Showing 45001 words to 48000 words out of 132946 words

Chapter 16 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1119

of my body Doll, na yarda dake."

(Da kowanne kowanne abu dake jikina Doll, na yarda dake.)

Kalaman suka bata jwsrin gwiwar da a lokaci guda ta fara magana.

"Dazu da ka fita ina ta tunanin akan maganar da ka fada min, akan maganar wannan mutumin da kuke nema, nace me yasa baza ku duba har wajajen da ba'a tunani ba kamar irin su Prison, saboda wani lokacin mutane suna wasa da hankali ne kawai su yi abinda suka san ba za'a taba zato ba..."

Ta yi shiru, kamar ta kai ?arshe kamar kuma akwai sauran abinda zata fada. Shima yayi shiru bai ce komai ba, tsawon wucewar wani lokaci yana kallonta kafin muryarsa ta fito.

"All this while ina ta underestimating dinki ne ashe Doll, naga alama abubuwan da kika sani sunfi karfin tunani na, amma insha Allahu lokaci zai bude min su daya bayan daya.

Abinda kika fada yanzu was amazing, kinyi tunanin da ba ni va har su Faruk wani a cikinmu bai taba yi ba. Tabbas ana amfani da prisoners a irin wannan harkar sosai,mun sani amma Allah bai taba sawa munyi tunanin hakan ba, thank you so much da kika tuna min, Allah ya saka miki da alkhairi Amina kuma Insha Allah a yau zan kira Faruk, kuma daga gobe zamu fara binciken nan, muna da details din yadda siffar mutumin take da komai, so in har a gidan yarin yake, ba zai yi mana wahalar kamawa ba insha Allah."

Ta gyada kanta tana jin kamar wani abu zai fashe ne a cikin zuciyarta saboda jin dadin yadda ya fahimce ta a cikin kankanin lokaci yayin da shi kuma ya cigaba da kallonta, kuma kafin tayi wani tunani taji ya sunkuyo da fuskarsa dab da tata sannan a hankali yace.

"I want to borrow a kiss right now Doll, don in nuna miki godiyata, amma nayi al?awarin zan dawo miki dashi Allah."

Bata san lokacin da ta kyalkyale da dariya ba tana kokarin ture shi, amma sai ya kara rike ta yana fadin.

"Da gaske nake Allah, yanzun nan zan dawo miki dashi, kawai ki ara min."

Da ?yar ta samu ta fita daga hannunsa, ta koma falon ta barshi anan yana amsa wayar Ishaq, zuciyarta cike fal da daWin yadda ta isar da sa?on Amma cikin ?an?anin lokaci kuma ta samu fahimtarsa, ta gama da wannan babin insha Allah.

Kilishi ta jirayi abinda zai biyo baya, zata sha mamakin yadda asirinta zai tonu alhali ta san bata budewa kowa sirrinta ba, tunda ko ita ta san bata gaya mata ba, kawai sunyi amfani da kalamanta ne akanta. A yanzu saura abu na gaba da take da yakinin zai fi wannan... Abinda Amma tace ce.

_'...babu abinda zai faru, babu abinda zai sami yarinyar nan, amma kuma a idanun Kilishi komai zai faru, zaki cika mata wannan aikin nata sannan kuma zata kaimu Makkan har da wannan canjin na gida ma!_

Allah ya sani zuciyarta a tsaye take wajen jiran faruwar hakan.

"Zoben Sofia za'a fauko a cikin wannan ramin."

Hamida ta faWa tana nuna mata cartoon din da take kallo? a cikin Tvn, ta juya ta kalli ramin da take faWa kafin tayi dariya tana gaya mata cewa rijiya ce ba rami ba.

A daidai wannan lokacin ne kuma taji karar buWewar Gate alamun sunyi ba?i don ta san da daga cikin gida ne ta baya za'a shigo.

Ta gama canjawa Hamida rigar sanda aka kwankwasa kofar Wakin alamun koma waye ya karaso.

Don haka tayi saurin ajiye rigar a saman kujera sannan ta nufi wajen ?ofar, hannunta ya buWe a hankali daidai lokacin da fuskar matar ta shiga idanunta, tana tsaye da dogon hijabi tayin da fuskarta ke dauke da wani faffadan murmushi, kuma kafin kwakwalarta ta fara tunanin inda ta santa, taji muryar Hamida daga bayanta tace.

