Showing 99001 words to 102000 words out of 132946 words

Chapter 34 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1148

inda yanuwanta da suka zo suka nemi yarinyar kai tsaye kuwa sauran matan kuma suka shaida musu cewa ai mahaifin nasa ya kai ta can birni aikatau.

Saboda haka tun kafin a kai ga share makoki aka fara sa'in sa a tsakaninsu, suka tsaya akan cewar sai ya dawo musu da yarinyar, da kyar aka sulhunta wajen bashi wasu kwanaki da cewar ya dawo da ita, kuma basu ko tsaya an kai kwanaki bakwai ba ana share makoki da kwana uku gabakidayansu suka koma kauyensu.

Sai dai shi tun daga kan haka bai kara bi ta kan zancen ba yaji inda aka tsaya ya shiga harkokinsa, don haka a yanzu da ya riski wannan labarin daga bakin Jawad, har da kuma sunansa da zancen cewar shi zai auri yarinyar dashi ko k?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ammaninta ba zai iya zanawa a zuciyarsa ba, kafafunsa sunyi mutuwar tsaye ne na wucin gadi yayin da zuciyarsa ke maimaita kowanne batu Waya bayan Waya kafin ya girgiza kansa a hankali yana kallon Jawad Win.

"?arya yake, wannan zancen ba haka yake ba, a gaskiya babu wani alkawarin aure tsakani na da yarinyar nan, ya faWa maka hakan ne don ka rabu da ita kawai..."

Wadannan maganganun su Nura ya faWa masa bayan ya ?are masa dukkan wani bayani, kuna sune magan ganun da a lokaci guda suka ciccibo shi daga wata duniyar suka dawo dashi wata, yaji kamar ya saka hannu ne ya sauke masa wani tarin nauyi da yake yawo dashi a kirjinsa. Yana kallonsa lokacin da ya cigaba da fayyace masa komai...

"Ka gane... Da shi da mahaifinta abokan juna ne, to bayan rasuwar mahaifinta nata ne sai ya auri mahaifiyarta, a lokacin kamar daga ita har yanuwanta sunyi tunanin zata samu sauki ne a wajensa ko kuma sun ga cewa sun sanshi ne sai kawai suka amince, to ni ban san me yake faruwa ba bsyan na tafi amma dai na fahimci bata jin dadin auren, kuma da ya tashi tura yarinyar aikatau ya hana ta gayawa yanuwanta kamar dole yayi musu ne ya tura ta irin yadda yake yiwa sauran ?a?an nasa.

To sai bayan rasuwarta ne a yanzu sannan suka dage akan cewar ya dawo musu da ita, sai kuma gashi yanzu kun zo, to ina tabbatar maka da cewar yanzu can wajen yan uwan mahaifiyar tata zai maida ita, kai kuma ya kore ka ne don ya san da zarar ya mayar da ita ba zai amfana da kai ba shi yasa yayi amfana da wani abu naka ba, shi yasa yayi amfani da sunana ya gaya maka wannan labarin amma ina tabbatar maka duk abinda ya faWa babu gaskiya a ciki, don ni yanzu ma babu batun aure a gabana."

Tun daga farkon bayanin har zuwa karshe ya saurare shi ne da dukkan nutsuwarsa, da dukkan hankalinsa da kuma tunaninsa wajen tantance gaskiya ko kuma akasin kalaman nasa, sai dai duk iya nisan da hasashensa ke kaiwa, dawowa yake yi wajen gaskata shi da kuma yarda dashi,?idan aka cire muryarsa a idanunsa kaWai yana ganin tabbacin kowacce kalma da yake furtawa.

Yana jin yadda zuciyarsa da kuma kowanne abu mai hankali a jikinsa ke yarda dashi, don haka a lokacin da ya kai karshe, bai Sata lokaci ba ya shaida masa abinda yake son yayi masa bayan Nuran ya shaida masa cewa mutumin ba zai Wauki lokaci ba wajen sa wa a maida ita wajen yanuwan nata tunda har an riga an ?aiyade masa wasu kwanaki da sharaWin ya dawo da ita.

"So nake kayi kokarin da zai mayar da ita wajen yanuwan nata da wuri, sannan ka bi su har can ka gano ?auyen sai ka kira ni ka gaya min, zan biya ka ko nawa ne Nura..."

