu yi mata..."

A lokavi guda shiru ya ratsa wayar a lokaci guda tsawon sakanni bai ce komai ba, wannan matar dake miko masa receipt ta fasa ta ajiye shi kawai akan tebur Win sannan ta juya ta cigaba aikinta, idanunsa suka tsaya akan Zainab din da a yanzu take kallonsa, yanayin fuskarta na nuna alamun tambaya tana son taji idan yana so ne ta taso.

Sai kawai yayi murmushi yace.

"Shikenan Maamah sai mun dawo."

Yana faWin haka ya kashe wayar ya maida ita cikin aljihunsa, sannan ba tare da ya sake tunawa da matar da kuma receipt Win ba yayi gaba kawai, ?afarsa ta Wauke shi har gaban Zainab Win da tayi saurin mi?ewa ganin ya taho.

Ya tsaya a daidai gabanta, yana kallon yadda ta sunkuyar da kanta bayan ya tsaya a gaban nata, yadda zuciyarta ke bugawa a cikin ?irjinta tana ji kamar zata fito ne ko kuma zai ji ta, Allah-Allah kawai yake yi yace su juya su tafi gida, don duk yadda zuciyarta ta san cewa yana kyautata mata ne har yanzu tana tsoron kasancewarta tare dashi, don bata san wane irin hukunci zata fuskanta a wajen mahaifiyarsa ba idan har ta san irin yadda yake kulawa da ita.

Sai dai a lokacin da take tunanin zai fadi abinda take jira Win, sai wasu kalaman suka fito saSanin hakan, wasu kalaman da suka dasa aya akan a wannan bangaren na rayuwarta.

Wasu kalaman da daga ita har Jawad din basu da masaniyar cewar tasirinsu yafi ?arfin dukkan wani ?alubalen da kwakwalarsu zata iya hangowa... Wasu kalaman da sune ?arshen dukkan wata wahala da wani ahali suka daWe suna fuskanta!? Kuma wasu kalaman da sune sune karshen talalar da ubangiji ya kaddara akan wata halittarsa!

"Zainab zaki aure ni?!"

***

_Kun yarda da Labarin Awwalu?_

_Kuna ganin zai tabbatarwa da Hajiya Salamatu zancensa?_

_Me ya faru ne a cikin wayar Hajiya Salamatu? Wane kira ne kuke tunanin sai a lokacin ya katse?_

_Ku gaya min Jawad na shirin kwance tarin abubuwan da shi kansa bai san adadinsu ba..._

_Kalaman da kwakwalarsa ta yanke masa a lokaci guda suna shirin bude mana tarin abubuwan da muka dade muna jira a labarin nan... Insha Allah._

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*??AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*16*

