Showing 30001 words to 33000 words out of 132946 words

Chapter 11 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1134

ita da kuma Inna Danejo... Har Innan na ta tsokanarsa cewa jinin tsofaffi ne dashi don wai tana da kishiya data rasu mai suna Amina.

Sannan ga Ma'aruf ma, yadda ya dinga yi mata jiya kadai ya isa ya shaida mata irin nasa jin dadin, don har godiyar yayi ta radawa a kunnenta, godiyar ma da daga baya ta kasa tantance gabadaya ta mecece. Yanzu babban abinda ya rage shine ta roke shi ya barta taje gidansu kafin Hajiya Kilishi ta sake Wago da wani abun ko kuma ita ta cigaba da nata takun.

Don Allah ya sani tana kewar ?anuwanta fiye da yadda zata iya misaltawa, shi yasa ko a jiyan da suka yi waya da Fati da kuma Maryam a wayar Fatin, bata ko sake yi musu zancen zuwansu ba, don ta yiwa kanta alkawarin da kanta zata zo sai dai su biyo ta daga baya.

A wanan lokacin ne kuma Ma'aruf ya karaso ta bayanta, ta san shine don a lokaci guda ya? hanayensa zuro ta gefen cikinta duka biyun ya rungumota ta baya, fuskarsa ta sauka akan kafadarta guda Waya yayin da Wumin fatarsa da kuma na hannayensa suka ratsa jikinta a take... Zazzabi ne kuma ya kama shi?

Babu shiri ta juyo da sauri tana kallonsa, sai yayi mata wani guntun murmushi sannan yasa yatsansa Waya yana taSa gashinta da ya fito ta gaba kamar yana karkaWe mata wani abun, a lokaci guda taji zuciyarta kamar ta fashe a kirjinta, dumin hannayensa ya shiga ratsa fatar goshinta yayin da numfashinta ya fara rawa a kirjinta, ta zata ta fara sabawa... Sai kawai ta buWe baki tace.

"Zazzabi kake... yi?"

Ya girgiza kansa a hankali.

"Lafiya ta kalau, na gaya miki na warke tun jiya, ko baki yarda ba?"

Ta girgiza kanta itama.

"Jikin ka da zafi har yanzu."

Sai kawai ya jawo duka hannayenta biyu dake Wauke da kowanne dusters Win nan jikakku, ya kara su duka biyun akan kumatunsa sannan yace.

"Kina jin zafin har yanzu?"

Tayi wani guntun murmushi sannan ta girgiza kanta.

Ya cije lebbensa kaWan.

"Na so kince A'a, don ina da wasu hanyoyin da zan nuna miki cewa lafiyata kalau BabyDoll."

"Me yasa kake kirana haka nr?"

Yace.

"Saboda kina min kana dasu, wadanannan siraran ?antsanan da nake gani su Sahla suna wasa dasu da."

"Zanyi kiba kwanan nan, kar ka damu."

"Da gaske?"

Ya tambaya ysna kara matso da fuskarsa kusa da tata.

"... Me zai saki kiyi kibar?"

Tana murmushi har yanzu ta Wauke hannyenta daga fuskars ta dan ture shi baya ta kafadunsa sannan tace.

"Idan nayi zaka gani."

Yayi baya ya dawo sannan ya girgiza kansa.

"Ki gaya min idan akwai gudunmawata kinga sai na fara shiryawa tun yanzu."

Yadda yake maganar ya sata yin dariya kafin tayi kokarin juyawa a hankali don karasa shanyar na hannunta, amma ya dawo da ita.

"Seriously idan kiba kike so na san ta yadda zamu samo ta, kawai ki gaya min."

Ganin da gaske yake yasa ta kara ture shi tana dariya.

"Nan fa waje ne, beside rana tana tayi ma bamu yi breakfast..."

Muryarta ta katse sanda ya dora goshinta a saman nata, idanunta suka shiga haskawa da mamaki da kuma tsoro tace.

"Wani zai iya shigowa fa..."

Ya girgiza kansa, motsin na tafiya da nata kan.

"I don't care, let them... koma waye ban damu ba 'cox i'm trying to find my inner peace here." (Kwanciyar hankalina nake nema anan.)

