Showing 90001 words to 93000 words out of 132946 words

Chapter 31 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1127

Sadiyan da suka fahimci tabbas dubunsu ta cika zuwa wata dubun.

Sun tunawa da kowa shekarun da Hajiya Mardiyya ta shafe babu haihuwa s gidan alhali dukkan sauran kishiyoyinta na tara ?a?a, da kuma yadda ita Aunty Sadiyan ta dinga ziga ta akan shawarwari kala-kala, wadda bata dauki kowacce ba sai ta cewar tayi karyar tana da ciki, ta raini abinta kamar gaske idan lokacin haihuwarsa yayi, zasu samo jaririn da zata dawo dashi daga asibiti bayan sun tafi su biyu ba tare da kowa ba.

Kuma hakan suka yi, don kafin lokacin aka bawa Aunty Sadiyan labarin wata ungozoma acan wani kauye dake irin wannan harkar ta siyar da jarirai idan ta karbi haihuwa don a kaidar aikinta ta idan ta karbi haihuwa yaro bai zo da rai ba, ita ke binnewa, wai ladan aikinta kenan saboda jahilci irin na mutanen wannan ?auyen a lokacin, don haka idan har ta samu masu nema, to tana basu ranar da zata karbi haihuwa ne su zo, ita kum idan har ta ciro dan, to akwai wani lakani nata da take yiwa jarirai da tun kukan farko basa kara wani, zasu yi ta bacci ne mai tsawo har zuwa wani lokaci ta yadda za'a yarda da ita dewar sun mutu.

Da wannan dabarar take shaidawa nmasu haihuwa cewa dansu ya rasu, da sun ganshi sai a bata gawa ta taho da ita gida, inda daga nan zata samu hanyar da zata yi ta dauko jariri ta kawowa masu bukata su bata kudinta.

Aunty Sadiya tayi bayanin haka ce ta faru dasu, a ranar da suka yi karyar na?udarta ta tashi a ranar suka Wauki mota su biyu kawai ita ke tu?awa suka nufi can wannan ?auyen da a lokacin ake ce masa Yakura, amma a yanzu ya koma Garun Albasu, anan suka sami matar da babu wani bata lokaci suka bata kudinta ita kuma ta basu yaro, inda murnarsu ta ?aru ganin namiji ne.

Daga nan suka kama hanya suka dawo da cewar ta haihu kuma har an sallamo ta daga asibiti, kuma babu wanda ya zarge su aka shiga murna da shagalin suna... Kuma tun daga wannan lokacin suka binne wannan abin a tsakaninsu su biyu kawai ta yadda ko sauran ?anuwansu basu taSa sani ba sai a yanzu da ?waryar da suke ri?e da ita ta faWi har kasa ta tarwatse.

Yana iya jin muryar Hajiya Mardiyyan a cikin kansa har yanzu, yana jin yadda take magiya da kuma kukan gayawa Alhaji Bashir cewa wallahi sauran ?annensa mata da ta haifa shekaru biyar bayan shi ?a?an su ne na cikinta, ita da ?aruwarta sunyi garaje ne kawai na tunanin bata haihuwa na tsawon shekaru bakwai kafin lokacin da ta sami cikinta na gaske.

Ya rufe idanunsa a hankali ya buWe su kafin ya amsawa Aunty Sadiya da abinda take jira.

"Ina hanyar Kaduna..."

"Kaduna?"

Ta tambaya a lokaci guda.

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un.... Haba Jawad me yasa zaka kama hanya da sassafen nan? Tun Wazu muke nemanka, ina zaka tafi? A?alla ka saurare mu mana..."

Ina zai tafi? Ta yaya zai cigaba da zama a gidan nan alhali tun a daren jiya labarin komai ya zagaye gidan daga bakin Hajiya Yagana da bashi da tsntamar cewar ta ji dukkan tattaunawar da akayi.

Ta yaya zai kara zama yana kallon idanun kowa ba tare da wani bayani mai gamsarwa da zai iya kare kansa a wajen su ba? Bai ce ba zai dawo ba don ko Alhaji Bashir da yaje yiwa sallama abinda ya gaya masa shine zai dawo bayan ya sami ?anuwansa, kuma shi bai hana shi ba ko yace masa yayi garaje sai su....?

