Showing 54001 words to 57000 words out of 132946 words

Chapter 19 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1122

ba haka ba yanzu zan neme su in rasa."

Kwata kwata bata lura dashi a wajen ba, dai da wata Maryam daga bayansu ta kora sunanta.

"A kawo mana alala idan ya gama."

A lokacin ne ta ganshi, idonta ya shiga cikin nasa kuma ya haska da wannan tsoron fiye da wannan lokacin da yabi ta a baya, wannan karon babu mamakin, wani abu ne kamar tsoron kawai shi kadai, irin tsoron da ya gani lokacin da ya riko hannunta da kuma sanda ta tsaya daga bayan ?ofar nan, sai kawai ta Wauke kanta da sauri tana amsawa Maryam Win, kuma ba tare da ta jira komai ba ta nufi hanyar ?ofa da niyyar fita amma kafin ta kai ga fitan ya kira sunanta shima yana tsayar da ?afafunta a lokaci guda.

Da tazara mai dan yawa tsakanin wajen dining don da yake tsaye da kuma can bakin ?ofar, kuma ba daga murya yayi ba, amma a cikin hayaniyar dakin ta jiyo shi tsaf kuma ta sake juyowa a hankali, sai dai wannan karon bata kalle shi ba, idanunta na kan kwanukan data ri?o ne.

"Ki kai min abinci side dina yanzu."

Ya fadi abinda banda ita, bai shallake tunanin kowa ba.


***

Kusan minti goma kenan yana zaune akan kujerar falonsa yana jira, hayaniyar gidan ta ragu sosai don mazan duk sun tafi wajen reception, sai kiWan ?warya kawai da yake juyowa daga can nesa.

?ofar Wakin ta buWe a lokaci guda, a hankali tana gaya masa waye tun ma kafin ya Wago ya kalla.

Kuma bayan tayi sallama bata ce komai ba tayi kwana ta nufi hanyar dining da kayan dake hannunta, shima bai amsa sallamar ba ya mike yabi bayan nata, ko ta san yana binta bata juyo ba sai da taje har gaban teburin ta ajiye tray din hannunta tukunna.

"Why are you avoiding me?"

Kai tsaye ya tambaya yana lura da cewa hannayenta rawa suke tun kafin ma yace komai.

Sai ta juyo da sauri tana ?ara yin baya da ?afafunta saboda yadda ya tsaya dab da ita, kuma tuna cewar bata fahimci abinda yace din ba yasa shi saurin gyara zancen nasa.

"Me yasa kike guduna?"

Kanta na ?asa ta shiga girgiza shi.

"Wallahi ban ganka bane tun rannan, aiki nake tayi kullum... Mutanen da yawa."

"Kuma ke baiwar kowa ce da sai kinyi musu duk abinda suke so?"

Kai tsaye ya sake tambaya.

Ta sake girgiza kanta.

"Yawanci Wawainiyar yaransu ce, kuma yaran ne suke ta zuwa waje na."

Ya tuno sanda ya ganta da goyo da kuma wata yarinya a hannu, sai a yanzu tunanin Allah kadai ya san yaransu da take goyawa a rana ya kama shi, ba shiri yaja tsaki mai ?arfi.

"Kar na sake ganin kin dauki yaron wani daga yanzu."

Bata ce komai ba yace.

"Kin ji ni?"

Muryarsa na Wagawa kaWan, sai tayi saurin daga kanta alamun ta gane, har yanzu hannayenta rawa suke, yaji kamar ya kamo su ya rike a cikin nasa, amma kwakwalarsa ta gaya masa cewa bayan ?ara rikita ta da zai yi watakila zata iya yi masa ihu ma idan yayi hakam. Don haka sai kawai ya canja zancen da abinda yake son tambaya.

"Kinyi wanka?"

Tambayar ta tayar da wani dan karamin bom a cikin kan Zainab da yasa ba shiri ta Wago ta kalle shi tana zare ido, kuma shima ya lura da hakan don hannunsa Waya yasa ya sosa ?eyarsa sannan yace.

"Ina nufin me yasa bakya canja wannan kayan, me yasa kowa yayi kwalliya banda ke?"

Sai tayi kokarin hadiye wani abu a makogwaronta sannan tace.

"Ba komai dama... dama yanzu zanje in shirya."

Tunda bakinta ya furta 'dama' har sau biyu ta san ya fahimci ?arya take yi, ilai kuwa ba shiri ya hade ransa irin yadda take tsoro sannan yace.

"Zaki gaya min gaskiya ko kuwa?"

?walla ta taru a idanunta kafin tayi ?arfin halin fada masa sbinda ke cin ranta tun kwanaki, maganar da ta kasa gayawa kowa tunda bata da wanda zai saurare ta sai shi din da ta san ba zai yarda da karyarta ba.

"Bani da kaya ne."

