Showing 15001 words to 18000 words out of 132946 words

Chapter 6 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1135

abinda su Suraj din ke yi, kawai bai damu bane kuma yana sane yake barinsu. Kowa na diban kason sa amma kai so kake mu mu tashi a tutar babu? Ba don ma Perm Sec. ya shiga zancen mahaifin naku ba kai ka sani da yanzu bama kan wannan kujerar.

Wallahi idan na shiga lissafo maka kadarorin da matan nan suka tara yanzu zaka rike baki Jawad, amma ni gida uku fa kawai nake dashi har yanzu, ba don nayi fafutuka ta ma ba da bana jin ina da ko daya ai, kai kuwa banda motarka bana jin ka tara wani abu, karfi da yaji ka maida mu talakawa alhali muna iyo a cikin kudi Jawad?"

Ya lumshe idanunsa a hankali lokacin da ta kai karshe sannan ya juyo ya kalle ta.

"Mamah amsata ba zata canja ba kema kin sani,abinda nake gaya miki kullum shi zan kara gaya miki a yanzu, ba zan saci kudin mahaifina ba ba zan dauki abinda ba nawa ba, shi yasa nake aiki kin sani, su sauran matan nasa da yayansu ke zuwa su debo musu ai basu suka saka su a gaba suka roke su ba, kowa ganin damarsa ce tasa shi yin hakan, don haka me yasa ni zaki takura min, ba ga su Khairat nan ba? ( Kannensa mata biyu) Ki koya musu wata hanyar da zasu samo miki mana, ai ba maza ne kadai suka iya samowa ba."

Ya ajiye kofin hannunsa sannan ya mike tsaye, sannan yace

"Zanyi bako anjima, Dan Allah Mamah ki sa ayi mana abinci, wadannan duk basu yi min ba."

Ya fada yana nufin tarin cimar dake kan teburin daya tsallake, kuma bai jira abinda zata ce ba yayi gaba, ya zaro wayarsa ya kira Haron da suka yi akan lallai ya shigo Abujan don ta nan ne zasu hau jirgi zuwa Kano, ya gaya masa shi ba zai yi tafiyar mota ba.

Kuma awa guda bayan hakan sai gashi ya iso, suka zauna daga falon kasa na Sangarensu yayin da Haron ke ta mita akan tason shi da yayi babu shiri.

"Kaifa kake bukatar abin nan J, amma ni ka takurawa na taho rana tsaka, ina ga dole mu maida harkar nan ma taciniki don na fahimci ni zan sha wuya a banza."

"Ko nawa ne ka san zan biya ka, I never regret anything indai akan Rukayya ne ka sani."

Haron ya kalle shi lokacin da ya tsiyaya wani lemo mai sanyi a daya daga cikin tambulan Win da aka kawo musu sannan yace.

"Shi yasa ni kuma nake iya kokarina don inga na ciro ka daga wannan masifar, Haba ka kalli fa inda kake rayuwa, ni ban ma san kun canja wannan gidan ba, amma ka kallafa ranka akan wannan shashashar yarinyar, in the first place ni ban san ma me yasa zaka neme ta ba idan har ka san aurenta zaka yi."

Jawad ya gyada kansa alamun ya fahimta yana kallonsa sannan yace.

"Ina ga duk mun wuce wannan stage din Haro, mun karaso wajen da kace zaka taimake ni, ni kuma nake jiran inji ta hanyar da zaka taimake ni din."

Cike da takaici Haron yana kallonsa kafin ya buWe briefcase din da yazo da ita a gefensa sannan ya zaro wasu hotuna guda uku ya miko masa, ba tare da bata lokaci ba kuwa Hawad yasa hannu ya karba.

Hotunan mutum daya ne a mabanbantan llokuta har guda uku, na farko kamar ranar daurin aure ne, don a cikin jama'a yake sanye kuma da kaya masu babbar riga, na biyu kamar hoton wajen aiki ne, yana sanye da suit da kuma sumar gashinsa wadda aka gyara cikin wani style mai kyau, sai na karshe a bakin titi ne yana waya, hoton yayi kama da cewar a boye aka dauke shi sosai.