"Ka yiwa Allah da ma'aikinsa ka dawo Jawad, ka sani a cikinmu babu wanda ta taba cutarka, kuma bamu yi komai don mu cuce ka ba, to me yasa ba zaka saurare mu ba Jawad? Me yasa ko sau Waya ba zaka ji daga bakin mahaifiyarka ba... Tunda komai ya fito fili ka tunanin zamu sake Soye maka wani abu ne?"

Ya girgiza kansa a hankali kamar tana kallonsa.

"Kar ku damu Aunty Sadiya zan dawo...."

Abinda ya faWa kenan kawai sannan yatsun hannunsa suka ni kashe kiran, sai dai muryarta ta sake kwararowa kafin hakan.

"Ina wannan yarinyar Jawad? Ina Zainab?"

"Tana tare dani."

Amsar ta fito cikin tattausan amon muryarsa da tsabar ruWani da kuma tashin hankalin da yake ciki ya haifar dashi.

Kuma daga shi har Zainab Win, suna jin salatin da Aunty Sadiyan ta ruWe dashi kafin ya kashe wayar.

?ib kiran ya katse a kunnen Zainab, yana sake tonawa kanta sautin zuciyarta dake bugawa a ?irjinta, kuma bata juyo ba, bata juyo ta kalle shi ba, kanta na sunkuye tana kallon yatsunta dake girgizawa akan cinyoyinta, nemanta suke yi ita ta sani, shi tasa ko baccinta na jiya ta cika da mafarkai masu nauyi... Watakila gani suke tana da hannu a duk abinda Jawad ke yi.

Kuma ta sani ko a gaba suka sa ta bata da yadda zata iya yi musu bayanin cewa bata san komai ba, bata san me yake yi ba ko kuma su abinda suke yi, kamar koyaushe a rayuwarta babu wanda ya taba bata zabi a rayuwarta, komai faruwa kawai yake a gaban idanunta yayin da take jin tamkar an rufe bakinta an kuma daure hannayenta, kamar tana tsakiyar wani waje ne da bata da mafita kotawanne Sangare,kamar tana cikin kwale-kwale ne a tsakiyar teku ta yadda ruwa ya zagaye kowanne bangarenta... Don haka bata da wani zaSi illa ta zuba ido taga yadda Allah yayi da ita kawai.

Tana ji sanda ?arar wani kiran ta cika motar, sannan taji sanda muryar wani namiji ta amsa.

"Oga sir.."

Shine abinda ya fara faWa bayan sallama. Ta gefen idonta taga sanda ya dafe kansa yana yin baya dashi kafin ya amsa.

"Sulaiman ina ga a location dina saura bai fi minti biyar ba na kusa isa zuwa garin, ka tabbata mutumin da zaka hada ni dashi Wi yana nan a gari?"

Daga cikin wayar Sulaiman din yace.

"Yana nan Yallabai, bai fi minti biyar ba .a da muka yace min ya riga ya fito bakin titi yana jiranka, sunansa Nura, na gaya masa kalar motarka to da ka iso zai gane ka kawai."

Ya gyaWa kansa sau biyu yana faWin.

"Shikenan, nagode."

Sannan ya kashe wayar. Taji ?arar sanda ya ajiye ta a gefen dake tsakaninsu kafin abinda bata yi zato ba ya biyo baya...

"Zainab zaki ci wani abu?"

Muryarsa a hankali ta fito,cikin amon dake shaida mata cewa nasa ne, ya dawo daidai ba kamar Wazu da ta tabbata baya cikin hayyacinsa ba.

Sai kawai ta rufe idanunta a hankali tana jin Wumin kwalla na kokarin cika su.

"Kina jin yunwa?"

Ya ?ara tambaya a hankali, sai ta girgiza kanta a hankalin itama ba tare da tace komai ba, shiru ya sake ratsa motar na wasu sakanni kafin ya kunna ta su sake hawa kan titin, kuna tafiya yar kadan ta isar dasu cikin wani tsohon gidan mai da ya koma kasuwa kuma maciyar mutanen hanya, wajen da ya hada da tarin kantinan da kusan duk wani abinda matafiyi ke bukata zai samu.

Bai kashe motar ba ya barta a kunne har da mukullin a jiki sannan ya bude ?ofar motar ya fita, Zainab ta bishi da kallo ta cikin mutanen dake wajen, kayan jikinsa wani kalar yadi ne mai ruwan toka, tafiyarsa kadai ta banbanta da tarin mutanen wajen har zuwa sanda ya bacewa ganinta,? Idonta ya shiga yiwa cikin gidan man kallon sani amma nan da nan ta ?aryata kanta, ta dawo da idonta ya dawo kan mukullin motar.