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka, akwai wata member Win group Win nan da ta rasa mijinta sati biyu da suka wuce, ina rokon mu saka shi cikin addu'o'in mu Allah ya ji?ansa da rahama ya bata ha?urin rashi da kuma bayan Waukan marayu, mu kuma Allah ya kyautata namu zuwan. Ameen.*

~~~~~

_I'm seeing the pain, seeing the pleasure...I love to hold you close, tonight and always..._


*#Tariyar baya.* *(Flashback.)*

"Na fahimci har yanzu da saura a harkar nan Kilishi, shi yasa kika ce zuciyarki ta kasa kwanciya... Amma kar ki damu, tunda kin iya da tarin abubuwan da kika shallake a baya waWannan ma ba zasu yi miki wahala ba, ki cigaba da tsarinki kawai, ina garin nan har sai kaya na sun ?are, don haka kar kiji komai."

Da haka wayar tasu ta ?are. Hajiya kilishi ta mikie ba tare da ta kula da cewar bata kashe kiran ba ta? fita daga dakin, kai tsaye falon ta nufa inda anan take jiyo hayaniyar da bata san dalilinta ba, ilai kuwa isarta ke da wuya ta tarad da su Zahra da Sahla tare da wasu kawayensu da suke makota su biyu suna faman bare kayan decorations daga cikin ledodinsu, kaya ne gasu nan fal-kala, sai faman Waga su suke yi suna kokarin ganin ta yadda za'ayi amfani dasu.

"Duk wadannan abubuwan na meye?"

Kai tsaye muryarta ta katse su ganin har ta tsaya a falon basu kula da ita ba. Dukkaninsu suka juyo a lokaci guda, ?awayen nasu suka shiga gaishe ta yayin da Sahla tace.

"Mami, Ya Samirah ce tace mu fito mata dasu, za'ayi decoration din tarar Ya Abdurrahim ne gobe...."

"Abdurrahim!

Sunan yayi amsa kuwwa a cikin kan kilishi a take, kwata-kwata ta manta da lissafin zuwan nasa, tinda suka ui maganar da Baffa bata kara tunawa ba sai yanzu, abubuwan dake saman kanta dama cikinsa suna da yawa, kuma ta riga ta sani cewa yaron ba matsalarta bane a yanzu, ko zai dawo ne da irinsa guda dari ta sani bai isa ya tsaya mata ko a gefen hanya ba balle ya tare mata wani abun.

Don ma an samu akasi ne, kwakwalarsa taso ta taSa tun a wancan lokacin, wannan kwakwalar tasa da tun yana karaminsa babu abinda take kange shi daga ganewa.

Tana tuna wannan ranar, tana tuna ta kamar jiya, lokacin da taje har makarantarsu ta islamiyya a lokacin, ta haWa baki da maigadin makarantar, idanunta na hango mata yadda hannyensa ke cusa damin kuWin da ta bashi cikin aljihunsa, da yadda bakinsa ke washewa yana faWin bata da matsala ya gane yaron da take biWa, yana bayanin yana kallon idanunta dake boye a bayan niqabin fuskarta, bai ko damu da sanin kamanni ko wani abu nata ba.

Har ya kawo mata yaron ta Wauke shi kamar yadda tace a motar da tazo tare da wasu ?an daba guda biyu da Awwalu ya haWa ta dasu, don ko Awwalun a wannan lokacin bata yarda ya san abinda take shirin yi ba.

_"Kar ku kashe shi, so nake kawai ayi min abinda ?wa?walarsa zata taSu..."_

Haka ta gayawa mutanen a wancan lokacin, don bata yi niyyar kashe shin ba, kuma haka suka yi mata, don bayan ansha nema hankalin jama'ar gidan dama na malaman sa gabaWaya ya tashi, an tsince shi ne yashe a cikin wani kango a sume jini na fita ta hancinsa da kuma kunnensa.

Aphasia.

Haka likitoci suka kira cutar da ta same shi, sunce gefen kwakwalar sa dake aiki da bangaren magana ne ya sami matsala sakamakon toshewar jini zuwa wajen, farkon rashin lafiyar tasa yana iya magana amma a gutsirtsire, cikin sautin da ba'a ma fahimtar abinda yake cewa duk da cewar da kankantarsa a lokacin.

Likitoci sun bada shawarar yadda za'a dinga taimaka masa maganar da yadda harshensa zai koma daidai don sun tabbatar da cewar babu wani magani kwakwara game da cutar amma da yake shi yaro ne mai zuciya, tun a lokacin ya?i bada haWin kan hakan, ya daina maganar ma gabaWaya babu yadda ba'ayi ba amma haka ya taso kowa yana kiransa Kurma, don ko makarantar da yake yi a can ?asar ma ta kurame ce irinsa.

"Mami fulawa ta kare, kuWin drawer kuma sun kare su ma..."

Muryar Samirah da ta fito daga kitchen ta fada a gabanta tana dawo da ita daga tunaninta. Ta juyo ta kalle ta.

"Sati Waya kenan fa dana ajiye kudin nan Samirah,yanzu har kin karar dasu?"

Da murmushi a fuskarta tace.

"Wallahi Mami, abubuwan ne wannan week din da yawa, kinga munyi abincin sadakar uku na jikar Mama Rabin nan data rasu, sannan ga wannan shirye-shiryen dawowar Ya Abdurrahim Win kuma, surprise party muke haWa masa tunda ya hana kowa zuwa can.."

"Amma ni duk ban san da wannan ba."

"Mami kwana biyu fa ba kya ko zama a gidan nan, kamar wani abu yana damunki shi yasa kawai muka ?yale ki..."

Da murmushi a fuskarta sanda ta faWi hakan, amma da ta san tasirin da kuma yadda suka shiga cikin kan Hajiya Kilishi da watakila bata yi wannan murmushin ba.