"Baki da kaya?..." Mamaki ya fito a cikin muryar tasa.

"Last week ina zaune Maamah take gaya min cewa anyi wa kowa a gidan nan kaya set hudu na bikin, ke ba'ayi dake ba?"

Ta girgiza kanta.

"Ni nawa ma guda shida ne Hajiya ta bani."

"Ahaan..."

Ya fada alamun neman ?arin bayani, tayi shiru kamar ba zata ?arasa ba sai kuma tace.

"Su Janifa ne suka ?ona nawa..."

"What?"

Yadda muryarsa ta sake Wagawa yasa ta ?ara rikicewa, ta dago tana kallonsa tana kara yin baya da ?afafunta kafin tace.

"Wallahi bani nace suyi ba, ina cikin gida na dawo da daddare suka Webo su suka ?ona su a gabana, dama duka sauran kayana ma haka duke yi musu guda biyu kawai suka bar min, dan Allah kar ka fadawa Hajiya..."

A lokacin da take fadar hakan ta kai ?arshe da bangon wajen dining din kuma rawar da hannayenta ke yi ta ?aru, Jawad ya kasa daure kansa da abinda yake ji na tsoratar tata sai kawai ya ?arasa gabanta ya ri?o hannun nata, ai kuwa kamar yadda ya zata ta buWe bakinta zata ?wallara ihu amma yasa Waya hannun nasa ya rufe shi da sauri.

"Shut it, kar ki sake ki min ihu."

Ya faWa hannun nasa rufe da bakinta dayan kuma rike da nata duka biyu, ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta kafin ta hadiye shi a cikinta, dukkaninsu suka yi ajiyar zuciya a tare kafin a hankali ya dauke hannunsa daga fuskar tata yana kallon idanunta.

"Su waye su Jennifer? Kuma su nawa ne?"

Muryarsa ta fito ne a hankali saboda yadda yake kusa da ita. Zainab ta haWiye ?ullutun wani abu da har a lokacin bai gama barin ma?ogwaronta ba tana jin hannunsa ri?e da nata da kuma ?amshin turarensa da ya zagaye ta kafin tace.

"?akinmu Waya dasu, suma aiki suke yi. Su uku ne."

"Ya sunansu?"

"Da Janifa, da Uchi da kuma Amaka."

Ya Waga kansa a hankali alamun ya fahimta, amma bai matsa ba ya cigaba da tsayawa ri?e da hannunta kawai yana kallon fuskarta, ita ma tana kallonsa da nata idon da yake cike da tsoro da kuma rudani, sakanni suka wuce kafin tayi magiyar dake rubuce a ko'ina na fuskar tata dashi baya gani.

"Dan Allah..."

Ta faWi hakan ba tare da ta san ma me take roko ba, amma ga mamakinta sai magiyar ta fito kamar ta tuna masa da wani abu, kamar ta dawo dashi cikin hayyacinsa, yayi saurin sakin hannayenta sannan yayi baya ya juya, sannan ya koma cikin falon inda ya Wauko wayarsa da ya bari akan kujera.

Tana ganin haka gabanta na dukan uku-uku ta nufi hanyar waje da niyyar fita, amma ya katse ta ba tare da ya ko juyo daga inda yake tsaye ba.

"Ki koma ki zauna kici abinci."

Yana fadin haka ya kara wayar a kunnensa sannan ya juyo yana kallonta daga inda yake a cikin falon.

Magiya da duk wani bayanin da zata yi na banza ne ta sani, don haka sai kawai ta juya hankali ta koma.

"Ki zuba nawa nima."

Ya faWi abinda ya sake saka ?afafunta tsayawa, idan tace ta shiga uku, tana ganin kamar tayi wa halin da take ci rashin adalci, don Allah ya sani zuciyarta na dokawa da tsoron rashin sanin manufar mutumin nan akanta ne a kowacce rana tun daga wancan lokacin, idan aka ?ara da taraddadin alkawarin da shi da mahaifiyarsa suka ci alwashin yi mata tare da mahaifiyarta dake can gida cikin wata u?ubar kuma, sai ta tabbatar cewa ko ita kanta ba zata iya kwatanta halin da take ciki ba.

Ta karasa inda ta ajiye kwanukan a hankali lokacin da muryarsa ta ?ara shiga kunnenta.

"Kana wajen reception din ne?"

Daga cikin wayar aka bashi amsar da ya sake cewa.

"Okay, akwai wani aiki da nake son kayi min ne da zarar ka dawo."

Gajeriyar amsar da ba ciki ya bashi yasa shi kai tsaye ya cigaba.

"Akwai wasu da nake son ka kor ?n?a daga aikin ku ne... I don't care waye ya kawo su ko kuma wa suke wa aiki kawai ka tabbatar sun bar gidan nan a yau..."

"... Su uku ne, Jennifer, Uchi da kuma something Amaka."