Zuciyarta ta ayyana mata yadda zata koma mazaunin direban ta murda shi, da zarar ta tashi sai tashi sai ta juya kanta ta fita daga wajen, ta komawa dukkan hanyar da suka biyo a baya har zuwa cikin gidansu. Wata?ila?idan tayi hakan zata iya wanke kanta a wajen Hajiya Mardiyya da kuma Deluwa, watakila zasu iya yafe laifinta su mayar da ita gida wajen mahaifiyarta komai ya ?are, komai... Har dashi kenan? Wani bari na zuciyarta ya ayyana mata, kuma rashin sanin amsar yasa ta haWiye wani abu a ma?ogwaronta.

Cikin abinda yake ?asa da minti goma Jawad ya dawo har a lokacin tana sake-saken a ranta, bata ko ganshi ba sai ji tayi an buWe ?ofar gefenta, kuma kafin ta dago ya ajiye tarin ledojin hannunsa akan cinyarta sannan ya mayar da kofar ya rufe.

Idonta yabi ledojin da kallo tana jin kanshin kayan abinci kala -kaka da kuma nauyin robobin ruwa dana lemo da suke cikin tasu ledar daban, a cikin wata ?ar karamar leda fara, ta gano magunguna, irin magungunan da ya siyo mata jiya sak wanda suka bari a falon Sangarensa.

Mamaki ya kamata, tsananin mamakin wani irin mutum ne Jawad da kuma halayensa, sai dai wannan mamakin bai kai koi'ina ba sai a lokacin da suka isa kofar shiga garinsu 'Garun Albasu' minti biyar bayan barinsu daga gidan man nan, a lokacin da ta Wago kanta jin ya rage gudu suna kokarin sauka daga titi, lokacin da ta Wago da idanunta suka sauka akan kasuwar ?auyensu ta bakin titi kafin ka dangane da cikin garin, da kuma fuskar Wanuwanta Nura, (Wan mijin mahaifiyarta) yana washe baki yana tunkaro motar tasu da saurinsa.

A wannan lokacin abinda taji yayi kama da fadowar zuciyarta a cikin kirjinta, taji kamar ta faWo ne ta fice ta ?asan motar, tayoyin baya kuma suka bi ta kanta suka tarwatsa ta, jininta ya fallatsa a koina na jikin motar!

***

A cikin harabar tsakar gidan, mata ne kala-kala da kuma yara dake wasan su, matan na ayyukansu na yau da kullum wanda ya haWa da girke da kuma surfen hatsi kala-kala, kusan rabinsu na goye ne da ?ananun yara a bayansu yayin da suturarsu kaWai idan ka kalla, banda gini kasan dake zagaye da tsakar gidan zai shaida maka cewa mutanen karkara ne.

A wannan lokacin ne kuma sallamar wani dattijo ta karaWe koina a tsakar gidan, sau daya ya furta sallamar amma a lokaci guda yanayin wajen ya canja, yara suka mike a guje suka nufi kasan rumfar dake barandar dakuna suka taru waje daya gabadayansu yayin da matan kowacce ta mike tsaye suna amsawa, yan tsofaffin dake zaune suna aikin busa ne jadai basu mike ba.

Mutumin ya shigo sanye da vabbar rogarsa wadda ta banbanta da yar ciki, hular kansa mai kyau ce wadda dattin dake tattare da ita ya boye hakan.

"Ina Talatu? Talatu, Talatu....!"

Kakkaurar muryar tasa ta fada yana karasowar ciki. Matar dake amsa sunan Talatun tayi saurin sakin itace da ta debobdon kara wutar girkinta tayo gaba tana faWin.

"Gani Malam.."

Kuma tsaye ya nuna ta yana fadin.

"Wato Talatu rashin mutincin naki bai kai karshe ba dama? Sakin da na dannewa zuciyata ban yi miki wancan karon ba shi kike nema?"

Ba shiri Talatun ta dafe goyon ?ar dake bayanta sakamakon faWuwar gaban da taji ta ratsa har ta bayanta tana shirin kwance goyon.

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un Malam me kuma ya faru? Wallahi Malam vabu abinda na kara yi."