Kuma ba sai Haron ya sake yi masa bayani ba, ya riga ya fahimci waye tun da wuri, don idan zai iya tunawa ma ya tabacganinsa sau daya a wani taron harkar kasuwanci da ya halarta shekara guda baya, idonsa ya manne akan fuskar sa yana son ya gano banbancin dake tsakaninsa dashi, wannan banbancin da yasa Rukayya ta juya masa baya, banbancin da yasa ta rufe idanunta akan tarin kyautatawar da yayi wa rayuwarta ta kasa ganin kokarinsa, ko ma rabewar da zuciyarsa ke yi a lokacin da take gaya masa cewa bata dauke shi komai ba face abin wasa kawai, abin wasanta!

"Na gama samun duk wani background information akan gayen, ashe har aure ma ya sake yi..."

"What?"

A lokaci guda ya katse Haron da ke kokarin fara bayaninsa. Fuskarsa na kallonsa da tsananin mamakin da ya kasa tantance daga ina yake fitowa yana shiga jikinsa.

"Yes, ya sake aure ?an kwanakin bayan nan, amma naji ance kamar bashi matar kawai akayi don tare akayi auren dana sauran yanuwansa."

Sai kawai ya gyada kansa a hankali ba tare da ya san me zai ce ba, hakan yasa Haron ya cigaba da maganarsa.

"Ka san ni bana sanya a al'amarina, so na samu labari ance min zai hadu da wasu mutane gobe, na samu details Win da komai daga bangarensu, so kawai zamu yi masa aiki ne a lokacin."

Jawad ya dago ya kalle shi."

"Aiki? Wane irin aiki?"

"Plan dina shine mu kama shi for now, kar ka tambaye ni me zai faru bayan nan, mu fara gama wannan din tukunna."

Jawad ya kalle shi tsawo sakanni biyu.

"Ba zan tambaye ka ba, amma ka sani cewa I wont sign for any shit, idan har kashe shi ne plan dinka..."

"Wa yake maganar kisa anan J? biyu babu muka ce zamu sa yarinyar nan tayi, you want to make her pay ko ba haka ba? Then we are just going to make her pay kamar yadda kake so, ka yadda dani kawai."

Jawad ya sake kallonsa na wani lokaci kafin ya gyaWa kansa.

"To meye plan din?"

"Ba ma zamu bari ya isa wajen mutanen da zai hadu dasu ba, kafin ya isa za'a tare shi kawai sannan a juyo da motar, yaran da nasa sun nemo titin da komai har ma da daidai wajen da zasu tsaida shi din, shi yasa nace maka dole mu bar Abuja yau."

Jawad ya gyada kansa alamun ya fahimta.

"Idan har babu zancen kisa a al'amarin nan, I think hakan yayi daidai."

Haro ya girgiza kansa.

"Wannan gayen ba irin mutanen da za'a kashe su maganar ta wuce kamar iska bane J, daga shi har mahaifinsa suna da tarin connections din da ban san iyakarsu ba, don haka wasa kawai zamu yi dashi mu cimma manufarmu."

Kalaman ?arshe suka tafi kai tsaye cikin zuciyar Jawad suka yi masauki.

Wasa kawai zasu yi dashi, wasa... Ya cije lebbensa na kasa yana sake maimaita kalmar a ransa. Yanzu yake ji cewa da gaske Haro ya dauko hanyar cimma manufarsu, tunda har zsi bashi damar da zai nunawa Rukayya cewa mutumin da take wa kallon duniyarta, take wulankanta shi akansa shima bai fi karfin ya zama abin wasan a wajen sa ba.

Yana jin Haron na kokarin yi musu booking jirgin da zai tashi zuwa Kano lojacin da ya mi?e don zuwa dakinsa ya fara shiri, a lokacin ne kuma yaci karo da ita, wannan yarinyar, wannan yarinyar da ya ?i jinin ganinta, 6ar aikin mahaifiyarsa, tana tsaye daga koridon dake jikin falon haunnuta rike da wani katon faranti da ta shako kayan abinci dasu, kuma ba sai tace komai ba, rawar da hannayenta keyi tare da kwanukan abincin shine abinda kai tsaye ya shaida masa cewa tsaf taji dukkanin shirinsu!

