Showing 93001 words to 96000 words out of 132946 words

Chapter 32 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1153

a lokaci guda da sauran bayanin Sadik din ya Sace daga cikin kunnuwanta, ba shiri dukkan jikinta ya shiga rawa yayin da ta nemi gefen gadon nata ta zauna, hannunta daya da baya rike da wayar ya kamo zanin gadon don neman tallafi.

"Kana ina yanzu Sadik, ka bar wajen?"

Ta tambaya da sautin da taji kamar ba nata ba saboda ?arar buguwar zaciyar tata da shi kaWai take iya ji har a yanzu. Tun da rana da ta daga labulen dakinta ta kula da gajimaren da ya baibaye sararin sama,? ya rufe ta kusan bakidaya saboda haka babu kadawar iska sosai, amma bata tabbatar da hakan ba sai a yanzu da take jin gumi ko tawanne Sangare na lulluSe ilahirin jikinta.

"Ina daga gefe Hajiya, na le?a layin ne sai na dawo daga baya nake kiranki."

Wannan karon, muryar Sadik Win ta amsa tar a cikin kanta.

Sai ta mayar da wani abu dake shirin tasowa daga makogwaronta kafin tace.

"Motocin ?ansanda ne kaWai a wajen Sadik?"

Ya girgiza kansa.

"A'a akwai wata karamar mota kirar Accord."

Accord. Accord... Kalmar ta rangaWa a cikin kan Kilishi ta sigar tashin hankalin da ba'a saka masa rana ko lokaci. Accord motar Ma'aruf ce! Me yake shirin faruwa? Ta yaya zasu gano Awwalu? Ta ina? Ta ina tunaninsu zai iya samo Awwalu? Ba shi yaje ya mi?a kansa ba ta tabbata, don idan haka ne a ?ofar dakinta waWannan motocin ?an sanda ya kamata su tsaya ba'a gidan Awwalu ba.

"Sake komawa Sadik, sake komawa yanzun nan ka karanto min lambar karamar motar..."

"Hajiya..." Sadik ya furta muryarsa na shaida fargaba.

"Laifi ba'a manne yake a goshi ba Sadik, babu wanda ya sanka kuma babu wanda zai gane ka, ka koma ka karanto min lambar."

Yadda muryarta ta fito a kausashe tana shaida tsananin tafasa da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kuma rudanin da take ciki yasa Sadik haWiye maganar dake bakinsa sannan yace.

"Shikenan, bani minti biyu..."

"Kar ka kashe wayar..."

Ta katse shi da sauri, don bata sani ba idan har kofofin hancinta zasu iya sha?ar iska tsawon lokacin da zata jira shi. Tana jin ?arar takunsa, zuciyarta na bugawa tare dasu har zuwa lokacin da ya isa wani waje da hayaniyar mutane ta shiga kunnenta a lokaci gyda, taji shi yana ratsawa ta cikin mutanen kafin muryarsa ta fito da harafan nambar motar Ma'aruf cikin amon muryarsa da Kilishi ta sani cewa har bayan ranta ba zata taSa mantawa da ita ba. Don a wajenta, a bangarenta wannan lokacin shine mafarin komai, shine mafarin wata rayuwar da a yanzu bata santa ba.

***

*Current Situation...* *( Halin da ake ciki.)*

"Ta farka?"

Sune kalamai na farko da suka fara shiga cikin kanta, sune abinda ta fara ji kuma cikin amon da yake mafifici a wajenta, amon muryar da take tunanin ko a bayan kasa take babu ta yadda za'a yi ta kasa tantamce shi. Ma'aruf. Ma'aruf...

Zuciyarta ta biya sunan sau biyu kafin wata murya a cikin kanta ta ?wallara kara, Ma'aruf? Me ya kawo Ma'aruf inda take? Me yazo yi a wajenta a wannan lokacin? Tsaya wane lokaci ne ma? Sannan a ina take tukunna? Tayi yunkurin bude idanunta amma kai tsaye sai wata zuciyar ta hane ta da hakan kai tsaye don haka ta fasa a daidai lokacin da muryar wata mace ke cewa.

"Gashin idonta yana motsi, da alama yanzu zata farka..."

"Tun Wazu abinda kike fada kenan, just go and call the Doctor."

Taji Ma'aruf ya sake fada yanayin muryarsa kamar a hasale.

"YallaSai na san aikina fa, idan da bukatar kiran likitan ai..."

