Showing 21001 words to 24000 words out of 132946 words

Chapter 8 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1154

lumsassaun idanunsa suka tsaya akanta ba tare da yace komai ko kuma ya kifta su ba, zuciyarta ta shiga tsere a kirjinta, don duk da ta san rashin lafiya ce tasa idanunsa suka koma hakan, tana jin tasirin yanayinsu har kasan zuciyarta.

"Kin goge numbers Win nan?"

Ya sake tambaya a hankali, tayi shiru na wasu sakanni tana son ta tuno wadanne nambobi yake fada kafin ta tuna ranar da yace mata ta kwashe wasu nambobi daga wayar da ya bata zuwa ta hannunsa lokacin da suna hanyar dawowa daga jigawa.

"A'a suna nan a cikin wayar har yanzu."? Ta faWa a hankali, kamar idan ta Waga muryar tata tana tsoron zata fama masa wani ciwon ne.

Kuma saboda kokari sai da ya daga kansa sau biyu sannan yace.

"Akwai number Ishaq a ciki, ki kira shi kice masa yazo ya fitar dani daga nan."

Ta daga kanta sau daya sannan tayi kokarin? zare hannunta daga cikin nasa a hankali kafin ta mike yayin da ya maida idanunsa ya sake rufe du.

Akan kujerar dakin ta ajiye wayar tun bayan da alarm din Asuba ya tashe ta, don haka ta dauko ta ta shiga nenan nambar Ishaq din. Bugu daya biyu, uku aka dauka.

"Ma'aruf..."

Taji muryarsa ta kira sunan da manaki da kuma kuma kokwanto bayan saurin dske cikinta. Sai idonta ta koma kan Ma'aruf din da har yanzu idanunsa ke rufe sannan tace.

"Ba shi bane,? amma dai ya farka."

Jin muryar tata yasa taji kamar yayi ajiyar zuciya kafin ya sake tambaya.

"Kin tabbata ya farka?"

Ta daga kanta.

"Eh, shi yace in kira ka ma kazo ka maida shi gida, yace baya son zama anan."

"Kin kira Nurses din wajen?"

"A'a kai yace in fara kira tukunna."

Yayi shiru na wasu da?i?ai kafin yace.

"Bashi wayar."

Sai ta taso a hankali ?afafunta na taka laushin carpet Win wajen kafin ta isa ta tsugunna daidai gabansa, kuma kamar yaji ta ya sake buWe idanunsa wannan karin sosai a cikin nata.

"Zaiyi magana da kai." Bata san lokacin da fatar bakinta ta fadi hakan ba.

"Kin gaya masa abinda nace?"

Har yanzu sautin muryarsa a hankali yake fitowa, ta daga kai tana kasa janye idanunta daga cikin nasan, sai yace.

"Ki kashe wayar kawai."

Ta dan tsaya kaWan don ta tabbata Ishaq din daje cikin wayar yaji, amma ga mamakinta sai kawai taji shima yace.

"Rabu dashi gani nan zuwa."

Daga haka bai kara cewa komai ba kiran ya katse. Ta ajiye watar a gefe tana ganin yadda fatar idanun nasa ke sauka a hankali girmansu na kara raguwa, amma kuma duk da haka ita yake kallo.

"Zaka ci wani abun? Ko tea?" Ta tambaya tana ganin wautar ta, don a yanayinsa kowa ya kalle shi ya san bai gama dawowa haiyacinsa ba, kuma sai ya sake girgiza mata kansa sannan yace.

"Just stay Amina..."

Abinda ya fada kenan kafin idanun nasa su ?ara rufewa a lokaci guda, ta tsaya kusan sakanni biyar tana kallonsa kafin tajo tana son sake rike hannun nasa, don bata san me zata yi ba ma idan ta tashi.

Don haka haka ta mi?o shi ta riko nasa? a hankali, kuma ga mamakinta sai taji ya kara rike su shima, yana ratsa yatsunsa tsakanin nata sanyin dake jikinsu ya ratsa farar ta kamar dazu, sai kawai ta matso da kanta ta kwantar dashi a gefe gadon itama, tana kallon fuskarsa yayin da idanunta ke ?iftawa a hankali.