Ya rufe bakinsa daidai lokacin da ya sinkuyo da fuskarsa cikin wuyanta yayin da tasa duka hannayenta biyu masu rike da jikakkun duskter din nan ta ri?o gaban rigarsa saboda yadda take ji jikinta na rawa kamar zata fadi.

Kuma a daidai lokacin ne, wannan kofar bayan nan dake Sullewa zuwa hanyar cikin gida ta buWe, Hajiya Kilishi ta fara shigowa sanye da wani dogon hijabinta na sallah sannan ?awarta Hajiya Salamatu ta biyo baya, daga bayansu, Sameera ce ri?e da wannan jakar Pink, yayin da Surayya ke binta Wauke da Hamida.

***

_Watakila bani da abinda zance game da chapter nan, ku gaya min ra'ayinku kawai._

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*06*

~~~~~~~

_You will know when it's love, real love, 'cox you will start believing in destiny._

**

"A hankali zaki kwantar da ita ta gefe."

Amina ta faWa lokacin da Surayya ke kokarin kwantar da Hamida da tayi baci a jikinta kan gadon a hankali.

Surayan ta sunkuyo tana kokarin ajiye ta dadai inda Amina ta sake shimfida bargo da ta ninke gida hudu akan gadon.

"Kar ki sake ta sai ta taSa gadon."

Amina ta sake faWa a hankali lokacin da ta kai ?arshe da ita kuma a hankalin Surayya ta ajiye ta sosai akan bargon sannan ta zare jikinta da kadan kadan, da farko Hamidan tayi kamar zata tashi amma kuma sai ta koma ta kwanta alamun baccin ya dauke ta da karfi, Amina ta karaso rike da wani farin? mayafinta dan karami ta rufa mata a jikinta, suna kallo su duka biyun har fuskarta ta saki jikinta sosai akan bargon.

"Kar ki damu insha Allah ba abinda zai canja da zuwanta, kawaidai maganar da su Mami ke tayi alsn rashin kyautsawarsu ne da suka kawo ta da sassafen nan babu wani bayani."

Cewar Surayyan tana cigaba da kallon yarinyar. Amina tayi murmushi itama tana kallon yarinyar kafin ta sunkuyar da kanta a hankali tana kallon yatsun hannunta, ba wai zancen Hamidan ne ya dame ta a yanzu ba, tunanin tarin abubuwan da bata gama saninsu bane game da al'ummar gidan dama Ma'aruf din kansa, sannan kuma tunanin halin da ta lura Ma'aruf na ciki tun sanda taje falon.

Tayi zaton a yau sau Waya zuciyarta zata tsorata kamar yadda tayi a dazu, a dazun da taji karar buWe kofar nan ta baya, Samirah ta taba gaya mata cewar kofar tana kara ta samu mai ta saka mata, amma bata taba tunanin cewar mantawar da tayi zaiyi amfani ba sai a dazun da karar buWewar tata ta cika wajen, wanda a lokacin guda ta ture Ma'aruf daga jikinta ta ruga ta koma cikin gidan ta kofar kitchen din dake bayansu.

Bata san waye ba amma tun a lokacin zuciyarta ta gaya mata cewa koma waye din bai dace ya gansu a wannan yanayin ba, sannan bayan rashin dacewar ma ta sani hanya ce da al'amura zasu iya cakude mata tun yanzu, ilai kuwa sai ga mutanen da bata taba zato ba, Hajiya Kilishi da kanta har da wata da ta kira Aminyarta da kuma su Surayyan.

Ta tuno yadda hannayenta suka dinga rawa lokacin da take kokarin zaro dogon hijabinta daga cikin abin sallarta bayan ta taho da sauri zuwa daki, da kuma yadda Hajiya Kilishin ta dinga bin hijabin nata da kallo bayan ta fita gaishe su, kamar tana son Wage shi ne don ta gano wane irin kaya ne a jikinta.

Kuma kamar yadda Mamin take haka matar da ta kira kanta ?awarta take, duk da cewa tana ta faman addu'a da sanya fatan alkhairi a cewarta bata sami zuwa biki ba, sai dai daga ita har Ma'aruf don a wannan lokacin ba jinta suke yi ba, Ma'aruf din na can tsaye a hanyar kofar fita daga falon kusa da window yana waya da Ishaq rike da yarinyar da Surayyan ta shigo da ita yayin da nata idanun ke tafiya kansu duk bayan wucewar sakan guda tana jin zuciyarta na sake yin rawa a kirjinta.