Yana tuna alkawarin da Nuran yayi masa, tarin alkawarin cewa komai zai tafi daidai kuma bai san me yasa ba haka kurum ya yarda dashi, ya Webo adadin wasu kudade daga cikin wanda ya fito dasu a cikin dashboard Winsa ya bashi da cewar ya kula da ita har zuwa lokacin da komai zai daidaita, kuma bai sake bukatar komai ba ya juya motarsa ya bar ?auyen, ya riga ya fahimci cewa gaggawa shine mataki na farko da zai bata hanyar mafitarsa.

Bashi da wani ?arfi ko kuma wani iko akan mutumin nan ya sani, babu yadda zai iya dashi a yanzu tunda har Zainab ta riga ta shiga hannunsa, don haka zai bi shawarar Nuran, zaiyi hakuri har zuwa lokacin da zata bar cikin ikon nasa, wanda yake saka ran saka ran hakan da wuri kamar yadda ya gaya masa, shi yasa bai ko damu ba a yanzu kafin tasowarsa da Nuran ya sake kiransa a waya ya shaida masa cewar mahaifin nasa ya ajiye Zainab ne a can cikin dakin uwargidansa inda ba zai iya zuwa ba don haka ba zai iya hada shi da ita a waya ba kamar yadda suka yi kafin rabuwarsu.

Wani abu ya wuce ta makogwaronsa a hankali yayin daya tuna babban al'amari na biyu dake shirin faruwa da rayuwarsa, bai san takaimaimai me zai faru ba, bai san na abinda zai je ya tarar a garin Kanon da yake nufa a yanzu ba, abinda ya sani kawai shine, tun kafin haduwarsa da Nura, bayan ya baro kofar gidan mutumin nan, kira ya shigo wayarsa da wannan lambar da aka bashi,lambar da yake saka ran ko yaya ne zata bashi hanya ta kuma saukaka masa wahalar tafiya neman abinda ya fito dashi har hakan ya shafi rayuwar Zainab.

Sai dai kuma ya fahimci kamar yadda yake neman wani abu haka ma matar da ta amsa wayar take, bai tabbatar ba don wata?ila baya cikin haiyacinsa a lokacin amma ya fahimci ba lallai ne idan tana da wata kwa??waran bayani da zata iya bashi ba, zai je ne kawai don ya sami wani abun akan iya abinda yake dashi, don ya tabbata ita ta daWe tana nema, don haka tabbas zai samu wani abun da zai fi nasa.

Shi yasa ya yanke shawarar tahowa inda ta gata masa take a lokaci guda, ba zai koma Abuja ba, hatta wajen aikinsa ya riga ya rubuta takarda tun da asubahin yau ya tura musu na daukar hutu tsawon wasu kwanaki, kuma ya sani bashi da matsalar hakan don a shekaru biyu da suka wuce ko hutun karshen shekara da ake bawa kowanne ma'aikaci shi bai taSa karba ba.

Su Hajiya Mardiyya kuwa bai ?ara ganin kiran daya daga cikinsu ba tun dazu, ya gaya musu zai dawo, kuma ya san hakan kadai ua ishe su su fahimci cewa ya riga ya yanke hukuncin da babu wani kuma da ya isa ya saka shi ya canja, tunda sun sanshi, sun san halinsa da kuma abinda zai iya tun kuruciyarsa.

Matar ta turo masa da address Win inda take, a tunaninta a garin Kano yake shima, don kai tsaye ta gaya masa cewa zata jira zuwansa a yau din, shi yasa ya tabbatar da cewa itama nema take kamar shi.

Ya bude idanunsa a hankali sannan ya zura hannunsa cikin aljihun rigarsa, rigar da ya canja a cikin garin Kaduna inda ya nufa bayan rabuwarsa da Nura, Gidansu wani abokinsa Hashim ya nufa kai tsaye inda yaci sa'a Hashim din kuwa na nan, a gidan ya bar motarsa sannan yayi wanka ya canja kaya zuwa wasu riga da wando da ya tsaya a wani boutique ya siya, rigar kamar ta sanyi ce amma bata da nauyi, tana da hula mai girma wadda ya jawo ta ya rufe kansa da ma kusan rabi na fuskarsa, bayan kayan babu abinda ya dauja sai wayarsa da kuma wallet dinsa inda ya jera mint din kudaden da ya ciro.