***

*Awanni biyu bayan hakan.*

"Mami ni na san Ma'aruf, wallahi idan ya farka ya sake ganinsa a wajen nan abinda zai biyo baya zai fi muni akan wanda ya faru jiya."

Ishaq ya fada lokacin da yake tsaye a kofar dakin, yayin da daga ciki wasu Nurses ne guda uku matsbiyu da namji daya ke kokarin dora Ma'aruf akan wani gado mai taya da za'a fita dashi.

Amina na tsaye daga gefensu ri?e da jakar ?an kayayyakin da aka kawo musu idonta yabi hannun Waya Nurse din da ta riko kansa da kallo, tana kallon yadda hannunta ya nutse cikin gashin kansa, wani abu ya motsa a cikin zuciyarta.

Sai kawai ta juya tana sauraren Ishaq Win dake cigaba da yiwa Mami bayanin da yasa dole ya nemi sallamar wa Ma'aruf, yana rokonta akan ta kira Baffa tayi masa bayani akan cewar ya bari a dawo da Ma'aruf gida don yanzu suka gama waya dashi yan fadan cewar don me ya biyewa Ma'aruf Win yace a sallame shi, saboda kawai yace baya son zama a asibitin.

Kuma bai sani bane amma ita kanta Mamin bata so hakan ba, da zata sami dama nata ?orafin zata yi itama. Don kamar yadda ta faWa mata a yau ne zata aiwatar da koma meye kudirinta, kuma abu na karshe da zata so shine ace Ma'aruf? baiyi nisan daga gare ta ba ta yadda ba zai iya kawo mata giftawar wata matsala ba komai kankantar ta.

Ta maida wayarta jaka lokacin da Nurses din nan suka shiga tura gadon da suka Wora Ma'aruf Win dake bacci har yanzu, don tun bayan wannan farkawar, bai kara bude idanunsa ba.

"Amina."

Muryar Ishaq da ya karaso cikin Wakin bayan fitar Nurses fin tasa ta dawo dq hankalinta kansa.

"Bai ce miki komai ba bayan sakon da kika bani lokacin da ya farka?"

Ta girgiza kanta a hankali.

"Cewa kawai yayi in gaya maka kazo ka fitar dashi, kuma bayan kiran ya katse ma bai sake cewa komai ba."

Ta gyada kansa yana maida wayarsa cikin aljihu.

Shiru ya ratsa na dakika biyu kawsi kagin ymuryarsa ta sake fitowa.

"Mun gode sosai da abinda kika yi Amina, this is the first time da wani ya taba zama da Ma'aruf a irin wannan yanayin bayan ni."

Bata san me zata ce ba, don haka ta gyada kanta a hankali tana kallon jakar hannunta da ta rike. Ya juya ya fita daga dakin har a lokacin bata dago ba, rayawa take a zuciyarta cewa idan har daga yanzu za'a fara yi mata godiya akan duk abinda zata yi, watakila za'a zo lokacin da za'a rasa wajen ajiye godiyar ma.

****

Hajiya kilishi ta tsirawa sakon da ya shigo wayarta ta nambar Awwalu ido, ta karanta ta sake karanta yadda yake gaya mata dukkan tsarindu ya tafi daidsi lokaci kawai yske jiracda kira ta kafin wani irin murmushi ya subuce a bakinta.

Me yasa take mantawa ne wai? Itace fa, itace wannan Kilishin da ba ta taba saka abu a gaba bata cimmasa ba, to don me kuma a yanzu take iya saka kokwanto a ranta? Me yasa take yiwa komai tunani biyu bayan gashi Aminar ma ta riga ta sami kanta.

_Saboda faruwar komai yana sauri da yawa..._

Wani gefen tunaninta ya ambata mata amma sai tayi cilli dashi gefen da ya fito a lokaci guda, ai yarinyar ta gama tsorata da ita ta sani, ta gaya mata cewar taSa dan'uwanta da tayi ba karamin abu bane da ba za ta so a sake irinsa ba, don haka ta riga ta gama yarda da ita, tunda har ta iya aikata wannan umarnin da ta bata a kudundune, umarnin da yaci sunan lauje cikin nadi, amma kuma tsaf cikin hikimarta ta ware nadin ta fidda laujen cikin sauki.