***

Karo na ba adadi Amina ta kalli agogon dakin, zuciyarta ta kara yin nauyi a kirjinta, rawar hannayenta ya karu, amma sai tayi saurin danne hakan ta hanyar daukan wani ?aton mangwaro dake gabanta.

A bangaren Inna Danejo suke wadda bayan fitar Ma'aruf Samirah tazo ta gaya mata isowarta don haka ta ?ulle gidan suka taho tare, inda ta tadda dukkan sauran jama'ar gidan kowa yazo don saukarta.

Kuma ba'a dade ba aka shiga hayaniyar rabon tsaraba kamar yadda ta fahimci ana yi duk sanda Inna Danejon tayi tafiya ta dawo, su Msma Rabi dama wasu da bata san su waye ba sun zo ana ta faman kwance tsaraba kala-kala, Samirah ce ke gaya mata cewa in dai Inna Danejo taje Bakori to ba gidan kadai ba, tun daga farkon layinsu har karshe kowanne gida sai an kai masa tsarabarsu, abubuwa ne kala-kala har da wanda ita bata taba gani ba ma sai faman rarrabawa ake yi bisa umarnin da Inns Danejon ke bayarwa.

Kusan ita dasu Mama Rabi ne ma ke ta aikin don Samirah ita nata na amfanin gida kawai take ta warewa, tana yi suna fadansu ita da Inna Danejon akan cewar tana diban komai da yawa, Munaya kuma tsince-tsincen duk abinda ta san zata iya ci take yayin da Surayya ke ta aikin danna wayarta taje ta nanike a jikin Inna Danejon dake ta nan-nan da ita, wanda sai a lokacin Amina take jin wai sunan maman Inna Danejon aka saka mata, shi yasa duk gidan tafi shiri da ita akan kowa.

A lokacin ne kuma Samirah ke gaya mata cewar gobe Amaren da akayi bikinsu tare zasu zo, don haka duk tarin taraddadin dake zuciyarta, sai taji itama tana murna da zuwan nasu, don a?alla koyaushe tana jin hirarsu kala-kala a bakin su Samiran.

Ta cakuda hannayenta duka biyu waje daya lokacin da Mama Rabi ta karbi aikin da take yi tace taje ta huta, Inna Danejonnkuma ta miko mata wata damammiyar fura mai gardi a cikin roba tana yi mata nata sannun itama, kuma duk da yadda take murmushi akan fuskarta hakan bai ?arasa har cikin zuciyarta ba, don bai isa ya kore halin da zuciyarta ke ciki ba.

Ta samowa kanta mafita ta sani sai dai duk da hakan mafitar bata canja daga umarnin Amma ba don ba zata taSa iya kin bin maganganunta ba, itace gatanta ta sani kamar yadda ta san maganganunta sune fitilar da zasuvgitar da ita daga duhunnda taje ciki, don haka a dole ta tsamo kanta daga rudanin zuciyarta ta yanke hukuncin aiwatar da umarnin Amma tare kuma da samawa kanta mafitar da take ganin zata jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya.

Zata yi abinda Amma tace, zata aikata umarnin Kilishi ta hanyar samun gaskiya da kuma yardarta, sannan zata yi jinyar Ma'aruf ta hanyar da hakan zai ?ara sha?uwa tsakaninsu, a yanzu zuciyarta ta riga ta karSe shi da dukkan iyawarta, don haka zata ajiye komai a gefe ta gyara rayuwarsu kamar yadda ya ro?e ta, kamar yadda yake so... Idan tayi hakan ta san zata samu sau?i a zuciyarta na ganin laifi da kuma rashin kyautawarta.

Hannayenta suka kara rawa lokacin da ta tuno yadda suka kasance dazu da safe, dama abinda ya rada a kunnenta kafin ya fita bayan tambaya karbi robar zogalen nan.

_You are really making me insane, and I like it..._

Tana iya tuna yadda wasu abubuwa ke harbawa a cikin kanta wannan lokacin, dama yadda jikinta ya dinga rawa a cikin hanayensa kafin ya janye ta a hankali yana gaya mata cewar zai fita a cikin kunnuenta.