"Maigida..."

Saurayin dake zaune a kujerar gefensa ya faWa a hankali, ya juya ya kalle shi yana yin baya da hular rigarsa, wanda hakan yasa Saurayin ya kara yin murmushi kafin yace.

"Nace dan Allah ko zaka taimaka ka dan dauke ni a hoto, this is my first time hawa na jirgi, so ina so nayi posting a acconuts dina na social media ne..."

Ya faWa yana ?o?arin mi?o masa wayar hannunsa, babu yadda zai yi sai kawai ya gyada masa kai sannan ya karbi wayar ya danyi baya kadan yayin da saurin ya gyara zamansa a jikin kujerarsa dake kusa da taga, ai kuwa yayi masa hotuna guda biyar masu kyau sannan ya mika masa.

"Nagode, Nagode sosai, It means alot sir!"

Cewar saurayin yana murmushin jin dadi har da hade tafukan hannayensa biyu, kuma bai san me yasa ba sai kawai ya nuna masa kwalin wani abu a hannunsa da ska rubuta 'Free-dat' sakon kai abun ne yasa mutanen da suke do suka bada kudin jirgi a kawo...

"... Idan ba haka, babu abinda zai sa in hau jirgi a wannan matakin da nake a rayuwata."

Bai san lokacin da murmushin da bai shirya masa ya subuce a lebbensa, ba wai kuma murmushin abinda ya fada bane, murmushin jiye wa matashin dadin rayuwarsa yayi, dadin wannan lokacin da yake ciki da bashi da wata damuwa mai yawa, tazarar shekarunsa bata da wani yawa sosai ya sani, amma shi yanzu ne lokacin da komai yake hargitse masa, rayuwarsa ma gabaWaya ta canja a cikin kwanakin da basu fi ?arfin ?irgen yatsunsa ba. Ya rasa identity Winsa sannan kuma yana shirin rasa yarinyar da yake ganinta a matsayin wani Sari na rayuwarsa.

Ya tabbbata laifinsa ne ke bibiyarsa, ko ma ya fara, don shi da kansa ya sani cewa? wanda ke aikata laifi irin nasa karya ne rayuwarsa ta dinga tafiya daidai,karya ne ka sabawa Allah akan haninsa kuma ace baka fuskantar wani kalubalea ruywarka, idan kuma hakan ta faru to kuwa tabvatas ka ji tsoron haduwarka da shi... Don ko hausawa sun ce 'Alhaki kwikwiyo ne, duk inda kayi sai ya bi ka.'

Ya sani cewar ya biyewa shedan a rayuwarsa,ya aikata rarin abubuwan da sanari da yawa a wannan zamanin ke ganin cewar ba laifi ne, kamar suna halattawa kansu ne ma wasu sabon Allahn a cikin lissafin morewarsu ta duniya, amma zai rantse da ubangijinsa tun daga lokacin da zuciyarsa ta fara fuskantar Zainab da kuma al'amarinta, ko shisha bai kara dandanawa a bakinsa ba, yana jin kansa ne kamar ya zama commited na tarin irin abubuwan nan da yake ganin bashi da lokacinsu, ko abokinsa Haro a yanzu su kan dade ma basu yi waya ba ganin yaki maida hankali game da shirin da suke yi akan Rukayya.

Rukkaya. Ya lashe lebbensa kadan sabida ambatar sunan da zuciyarsa tayi, tana ina a yanzu? Me ke faruwa a cikin tata rayuwar? Don ya tabbata ba shi kadai ne yake fuskantar sakamakon laifin da suka dade suna aikatawa a rayuwarsu ba, kwarai ko da ga nesa ne zai sp sanin halin da take ciki don ko layin da take samunsa dashi ma a yanzu baya wajensa, ya daWe da bawa wani masinja a Office Winsu kyautarsa tare da sabuwar waya bayan ya kawo masa korafin rasa wayarsa da yayi.

Jirgin ya sauka a Kano da misalin ?arfe 7:24 na yamma, yayi sallama da wannan saurayin mai sakon Free-dat sannan bai bata wani lokaci ba kasancewar bashi da kaya ya fito daga wajen, a cikinnairpot din ya samu mai motar da yayi haya har zuwa address Win gidan da matar ta turo masa.