"Babu abinda kika kara yi? Karya nake yi miki kenan? Ko kuma shi wancan ?aton Gardin? da Nura Wan gidan Malam Sadi ya rako min shi har majalisa suka zo nema ki dake ?aryar suke? Dududu kwana nawa kenan da kika shigar min da mutum har Wakin aurenki? amma ace duk uw*r tarzomar da aka sha baki hankalta ba? Allah wadaran auren jinin Hanne wallahi...!"

Ya fada muryarsa na dagawa, dagawar da tasa sauran matan dake gefe murmusawa suna kallon junansu. Talatu ta sake talkafe goyon bayanta tana girgiza kanta.

"Wallahi Malam, bani da masaniyar komai, ni ban san me suke nema a wajenta ba, ban san ma me yi musu kwatancena ba..."

"Ina zaki sani Talatu? Dama ina zaki sani... Muna zaune a majalisa kawai mota ta faka aka ce wai gidana ake nema, kin kunyata ni a cikin jama'a, ace ina zaune a gida da mata amma wasu maza daga waje suna zuwa nemanta? Wallahi darajar Malam da na karbi aurensa a wajenki kawai kike ci Habiba, amma anyi na farko anyi na biyu, na rantse da kabarin ubana aka sake samun wani Wan kaza-kazan da zai zo nemanki sai kin bi shi, billahillazi kafar sa kafarki, na gama zaman aure dake..."

Talatu ta gyada kai cikin amincewa da sauri sannan kafafunta suka durkusa har kasa cikin kasar wajen tana neman afuwa. Kuma sai da ya gama cikarsa ya bayse sannan yayi kwafa yace.

"?auko hijabinki, suna soro muje inji me ke tafe dasu."

Sai ta girgiza kanta, tana kallonsa tace.

"Wallahi Malam ba sai na fita ba, waWancan mutanen da suka zo sun bar lambar wayarsu suka ce in kira su idan na samu wani labari, to indai suma Hanne suka zo nema zan basu lambar su nemi waWancan su gaya musu komai, ka yarda dani Malam wallahi bani da wata ala?a dasu."

Muryarta na rawa?cike da tsoro yayin da yake kallonta idanunsa na haskawa da dimbin bacin rai da kuma fushin da a zuciyarta take kirga adadin kwanakin da zasu wuce kafin ta sake samun fuskarsa.

Muryarsa cike da ba'a, yace.

"Akwai abinda zasu nema ne da ya wuce Hannen? Duk danginku akwai mai jawo muku tsiya ne kamar ita?"

Talatu bata ce komai ba tana tsugunne a gabansa, hannayenta dake tallafe da goyon ?arta na rawa a ?asan goyon, kuma bata san lissafin da yake yi ba tsawon wucewar wasu mintuna kafin yace.

"Tashi ki Wauko lambar, wannan shine na farko da kuma na ?arshe a lamarin nan na gaya miki Talatu..."

Ba shiri sai ta mi?e tsaye, kuma bata ko damu da karkaWe kasar da ta Sata kafafunta ba, ta mi?e da sauri ta nufi ?ofar Wakinta, kuma cikin abinda bai wuce minti guda ba ta dawo ri?e da wata farar takarda da take a mi?e samSal, ya fizga tamkar zai yaga sannan ya juya ya nufi hanyar fita.

A ?ofar gidan ya tadda Jawad da kuma Nura dake tsaye suna jiransa, ya juya ya kalli motar da suka bari a can gaban gidan, wannan yarinyar dake ciki har yanzu tana nan, ta juyo tana kallonsu idanunta na na kallonsu a zare, sannan ya kalli tarin yara har da matasan da suka tsaya daga can nesa suna kallo su, don labarin ma?udan kudin da aka bashi ya danna a aljihu bayan ya fara fadan babu mai ganin matarsa ya kusa biye kunnen duk wanda ya sanshi a lokacin.

Ya ja tsaki mai tsawo yana fadin.

"Allah wadaran munafukai...!"

Sannan ya juyo ya sake kallon Jawad Win dake a gabansa.

"Yallabai, matata tace bata da wani bayani da zata yi maka don Hanne ta rasu shekaru shida da suka wuce, amma ga wannan lambar, idan ka kira watakila zaka sami wani bayani a wajensu, don suma kamar kai sun zo nemanta kwanaki."