"Mariya???"


***

"Mun yi magana da mutanen, sunce hodar zata samu zuwa jibi, mutumin da zai kawo jirgi zai biyo don haka ka shirya gobe zaka tafi lagos, don bana son ta ko kwana a hannunsu, kudin dana kashe akanta da yawa, ba zamu yi sske na dage ba."

Hajiya Kilishi ta faWa a cikin wayar da take yi. Awwalu ya nisa alamun a kwance yake kafin muryarsa ta fito.

"Daga wace ?asa ma kika ce za'a kawo?"

"Mexico." Ta bashi amsa kai tsaye.

"To wai ta yaya ma za'ayi amfani da ita ne.?"

"Ba kai zaka yi ba, me yasa kake tambaya ta?"

"Saboda na lura tunda kika shigo da yarinyar nan cikin al'amarin nan na fara rage sanin wasu abubuwan. Kuma kina ganin kamar ban cancanci hakan ba."

Sautin muryar tasa ya fito ne da wani irin kauri alamun akwai layin harzuka a ciki. Sai kawai tayi murmushi sannan tace.

"Kar mu fara wannan Awwalu. Ka soke wannan tunanin a cikin ranka, ka kori shaidan daga gefenka. In dai akan wannan hodar ne ka bude kunnenka ka ji.

A cikin kwallin yarinyar za'a saka, a hankali take aiki, ana saka mata yau da gobe zata fara da ciwon ido, ciwon idon ne zai ta ?aruwa ana kuma cigaba da saka mata a haka har idon ya rufe gabaWaya ba tare da ko likitoci sun gano dalilin hakan ba."

Ta kai ?arshe ba tare da yace komai ba, kuma jin shirun nasa yasa ta ?ara da cewar.

"Idan mun gama da wannan sai kuma mu koma kan ?afarta, na tabbata lokaci zaiyi mana daidai da sanda zan gama da abinda ke gabana, kaga kenan zan tafi ba tare da na bar kowanne dutse a kife ba."

"Haka ne, Allah ya bamu sa'a, zan siya ticket Win jirgi anjima insha Allah."

Yadda ya fadi hakan a lokaci guda, kai tsaye, kuma yadda kalmar Allah har sau biyu ta fito a bakin Awwalun yasa ta tsayawa da nata shirun kafin a hankali a furta kalmar 'Ameen.' din da bata jin ta kai ?arshe sanda ya katse wayar.

Wayar ta katse tare da katsewar numfashinta da kuma tsayawar idanunta akan mudubin da taje kallo a gaban ta.

Me Awwalu yake nufi?

Me ke shirin faruwa ne?

Wake shirin girgiza mata tebur ne?


***

_Kun yarda da tunanin Amma? Kun gamsu da yadda ake amfani da zurfin tunani wajen samun mafita?_

_Ina so in dan haska muku wani abu anan, abubuwa da yawa na faruwa a cikin rayuwarmu da zasu wuce ba tare da mun basu wani muhimmanci ba, wani hira ce wani kuma actions ne._

_Amma kuma a cikin abubuwan nan akan samu abubuwan dake Sullewa zuwa abinda zai zame mana mafita a wasu matsalolin namu na rayuwa. Ba komai zamu dinga mantawa ba, ba komai zamu dinga shashantarwa ba... Komai kankantar abu zai iya zame mana mafita a wani babban al'amarin na rayuwarmu._

_An halicci ?wa?walwa da fadi, don haka bude ta ki zuba tarin abubuwan da baki san lokacin da zasu amfane ki ba._

_And kuna tunanin Amina ta gane wacece Mariya kuma daga ina take?_

_Ku taya ni gayawa Ma'aruf cewa Wan kunne yana da amfani a adon mace...=??_

_Sannan team Kilishi, me Awwalu yake shirin jawo muku ne?_=??

