Showing 84001 words to 87000 words out of 132946 words

Chapter 29 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1152

babu mutum a cikin gidan tun sanda ya tako ?afarsa ciki shine ya tabbata.

Babu kowa, babu kowa a cikin gidan banda shatin tayoyin motar da suka tarar a jikin kasar waje ta compound Win gidan, shatin da ?an sandan suka tabbatar da cewar bai daWe ba, babu daWewa da fitar mota a gidan.

Bai san lokacin da yayi baya ya zauna kan wata kujera dake cikin falon ba yayin da hayaniyar ?an sanda da kuma sauran tanen da suka zo dasu ta tafi kan wata jaka da suka tsinta a cikin falon, wata jaka da babu komai sai tarin wadu CD's da kuma computer guda daya.

Yana jin abinda suke fada, yana jin suna fadin cewa kayan ba karamar kadara bace da zata iya kaisu ga abinda suka zo nema, amma shi ba wannan ne a ransa ba, ba hakan yake do ba, ba kuma hakan yayi fata ba. Burinsa yaga ko waye wannan Awwalun, burinsa yaga fuskarsa yaga WAYE SHI, ya ga waye wanda ya daWe yana cutar dasu a duniyar nan ya kuma san dalilinsa.

So yake ya tambaye shi me suka yi masa? Me suka yi masa shi da mahaifinsa da dauki aniyar tarwatsa su? Wane irin laifi duka yi ko kuma ta ta yaya suka cutar da rayuwarsa da yake bata lokacinsa yana kuma sadaukar da dukiyarsa da fasaharsa don ganin karshensu? Abinda yake so a wannan lokacin kenan, so yake ya ri?e wuyansa a cikin hannayensa ya tambaye shi me suka yi masa... So yake ya dake shi, ya mare shi, ya naushe shi har sai yaga ha?oransa suna biyo jini suna fitowa....

"Kusan duka Cd's Win are write-protected, sai mun je office zan iya aiki akansu."

Cewar wani a cikin ?an sandan nan yana ?o?arin danne-danne a cikin computer dake hannunsa bayan ya gwada CD guda Waya a ciki, kuma bayan hakan yana ji mutum biyu da suka buWe computer hannunsu suna faWin itama a ?ulle take da password.

Wayarsa tayi kara a lokacin, hannunsa ya zaro ta a hankali daga aljihunsa, Ishaq ne.

"B kana ina? Tun dazu nake kiran wayarka ta?i shiga, gani har nazo Airpot daukan Abdurrahim, ka manta ko?"

Sai kawai ya cusa hannusa gabaWaya cikin gashin kansa.

"Wallahi na manta Ishaq, ina nan ina wajen aikin nan ne, amma bari mu gani, may be kafin jirgin nasu ya sauka I'll be there."

Ishaq dake zaune a cikin motarsa a harabar filin airpot din ya gyada kansa.

"Kayi kokari Dan Allah Ma'aruf, don kafin in fito Baffa yayi fadan me yasa baka gida bayan ka sani."

Ya sake gyada kansa a lokacin da Faruk dake tsaye tare da wani Wan sanda ya matso daidai inda yake zaune.

"Zan zo yanzu insha Allah, bari mu kammala."

Kuma da haka wayar tasu ta kare, ya sauke ta san da Faruk din ke cewa.

"Kar ka damu Ma'aruf, zamu sami wani abu a cikin waWannan kayan insha Allah, kuma zasu saka security daga yanzu za'a saka ido akan gidan nan 24/7, we are close to finding them Insha Allah."

Abinda dukkaninsu basu sani ba shine, amsar da suke nema a yanzu tare da mabuWin da zai bude komai ya kuma kawo karshen komai Win yana dab da taka kasar Nigeria!

***

"Naira miliyan tara!"

Muryar mutumin ta furta a hankali yana kallon wanda ke gabansa, a zaune yake akan doguwar kujera da ta cika kusan rabi na dakin, don bayan ta mi?e ta zagayo ta bari Waya cikin wani shape mai kama da C, kalarta milk ce kamar yadda tattausan carpet Win da aka baje a Wakin yake, akwai labulaye da suke kalar brown, kalar da ta dace da fentin Wakin da kuma sauran kayan furnitures Win da kyawunsu ke ?ara haska haduwar Wakin.

