Showing 117001 words to 120000 words out of 132946 words

Chapter 40 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1145

zagayen halin da take ciki, ya tuno mata da dukkan abinda ya faru kafin sumanta da ma irin tashin hankalin da ta shiga...

Ko kuma tashin hankalin da har a yanzu ta farka a cikinsa, tunda bata san me ya faru ba har a lokacin, bata san ina Ma'aruf yake ba sannan bata san a wane hali yake ciki ba, tun a lokacin aga yanayin fuskokin su Munayan da suka shigo wajenta tunaninta ya gaya mata cewa abinda ya faru ba labari ne mai daWi ba, sannan a lokacin ta ?ara tabbatar da cewar da gaske tunaninta hakan ne tunda bata ganshi ba.

Ta sake bude idonta a hankali, lokaci ya nuna mata ?arfe goma sha biyu na safiya wanda hakan ya tabbatar mata cewar har a yanzu tana cikin wannan ranar ne tunda da sassafe ne lokacin da su Munaya suka zo suka same ta.

?ofar Wakin ta buWe a sannan, Aunty Ma'u ta shigo bayanta goye da ?ar ?aramar ?ar ta, hannunta da rike da wani a kwandon kwanukan abinci.

Amma ta amsa sallamarta tana juyawa.

"Bata farka ba dai ko?"

Ta tambaya tun kafin ta karaso.

"A'a har yanzu, amma Nurse din da ta fita tace ba zata dade ba zata farka."

Aunty Ma'u ta ajiye kwandon abincin sannan ta sauko hoyon yar tata dake bacci Amma ta karbe ta.

"Su Tanti suna hanya, tace akan kwana suka hadu da Safiyya yanzu zasu taho."

Kuma sai da ta zauna daga gefen gadon sannan tace.

"Ya muka ji da wadannan abubuwa da suka faru Amma? Labari haka rana tsaka babu daWin ji..."

Amma ta gyara kan yarinyar dake cinyarta tace.

"Wallahi Ma'u muma?haka muka tashi da kira wai an kawo ta asibiti ta suma, yanzu su Maryam suka koma su ma tare da yariyar dake wajenta Hamida, don likitan yace da ta farka zamu iya tafiya, rashin kwarin jikinta ne yasa suman ya same ta a lokaci guda."

Aunty Ma'u ta gyada kanta tana sake kallon Aminan dake kallonta ta tsakanin gashin idonta.

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un...? ?ari fa akace ta kusa yi Amma, wannan wane irin labari suka gaya mata?"

"Su waWanda muka tarar anan sun ce ai tun kafin ma su san wannnan al'amarin aka kawo ta asibitin.? Komai ya rikice ne kawai Ma'u don ita kanta Tantin da muka yi waya ban iya gaya mata wani abu ba tunda har yanzu su ma babu wanda ya gama sanin abinda ake ciki, Munayan tace min sun san dai an tafi da ita Kilshin wajen ?ansanda daga asibitin nan, shi kuma an kwantar dashi."

Aunty Ma'u ta gyada kanta.

"Irin wannan sai an kwana biyu dama za'a san me ake ciki tunda su kansu yanzu hankalinsu ba'a jikinsu yake ba."

Amma tace.

"Duk sun taho ma, har da ?arta daya Sameerah, suran ne suke can gida tare da wasu yanuwansu don Mama Rabin da na hadu da ita tace gidan ya zama kamar na makoki daga safiya zuwa yau..."

"Allah ya kyauta, ni wallahi banyi mamaki ba Amma, a wannan zamanin jama'ar da suke da fuska biyu wajen cutar al'umma suna da yawa, kuma ba ma wai sai a wani babban abu ba, wani ko ba zai samu komai ba idan ya nuna baya kaunar ka a bayan idonka zai ji daWi, kawai dai ita nata yayi yawa ne, cuta da kuma zaluntar ciki tafi karfin tunanin mutane ire-irenta da yawa.."

Amma ta yi shiru kafin tace.

"Zancen babu daWin ji Ma'u, iya wanda ya fito a yanzu kaWai balle kuma abinda zai fito daga baya, ?an uwanta ma wasu basu yarda ba, abin ne kamar mafarki, kamar labari...? Sai dai addu'a kawai."