Plate Win tangaran Win da Zainab ta ri?e a hannunta ne ya fadi har ?asa tarwatse a wajen!

***

*NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*

"Ke ma kanki Nafi kin san babu haufi a zancena, da matar da kuka aika taga wannan layar da yanzu wani zancen muke ba wannan ba, amma tunda har an samu akasi..."

"Akasi?"

Rukayya ta faWa tana katse Hajiyar Sudan Win dake bayani a gabansu, dukkaninsu suna zaune a falon dake saman gidansu ne suna tattauna matsalar bacewar layar nan da Mariya bata gani ba a cikin jakar Hamida, don tun bayan da al'amarin ya faru, sai a yanzu suka sami Hajiyar Sudan suke shaida mata kasancewarta mace mai tarin hidimomi akanta.

Kuma a yanzun da Rukayya ke tunanin zata basu wata kalwakkwarar hujja akan al'amarin, sai kuma taji tana kiran kalmar akasi, wane akasi za'a fara lissafi tun ba'aje koina ba?

"Nayi zaton kince babu wanda zai ga layar sai wanda ya wanke hannunsa da wannan ruwan? To wane akasi za'a samu idan har abinda kika fada gaskiya ne?"

Ta tambaya ranta a Sace kamar yadda a kwanakin nan ta saba kasancewa a cikinsa. Hajiyar Sudan ta haWe nata ran itama sannan tace.

"Abinda na fada gaskiya ne,wannan aikin ba'a kanku aka fara yinsa ba, kuma duk wadanda nake bawa, babu wanda ya taSa yi min ?orafin ba'a sami daidai ba, to kuwa ai dole akasin daga gare ku yake... Kuma wannan shine karo na ?arshe da zaki kara Waga min murya kin ji ni ko?"

Kafin Rukayyan ta sake cewa wani abu, mahaifiyarta Hajiya Nafisa tayi magana tana ?o?arin shiga tsakaninsu.

"Yi hakuri Sadiyavranta ne ya Saci na sani, kwana biyu a haka take ne, nima tunda Mariyan ta dawo ai abinda nake ta faWa kenan, nace duk yadda akayi matsala aka samu wajen sakawar, fatanmu dai shine ace layar Sata tayi ba, kar ya zama ita yarinyar ce ta gani."

Ta janye idanunta a hankali daga kan Rukayyan da har a lokacin ke kallonta sannan tace.

"Wannan ba matsala bace, ko yarinyar ta gani ko bata gani ba akwai wata hanyar da za'a bi ku sami abinda ake so ba tare da illar wancan ya shafi wannan ba."

"Yauwa Sadiya, na san ai kowacce dama bata faduwa ?asa banza a wajenki, shi yasa na dage sai kinzo din.?Allah na tuba ba don ke ba ai da bamu san hanyar da muke bi ba a yanzu, ki ?yale wautar Ru?ayya kawai a gefe, na tabbatar miki damuwa da kuma tunani ne kawai suka sa ta yin hakan."

Ta faWi hakan lokacin da Rukayya ke sunkuyar da kanta cike da takaici, ta kusa kaiwa bango, ta kusa ?urewa, daga mahaifiyar tata har Hajiyar Sudan ta kusa daina saurararsu, ta kusa fara bin hanyarta, don bata ga inda suke motsi ba a wannan gaSar... Amma lokacin da Hajiyar Sudan tayi ajiyar zuciya tace.

"Aikin gaske zamu yi mata, Nijar zata shirya mu tafi, akwai wajen da idan muka je ina tabbatar muku babu haufi akan komawarta."

Sai kawai wani murmushi ya suSuce a bakinta, irin wannan aikin take so tabbas! Wanda za'ayi kamar da gaske ake yi, don ita da gaske take yi, da gaske take har cikin ranta, ba ma ta ?arta take yi ba, wannan lissafin daga baya ne, fatan ta kawai ta sake mallakar Ma'aruf a karo na biyu kuma ko tawacce hanya!



***

*Karfe tara da rabi ba dare.*

Amina ta sake gyara kwanciyarta akan gefen kafadar Ma'aruf, film din da suke "The life we had" wanda sai a yau Allah yayi zasu sami damar kalla baiyi ko rabi ba, amma Ma'aruf yayi korafi yana kushe shi da tun tana ?irga shi har ta daina.

Karfe tara da rabi na dare ne a lokacin, Hamida ta gama nata kallon tayi bacci akan kujerar dake gefensu, don yau tasha zirga-zirgar da bata saba ba, Ma'aruf ya kaita makaranta anyi dukkan wani process na registration an gama shi a yau da cewar ranar monday zata fara zuwa, sai murna take yi tun yanzu duk da su Hajiya basu so hakan ba, musamman Inna Danejo da suka shiga wajenta dazu, tana ta korafin cewa islamiyya ya kamata a fara saka ta zuwa wata shekarar tukunna.