Mutumin na zaune ne daga shi sai gajeren wando da kuma wata yaloluwar T-Shirt yayin da teburin gabansa ke cike da wasu kwalabe da kuma kule-?ullen da ba sai an tona ba kowanne mai hankali zai san cewa abubuwa ne da ya kamata a li?a musu ayar tambaya.

"Naira miliyan tara ba wasa bane..."

Mutumin ya sake faWa yana Wora kafafunsa duka biyu akan teburin dake gaban nasa wanda hakan yasa wasu abubuwa dake kan teburin suka faWi. Awwalu dake zaune daga can ?arshen Wakin hannuwansa da kafafunsa duka a Waure, idanunsa suka bi kayan da suka fadi sannan ya sake dawo dasu kan mutumin.

"Munyi yarjejeniya da kai Awwalu, ka san ni, na sanka kuma ka san ba'a a cin kuWina? a kwana lafiya..."

Ya faWi haka sannan ya Wago daga kishingiWar da yayi, a gefensa katinan bankin Awwalun ne wanda suka samu a cikin wallet Winsa, ya Webo su guda uku sannan ya watso su, suka taho tun daga inda yaken har zuwa kan fuskar Awwalun kafin su tarwatse a jikinsa.

"Babu komai a cikin waWannan accounts Win, mun duba gidanka ma babu ko sisi..."

Mutumin ya hade hannayensa biyu sannan yace.

"Bana so in taba ka Awwalu ka sani, ka san wannan ne dalilin da ya sa na daga maka kafa tsawon watanni, ka san wannan ne dalilin da yasa na dade da yi maka shiru kuma ka san shine dalilin da yasa ni da kai muke kallon juna a yanzu..."

Ya kai idanunsa kan agogon dake manne daga can saman dakin sannan yace.

"... Zuwa nan da ?arfe shida, zaka iya zama tarihi Awwalu, don zan gwammace in kashe ka da ace ni da kai muna cigaba da rayuwa a duniyar nan kuma babu kudina a tsakaninmu."

Ya kai karshe a lokacin da Awwalun ke kokarin gyara zamansa don duk abinda yake fada gaskiya ne ya sani, ?antaro abokin huldarsa ne da suka daWe suna harkar cinikayya tare, a yanzu kudin da yake faWa miliyan tara, kuWin wasu kayayyaki ne da ya karba a wajensa ya aikawa da wani kaninsa dake can garinsu don ya fara kasuwanci, kuma ba wai ya hana shi kudin saboda wani dalili bane ba, bai bayar bane saboda ya manta, a kwanaki biyun nan da al'amarinsa da na Kilishi ke cakudewa, kwakwalarsa ta manta da tarin abubuwan da bai san lissafinsu ba.

Lokacin da mutanen ?antaro suka shigo gidansa, yanayin shigar kayansu da yadda suka rufe fuskarsu, ya bashi tunanin cewa mutanen Kilishi ne don wannan ne kadai tunaninsa a yanzu, abinda yake gujewa kawai kenan, ya gansu ne da tunanin ire-iren mutanen daya taba hada ta dasu ne wanda suka kashe Jamal.

Sai a lokacin da ruwan da aka watsa fuskarsa ya farkar dashi daga suman da yayi, ya bude idanunsa akan ?antaro da kuna yaransa sannan ya fahimci cewa zaren kaddarar tasa da saura, bai kai karshe ba har yanzu, yana da lissafin wasu kwanaki kafin a zo gabar da sa'ar da ya dade yana talawa zata ?are, don ya riga ya sallama a yanzu, tunda har bai samu abinda zai bashi yardar Hajiya Salamatu ba shikenan duk wani shiri da kuma fatansa ya kare, don a tsarinsa yana so yayi amfani da Hajiya Salamatun ne su boye laifinsa wajen tonawa Kilishi asiri.

Amma tunda bashi da wani mataimaki a yanzu, to ya san babu ta yadda za'ayi yaje ya tunkari iyalan Bakori don tonawa Kilishi asiri ba tare da ya bankada nasa ba shima.