Sai dab da magariba sosai sannan komai ya natsa, suka gama haWa kan tsarabar nan tsaf, sannan ta samu tayi sallah, har kowa ya tafi sai ita kadai a bangaren Inna Danejon, don bata san me zata koma bangarensu a wannan lokacin tayi ita kadai ba, jira take amma bata san ma abinda take jira din ba, dawowar Ma'aruf ko kuma akasin sa??

Kuma da misalin karfe bakwai da rabi daidai, sai dukkan wani tunaninta dama kokwanton ta yazo kan gaSa, sannan fatanta dama duk wani tsarinta ya tafi daidai lokacin da kiran Hajiya Kilishi ya riske ta.

Mama Rabi ce ta shigo ta gaya mata sakon, kuma bayan hakan bata ce komai ba don haka Inna Danejon ma bata yi wani tunanin komai tayi mata sallama ta fito tare da tata katywar ledar kayan tsarabar.

A harabar gidan ta hango Mamin, tana tsaye a jikin motar ta kirar Camry yayin da Malam Sani direba ke ciki ya kunna motar, hasken gitulun danjojinta na haskawa ta kowanne gefe, tafiya kawai take yi har suka karasa tare da Mama Rabin dake fadin.

"Hajiya ashe har kin fito."

Kuma Mamin bata amsa ba, sai ta kalli kayan hannun Aminan kawai sannan tace da Mama Rabin ta karba ta tafi dasu.

Kwatanta yadda zuciyar Amina ke bugawa a kirjinta wannan lokacin wani abu ne da ba zai bayyanu ba, don kafafunta ma bata jinsu a jikinta kwata-kwata, yayin da jikinta yayi shafal kamar fallen takarda.

"Amina..."

Hajiya Kilishin ta kira ta cikin sautin muryarta da ya fito tar a shirun harabar compound din.

Bata amsa ba don bata san me zata ce ba, tana kallonta ne kawai da dukkan taraddadin dake yawo akanta, kuma ga mamakinta kawai sai taga tayi wani irin murmushi mai fadi da ya tabo har cikin idanunta kafin ta fadi abinda ya tsayar da duk wani hargitsin kanta cak!

"Ma'aruf yana asibiti, yanzu Ishaq ya kira ni yake shaida min!"

Maganganun suka fito tar cikin muryarta, kuma bata jira komai ba sai ta miko mata wata takarda da sai a yanzu ta kula da ita a hannunta.

"Ga nawa albishir din Amina, kamar yadda kema kina bani naki."

Bata san tsawon sakanni nawa ne suka wuce kafin ta ita sa hannu ta karbi takardar amna idonta da kwakwalwar ta basa gane ko meye a jiki balle har ta kai ga fahimta, kuma abinda Mamin ta gane kenan saboda haka tace.

"Appointment ne na wani asibiti a Indiya, za'a kai Aminu a gyara masa kafafunsa, na biya komai, saura shi da mai raka shi su fara fafutukar visa."

Ta fadi hakan sannan ta yi shiru tana kallon yadda hannun Aminan ke rawa tare da takardar, sai kawai ta sake wani murmushin sannan tace.

"Me na gaya miki ne Amina? Komai mai sauki ne umarni na kawai zaki bi, shikenan sai in mayar miki da duniyarki kamar aljanna."

Abinda bata sani ba shine a wannan lokacin Amina ba jinta take yi ba, kwata-kwata bata saurarar abinda take fada take yi ba, maganganun Amma mahaifiyarta ne kawai ke yawo akanta.