"Ni zaki gayawa kin san aikin ki? Kin san aikin ki tun 8 kike zirga-zirga anan ta tashi ne?"

"B, Calm down ta san me take yi mana..."

Muryar Ishaq tayi saurin katse shi.

"Wannan tabe-taben banzan ne ta san abinda take yi Ishaq?"

Ya sake faWa muryarsa na cigaba da Wagawa cikin fushin dake fitowa karara, kuna matar bata yi shiru ba ta sake cewa.

"Amma dai ka san mu bamu isa mu tashe ta ba idan har..."

"I don't f*cking care! Idan har me?all I know is mun kawo ta nan ne don ta sami lafiya."

?arar sakin wani abu ta cika iskar dakin kafin muryar matar ta sake cewa.

"Then ga ka nan gata ai, sai ka bata lafiyar."

Da haka taji matar ta juya karar takunta na yin nisa daga inda Kilishi take a kwance yayin da maganganun su Ishaq Win ke ?ara shiga kunnenta, sai dai ba su Hajiya Kilishi ke saurare a wannan lokacin ba, tunaninta yayi baya ne yana tarewa ga abinda ya faru jiya don ta fahimci abinda ke faruwa yanzu.

Abinda ya faru bayan Sadik ya kira mata lambar motar Ma'aruf a ?ofar gidan Awwalun, cewa tayi ya jira ta a wajen gata nan zuwa. Don a lokaci guda kwakwalarta ta gaya mata cewa tunda har ?ansanda suka zo neman Awwalu basu same shi ba, to tabbas dole ne ita ta fito su san yadda zasu yi su nemi inda Awwalun yake a wannan daren ita dashi don ta gama da babinsa kafin komai ya caSe mata.

Don haka tayi saurin yin transfer wasu kudade daga bankinta na ajiya zuwa na amfaninta da kowa ya sanshi da ita sannan ta debi kayan waWannan allurorin ta zuba a leda ta fita, ta fita a lokacin da kusan duk jama'ar gidan ke Sangaren Hajiya Maimuna na murnar dawowar Abdurrahim, ta fita babu wanda ya ganta don ko Maigadi bata samu a gate ba shima.

Da kafarta ta taka har bakin titi inda ta samu wani mai keke napep Win da ya sauke ta a shagon wani mai POS ta ciro dubu dari biyar daga account din ta zuba su a wannan ledar don ta riga ta gama shirya yin asarar ko nawa ne a jiyan don samun inda Awwalu yake.

Tana iya tuna yadda zuciyarta ta dinga bugawa a kirjinta a lokacin, tana iya tuna yadda ta kasa zama waje guda cikin keke napep Win zuciyarta na cikowa a ?irjinta,
har ?o?arin tsugunnawa tayi ta kuma yi ?o?arin tashi tsaye, daga baya ma taga kamar mutumin baya gudu sosai don haka tace dashi ya tsaya, ta sauka ta bashi kudinsa sannan ta tsaya neman wani, tana tsaye tsabar ruWewa da kuma yadda kanta yake juyawa sai taga kamar daya barin titin an fi samun keke napep Win da babu kowa.

Kuma a lokacin ne abin ya faru, a lokacin da tazo tsallakawar ne motar ta buge ta, taji lokacin da ta tashi sama, numfashinta na biyo ta sannan taji lokacin da ledar hannunta ta suSuce, tana gaya mata cewa? kuma abu na ?arshe da zata iya tunawa kafin numfashinta ya yanke shine taji hayaniya da kuma salatin mutane da yawa a saman kanta.

A yanzu a asibiti take kenan, asibiti ne daga maganganun da taji suna yi a saman kanta.... Salatin da bakinta ba zai iya ba shi zuciyarta ta karanto ta kuma sake karantowa, ina ledar dake hannunta ina kuma wayarta? Me yake shirin faruwa ne? Wane irin mummunan mafarki ne wannan? Ta yaya Allah zai jarabce ta da hadarin da har zai kai ga kwanciya a asibiti a wannan halin da take ciki? Ina ledar hannunta ina wayarta? Inalillahi wainna ilaihir raji'un... zuciyarta ta ambata tana sakewa, don abu na ?arshe da zata so yanzu shine ace ledar hannunta dama wayarta tana hannun da bai dace ba, hannun da zsi iya tona asirinta ba tare da wata wahala ba.