Don haka fatansa kawai shine ya bar garin Kano a yanzu, yayi nisa da arewa ma? gabaWaya, ya tafi inda ko yanuwansa baza su sani ba, idan yaso da ya sami lokaci sai ya zauna ya gyara wadannan CD's din da ya dade yana recording muryar Kilishi a ciki, ya cire duk inda ta ambaci sunansa da kuma muryarsa, idan yayi haka, sai ya turawa da Ma'aruf hakan yana daga inda yake, ya tonawa Kilishi asiri ba tare da kowa ya sanshi ba, idan yaso duk binciken da za'ayi idan basu gano shi ba, za'a karyatata ne a dora laifin akanta ita kadai.

Don haka a yanzu da ?antaro ya kama shi zaiyi amfani da wannan danar ne kawai ya kwana biyu a wajensa, zai bari su rike shi ne har zuwa lokacin da hankalin Kilishi zai karkata daga kansa don ya san ?antaro karya yake ba iya kashe shi zai yi ba, shi Wan kasuwa ne kawai mugu, amma muguntarsa ba ta tsallake wani geji.

Babban tashin hankalinsa kawai a yanzu shine wannan jakar da ya rasa, tunaninsa dama duk wani lissafinsa suna kanta ne, don idan har ya rasa ta bai san me ya kama ba a rayuwarsa, dukka wani tanadi dama kuma nadamarsa zasu tashi ne a banza. Don haka a lokaci guda da ?antaro ya watso masa waWannan katinan a fuskarsa a lokaci guda wata dabara ta haska a cikin kansa.

Dabarar da ya san ba makawa itace kadai hanyar mafitarsa a yanzu, hanyar da zai tserar da kansa.

"Kayi hakuri ?antaro..."

Ya fada kai tsaye yana kallonsa.

"... wallahi banyi niyyar cutarka ba kuma ba guduwa nake shirin yi ba, kawai kwana biyu na shiga wani al'amari ya Wauke min nutsuwata gar na manta. Amma yanzu zaka sami kudinka, wadanannan kananun accounts ne da katinansu ma sun dade da lalacewa, akwai wadanda nake ajiyar kudi masu yawa a ciki, su kusan duka dukiyata ma suna cikinsu ne, amma na barsu a cikin jakar dake hannuna lokacin da suka buge ni,ku duba ciki zaku gani."

Dantaro ya kalle shi tsawon lokaci, ya kalle shi sosai yana nazarin sa, sai kawai ya murza yatsunsa biyu a iska suka fitar da wata kara ba mai yawa ba, amma duk da karancinta a lokaci guda kofar falon ta bude, wani katon mutumi ya shigo, Awwalu ya gane shi a matsayin daya daga cikin wadanda suka kamo shi, banbancin kawai shine a lokacin fuskarsa a rufe take a yanzu kuma ya buWe ta.

?antaro ya nuno shi kafin ya ce da mutumin.

"Kun ga jaka a hannunsa?"

"Eh yallabai, mun ga jaka amma babu komai a ciki sai wasu kaset don haka bamu taho da ita ba..."

"Ku koma gidan dauko ta."

Ya fadi hakan yana katse sauran bayanin mutumin kai tsaye wanda yayi saurin gyaWa kansa sannan yace.

"Yanzu kuwa yallabai."

Da haka ya juya ya fita. ?antaro ya sake juyowa ya kalli Awwalu idanunsa akansa yace.

"Wannan gidan gona ta ne Awwalu, a bayan gari muke don haka idan har na gane cewa karya kayi min, ka sani cewa zan iya yi maka duk abinda na ga dama anan in gama ba tare da ka sami mai taimakon ka ba."

Awwalu ya gyada kansa.

"Babu dalilin da zani sa inyi maka ?arya ?antaro, ka yarda dani idan har an samo wannan jakar baka da matsala."

Sai dai abinda daga shi har Awwalun basu sani ba shine, matsalar da yake faWa kuma matsalar da kowannensu ke gujewa, tana dab da taka kasar Nigeria a lokacin!

***

Wayar dake hannun Kilishi ta katse a karo na ba adadi da take danna lambar tana katsewa.

Idonta ya sauka akan tanadin data gama yi akan Awwalun, tanadin da yazo a safiyar yau da aka kawo mata har airport taje ta karba, a cikin kwali yake a rufe, amma duk da haka sai da ta bada dubu dari biyar ga ma'aikatan wajen na toshiyar baki sannan aka bata shi ta taho, don duk da basu san meye ba, jikinsu ya basu cewar ba abu ne da hukuma zata yarda dashi ba, tunda ko daga can kasar da aka kawo shi ma, cikin sirri wani ma'aikacin jirgin ya fito dashi.