***

*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
*Gidan Hajiya Salamatu.*

Babu irin sake-saken da Hajiya Salamatu bata yi a zuciyarta ba bayan sun gama waya da mutumin da ya tabbbatar mata da cewar shine ya turo sako cikin wayarta game da matar nan Hanne, kuma ya tabbatar mata da cewar zai same ta har inda take a yau.

Ta dauki wayarta da niyyar kiran tarin mutane amma tana fasawa, sai karshe da tunaninta ya tsaya kan kaninta mai bi mata da shima yake zaune anan cikin unguwar da take sannan ta kira shi, kuma a wayar ta kasa shaida masa komai sai da yazo gidan tukunna.

Kallon da yayi mata bayan ta gama yi masa dukkanin bayanin da Awwalu yayi mata da kuma yadda suka je har Garun Albasu nemsn Hanne da ma sakon da ta samu a yanzu,kallo ne da bata taba gani a idanunsa ba, kamar yana shirin cewa watakila ta samu cutar tabin hankali ne ko kuma zaiyi mitar ta taso shi akan abinda yake kamar almara, amma sai ya girgiza kansa sannan muryarsa cikin kokarin kwantar mata da hankali yace.

"Zamanin nan babu abinda ba ya iya faruwa Ya Salamatu, mutane sun haukace akan kudi yanzu, babu ta hanyar da ba za'a biyo ba don a yaudare ka yanzu, kar ki bari wasu suyi wasa da hankalin ki. Ni shaida ne da Kawu Muhammad da Yaya Murtala Allah ya jikansu, su suka binne jaririn da kika haifa matacce tun a wannan ranar...."

Saita girgiza kanta taba katse shi tun kafin ya karasa.

"Wallahi Nasir tun a wannan ranar da na rike jaririn da aka bani ban ga kamanni na ko kuma na Ibrahim a fuskarsa ba... Kuma banji komai ba, banji sani abu da ya danganta ni da wannan yaron ba."

Yana kallonta sai kawai yayi dariya ya girgiza kansa.

"Ba fa jiya ko shekaranjiya muke zancen al'amarin nan ba Ya Salamatu, shekaru kusan talatin da nawa kenan... ?"

Sai ta ?ara Daga kanta alamun amincewa sannan tace.

"Shikenan naji mu ajiye zancen nan Nasir, yanzu dai ai ba abinda ya kai ga faruwa, mutumin zai zo kuma zai same ni ne ni da kai saboda haka idan ma har akwai wani abu a ciki sai ka taya ni ganewa."

Da haka ta rufe bakinsa, bai ?ara cewa komai ba, suka zauna jiran mutumin da a cikin zuciyarta bata da tabbacin cewa zai zo Win, don haka tayi tarin sake-sa?en da bata san iyakarsu ba har lokacin a ya tafi sallar magariba a masallacin wani gida dake makotan ta ya dawo.?

Yar aikinta ta kawo masa tarin abincin da yana ci yana kallon wasan ball a Tvn falon nata, hankalinsa kwance kasancewar ya gayawa matarsa inda yake, amma ita nata hankalin ya kasa kwanciya ta shiga daki ta fito har compound din wajen ta dawo yafi kirgenta, gani take yi kamar mafarki ne, kamar ba gaske bane abinda ke shirin faruwa, don hatta hasken fitulun gidan nata gani tayi sun disashe a idanunta, sun koma yanayin da mutum ke gani kamar a mafarki, kana ganin abu amma ba kamar daga nesa ba tar ba.

Hatta Nasir din sai da yace ta kwantar da hankalinta, idan basu ga kowa ba Allah ya tseratar da ita kenan, sannan a agogon falon nata ya nuna mata adadin mintunan da zai iya karawa a gidan don a kunnenta mutane har biyu sun kira shi da cewar suna jiransa.

Sai dai ?arfe takwas da minti uku daidai, lokacin da wayarta tayi kara, zuciyarta ta buga tare da amon sautin kiran sannan numfashinta yayi nauyi a kirjinta ta yadda da kyar ta sauke shi ganin lambar da take jira ce ke kira, Nasir yayi mata alamun ta Wauka. Kafin ta sake fitar da wata ajiyar zuciyar ta kara ta a kunnenta.