Tayi kokarin yin motsi kaWan, a lokacin ne taji yadda kanta ke juyawa kotawanne Sangare, jikinta yayi tsami kamar anyi mata duka.

"Har yanzu akwai ?an sanda a ?ofar?"

Taji muryar Ishaq ya tambaya, tambayar da ta haddasa dokawar ?irjinta a lokaci guda, bugawar da ta nemi dagargaza zuciyarta, bakinta ya sake karanto kalar wani salatin da bata taba sanin ta iya shi ba... ?an sanda? A ina?

"Suna nan baza su tafi ba ai, Baffa yace babu yadda baiyi? dasu ba, amma har sun tura maganar sama, don haka babu yadda za'ayi a rufe case din tunda shi DPO din da ya kade ta ma yaki saurarar Baffan su sake magana."

DPO? DPO'n ?an sanda ne ya kaWe ta? Kuma yaga abinda ke cikin ledar hannunta? Yaushe duniya ta tsuke har haka?

Muryar Ma'aruf ta fito da kaushi, kaushin dake shaida tsananin Sacin rai mai haWe da tashin hakalin da baya Suya. A cikin kanta ta kintaci cewa ya girgiza kansa kafin ya cigaba da cewa.

"There must be a mistake dole Ishaq, me Mami zata yi da allurar ?waya irin wannan? Sannan har da kudi five hundred thousand a cikin leda? Na yarda framing dinta kawai wasu ke ?o?arin yi tunda ko Baffa ma bai san da fitar ta ba... Kuma ban san me yasa ba amma jikina yana bani cewa wannan al'amarin yana da alaka da case Win da muke yi, shi yasa nake so ta farka tayi bayanin komai waWannan ?an i*kan su bamu waje."

A wannan lokacin ji tayi kamar ta mi?e zaune ta girgiza kanta, ta gaya musu cewa ba zai yiwu ace komai ya caSe mata a wannan lokacin ba...

Ba zai yiwu ba, tana da sauran lokaci,? damarta bata taba karewa ta sani, tsarinta kullum daidai yake tafiya don haka ko a yanzu da take iya jin tsananin damuwa daga muryar Ma'aruf ta sani zaren bai ?are mata ba, tana nan a Mamin da take a idanun kowa abunda ya rage kawai shine ta bude idanunta ta ture wannan ?alubalen ta cigaba daga inda suka tsaya... Zata san yadda zata yi ta fidda kanta ta sani... Sun ga ledar a hannunta amma hakan ba zai basu tabbacin komai ba tunda babu wayarta.

Wayarta, babu wayarta, basu same ta ba, don haka ba shiri ta haWiye wani abu a ma?ogwaronta, komai da sauki, komai zai zo da sauki kenan, ba'a kama Sadik ba, tana da sauran fata ta san yadda zata yi komai ya tafi daidai, ta sani.... Ita Kilishi ce kuma ko a wani hali tana da mafita...

"Ka cire tunanin wadannan mutanen a ranka B, babu inda zasu je idan har ba umarni aka basu daga can ba."

Ishaq ya faWa daidai lokacin da ya daga wayarsa kuma ba sai yayi wani bayani ba daga gaisuwa kawai Kilishi ta fahimci cewa da Hajiya Maimuna yake magani.

"Mami baza su barku ku shigo ba, mu ma da I.D cards Winmu muka yi amfani, yanzu ma so muke mu samu ta farka watakila komai zaiyi sauki..."

A lokaci guda hankalin Kilishi ya dugunzuma ya ?ara tashi, ak'amarin ya kai har a hana nakusantan ta ziyartar ta? innalilahi wa'inna ilaihir raji'un! Ta ina zata fara neman mafita idan har al'amarin ya kai haka? Me zata fara kamawa a yanzu? Ta ina zata fara bayanin inda ta samu allurar da kuma wajen da zata je? Wannan wane irin mummunan tashin hankali ne? Me yasa komai zai Sare a lokacin da bata shirya ba? Me yasa sai a wannan nisan sannan ?alubalenta zai zo? Don ta yarda har yanzu wannan ?alubale ne, babu ta yadda za'ayi ace wannan shi zai kawo ?arshen ta, tana da mafita a komai na rayuwarta, tana da ita ta sani! Kawai zata fuskanci wahala ne kafin ta daidaita komai.

"Hajiya ce, wai su Samirah ne har da kuka zasu taho..."