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*10*

~~~~~~~

_A love so wasted._ _- Unknown_


**


"What?"

Ma'aruf ya faWa da tsananin mamaki yana kallon fuskarsa a cikin mudubin Wakin dake fuskantarsa.

"Baka ji ni bane ba? Nace maka auren Munaya nazo nema."

Mamaki ya nuna tar akan fuskar sa yana shafa gashinsa ta baya.

"Wallahi da na iya zagi zan Wura maka wanda zaka kwana kana juyi Ishaq."

Daga cikin wayar Ishaq yaja tsaki sannan yace.

"Ai na gaya mata raini zata jawo min, amma tace in fara tambayarka tukunna, da wallahi sai dai kaji zancen."

Ma'aruf ya girgiza kansa.

"Let's talk serious, me kake nufi wai?"

"Da gaske nake B, ina son kanwarka, zan aure ta, kuma na gaya mata itama ta yarda, da Baba Usman zan gayawa amma wai sai tace in fara gaya maka tukunna, ban san me yasa yaran nan suke girmama ka har haka ba."

Tsabar mamaki bakinsa ya kasa rufuwa, sai kawai ta sake girgiza kansa sannan yace.

"Wallahi ban san baka da kunya ba sai yanzu Ishaq, ni kake tambaya wai kazo neman auren Munaya Ishaq?"

"Allah ya tsinewa kunya in dai taka zanji Ma'aruf, kai kanka ina ka ganta da za'aji maka? Maimakon ka fara godewa Allah ma kun samu mutumin kirki kama ta sai ka fara aibata ni? Ni dama na san wallahi raini Peaches zata jawo min kawai don tayi insisting ne."

Ma'aruf ya gyaWa kansa.

"Wato Peaches Ishaq, Munayan ce Peaches? ?ar mutane ce fa..."

Dariyar da Ishaq yayi a cikin wayar, dariya ce da ya dade baiji yayi irinta ba kafin yace.

"Kai ta gidanka ba ?ar mutanen bace ba? Malam in zaka shige min gaba muje wajen su Baffa kayi magana."

"Ba zanje ba, baza'a baka ba."

"Nagode Babban Yaya, Allah ya ?ara girma."

Da haka ya kashe wayar, Ma'aruf ya cije lebbensa yana jinjina al'amarin a cikin kansa, yana jin kamar ba gaske ba, wani iri, kamar a labari cewa wai Ishaq ne ke son Munaya, yarinyar gabadaya shekararta nawa? Shekara ta biyu take fa a Jami'a, kuma a Sangaren karatun da take yi na densistry bai taSa zaton cewa zaiji wannan al'amarin a kusa ba, Allah kaWai ya san yadda akayi Ishaq ya hure mata kunne.

Sai kawai ya zura wayarsa a aljihu sannan ya fita daga dakin da niyyar zuwa gobe yaje ya same shi suyi maganar hankali.

Tun daga korido yake jin maganganu alamun ?aruwar wani a gidan, don haka ya karasa a hankali tafin kafarsa na taka tiles Win wajen, ya ?arasa daidai lokacin da Amina ke kokarin ajiye tiren ruwa da lemo a gaban wata mata yayin da matar ke kallon Hamida tana faWin ta taho wajenta, ya tsaya daidai inda su baza su ganshi ba amma shi yana gano su.

"Au ba zaki zo ba sauraniyar Mama? Ba tafiya zanyi dake ba, kinga kaya ne nan ma Mammy tace in kawo miki."

Hamida ta matse kafadarta daya tana cigaba da kallonta ba tare da tace komai ba.

"Haba Princess din Daddy, Mama Mariya ce fa... Har labarinta fa kika bani."

Cewar Amina da murmurshi a fuskarta, amma duk da hakan Hamidan ta matse kafadarta.

"Ai shikenan kyale ta, da kanta zata zo,ni kujera ce ai."

Dukkaninsu suka yi dariya kafin Amina ta koma ta sami waje a kujerar da Hamidan ke zaune, suka gaisawa da matar da har a lokacin Ma'aruf bai gane daga ina take ba.

"Ai maman tata ce tace inzo in kawo ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?mata wasu kaya da aka manta ba'a hado dasu ba, har da na wasanta ma."

Ta faWa tana mi?o wata jaka dake gefenta.

Kuma yana ganin yadda Amina bata karSi jakar ba, amma fuskarta da murmushi? tace.

"Ai kuwa ?ika tana kewar kayan wasan nan, don tunda tazo kallo kawai muke ta sha."

Matar ta sake dariya kafin tace.