"Sunanta Hamida Amina, ?arsa ce."

Abinda Mamin ta fada kenan bayan lurar da tayi da kallonsu da take yi da kuma cewar wayar Ma'aruf Win ba mai karewa ba ce a kusa.

Tana tuna yadda zuciyarta ta doka a ?irjinta kafin ta haWiye wani dun?ulen abu tana wasa da yatsun hannunta.

"Nayi zaton ai a cikin surutan yaran nan sun gaya miki zancenta, tunda tun kafin bikin ku ake ta case din dawowar tata wajensa."

Sai ta girgiza kanta a hankali yayin da Surayya ke cewa.

"Mami hirar ce dai bata taba zuwa ba idan muna tare, amma ai ko daga colander bakin Samirah zata iya ji."

Amina bata ce komai ba har sanda Hajiya Kilishin ta sake cewa.

"Kuma shima ban ce ya gaya miki bane shi yasa duk aka taru aka manta."

Ta fadi hakan muryarta na haskawa da wani irin yakini da kuma izza wadda wanda ya santa irin sanin da tayi mata ne kawai zai fuskanci manufar kowacce kalma dake bayan maganar tata, da kuma dabarar cewa itace mai juya duk wani al'amari da ya shafi mutanen gidan. Kuma Amina tana tuna yadda wata busashshiyar iska ta shiga wucewa ta makogwaronta kafin ta gyada kanta.

Samirah ta tafi a lokacin don tace kitchen ta baro ta taho, don haka ko da ta gama gaishe dasu bata zauna a falon ba, ta mi?e ta dawo Waki, a bakin gadonta ta zauna tunaninta na zarya kan tarin abubuwan da bata san yawansu ba a cikin kanta yayin da take jin muryoyinsu daga nan Ma'aruf ya dade yana wayar nan kafin taji ya gama su dawo magana dasu Mamin, tana jin muryarsu amma bata san me suke cewa ba har zaman shirun ya ishe ta, gashi wayar nantana hannunsa balle ko ba ta kira Amma don ta sanar mata ba, ta kira taji ya jikin Aminu.

Sai kawai ta fito da wasu mayafai da hijabanta da har yanzu ke cikin akwatunan lefen nan ta fara ninke su tana samo musu waje a gefen inda take sa kayanta, a haka Surayyan ta karaso ta same ta Wauke da yarinyar da tayi bacci.

"Ki kyale Mami kawai Amina, na san Ya Ma'aruf zaiyi miki bayanin komai, ita ba lallai taga hakan a matsayin wani abu bane."

Surayyan ta ?ara faWa?wannan karon tana kallonta, kuma ba shiri itama ta dago da fuskarta ta kalle ta.

A zagayen tunaninta kaf dama yadda ta fahimta tayi zaton ai babu mai iya ganin rashin daidain Hajjiya Kilishi balle har a su fahinta, amma da sigar da Surayyan ke mata magana a yanzu sai taga kamar tana nuna cewar bata ji dadin yadda Mamin tayi mata maga a dazu bane wanda ita ta san dalili, Ma'aruf baya zaune a wajen... ?awarta kuma Hajiya Salamatu ta riga ta san da abin dake tsakaninsu da alama, Surayyan kuma dake zaune bata damu da abinda zata yi tunani ba.

Lokacin da suka fita zuwa falon babu kowa, su Mamin sun tafi Ma'aruf kuma bata san inda yake ba, Surayya tayi mata sallama ita kuma ta kwashe kayan lemonta da basu taSa ba ta koma kitchen.

Zuciyarta na ta sake-sake tana maida kayan wajensu lokacin da taji shigowar Ma'aruf yana waya, kuma daga sautin muryarsa ta ji ya wuce zuwa hanyar daki don haka ta dauko kayan breakfast dinsu da ta riga ta haWa ta taho zuwa dakin.

"Ka bar ta kawai Ishaq, ka barsu kawai... tunda ka tura musu da wannan shikenan I have my plans against them. Sun yanke wannan hukuncin, na karba, zasu ga me zai biyo baya kuma."