Taji Ishaq ya faWa bayan ya ajiye wayar da yake yi.

"Babu wanda zai zo, su bari mu san me ake ciki ma tukunna, idan sun zo me zasu yi?..."

Cewar Ma'aruf yana jin tasirin abinda ke zuciyarsa na yin yawa, kuma Ishaq din bai ce konai ba, shiru ya ratsa dakin kafin wayarsa tayi kara, kuma yana jin ya dauka? ya fara waya zuwa office Winsu, sai kawai ya mi?e, ya mi?e tsaye ya nufi kofar Wakin, kuma bai kira komsi ba ya kama hanya ya fita.

Missed call Win Faruk guda biyar ne, duka bai san lokacin da ya kira ba sai kuma na Amina guda biyu.

Amina ya fara kira kafin Faruk Win, kuma sautin muryarta, wannan sassanyar muryar tata, shine abu na farko da ya tuna masa da irin tarin wahala da kuma gajiyar dake jikinsa, wanka kawai yayi a jiya lokacin da Baffa ya kira shi da zance mafi tashin hankalin da hafi ba zagayen halin da yake ciki, cewar wani dan sanda ya kira shi da cewar ya kade Mami akan titin hanyar gidan Gwamna, sannan sun tsinci wasu miyagun kwayoyi a cikin ledar dake hannunta.

Yana iya tuna magiyar da ta dinga yi masa a lokacin, magiyar cewar ya fada mata abinda ke faruwa, amma bai iya ba din,rigar da take miko masa a lokacin ya karSa kawai ya zura a jikinsa sannan ba tare da ya damu da taje barbajajjen gashin kansa ba ko kuma ya shafa mai ya dauki mukullin motarsa kawai ya fito, ya fito ya barta ita da Hamidan dake binsa a baya da nata tambayoyin da kuma kwanukan tuwon nan da yaci burin huce gajiyarsa dashi kamar me...

"Babydoll...."

Muryarsa ta fito a hankali bayan ya shige cikin motarsa. Kuma maimakon ta amsa sai tace.

"Ya jikin nata? Hajiya tace har yanzu bata farka ba."

Hannunsa daya ya mi?a cikin barbajajjen gashin kansa sannan ya rufe idanunsa gabaWaya yana jingina da kujerar motar.

"Bata farka ba, amma soon insha Allah."

Amina ta gyada kanta, tana zaune ne akan kujerar falon gidan tare da Hamida tmda tayi bacci akan cinyarta, basu dade sosai da dawowa daga cikin gida ba, don kamar kowa suma kusan a zaune suka kwana ana jimamin abinda ya farun, a yanzu ma ta dawo ne ta yiwa Hamidan wanka ta kuma bata abinci, wanda bayan ta gama ne bacci ya dauke ta.

"Kana tare da ita ne?

Ta sake tambaya a hankali. Ya girgiza kansa a hankalin shima.

"Na fito,ina mota yanzu."

"Dan Allah ka dawo gida kafin ka tafi wani waje... Baka ci komai ba fa.." ta fada ksmar zata yi kuka.

Yayi shiru kaWan kafin yace.

"Kina ganin zan iya cin wani abu yanzu?"

Ta gyaWa kanta a hankali.

"Zaka iya Sugar, saboda babu abinda zai faru insha Allah, komai zai tafi daidai kawai jiran sakamakon ne mai wuya..."

Ya gyaWa kansa a hankali.

"Na sani Noor, da wuya sosai... Mami kamar mahaifiyata ce, ina jin ta har cikin raina wallahi hankalina ba zai taSa kwanciya ba ace wasu sun saka ta a cikin wannan halin, babu abinda ya same ta amma har yanzu bata farka ba Amina, bamu san meye matsalar ba har yanzu, amma kuma duk da haka ace gaan saka ?an sanda suna gadinta sun hana kowa shiga..."

?wallar da ta cika idanun Amina ta gangaro zuwa kumatun ta, Allah ya sani tsoro take ji, tsoro take ji sosai na ranar da Ma'aruf zai san wacece Kilishi, don bata san yadda za'ayi zuciyarsa ta iya daukar masa hakan ba, bata sani ba ma idan har zai iya daukan...

Sai ta share su da bayan hannunta Waya sannan tace.

"Babu abinda zai faru Insha Allah Sugar, alkhairi kaWai Allah zai azurta rayuwarmu dashi insha Allah."

"Insha Allah." Ya faWa a hankali yana buWe idanunsa sannan yace.