_.... Kamar wani abu yana damunki shi yasa muka kyale ki..._

Wannan wajen ya maimaita a cikin kan Hajiya Kilishi fiye da yadda zata iya ?irgawa a cikin sakannni kawai, ?arta ce wannan, ?ar da ta haifa a cikinta... Itace take gaya mata cewa sun ?yale ta saboda tana cikin damuwa, sun ?yale ta ba tare da sun damu su ji abinda ke damun nata ba a matsayinta na mahaifiyarsu.

?wakwalarta ta tariyo mata wani abu a lokacin, tabbas ba zata iya tuna rana guda da wani a cikin ?a?an nata ya taSa damuwa da damuwarta ba, Ma'aruf ne kawai... Ma'ruf ne kawai ke taSa nuna damuwarsa akanta idan har wani abu ya same ta, ko a yau ma s gajiye ya dawo yadsa ta fahimta daga muryarsa, smma ssi da ya kira ya gaishe ta ya gsya mata ya gaji ba zsi iya shigowa ba kafin ya shiga gidansa, amma? a vikin yan shekarun nan ba zata iya tuna rana guda da ta taSa ganin wata damuwa mai zurfi daga wajen ?a?an nata ba har kuwa waWanda ta yiwa aure yanzu, su kan dauki lokaci basu kira ta ba sau da yawa sai dai taji su suna waya dasu Samira.

Wani abu ya wuce daga makogwaronta yana son dasa mata wani abu da ba zsta taba yarda ba, don haka sai kawai ta gyada kanta sannan tace da Samiran dake tsaye tans kallonta.

"Bari na kawo miki, har da na cefanen wannan watan ma jiya Baffa ya aiko dashi kun fita."

"Yawwa Mami, Madallah."

Abinda tace kenan kawai sannan ta juya tana gayawa su Zahra abinda zasu yi. Sai itama ta juya tana jin kamar zuciyarta tayi nauyi da abinda ya faru, amma kuma
kwakwalarta ta cigaba da gaya mata cewa hakan ba komai bane, da zarar lokacin da zata kammala komai yazo, su da kansu zasu gane gatan da ta daWe tana yi musu, yaushe aka taSa halittar ?a?an da suka juyawa uwarsu baya a duniyar nan? Shaidan ne kawai ke kokarin cin galaba akanta.

Ta isa cikin dakinta lokacin da idonta ya kai kan wayar da ta bari akan gado, mitunan kiran na da suka yi da Hajiya Salamatu na nunawa akan fuskar wayar har yanzu, mamakin yadda akayi bata kashe ba kuma itama Salamatun bata lura ba ya kamata, sai kawai ta ?arasa ta Wauke ta, har zata kashe sai kuma taji wani abu kamar murya na magana don haka ta kara ta a kunnenta kuwa daidai lokacin da ta jiyo muryar Hajiya Salamatun daga can ciki tace.

_...a idon duniyar nan...!"_

Mamaki ya gifta a ranta na ma'anar hakan, amma sai wani gefen tunaninta ya bata cewar watakila hirarta ce kawai da wasu mutanen tunda gidan nata baya rabo da jama'a, don haka sai kawai ta kashe kiran ta ajiye wayar akan gadon sannan ta tafi daukowa Samirah kuWin.

Da ace dan adam yana da ikon dawo da lokaci baya zuwa sanda yake so, da tabbas Kilishi zata so dawo da wannan ranar kuma wannan lokacin fiye da sau dubu a rayuwarta.


***

*?arfe tara na safiya.*

Amina ta kunna gas Win da ta Waura frying pan da mai a cikinsa, idanunta suka tsaya akan man har lokacin da ya fara zafi, yayi zafin yama fara shirin ?onewa kafin ta farga ta zuba haWin ?wan da ta haWa akai.

Minti talatin kenan, minti talatin tun bayan dawowarsu daga asibiti, don a Wazu da asuban nan bayan ta gaya masa abinda take tunani yace ta shirya su fita, ya kira Munaya yace tazo ta dauki Hamida zasu fita.

Tun gari bai gama haske ba ta shigo ta dauke ta zuwa cikin gidan tana bacci ma bata san me ake yi ba, kuma tana ta tambayar inda zasu je amma bai ce mata komai ba sai da suka tsaya a gaban wani Wan karamin Private asibiti da a samansa aka rubuta 24hours, (awa ashirin da hudu.).

A asibitin aka haWa ta da wata Nurse bayan ya yi musu bayani, kuma minti takatin bayan hakan aka tabbatar musu da abinda suka zo nema cewar da gaske tana da cikin.

Ta sani, tunda Amma ta gaya mata ta yarda kuma tana ji a jikinta ma, amma a wannan lokacin sai take ji kamar wani sabon labari ne, kamar an tabbatar mata da wani abu ne da a baya yake yawo a iska, kuma tun a cikin asibitin nan ta sani kwatanta irin murnar da ta gani a idanun Ma'aruf, wani abu ne da bata tunanin yana da geji, sai kuma tazo ta tankwaSe komai a lokaci guda da ta gaya masa cewa bata so zancen ya fita ko'ina tafi son ya barshi a tsakaninsu.

Bata so ayi wani na ukunsu da zai sani, ta gaya masa tana da dalilinta kuma zai san hakan a gaba, amma bai fahimce ta ba, tayi kokarin ?ara yi masa bayanin amma sai kawai yace ta kyale shi kuma a wannan lokacin da ta kalli idanun nasa ta san babu abinda ya fi dacewa illa ta kyale shin, don ta kasa tantance tsakanin farin ciki da kuma rashin fahimtar tata wanne yafi yawa a cikinsu.

Ta ?arasa soya ?wan gabaWaya, ta fito da dankalin da ta soya a deep fryer, ta hada komai waje guda tare da kayan shan tea, sannan ta koma ta kwaba fulawa da kwai da butter tayi wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login