Don haka bata da sauran matsala ta sani, ko an dawo da Ma'aruf gidan umarni kawai zata bata na cewar kar ta sake ta bari ya fito, da wannan ta san zasu iya gama komai ita da Awwalu kafin jibi, tunda ko Baffa sai gobe zasu dawo suma.

Ta sake wani murmushin a hankali tana hango lissafinta. Tazarar fa kaWan ce, saura kaWan su ?arasa ga ?arshe inda komai zai fashe, taji tana taya Amina murnar shigowa cikinsu, don wahalar da zata yi kadan ce, ita da Awwalu sun daWe suna tsarawa da gina komai bi da bi.

Wayarta tayi kara a lokacin, Awwalu ne, ta dauka ta kara a kunnenta,

"Hajiya ki fito yanzu komai ya kammala."

Ta gyada kanta ba tare da ta amsa a fili ba.

Ta kashe wayar tana wani murmushi sannan ta jawo mayafinta, ita da dawowa gidan kuma sai lokacin da ta kammala kaso mafi yawa na cikar burinta.

Abinda bata sani ba shine, ubangiji ya kadarta tafiyarta a wannan lokacin ne don faruwar wani abu da tunaninta bai taba hango mata ba.

****

*Karfe biyar da rabi na wannan ranar.*

Karo na farko a rayuwar Ma'aruf da ya taSa bude idanunsa cikin irin wannan yanayin yaga ?anuwansa zagaye dashi fal, Awa kusan uku kenan tun bayan farkawarsa amma har yanzu zuciyarsa ta kasa ?arasa yarda da ganinsu gabadaya tare dashi kuma ba a ko'ina ba a cikin gidansa.

Samira ce ta gaya masa cewar Amina ce ta sanar dasu an dawo gida don haka tun da rana kafin ya farka suka zo har dasu Salma, Shukra da Safiyya wanda suka zo a ranar, ga dadin dadawa Inna Danejo da itama Mama Rabi ta rako ta tun daga cikin gidan har nan.

Tana zaune daga gefensa inda aka kwantar dashi a falon tana ta karanto tarin addu'o'i daga cikin carbin ta take ja tana gaya masa cewar rubutu zata sa ayi masa na Alkur'ani gabaWaya don? ita ta gaji da yawan maganin asibitin da har yau bata ga amfaninsa ba.

Kuma tun da Ma'aruf yake a rayuwarsa, tun daga lokacin da ya sami ciwon nan, idan har bashi da lafiya ya sani cewar sai dai ya farka ya ganshi a London asibiti ko kuma tare da Ishaq a gefensa.

Ko lokacin da yana tare da Rukayya baya bude idonsa ya ganshi a gida kuma ko shi a baya bai taba ganin wani abu game da hakan ba, don idan ba zai manta ba a cikin hira Mami tasha gaya masa cewar hakan shine daidai, bai kamata ya dinga mu'amalantar kowa ba har sai yanayinsa ya sauko ya daidaita.

Shi yasa a karo na farko da ya farka a yanzu yaga mutane zagaye dashi sai yake jin wani iri a zuciyarsa, wani irin yanayi da bai san dame zai fassara shi ba, kallonsu kawai yake yi tun bayan da ya bude idanun nasa, kowanne da murmushi a fuskarsa suna tambayar lafiyarsa da kuma yadda yake ji.

"Ya MB kace min ka warke dan Allah, ni ban san haka ciwon ka yake ba wallahi, ban taba ganinka a haka ba."

Shukra ta fada tana gyara glasses din dake fuskarta tana kallonsa. Kuma sunan da ta kira shi dashi ya tuna masa da dadewar da yayi bai gansu ba tun bayan aurensu, ya san dai kowaccensu ta kira shi sau daya sun gaisa amma bai kara?jinsu ba bayan hakan, dukkaninsu sun canja, musamman Safiyya da tayi wata irin kiba a watanni biyu kawai tana gaya masa cewar da wuri zasu tsufar dashi idan ska kalle su aka cewa su kannensa ne.

Kuma maimakon ya bata amsar abinda ta tambaya sai kawai yace.

"Ya project work Win naki kuwa Kin gama?"

"This is your answer ya warke kenan, don ni na tabbata da yace miki da sauki to wallahi Yaya bai warke ba."