Muryarsa ta fito ne a hankali da tsananin damuwar dake kwance fal a cikin ransa, damuwar da tun a dazu ta san da ita, amma yawanta a yanzu ya ninku ta yadda take jin da zata iya, zata ?wace wannan wayar ne don kowa ya daina kiransa yana ?ara gaya masa abubuwan dake hargitsa shi.

Yana zaune daga gefen gadon ya sunkuyar da kansa hannunsa Waya ri?e da wayar Wayan kuma ya zura hannunsa a cikin gashinsa yana magana. Ta karasa ta ajiye tray din hannunta akan bedside drawer dake gefen gadon.

Ya dago ya kalle ta sau daya sai kuma ya cigaba da sauraren bayanin da Ishaq din ke yi ta cikin wayar. Tana jin yadda jikinta babu nauyi kwata-kwata? ta shiga kokarin hada tea a kofi guda bayan ta zuba dankali da kwan da ta soya a plate ta ajiye a gabansa, lokacin da ta gama haWa tean ta juyo don ta miko masa ya gama wayar.

"Kin zuba naki?" Muryarsa ta fito a hankali yana kallonta.

Sai ta girgiza kanta.

"Yanzu zan zuba, ka fara karSa tukunna."

Sai kawai ya mi?o hannunsa ya riko kofin, ya hada har da hannunta gabadaya, ya zagaye yatsunsa a jikin natan.

"Mami ta miki bayanin komai?"

Komai? Idan har komai Win yana cikin kalma biyun da ta faWa cewar yarinyar ?arsa ce to kuwa tayi mata bayanin, abinda ya rage kawai shine a fahimtar da ita don bata gane ba, babu abinda ta gane a zuwan nasu da sassafen nan har kuwa rare da Aminiyarta da kuma yarinyar da aka zo ala shimfide a gadonta, amma sai bata ce komai ba, don bata san ta yadda zata fara gaya masa tarin tambyotin dake cikin kanta ba.

Yana ri?e da hannunta da kuma kofin lokacin da ya fara maganar da a farkonta bata gane komauba.

"Rukayya kamar Family freind dunmu ce tun da dadewa, mahaifinta abokin Baffa ne, sunyi aiki tare kuma sunyi kasuwanci tare kafin kowa ya buWe nasa kamfanin. Ita kadaice a gidansu mace tana yayye da kuma kanne maza, amma tun a wancan lokacun ba ma shiri da sauran ?anuwan nata saboda ra'ayinmu da ya banbanta.

Ita kaWai ce a gidansu kowa yake shiri da ita, kuma tun a wannan lokacin ra'ayinta ya karkata sosai a kaina ta yadda take kyautata min fiye da kima har sai da kowa ya fahimci cewa she's interested in me. To sai wani abu ya faru a wannan lokacin da ya zama mafarin ciwo na, rayuwata ta canja gabadaya ta yadda na tashi daga yadda kowa ya sani zuwa wani abun daban.

Amma duk da haka bayan mun kammala karatu sai ta dage akan bakanta, and I've no right da zan iya cewa A'a, saboda ko Baffa a lokacin ya matsa da cewar inyi aure kuma ni ba wannan ne a gabana ba, ina wani bincike ne da nake ganin cewa zan iya gama shi a wancan lokacin saboda haka above all the girls a sannan sai Rukayya tafi kowa zama wadda ya dace na aura.

Bayan auren mu, da shekara biyu, sai zaman yazo karshe, lokacin Hamida tana Baby...."

Yayi shiru yana shafa hannunta akan kofin kafin ya cigaba.

"Na yarda na bar yarinyar a wajenta ne a lokacin saboda karama ce kuma ko baka haka ba dole a wajenta ya kamata ta zauna dama, sai dai duk da haka munyi wani sharadi a lokaci da zai bani damar Waukarta bayan na kammala abubuwan gabana.

Lokacin da ake shirin fara aurenmu dake, lokacin naga Hamida a wani waje da bai dace ba tare da wata Christian wai ita take kula da ita, da na dauke ta na kai ta wani creche ne tunda ba zan iya kawo ta gida a lokacin ba kuma a can ta zauna har bayan kin zo gidan nan.