Idanun Jawad na kallonsa har yaje karshen zancensa, ba haka yaso ba ko kadan, yaso akalla yaga Talatun yaji bayanin komai daga wajenta, tunda sun sha tambaya tare da wannan matashin Nura amma babu wanda ya gane Hannen da suke nema sai da kyar aka samu wanda ya faWa musu cewa matar ta daWe da barin garin amma akwai wata Talatu da zata iya basu labarin inda take.

Kamar zai yi magana, amma sai zuciyarsa ta shawarce shi da cewar yabi mutumin a haka, don ya lura idan ya matsa za'a iya samun matsala, yau ya fara nema ba lallai ya samu komai a yau ba dama... Don haka sai kawai ya gyada kansa sannan hannunsa ya karSi takardar kafin bakinsa ya furta godiyar da bai san ta wace sigar kalamai suka fito ba... Idanunsa suka manne da suna da kuma nambobin dake rubuce a jikin takardar lokacin da mutumin ya juya yana zagin jama'ar dake shirin taruwa a kodar gidan bunun.

Hajiya Salamatu.
080673....

****

Ruwan da ya sauka akan fuskar Awwalu mai tsananin sanyi ne fiye da na farko da ?antaro yasa aka watsa masa awanni kaWan da suka wuce.

Ya buWe idanunsa cikin tsananin firgita, yana kallon wadanda ke tsaye a gabansa, da farko inuwoyi idanunsa suka fara nuna masa kafin fuskar ?antaron dake saitinsa ta fito tar cikin hasken safiyar dake ratsawo cikin fankon Wakin da aka kawo shi aka kulle tun a daren jiya.

"Ni zaka yiwa shunen ?an sanda Awwalu? Ni zaka sa in aika yarana gidanka alhali ka aika ?an sandan can? Ni zaka yaudara Awwalu?"

?an sanda! Kalmar ?an sandan ta doka wata irin tsawa a cikin kan Awwalu a lokaci guda tana sa shi wartsakewar da ba shiri.

"?an sanda suka gani a gidan nawa?"

Muryarsa ta fito tare da shakku da kuma tashin hankali da baya neman tabbacinsa, kuma ?antaron bsi yi maganar ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yayi wa yaransa biyu daje tsaye da bokitai alama da su karasa zuba masa ruwan bokitan dake hannunsu wanda Waya na zafi ne Waya kuma na sanyi, mai rike da na zafin ne ya fara juye masa tun daga saman kansa sannan na sanyin ya kwara masa shima har ?asa.

Tasirin zafi da kuma sanyin da suja ratsa jikinsa suka sa dukkanin jijiyoyinsa ri?ewa bakiWaya, ya shiga kokawa da dawowar numfashinsa a kirjinsa kafin ya muryar ?antaron ta ratsa kunnensa.

"Kai baka isa ka tona min asiri ba Awwalu, wallahi, wallahi daga yau taka ta kare!"

Kuma ga mamakin ?antaro sai kawai Awwalun yayi murmurshi, murmushi mai fadi sannan ya girgiza kansa, don abinda Dantaron bai sani ba shine su duka biyun ne tasu ta ?are!? Tunda ya riga ya jawo shi jikinsa shikenan tasu ta kare gabaWaya!

***

_Me kuke tunani ya haWa Kilishi da Wan sanda?_

_Kuna tunanin hakan wani shirinta ne?_

_Shirinta na gaba wato kashe Baffa?_

_Ko kuma wata kaddarar ce daban?_

_Me kuke tunani ya faru lokacin da su Jawad suka shigo Garun Albasu?_

_Zainab bata shaida masa Garinsu bane? Ko kuma Nuran da yazo bai gane ta bane?_

_Jawad ya samu lambar Hajiya Salamatu, me zai biyo baya?_

_Mabudin komai dai, ya riga ya iso!_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*??AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*20*

_Inch by inch. Life is a cinch. Yard by yard. Life is hard._ _ John Updike,?Rabbit Redux_

~~~~~~

*Tariyar Baya.( Flashback)*

"Hajiya akwai matsala fa, motocin ?ansanda ne gasu nan zagaye da gidan, na tsaya daga gefe ba zan iya karasawa ba...."

Muryar Sadik din ta faWi kalaman da a lokaci guda suka dako zuciyar Hajiya Kilishi da wani irin tasirin da tunda take a rayuwarta bata taSa jinsa ba.

Bugun zuciyar tata ya cika kunnuwanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login