Cewar Salma tana karasowa rike da kwanon furar da Inna Danejo tasa taje har bangarenta ta dauko shi. ta zubo wani potate Win dankali a ciki daga kitchen, tana karasowar kuwa Inna Danejo dake gefensa ta karba tana fadin.

"Muhammadu juyo nan kasha wannan, na gaya maka ni ban yarda da wannan she*gen ruwan da ake sawa ba ace wai shima abinci ne, gashi nan tunda ka farka ai kake ta shan ruwa da yana aiki ai ko shi ba zaka nema ba."

Ya juyo ya kalleta, ta debo abincin da niyyar bashi, sai kawai ya girgiza kansa yace.

"Ni ba haka matata take bani abinci ba."

Su Salma suka kyalkyake da dariya ba shiri yayin da kafin Inna Danejo ta kai karshen salatin ta Surayya ta shigo tana fadin cewar ga wani likitan nan ya karaso da sakon cewar Baffa ne ya turo shi, don a dazu bayan farkawarsa sun yi waya da Baffan har ma da Baba Usman suna tambayar yaya jikin nasa, kuma a cikin muryarsu kaWai ya fahimci su ma sunji dadin yadda wannan karon ciwon nasa bai tsawaita ba.

Inna Danejo ta ajiye farantin hannunta tana fadin ace masa ya shigo, Ma'aruf ya juyo yana ce mata ta bashi furar tace ai kuma yayi wa kansa kenan ya zauna da yunwar cikinsa idan matar tasa tazo ta bashi.

A lokacin ne kuma yadso ya tambayi inda Aminan take don tun bayan lokacin da ya farka sau daya ya ganta sanda da ta kawo masa ruwan farko da ya tambaya, amma kafin ya bude baki Shukra ta matso tana dariya ta Wauki plate din?tana faWin ita zata bashi.

A lokacin ne kuma Zahra da Sahla da suka fito daga hanyar koridon dakunan gidan.

"Ina Aunty Amina?"

Suka tambaya a tare muryarsu na shaida murna.

"Me kuka je kuka yi mata a daki?"

Safiyya ce mai tambayar tana kallon hannun Sahla data boye a baya.

"Babu komai, kawai tambayarta zamu yi wani abu."

Salma ta kalle su tace.

"Makaryatan banza ai idan bincike ne kun iya shi, na gaya muku duk ranar da zaku zo gidana walkahi ku gaya min kulle koina zanyi ku zauna a falo.

Munaya dake zaune a gefe ta kalle ta.

"Har yanzu baki san abinda ke tsakaninku da Samirah bane, shi yasa kike ganin na wadannan yaran wani abu suke yi."

Da sauri Salman ta juyo tana rokonta ta gaya mata abinda Samiran ta daukar mata amma tace ita ba zata fada ba ba,? ta bari duk ranar da Allah ya tashi tona mata asiri zata gani da kanta yayin da Inna Danejo ke fadan hada husuma babu kyau.

"Wai ina Samiran ne ma, ni tazo in bata sakon cupcakes."

Safiyya ta tambaya daidai lokacin da Surayya ta shigo tare dasu Faruk da kuma likitan nan, hannunta na dauke wani dan karamin yaro da a lokaci guda Ma'aruf ya gane cewar Aarif ne Wan gidan Faruk, kuma bai gama tunanin ba Shaida natar Faruk din ta shigo biye da sauran ?a?ansu biyu mace da namiji.

"Yaya, su Aunty Shaida ne duka zo."

Cewar Surayyan kasancewar dama ita tun da ta san Shaidar don yayar ?awarta ce.

Kowa ya amsa sallamar su da fara'a yayin da Munaya ta taso a lokaci guda tana? kokarin daukar Aarif din dake ta mika hannu zai koma wajen mamansa alamun kyuiya yake yi.

Shahida ta karaso har gaban Inna Danejo tana gaishe ta yayin da likitan nan ke kokarin cire allurar drip din daje hannun Ma'aruf din, shima ta gaishe shi sannan ta gaya masa cewa Faruq din yana waje tare da Ishaq wanda shima ya karaso a lokacin.

Da haka ta juya wajensu Safiyya tana gaishe su da???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? tambayar Yaya mai jiki. Tambayar da tasa sai a lokacin hankalin kowa ya lura cewar Amina bata wajen kuma kowa ya tabbatar da cewar bai ga lokacin da ta fita ba.