"Allah ya kyauta, Allah ya basu hakurin Waukar hakan ya bi musu hakkinsu, sai a godewa Allah don watakila da lokaci ya ja, zata iya aikata fiye da wanda tayi ma a baya."

"Wannan haka yake, don al'amarin yafi karfin tunaninki, Allah ya bata fikira da kuma dabarar da ta bari shaidan ya karbi linzaminsu."

?walla ta cika idanun Amina a lokacin tana hana mata ganinsu bakiWaya sannan tunaninta ya cilla kan maganganunsu tan son fahimtar da kanta abinda bata gane ba... su waye suka yi hatsari? Wanda take nufi an kawo asibitin Ma'aruf ne? Abinda su Munaya zasu gaya mata kenan? Abinda ta kasa tsayawa ta ji kenan? An kama wani? Hajiya Kilishi ce? To ta yaya hatsarin ya faru? Komai yazo ?arshe kenan? A wane hali su Samirah ke ciki? Baffa... Sauran mutanen gidan.... Ma'aruf ma...

Wadannan tambayoyin su suka yi ta haskawa a cikin kanta har lokacin da taji Amman tace.

"Bari na sake lekawa can inda aka kwantar dashi naga me ake ciki dama jiran ?arasowar ku nake kar a bar ta ita kaWai."

Ta faWi hakan sannan ta mi?e tsaye ta juya kan wata kujera daga can jikin bango ta ajiye yarinyar.

Amina bata ga sanda ta fita ba ta dai ji ?arar rufewar ?ofar da kuma muryar Aunty Ma'un bayan nan tana kwatance wa su Tantin da suka kira ta a waya, don haka bata bude idanunta ba sai a daidai lokacin da ta kai ?arshe a wayar wanda hakan yasa tana bude idon ta kula da ita

"Alhamdlilah, Amina kin tashi? Sannu..."

Ta faWa kai tsaye tana ?arasowa gaban gadon.

"Sannu Amina, sannu...."

Ta sake faWa tana rike hannunta wanda ba'a saka masa allurar drip Win da take ji a jikinta ba, sai tayi kokarin mi?ewa a hankali tana kama hannun Auntyn Ma'un sosai.

"Sannu..."

Ta ?ara faWa tana ri?e ta.

Bakinta a rabe yake kaWan amma bata ce komai ba... Wani abu ya wuce ta ma?ogwaronta tana ?o?arin gyara zamanta.

"Bari in zubo miki abinci ki iara jin kargin jikinki.."

Aunty Ma'u ta sake faWa tana ?o?arin juyawa, sai tayi saurin kamo hannunta da sauri tana kallon ta.

"Aunty me ya faru? Su waye suka yi hatsari?"

Muryarta ta fito a bushe kamar yadda lebbenta yake. Aunty Ma'u ta girgiza kanta.

"Bari ki fara cin wani abu? Amina..."

"Aunty dan Allah..."

Ta katse ta tun kafin ta ?arasa. Tana jin yadda wani abu kamar kwalla na kokarin cika idanunta yayin da bugun zuciyarta ke dokawa ta yadda bata tunanin ko yawu zai iya wucewa ta makogwaron nata.

Sai kawai Aunty Ma'un ta dawo ta zauna a gefen gadon ba tare da ta saki hannunta ba sannan tana kalonta sosai tace.

"Ma'aruf ne yayi hatsari tare da Hajiya Kilishi Amina, amma ba wani abu ne ya same shi ba, jikin nasa da sauki, kar ki daga hankalinki sun ce babu abinda ya same shi... Ki samu ki ci wani abu yanzu, Amma tace za'a iya sallamar ki a yau, sai mu je ki ganshi...."

Abinda ta fada mata kenan, abinda ta rude ta dashi har ta kwantar da hankalinta ta iya cin wani abu a abincin da ta kawo ba tare da ta san cewa babu zance Waya daga da yake gaskiya ba a duk abinda ta fada.

Don bayan Amma ta dawo har kuma an kira likita ya sallame ta, tun daga hanyar zuwa wajen ta fahimci cewar al'amarin yafi karfin yadda ta lissafa shi... Babu kowa a wajen lokacin da suka isa, su Hajiya Maimuna da duk dimbin jama'ar da suka taru a wajen lokacin da aka kawo shi duk sun koma gida, can gidan da a yanzu ya koma kamar gidan zaman makoki saboda ?arancin tashin hankalin da ya wanzu a cikinsa.