_"... A tafin hannunki zaki dora Kilishi Amina, a tafin hannunki zaki dinga juya ta ba tare da ta sani ba, duk abinda kike so har ma da wanda baki roka ba zata yi, da kanta zaki sa tayi ta ha?a ramin binne kanta har sai yayi zurfin da zai rufe ta!"_

***

_Me ya faru da Ma'aruf?_

_Kun fahimci cewa mun fara wasa da hankalin Kilishi?_

_Kun fahimci kudirin Amina?_

_Kun fahimci inda rayuwarsu ke shirin kaimu?_

_Me zai faru game da tsarin su Jawad?_

_Me ke shirin faruwa da Zainab? ( ?ar aikin gidan su Jawad.)_

_Allah yasa baku manta da Hameda da kuma mamanta Rukayya ba... Suna nan tafe._

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*04*

~~~~~~~

_There are feelings that can't be explained._ _- Unknown_


**

A cikin asibitin, daga cikin wani dogon korido?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? mai Wauke da kofofin kala-kala, Hajiya Kilishi na tsaye ita da Faruk yayin da daga gefenta kan kujerar masu jira na asibitin Amina ce ke zaune suna sauraren bayanin da Faruk din ke yi.

"Wallahi Mami mun gama duk abinda zamu yi, munyi sallama lafiya kalau da shi har ma da wanda muka hadu dashi din, kowa ya hau mota muka rabu a wajen round about din nan, to ni nayo gaba kawai sai go slow ya tare ni kafin inyi nisa, anan naji wasu mashin da suka karaso suna hirar fadan da suka baro ana yi a baya, daya yana cewa wai ai ya san mai dukan sunansa Ma'aruf yana aiki tare damu a kamfani, naji yana bawa abokinsa labarin daya incident din a ya faru dashi da Daniel.

Da kyar na fita da go-slown nan na koma, kuma lokacin da naje ma har an raba su an dawo da Ma'aruf din motarsa mutane suna ta rike shi, ina masa magana amma kamar bai gane ni a lokacin ba, shine na kira Ishaq, sai da ya karaso sannan da kyar yasa shi ya yarda ya baro wajen, amma tunda naje abu daya yake ta fada wai a barshi ya karasa kashe mutumin yana da sakon da zai bashi."

Hajiya Kilishi tayi ajiyar zuciyar dake shaida tsananin damuwarta kafin tace.

"Kuma ko bayan fitar tasa ma munyi waya sai kuma na kira shi daga baya bai dauka ba."

"Ai Mami gabadaya wayoyin nasa ma da wallet da komai an kwashe, da yake bude motar kawai yayi ya fita a lokaci guda, to a wannan hayaniyar Sarayi suka samu dana suka kwashe komai, har mukullin motar sun tafi dashi, ita kanta motar ma don baza su iya dauka a lokacin bane."

"Tana ina yanzu?" Kai tsaye ta sake tambaya.

"Tana wajen, nasa wasu dai sun tura ta zuwa gefen titi, sannan na basu kudi su kwana a ciki saboda ban ma san inda za'a nemo spare key dinsa a dauke ta ba."

Duk wannan bayanin da Faruk ke yi, Amina dake zaune daga kujerar baya ta masu zaman jira a asibitin idanunta na manne ne da kayan Faruk?din, farar shadda ce a jikinsa wadda gabadaya gabanta ya Saci da jini har zuwa kowanne hannun na rigar, zuciyarta na bugawa da motsin dake shaida girman laifinta da a yanzu take ganinsa karara, yayin da kalaman ke yawo a cikin kanta, tana yarda da kowacce kalma Waya bayan daya dake maimaitawa daga cikinsu.

Suna gaya mata cewa tabbas babu abinda dan adam zai samu a duniyar nan cikin sau?i, sannan kuma babu wani abu da mutum ya kamata ya fito yayi takama dashi a duniyar nan, don ana zuwa gabar da rayuwa ba zata baka zabi ba, zaka zo kayi wani abu da ko a mafarki ba zaka taSa tunanin aikata shi ba.

A baya zata rantse da Alkur'ani wajen karyata duk wanda zai zo ya shaida mata cewar zata iya aikata wani abu najamancin wannan, amma sai gashi a yanzu da hannunta ba tare da tursasawar kowa ba tayi abinda take jin tambarinsa ya Warfanu a zuciyarta ta hanyar da ba zai taba goguwa ba, don idan har za'a lissafa da sunanta a cikin wanda suke da kamasho a yau wajen faruwar wannan tashin hankalin, wajen zama sanadin da har mutane biyu ke kwance a asibiti, da kuma fitar jinin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login