Babu wanda ya san menene, kuma kudin data basu ya toshe musu bakin tambaya, sai a yanzu da ita ta bude sannan ta ga meye a ciki ta kuma karanta komai dalla-dalla.

Allura ce, allura ce da ruwanta a cikin wata yar karamar kwalba da sai da ta saka gilashinta ta ita karanta rubutun dake jiki.

Ruwan dake ciki high dose ne na Ritalin, cocaine, Adderall, da kuma wasu amphetamines Alcohol Hallucinogens Opioids, dake tafiya kai tsaye zuwa cikin kwakwala su lalata wasu Sangare a cikinta ta yadda hankali zai gushe.

Bayan haka ta gama tsara komai, ita kadai ba tare da taimakon kowa ba, tasa an kama mata hayar wani gida acan hanyar Na'ibawa inda zata kira Awwalun can, sannan ta samu wasu inyamurai guda biyu da zasu taimaka mata. Tunda har da kudi komai ba matsala bane a wajenta.

Idan komai ya kammala kuma, ita da Sadiq zasu je gidan nasa su Webo duk wani abu da yake ta?ama dashi akanta sannan su goge duk wani abu da zai iya bawa jami'an tsaro? wani bayani akanta tunda ta san dole al'amarin zai haWa da hukuma idan har Awwalu yayi kwanaki baya gidansa.

To amma idan har ta gama wannan tsarin me zai sa kuma ta nemi Awwalun a yanzu ta rasa, lebbenta ya cije ta gefe guda ganin kiran ya sake tafiya kuma ya katse, ?arya ne ace Awwalu ya iya gano cewar tana yin shiri akansa, mataimakinta ne ta sani, amma bata bashi damar da zaiyi wannan tunanin ba, zuciyarsa da ta ruWe shi ta ja shi wajen tunanin bijire mata bata isa ta haska masa wani abu akanta ba.

Hannunta ya lalubo lambar Sadik a cikin wayar, wanda bugu Waya biyu ya Wauka.

"Kana ina?"

Daga cikin wayar Sadik yace.

"Ina Yankaba Hajiya."

"Yaushe rabonka da gidan Awwalu?"

"Ai Hajiya tun ranar da kika ce kar na koma idan bashi ya kira ni ba, to shima kuma bai kira ni ba shi yasa kawai na shiga harkata."

Ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya.

"Ka tafi gidan yanzu Sadik, ka gano min me yake faruwa, yana nan ko baya nan."

Sadik din ya gyada kansa.

"Shikenan Hajiya, amma nima ina son in tuna miki fa cewa lokaci fa yana ?ara tafiya, naji shiru kuma, gashi ni ina son hada kaya in bar kasar nan kin sani Hajiya."

Kilishi ta gyada kanta kusan sau biyu a lokaci guda.

"Kar ka damu Sadik, ina tunanin daga yau zuwa jibi ma mun kammala komai na sallame ka, kai dai kawai yanzu kaje ka nemo min Awwalun, da mun same shi shikenan, rabin matsalar mu ta warke m u ma."

Sadik ya danyi shiru kafin ya gyda kansa yace.

"Shikenan, Normal Hajiya, sai kin ji ni."

Yana faWin haka ya kashe wayar gabaWaya. Kilishi ta sauke tata daga kunne tana sake yin wata ajiyar zuciyar, fata take da dukkan abinda ke cikin ruhinta na ta sami Awwalu a yanzu... Don taga alamun komai na shirin tsaya mata ne idan har ta rasa mafita a wannan al'amarin nasa. Shi yasa a Wazu bayan ta fita zuwa airport ta dawo, bayan ta tabbatar maganin nan yana hannunta, zuciyarta ta lissafa mata cewa ta fara rage sauran abubuwan dake gabanta kawai.

Don haka a karo na biyu kafafunta suka sake kaita zuwa Sangarensu Ma'aruf, Su Samirah na can na shirye-shirye a cikin gida don haka ta tabbata babu wanda zai neme ta har ta gama abinda ya kaita.