Don haka ita kadai aka bari ta shiga wajen yayin da su Amma suka tsaya daga waje... Kuma Amma ce? ma ta danyi mata bayanin abinda ya same da taji daga wajen su Hajiya Maimuna lokacin da tazo ta same su... Likitocin sun ce bugun zuciyarsa baya tafiya daidai, sannan ya farka sau biyu amma duka ba'a haiyacinsa yake ba... Sannan bayan haka numfashinsa ma baya iya fita daidai (Respiratory insufficiency).

Bata san tsawon mintunan da ta shafe tsaye a wajen ba,ta san dai kawai lokaci mai tsawo ya tafi zuciyarta na ta sake-sake da tunanin ayyana halin da Ma'aruf ko kuma sauran ahalin gidn ke ciki kafin wata Nurse ta gaya mata cewa su Amman dake waje suna jiranta.

?afafunta suka dauke ta zuwa waje, dogon koridon asibitin inda t barsu a zaune, dogon hijabi ne a jikinta na Maryam wanda Baba ya dawo daga baya ya kawo mata, ta fita daidai lokacin da su Amman ke gisawa da Ishaq da kuma Abdurrahim wanda suka ?araso a lokacin, kuma kallon Ishaq din kawai tayi taji kwalla ta cika idanunta don haka kanta a sunkuye ta karaso gabansu sanda suka shiga gaishe ta da jiki shi da Abdurrahim Win da kawai Wago mata hannu yayi.

Ta share hawayenta da bayan hannu sanda Amma ke gaya musu cewa ta kira su Hajiya Maimuna babu wanda ya Waga idan yaje yace musu zasu tafi da ita gida zuwa jibi don ta kara jin daWin jikinta tunda Hamida ma na can tare dasu Maryam, Ishaq Win ya amsa amma ko daga muryarsa kaWai Amina ta san cewar har yanzu ba'a haiyacinsa yake sosai ba, tashin hankalin da shi da kuma zagayen al'ummar dake gefensa ke ciki ya isa ya sa shi a kowanne irin hali.

Kowanne irin halin da mutum guda daya yayi? sandinsa ga tarin mutnen da a yanzu ita kanta bata san adadinsu ba....

Kilishi....!


****

Tana zaune akan kujerar da teburi ya raba ta da wadda Wansandan dake kallonta ke zaune.

"Hajiya gwara ki buWe baki kiyi bayani kawai, komai yazo karshe, mun kama duk wani wanda kike mu'amala dashi a harkar ki, hatta sabon yaron ki Sadik Awwalu yayi mana kwatance munjeun taho dashi, sannan mun kama likitan da kika hada baki dashi a asibiti ma da cewar kin makance, so ki bude baki ki yarda da laifinki, Shari'a sabanin hankali ce da za'a iya yi miki rangwame, baki da kowa kuma baki da komai a yanzu, don bana tunanin koa cikin iyalanki ko kuma yanuwanki akwai mai bin goyon bayan ki a yanzu.... Zai fi kyau ki sallama ki saukaka mana aiki Hajiya..."

Dan sandan yayi dukkan wannan bayanin yana kallon Hajiya Kilishi, yana kallon fuskarta da take manne da baneji a wajaje da yawa da kuma karyayyen hannunta wanda aka sakale shi ta wuya bayan anyi mata gyara, idanunta a tsaye suke cak!

A tsaye tana kallonsa, tsawon sakan Waya biyu, uku... Kafin ya mayar da kansa kan file din dake bude a gabansa wanda akan farar takardar dake kai, jerin laifukan da ake zarginta dasu ne wanda tun farkon suka rubuta bayan an tabbatar da kama ta da kwayoyin nan da kuma wanda a yanzu suka ?ara samu daga bakin yanuwanta bayan hatsarin da ta samu na biyu.

Baki da kowa kuma baki da komai...!