Mami tace in dawo da ita nan amma banyi hakan ba saboda nafi son komai ya tafi a hankali, don ni dake ba mu gama fahimtar juna ba a lokacin, so I have my plans yadda komai zai tafi daidai amma sai gidan su Rukayyan suka kasa jira na suka kai zancen kara kotu wanda a jiyan ya kamata inje amma ban samu zuwa ba, Ishaq yaje kuma basu yarinyar kamar yadda muka san dama hakan ce zata faru.

Amma kawo ta da suka yi a yau ban san dashi ba Amina, Dukkaninmu babu wanda ya san dalilin da yasa suka yi hakan, abu daya kawai na sani shine, Hamida tazo wajena kenan Amina ba zata taba komawa hannunsu ba ko me zasu yi a duniyar nan kuwa."

Yayi shiru yana kallon yanayin fuskarta, yadda idanunta ke nuna cewa kwakwalwarta tana daukan dukkan maganganunsa a wani ma'auni da ya kasa tantance shi, don haka sai kawai ya karasa jawo ta gabansa a hankali, har yanzu kofin na rike a hannunsu su duka biyun. Kuma saura kadan goshinsa ya hadu da nata yace.

"Doll, zaki taya ni mu rike ta?"

Muryarsa a hankali ta fito, da wani amo da kamar auna shi ne ya tabbatar zai kassara kowanne abu mai kwari a jikinta da kuma cikin kanta, numfashinta kawai take ji yana fitowa da saurin da yafi daidai, kuma ta san ya fahimci hakan amna da yake a kowanne yanayi Ma'aruf shi din ne dai sai ji tayi yace.

"Idan tunani kike zata hana mu wani abin Doll kar ki damu, I will always find a way, na miki alkawari."

Bata san lokacin da ta ture shi baya da hannu daya sannan ta mi?e tsaye, ya rike kofin data bar masa, ya kalle ta da murmurshi a fuskarsa lokacin da wayarsa ta sake kara.

Ta juyo ta kalle shi kamar zata ce wani abin game da wayar, ya daga mata gira Waya yana kai kofin bakinsa, sai kawai ta kasa cewa komai din ta juya zuwa wajen wardrobe Winta.

"B, yanzun nan Waya daga cikin mutanen RTL ya sake kira, ya bamu details akan mutumin nan da yazo ya karbi kudin."

Abinda Faruk ya faWa kenan, bayanan layi biyu da a cikin sakanni biyu kawai da suka da suka yi ?o?arin goge duk wani dukkan hargitsin da ya tashi dashi a safiyar yau, bakinsa ya furta hamdalar da bai san lokacin da taji bakin nasa ba.

Yaji zuciyarsa na washewa da yakinin fawwalawa Allah al'amarinsa, a yau kaWai ya tashi da matsaloli har guda biyu wanda suke jigo kuma manya-manya a rayuwarsa, amma sai gashi tun kafin ya kai breakfast bakinsa ya fara samun rabi na waWannan matsalolin sun fara gushewa.

Idonsa ya sauka akan Amina data dauko wani farin abu dan karami ta karaso kan gadon daga daya gefen tana ?o?arin kara rufawa Hamida dake motsi kamar sanyin fankar dakin ne ke damunta.

"Alhmdlilah."

Ya furta a hankali yana cigaba da kallon halittu biyun da yake ganin sun zama wani jigo naduniyarsa a yanzu.

Abinda bai sani ba shine, akwai wasu lokuta da bawa ke kaiwa gabar da karshen wahalhalunsa a duniya ke karewa, akwai gabar da mutum ke zuwa inda komai zai tsaya, komai din da ya danganci dukkan wani kunci da hargitsin rayuwar da ya fuskanta, akwai gabar da mutum ke girbe tarin hakurinsa da ya shuka, akwai gabar da mutum ke fahimtar cewa Allah na karbar dukkan addu'o'in sa, sannan akwai gabar da mutum ke iya canja karin maganar bahaushe da cewar...

Rana dubu ta barawo... Rana dubu ma ta mai kaya!

***

_Ina ga mun tatttaro dukkan ksn matsalar mu a yanzu, so wa shiryawa fara samun revenge?_

_Waya shiryawa ramuwar gayya da ake cewa tafi ta gayyar zafi?_

Littafin nan na siyarwa ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login