"Zan aiko direba ya karSa min abincin, ba zan iya dawowa gida yanzu ba Babydoll, ayyukan dake jira na a office suna da yawa, yanzu ma na ga missed call din Faruk kusan biyar ban dauka ba."

Ta cije lebbenta kaWan na ba hakan ta so ba, amma tasirin uzirin da ta san dole ne tayi masa ya danne son ran nata don haka tace.

"Shikenan Allah ya kaimu yazo Win..."

"Kar ki sake yin komai, ki bar min Wumamen tuwon nan kawai."

Tayi murmushi jin daWin cewa har yanzu bai manta da tuwon ba sannan ta gyada kanta a hankali.

"Insha Allah Habibi albi."

Ma'aruf ya sake lumshe idanunwansa yana jin tasirin muryarta da kuma sabon sunan a jikinsa. Yayi shiru kawai ba tare da yace komai ba, itama tayi shiru bata sake cewa komai din ba, kuma a cikin shirun yake yake jin kamar dukkan gajiya da kuma damuwarsa suna bin iska ne, sai dai hakan baiyi nisa ba sakamakon shigowar kiran Faruq da ya sake shigowa, ya Wago da wayar ya kalla kafin ya sake maida ita kunnen nasa.

"Babydoll ki min hakuri please, zan Wauki kiran Faruq."

"Ba komai, kaje kayi aikin ka kawai, amma dan Allah ka turo direban da wuri."

"Insha Allah thank you so much for ur care." ( Nagode sosai da kulawarki.)

"Aiki na ne Sugar."

Ta faWi abinda ya saka shi murmushi ba shiri, murmushin da yake Wan mitsitsi amma ya taSo har cikin zuciyarsa.

Kiran Faruq Win ya Wauka ya kara a kunnensa.

"Faruq..." Ya furta muryarsa na fitowa yadda take.

"Ma'aruf kana ina?"

"Ina asibiti. Har yanzu bata farka ba."

Ya faWa yana kallon rubutun 'Amenity 4' Win dake can gabansa kamar yana son ya tabbatarwa kansa da hakan.

"Kazo office yanzun nan Ma'aruf, ga Brothernka anan yana buWe mana aiki..."

Ba shiri ya mi?e zaune sosai yana buWe idanunsa.

"Wane brothern? Waye? Me ake yi?"

Ya jero tambayoyin a lokaci guda harshensa da ma muryarsa na ?o?arin karyewa wajen tambaya.

Daga cikin wayar, Faruk yayi murmushi mai sautin da ya ji shi kafin yace.

"Brothernka da ya dawo jiya Abdurrahim, yaron nan wuta ne B, kazo ka ga aikin da yake yi, gabadaya forensic department din da muke dasu baza su iya ba B... Walkahi kowaye a bayan aikin nan, al?iyamarsa ta tsaya!"

Faruk ya faWi hakan a lokaci guda da? kwakwalar sa ta tuna masa abinda Baffa ya gaya masa da safoyar yau.

_"Abdurrahim ya fita yace zai fara zuwa kamfani, inaga daga nan zai zo ya ganta shima idan zasu bari ya shiga...!"_


***

A ?ofar wani ?aton Gidan ?asa Jawad ke tsaye a jikin motarsa, idanunsa na kan ?ifar gidan ne wanda tarin mutane ke ta fitowa ta cikinta kamar gidan tururuwa.

Har yanzu lissafi kwakwalar sa kawai take yi na yadda abubuwa ke faruwa dashi bi-da bi, yadda duniyarsa ke tsukewa tana waje guda tarin abubuwan na bayyana gare shi, Waya bayan Waya kuma kowanne baya yin nisa da guda.

Kusan minti talatin kenan a dazu da Zainab ta gaya masa cewa garinsu ya kawota, garinsu,inda gidansu yake kuma inda mahaifiyarta take. Mamakin hakan ya harba cikinnkwakwalwarsa da tasirin wani abu da bai san shi ba, tsayawa kawai yayi yana kallonta yayin da hannunsa ke kan sitiyarin motar yana kokarin juyawa, bayan sun rabu da Nura ne, wannan saurayin da yayi masa rakiya har gidan da ya samo lambar da bai tabbatar idan zata amfane shi ba.

A lokacin har sun sauke Nuran ya juya kan motar suna shirin barin garin, kanta yana ?asa tana wasa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login