Sune kalaman dake maimaitawa a cikin kwakwalar Kilishi, suk sae dawowa suna komawa baya a lokacin... Tun bayan lokacin da Ma'aruf ya fitar da ita daga asibitin nan, tun daga lokacin tunaninta ya tsaya, komai ya faru ne a idanunta kamar tatsuniya, kamar wani mummunan labarin dake faruwa a cikin mafarkin yaro, bata gama warware zaren daya kulle ta a cikin al'amarin cewa yansanda na jire da ita suna nemanta ba, batagama lissafa hanyar mafitar ta da ta fara budewa ba,bata yi komai ba,tana cikin zagaye guda daya nesa kuma ga abinda zata ya kira da tashin hankalin duniya da kuma lahira ya riske ta.

Jiya rana ce da bata taSa tunanin tunanin Allah zai haiccce ta ba a duniyar nan, a dukkan tsare-tsare da kuma lissafin da a tsawon rayuwarta bata taSa hangen irin abinda ta gani ba a jiya, tana tsara komai kuma komai din yana tafiya daidai, kawarta Salamatu ce ma kawai kan tuna mata da cewar a duniya take ba'a aljanna ba cewar wani abun zai iya zuwa mata a karkace, amma ko yazo din, tana daga kwance take sa hannun guda ta gyara shi.

Alah ya bata tarin nasarori a rayuwar nan, bata jin akwai abinda ta taba zanawa zuciyarta da bai faru ba, bata jin ta taba ko da hasashen manufarta ne kuma hakan bai kasance ba, to dan me yasa sai a yanzu da rana tsaka kawa komai zai gargitse mata kuma ta yarda?

Ta yarda ta rasa Ma'aruf, ta rasa shi ta rasa kulawa da kuma ?aunarsa. Babu kalamansa ko a cikin kanta, ta ji su a lokacin da ya fade su kuma ta barsu a wajen, babu abinda ta dauko sai ciwo da kuma takaicin rasa shi da tayi ta wannan hanyar a raywarta, ta shirya dama, ta shirya barinsa don haka ta dade tana ywa zuciyar tata tanadi na wasu abubuwa da zasu dauke hankalinta bayan ta bar cikin rayuwarsu, amma da hakan ya faru a lokacin da bata shirya ba sai ya dake ta da tsananin tashin hankalin da bata ?ara ganin wani abu da ya tsorata ta ba bayan hakan ba.

Ko sanda ya danna kan motar suka tafi suka daki bishyar nan, bata ji tana tsoron mutuwa kamar tashin hankalin cewa an riga bude ainihin kammaninta a idanunsa ba.

Da kuma sanda ta kalli idanun su Baffa, Baba Usman, Ishaq, abokin Ma'ruf mai suna Faruq da kuma Abdurrahim... Ta kalli idanunsu ne tana jin zuciyar fayau yayin da tunaninta yake wasai, don tunda zuciyarta ta karSi tashin hankalin wajen Ma'aruf bata tunanin kuma akwai wani abu a duniyar nan da zuciyar tata zata sake rusunna masa, hatta Baffan kuwa, hatta shi din da ya zame mata tsani kuma hanya wajen aikata dukkan abinda ta wanzar a rayuwarta.

Tana kallon kowa ne kawai tana kuma jin abinda suke cewa, amma yadda bata furtawa Ma'aruf ko da kalma guda ba, haka babu abinda tace har wayewar garin yau, abu daya kawai take so ta yarda dashi shine cewar ba zata yi biyu babu ba, ba zata rasa Ma'aruf ta kunyata a idon duniya a rana guda ba sannan kuma ta rasa burin rayuwarta ba, ba zata taSa iyawa ba, ba zata yarda an zo gaSar da zata je ?asa ba kamar yadda ta shar'antawa kanta a baya ba, har yanzu tana da yardar cewar damarta bata ?are ba, dole ne ta fidda kanta kamar yadda ta sa ba.

Dan sandan yace bata da kowa a yanzu,ta yarda, ta yarda da hakan... Don tun da ta rasa yardar Ma'aruf ta sani cewa ko yardar ?a?an ta ba zata samu a yanzu ba, don haka ta yarda zata barsu, zata bar kowa nata sannan zata bar kowa da ta sani, abinda bata yarda ba shine da yace bata da komai, wannan ne zuciyarta bata amsa masa ba don ita ta san tana da abinda zata kare kanta ko a gaban wane alkali ne a duniyar nan.