"Assalamu alaikum..."

Jawad ya furta daga can Waya bangaren, muryarsa can ?asa ta fito, tana shaida masa tarin gajiya da kuma tarin lissafin dake cikin kansa.

"Wa... Walaikum salam."

Hajiya Salamatu ta amsa a hanzarce.

Daga wajen wani madaidaicin gida kuma mai farin gate din da yake tsaye, Jawad ya kalli plate number dake jikin katangar kafin yace.

"Ina kofar gidan da kika bani address Win... Shine 1856L Sulaiman Crecent ko?"

Zuciyarta ta faWa har cikin cikinta kafin ta sa

"Nan ne, bari nayi magana su shigo da kai."

Da haka ta kashe wayar, hannunta na rawa ta shiga neman lambar maigadi.

"Gashi nan ya iso Nasir, yanzu zai shigo."

Ta fada, kuma lokacin da Maigadin ya dauka bayan bugu daya, taji ne kamar tayi ihu wajen saka masa albarka.

"Akwai bako a waje ka shigo dashi yanzun nan."

"To Hajiya."

Ya amsa da sauri shima jin yansyin muryarta, Hajiya Salamatu ta ajiye wayar sannan ta tafi da sauri wajen tagar dakin dake fuskantar saitin bakin gate ta buWe labulen, tana ji Nasir na cewa kar ta fita ta bari ya karaso tukunna.

Akan idonta maigadin ya fito daga dakinsa, ya bude kifar gate din ya fita sannan bayan sajanni uku kofar ta sake budewa suka shigo tare, tana hango su suna tahowa zuwa ciki kuma tun daga can zuciyarta ta shaida mata cewa ba wani babban mutum bane kamar yadda ta zata,matashi ne yaro daga shigar dake jikinsa ta wando da riga mai hula da kuma ?irarsa ma, suna kara matsowa tana kara ganin tsawonsa kamar na daWuwa, tsawon da a lokaci guda tasirinsa a idanunta ya zarce cikin zuciyarta ya sami mazauni.

Nasir ya riga ta tafiya ga kofar falon a lokacin da suka karaso, don bayan ta saki labulen ta juya da sauri ta tadda shi hana kokarin bude kofar tin kafin ma su buga.

"Yallabai barka dai, barka... Dama Hajiya ce tace a shigo dashi, bakonta ne."

Maigadin ya fada a lokacin da kofar ta bude a gabansu, tana tsaye daga bayan Nasir Win sanda Maigadin ke fadar hakan sai dai ta tabbata daga ita har Nadir din bashi suke kallo ba, idonsu na kan matashin ne da ya saka hannu ya ture hular da ya rufe kansa, fuskarsa ta fito tar a cikin hasken fitilar wajen.

Ibrahim.

Shine mutumin da Hajiya Salamatu ta gani tsaye a gabanta.

Ibrahim Shanawa.

Mijinta na farko a duniya, mijin da ta fara zaman aure tare dashi, shine sak a tsaye! Cikin shekaru da kuma ?uruciyar da ta aure shi, wannan lokacin da kyawunsa da kuma dukiyarsa suka rufe mata idanu daga ganin kowa a duniyar saSanin shi... Amma ta yaya zai cigaba da kasancewa a haka bayan ita ta tsufa ta manyanta?

Wannan tunanin shine ya daki tsakiyar kanta a lokaci guda yana son tabbatar mata da cewar abinda take gani ba daidai bane, sai dai muryar Nasir da ta fito a lokaci guda ta katse wannan tunanin daga tabbatuwa, ta gaya mata cewa ba ita kaWai take ganin abinda idanunta ke nuna mata ba...

"Innalilahi wa'inna ilaihir raji'un...!"


***

*Bakori Enterprises*
*Administrative Office.*

_Zan iya fara restarting wani amma still shima ba lallai sautin ya buWe ba sai da Frea-dat Win._

Idon Ma'aruf ya karanta abinda Abdurrahim ya rubuta a fuskar wata Tablet da koyaushe tana hannunsa da ita yake nagana ta hanuyar rubuta dukkan abinda zai ce da dan yatsansa, ya karanta yaje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login