"Sai kuma wata mantuwa da akayi, a cikin waccan jakar tata wai akwai wani kayanta data manta shine take son in taho mata dashi yanzu."

Mariyan ta fada har yanzu da murmurshi a fuskarta, murmushin dake tsayawa iya fatar bakinta kawai ba tare da ya ?arasa ko'ina ba, don a wannan lokacin tana jin muryar Rukayya tana amsawa a cikin kanta da umarnin data bata kafin tahowarta, umarnin da ta bata bayan tasa ta shafe hannunta da wani bakin ruwa.

_"Idan kika gaya mata haka ta dauko miki jakar, zip din farko zaki bude, akwai wata bakar leda a ciki. Kina zaro ta sai ki bude kamar zaki tabbatar da abinda ke ciki, budewar kawai nake so kiyi Mariya, da kin bude shikenan kin gama cika aikin ki, sai ki kulle ta kawai ki dawo, ki dawo min da ita ki karbi kudinki. Cif dubu hamsin babu ragi."_

Tana iya tuna yadda zuciyarta ta cika da murna a lokacin, ta cika da wani irin Woki da kuma farin ciki, albashinta dubu ashirin ne kowanne wata idan an cire alkhairin da take samu a gidan, kuma ta kwashe shekara da shekaru tana aikin, don haka idan har ba adashi ta Wauka ba, ?arya ne ta tuna ranar data ri?e dubu hamsin a lokaci guda ta kanta.

_"Zip Win baya zaki bude ledar tana ciki, babu mai ganinta sai ke da kika wanke hannunki da wannan ruwan don haka kar ki tsaya komai, kina budewa zaki ganta .."_

Maganar da Hajiya Nafisa ta sake jaddada mata ta shiga kunnenta. Sai tayi saurin gyada kanta lokacin da Aminan ke mi?ewa da niyyar zuwa Wauko jakar.

"Who's she?"

Ma'aruf ya tambaya lokacin da ?afafunta suka tsaya a gabansa, fuskarta na nunawa da mamakin ganinsa da tayi a wajen. Sai kawai ta matso dab dashi sannan a hankali tace.

"Daga gidansu Hamida take, sa?o ta kawo."

Tana faWin haka kawai ya girgiza kansa.

"Dan na kawo miki Hamida bance har da Family Winta ba, babu ruwanki dasu, don me yasa zaki buWe mata kofa?"

Yadda yayi maganar yana ?o?arin Waga muryarsa yasa tayi saurin dago da hannunta ta rufe bakinsa. idanunta na haskawa da wani abu kamar mamaki, wani abu da yasa shi fahimtar cewa ransa ne ke ?o?arin Saci, don haka sai kawai ya girgiza kansa yana ri?e hannunta data fora akan bakinsa sannan yace.

"She's leaving." (Tafiya zata yi.)

Tafiya? Saboda me? Ta yaya zai ce yace mata ta tafi? Sai dai kafin tayi magana yace.

"I have my plans against mutanen nan, babu wanda zai sake ganinta for the meantime a cikinsu, don haka kar ki sake buWewa kowa kofa idan har kin san daga nan suke."

Muryarsa ta fito ne da wani irin kauri da kuma ikon da bata taSa ji ba yayin da fuskarsa take Wauke da wani irin yanayin da har yanzu bata san shi ba. Sai ta gyaWa kanta, amma duk da haka ta daure tace.

"Yanzu zata tafi, amma dan Allah ka bari in Wauko mata sakon tukunna, Wauka kawai zata yi sai ta tafi."

Idan har bai bari ta Wauko mata jakar nan ta duba taga cewar babu abinda suke nema ba, bata san me zata ?irga a matsayin nasararta da kuma sakonta da zai isa gare su ba, ya tsaya kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya gyada kansa a hankali yace.

"Ki Wauko ta tafi, I'll be out in two minutes, idan na fito ganta zan mata duk abinda yazo kaina wallahi."

Tana jin haka tayi saurin gyaWa kanta sannan ta saki hannunsa da sauri ta karasa dakin, bata ko tsaya rufe wardrobe din ba ta dauko jakar ta fito, ta samu baya wajen don haka kai tsaye ta karasa cikin falon.

"Ai tace sa?on itama ba nata bane, wai can Adamawa za'a kai, sai da aka zo tafiya dashi ta duba taga yana nan wallahi."