Amma ba za'a kai nan ba ma, ba zata je gaban kowanne alkalin ba, zata yi nisane da kowa, zata yi nisa zuwa wani waje da zata kafa sabuwar rayuwarta, sabuwar rayuwar da ta san a cikin lokacin da zai ja mata... Dole ne yayanta zasu dawo gare ta, dole ne watarana zasu juyo su waiwaye ta, don meye yake raba ya'ya da uwarsu a duniyar nan?!

Sai kawai ta mika hannunta mai lafiyar ta janyo file din dake gaban Wan sanda, ya dago ya bita da kallo fuskarsa na shaida mamaki da kuma tunanin abinda take shirin yi, ta ajiye file din sannan ta sake mika hannunta alamun ya bata biron da yake rike dashi, sakan daya, biyu... Kamar ba zai bata ba sai kuma kawai ya mika ma tan, bayan ta karba yana kallon yadda yatsunta dama rubutun da take yi ke rawa, rawar dake shaida rikicewar da yanayinta ke Soyewa.

Lambobi ne, lambobi ta rubuta guda goma wanda ba sai ya tambaya ba ya san lambar asusun banki ne (account number), ta ajiye biron akan file din sannan ta sake turo masa shi gabansa.

Idonsa ya kalli lambobin sannan ya dago ya sake kallonta, a lokacin ne kuma tayi magana ta faWi abinda ba ga Wansandan ba kadai, har ga ita kanta ya tabbatar mata da cewar har yanzu tana nan a matsayin Kilishinta.... Tanan bata canja ba!

"Akwai kudi sama da miliyan dari huWu a cikin account din nan, ka taimake ni in fita daga wannan wajen, ka taimake ni inyi nisa daga dukkan wadannan matsalolin dake rubuce a cikin file dinka, ni kuma nayi alkawarin zan baka rabin kudin da nake dashi, zan gyara rayuwarka ta yadda har ka koma ga ubangijinka ba zaka taba sanin Wacin Babu ba!"

Ta kai karshe a lokacin da idanun Wan sandan ke kallonta da wani irin yanayi mai wuyar fassara a lokaci guda!

***

A cikin Wakin asibitin ba ka jin komai sai ?arar kaWawar iskar Acn da ya kaure ko'ina.

Hajiya Mardiyya ta girgiza kanta ri?e da wayar dake kare a kunnenta kafin tace.

"Kar ku damu Khadija, ki bawa su Innan ma hakuri, tahowarmu ba zata wuce gobe zuwa jibi ba insha Allah, ni ban san haka wannan asibitin yake ba da muka dauko ta wancan na gwamnatin muka kawo ta nan, su bamu refferal kawai abu na neman gagara... Ashraf dai yace yayi magana da likitan dazu, ni ko bai yarda ba zan dauko ta ne kawai mu dawo ba zan jira ba."

Ta gyada kanta sannan ta sake cewa.

"Eh, Ahmad ne ya taho yau, da asuba ya kira ni yace Babansu yace yazo ya kawo min sa?o... Amma shi kadai ya taho banda sauran."

Wadda suke wayar a ciki ta amsa kafin ta ta lashe wayar tana ajiye ta a gefen bedside drawer dake kusa da gadon, kusa da gadon da Rukayya ke kwance idanunta a rufe.

Kusan awa guda kenan da ta samu bacci, awa guda bayan ta farka da tarin surutan da a ciki basa iya gane komai sai sunan Hamida ?arta da kuma Hajiyan Sudan da take ambata, Ashraf yace zai iya yiwuwa shine abu na ?arshe da ta dinga fada lokacin da hatsarin ya faru, ta ga Hajiyan Sudan din a wancan asibitin na farko da suka je dauko Rukyya, ita bata ganta ba kuma bata bari ta ganta din ba, babu kowa a wajenta kafafunta na karye duka biyun an nade su da bandeji an kuma dage su zuwa sama.

Tana ji wata Nurse na faWan cewar har yanzu ba'a sami wani danuwanta da zai zo ya biya kudin treatment da akayi mata ba... Bata ce komai ba suka biya kudin Rukayyan kawai suka karbi sallama suka juyo.

Don abu na karshe da zata yi a rashin hankalinta shine ta nuna wata mu'amala tsakaninta da Hajiyan Sudan Win a gaban Ashraf, ta sani kashinta ne zai bushe idan har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login