Sai dai kafin hakan ya kai ga nisa, kofar falon ta bude, kuma Aminan da ake nema ta shigo a lokacin tare da Samiran da suka fita tare, sai dai duk wanda ke Wakin basu yake kallo a lokacin ba.

Wadda ke zaune akan kujerar da Samira ta turo zuwa cikin falon a hankali ce... Hajiya Maimuna.

Shiru ne ya ratsa ilahirin falon a lokaci guda kafin kowannesu ya rufe da kiran sunanta, hatta Inna Danejo sai da tayi murmushi tana kallonta, don a tarin jama'ar gidan kaf, kowa ya san kawaici irin na Hajiya Maimuna, ba karamin kokari Amina da Samira suka yi na sawa tazo ba, tunda tun rana ta san inda dukkaninsu suka taho amna bata ce zata zo ba.

Ma'aruf ya kasa rufe bakinsa a lokacin da yake kallon Hajiya Maimunan dake Samirah ke turota tana karasowa gabansa. Keken tayar ya hawo har kan carpet din ta iso daidai gabansa da kuma Inna Danejo wadda ke fadin taso Baffa yana gari yau yaga Maimuna a gidan Ma'aruf, don ko sanda yana tare da Rukayya har suka rabu bata taba takawa gidansa ba.

A lokaci guda wani abu kamar kwallar da bai san dalilinta ba ta cika idanunsa lokacin da? Hajiya Maimunan ta gama gaishe da Inna Danejo ta juyo tana tambayar yaya jikin nasa, bai ma san da wadanne irin kalamai ya amsawa tambayarta ba, ya san kawai a wannan lokacin idanunsa na kallon Amina ne dake can tsaye a baya da murmushi a fuskarta tana gaisawa da Shahida tana kuma kokarin daukar Aarif da ya gudo daga hannun su Munaya ya koma wajen Shahidan.

Zuciyarsa yaji tana gaya masa cewa ko da iya wannan alkhairin nata na yau kaWai, zai kyautata duniyarta da dukkan iyawarsa.

***

*?arfe tara da rabi na dare.*

Kowa ya tafi a lokacin, hatta su Ishaq bayan ya takura musu sun shaida masa dukkan abubuwan da yayi missing dinsu a ranar, farko shine shari'ar Hamida da shi kansa ya manta da ita a yau,Ishaq din ya gaya masa cewar yaje ya dauko yarinyar ya tafi da ita kotun, kuma duk iya kokarinsa a gaban Alkalin, ba'a je koina ba alkalin ya yanke hukunci da cewar yarinyar ta koma wajen mahaifiyarta idan yaso tunda ya bada uzurin mahaifin nata bashi da lafiya, ya yanke hukunci cewar duk sanda ya warke zai iya sake shigar da kara sai a zauna a sake tattaunawa.

Na biyu kuma shine zancen haduwarsa da mutanen RTL din nan, Faruq ya gaya masa cewar babu yadda baiyi yayi contacting mutanen ba amma ya kasa samun su kuma suma basu ce masa komai ba. Sannan Ishaq ya shaida masa cewayasa snyi deactivating gabaWaya cards dinsa da aka Wauke kuma barayin basu sami danar fitar da komai ba.

Har suka tafi Faruk yana ta kokarin ya kwantar da hankalinsa akan cewar ya san ba wani issue ne babba ba amma har suka kammala zancen suka tafi jikinsa bai bashi haka ba, kawai ya ajiye zancen ne a gefe sanin cewar idan ya saka a ransa tabbas abin zai hadu ya dame shi tunda wancan case din ma har yanzu basu karasa shi ba, don haka ya hakura ya barwa karin samun saukinsa komai.

A yanzu gidan daga shi sai Amina ne, kowa ya tafi, su Salma tare suka koma cikin gida tare dasu Inna kuma ya san zuwa yanzu ma duk sun tafi. Kuma Hajiya Maimuna da har ta tafi fara'ar fuskarta bata Soyowa, kuma yana jin sanda taje ta addu'a da sawa Amina albarka daga can bakin kofa inda suke sallama.

Hatta Faruk sai bayan da suka yi sallar Isha ma sannan suka tafi don suna ta hira tare da Ishaq, yayin da Amina ke tare da Shahida a kitchen don dukkaninsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login