Cewar Matar tana ?arSar jakar har yanzu da murmurshi a fuskarta, ta mi?a mata da nata murmushin itama sannan ta zauna a kujerar dake fuskantar ta tana cugaba da murmushin dake nunawa tar a fuskarta.

_...wasa da hankalin mutane yana daya daga cikin abubuwan mafiya daWi a duniyar nan, ina jin dadi duk lokacin da na koma baya na kalli fuskokin mutanen da na Waure su tamau da hannayena ba tare da sun sani ba._

Wannan na daya daga cikin maganganun da Kilishi tayi mata ranar da ta fara bude mata ko ita wacece, amma ta manta su, basu sake zuwa cikin kanta ko sau Waya ba sai a yanzu, sai a yanzu da take kalllon fuskar Mariyan dake bayani tana kokarin neman zip din da aka kwatanta mata, da sanda ta gane shi, da sanda ta buWe, da kuma sanda hannunta ya shiga ciki kafin yanayin fuskarta ya canja a lokaci guda jin babu komai.

Sai kawai wani murmushi mai faWi ya Salle daga bakinta, tabbas mata masu wayo dole ne su ji da kansu.

***

"Tunda bank statement dinki za'a bayar, dole za'a haWa da affidavit da kuma I.d card dinki wanda yake dauke da signature."

Muryar Muhd, wani ma'aikaci a wajen da ake harkar shige da fice na visa ya fada cikin wayar dake kare a kunnen Hajiya Kilishi.

Hajiya Kilishi ta nisa sannan tace.

"Babu damuwa Muhd, duk zasu taho dasu, idan nasa kudin da zasu isa a cikin account din shikenan komai zaiyi daidai ko?"

"Eh, amma idan da hali Hajiya ki dan bar wani abu ko da dubu dari ne."

"Shikenan babu matsala, nagode."

Da haka ta katse wayar, tana tashi ta dauko wata jaka da ta fito da ita a gefen wardrobe din dakin, ta koma kan gadon ta zauna sannan ta fito da dukkan takardun ciki, a cikinsu ta dauko wata ?ar karamar takarda mai dauke da rubutun nambobi ta kwafi nambobin masu shaida wata account number sannan ta tura iya adadin kudin da ta san zasu isa a komai da komai na tafiyar su Aminu har kuma da dorin da muhd Win yace.

Ta tura kuma bayan an turo mata da sakon kwasar kudin, bata san sanda tayi murmushi ba ganin yadda wani Wan mitsitain adadi ne kadai ya sauka akan zunzurutun kudin dake cikin wannan account din.

Jiya ta turawa da ?anuwanta kudin da take basu a karshen kowanne wata suma, amma duk da haka gani take kamar bata taba kudin ba... Kudin da take da yakinin ko Baffa bashi da adadinsu a yanzu, bama shi ba, kamfaninsu gabadaya da suke takama dashi na Bakorin bata jin adadin da suke dashi ya kai jimlar na accounts dinta gaba daya.

Ita kanta ta sani cewa tayi kokari kokarin da ba kowacce mace irinta ce zata iya shi ba, ganin tsawon shekarun da aka dauka tana cika rantsuwa da kuma burin data daukarwa kanta tun zuwa gidan nan, tun bata da komai sai zuciyarta da tanadinta, gashi har an rufa shekarun da ta tara manya-manyan ?a?an da har ta aurar da biyu a ciki.

Wani abu ya ratsa zuciyarta na cewar ?a?an da take wa rabin wannan hidimar ma har yanzu basu da masaniyar komai, matsalarta kenan, wajen da take ganin faduwarta kenan... A kokarin binne komai don ta tafi a tsaftatacciyar hanya, bata taSa nunawa waninsu kalarta ba, har gwara? Salma, a kwanakin baya ta kan gaya mata cewa tanadin da take yi musu mai kauri ne, don haka idan har akwai wani abu da zata iya kira da ?alubalen da take shirin fuskanta, shine na yage su Samirah da zata yi daga wannan gidan da kuma mahaifinsu.

Ta nisa a hankali, tana lissafi a cikin kanta. Komai yana tafiya daidai, ta riga ta gama da dukkan wata harkar kashe kuWi a shirye-shiryen tafiyar mahaifin Amina da kuma Wanuwanta Aminu, so take su tafi har su isa can a fara yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login