Tana tuna yadda idanun Aminan suka yi a lokaci guda bayan ta buWe ?ofar taci karo da ita, yarinyar ta riga ta gama tsorata da ita ta sani, shi yasa bata da wata fargaba akanta yanzu, ta san zata yi duk abinda ta sanya ta don tsirar da lafiyarta da kuma ta iyayenta da ?anuwanta.

Abu biyu kawai ya rage mata a yanzu, abu biyu kawai, idan har tayi mata aikin Hamida sai kuma ta kwantar mata da Ma'aruf nan gaba kadan lokacin da zata gama da Baffa, da anyi hakan, ita ta san ta yadda zata yi kuma ta raba aurenta da Ma'aruf Win kafin tafiyarta, don babu ta yadda za'ayi ta tafi ta barta a cikin rayuwarsa, ta haska shi da ita ne kawai don cikar nata burin ba don nasa ba.

Ita kadai take so Ma'aruf ya zama yana tunawa a kodayaushe, ita kadai take so ya dauwama yana danganawa da duk wani abu taimako da kuma jin dadi na rayuwarsa

_"Wannan shine maganin da zaki yiwa Hanifa amfani dashi Amina, gashi nan kamar kwalli yake, ki tabbatar kin sanya mata shi a idanunta kullum, abinda kawai nake so daga ke kenan, idan har naga tasirinsa a cikin kwanakin da suke a lissafe, a cikin waWannan kwanakin iyayenki zasu mallaki sabon gida Amina..."_

Abinda ta gaya mata kenan bayan ta mika mata garin da yake ba?i a cikin wani hadadden kwanson sa kamar kwalli, kuma a idanunta ta lura da cewar kamar yarinyar ta canja amma sai zuciyarta ta kasa danganta hakan da komai sai na canjin waje da kuma jin dadin da take ciki sabanin gidan iyayen ta.

Ta wullar da abinda tunaninta yake so ya fara, don ko kwanaki Aminar da kanta ta kai mata sachet din magungunan hana Waukar cikin da ta bata da bayanin cewar ya ?are... Kuma da hannunta ta dauki wani ta bata da ta san shima babu makawa zata shanye shi ne gabaWaya, don haka bata ce komai ba bayan zancen maganin Hamidar har ta baro wajen.

Ta dawo tana lissafin yadda abubuwa ke fara gara mata, yadda komai ke kara tafiya cikin tsarinta da kuma hangenta. Abinda bata sani ba shine, tsarinta dama damar ta take gani kuma take ta?ama da ita sun kawo wata gaSa da zata kai ?arshen kowannensu.

Ta gama rufe maganin da ta buWe a cikin kwalinsa, sannan ta mike ta mayar dashi cikin kayanta, bangaren nasu sgirun yake ba kowa, don su Samiran gabaWaya sun tattara sun koma Sangaren Hajiya Maimuna inda suke shirin tarbar Abdurrahim din a can, tana ji Surayya na waya da Amina tana gaya musu cewa da ta gama nata aikin zata shigo itama, wani abu da ya daWa tabbatar mata da cewar bata da wata matsala da yarinyar nan zata yi duk abinda tace hankali kwance.

Ta mayar da murfin wardrobe Win ta ruWe a lokaci guda da wayarta ta Wauki ?ara. Sanin ko waye yasa ta dawo da sauri kuma sunan Sadik da ya haska a kan fuskar wayar yasa ta Wauka babu Sata lokaci, kamar yadda babu bata lokacin muryarsa ta kwararo cikin kunnenta.

"Hajiya akwai matsala fa, motocin ?ansanda ne gasu nan zagaye da gidan, na tsaya daga gefe ba zan iya karasawa ba...."

Muryar Sadik din ta faWi kalaman da a lokaci guda suka dako zuciyar Hajiya Kilishi da wani irin tasirin da tunda take a rayuwarta bata taba jinsa ba.

Abinda bata sani ba shine, wani abu da zai zama sanadin tarwatsewar zuciyar tata gabaWaya yana dab da taka kasar Nigeria a lokacin!

****

"Ta kawo min maganin Amma..."

Muryar Amina ta fada tsaye daga cikin kitchen din tana kallon tukunyar tuwan data tarawa ruwa a cikin sink Win dake gabanta.

"Tace yana aiki ne a lokaci ?an?ani,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login