Hajiya Maimuna ce kadai bata ce komai ba, amma ko Mami bata so ba sai dai bata hana ba duk da ta fahimci cewar sai da Ma'aruf din yayi shawara da ita tukunna, don tans kara saninsa ne tana kara sanin cewa kusan kashi tamaninn na al'amarim rayuwarsa tare da Mamin yake fara yin shawara.

Yau tunda ya dawo daga office yana tare dasu Baffa akan zancen dawowar Abdurrahim gobe sai wajen takwas ssnnan ya shigo gidan yana gaya mata dalilin dadewar tasa, ta san Abdurrahim dun a lissafin jerin ?a?an gidan amma bata san komai akansa ba don basu yi hirar dasu Munaya ba kuma Mami bata taSa gaya mata komai akansa ba,da alama wani abu bai taba hado hanyarta dashi bane.

Mami, Hajiya Kilishi... Hajiya Kilishin da har yau bata sake ce mata komai ba, ko Wazu da suka shiga wajenta, sun gaisa ne kawai amma bata ce komai akan zancen Hamida ba da take jira ba, ta kula kamar wasu abubuwa sun fara shan gabanta ne ba zancen Hamidan ne a lissafinta ba ko kuma na bincikar waWannan pills din magungunan da tace ta dinga sha, wanda ko a satin da ya wuce ta tambaye ta game da hakan har sau biyu kuma ta tabbatar mata da abinda take son taji cewar tana sha Win... Jitmra kawai take yi lokacin da amsar da zata bata ta gaske ta fito.

"Doll seriously na gaji da film din nan, I want something else..."

Muryar Ma'aruf ta janyo ta ta daga tunaninta, idanunta akan Tv ba tare da ta Wago ta kalle shi ba tace.

"Something kamar me?" Muryarta ta fito a hankali cikin duhun dakin da hasken Tvn ne kawai akwai, don Ma'aruf ya kashe sauran fitulun dakin saboda suna damun Hamida a baccinta, tana ta juyawa sai da aka kashe tukunna ta nutsu.

Sai ya juyo bangarenta a hankali sannan yace.

"Kamar..."

Shirun da yayi bai karasa ba yasa ta ha?ura da kallon Tvn ta juyo da fuskarta itama tana kallonsa, tazarar dake tsakanin fuskokinsu bata jin ta kai ta inci guda don tana kwance ne a jikinsa sosai, idonsa ya sauka zuwa kan lebbenta a hankali, kuma ganin haka yasa tayi saurin juyowa ta dawo da fuskarta yadda take da farko a saman kafaWunsa, kumatun ta na shafar saman dogon hancinsa kafin ta juya din.

A lokaci guda kuwa yasa hannunsa Waya ya dawo da fuskar tata tana fuskantar tata sannan ya Wora goshinsa akan nata yana kallon idanunta bakinsa Wauke da wani guntun murmushi amma bai ce komai ba, sai ta dago da hannunta na dama ta dora akan gefen fuskar tasa itama, dogwayen yatsunta na shigewa cikin gashin kansa, hakan tasa shi lumshe a hankali idanunsa kafin yace.

"Ishaq ne yake gaya min cewa wai yana son Munaya."

Muryarsa ta fito a hankali yana kallonta, kuma bata san me yasa ba amma wani abu a cikin muryar tasa ya gaya mata cewa itace mutum ta farko da ya fara gayawa hakan, hakan yasa a lokaci guda wani murmurshi ya sauka a fuskarta.

"Da gaske? Wow! Masha Allah. Nayi farin ciki sosai wallahi, this is a good news Allah ya sanya alkhairi."

Ya fadi Amin din a hankali sannan kawai yayi shiru yana kallonta, sai tace.

"Me ya faru? Are you not happy?"

Sai ya girgiza kansa.

"Kawai ban san me nake tunanin bane, gani nake Munaya har yanzu yarinya ce, level two take fa..."

Gira guda Wayan da Amina ta dage ne yasa shi yin shiru ba tare da ya shirya ba.

"Yarinya? Munayan? Sa'a ta ce fa."

"Da gaske?"

Ya tambaya kamar bai sani ba, sai kawai ta cije lebbenta sannan tace.

"Kuma aka ka gaya masa?"

Yadda take ?o?arin hade fuskarta yasa shi sake girgiza kansa.

"At first na gaya masa hakan, amma Wazu a office yazo mun sake magana har mun tsayar cewar zan je in fara samun su Baffa ma in gaya musu."

Ta gyada kanta a hankali.

"Nayi zaton haka kace masa, da nima idan naje gida gobe kaga sai inyi zamana ince maka ni yarinya ce."

Murmushin da yayi mai fadi ne kafin ya saje hade goshinsu waje daya.

"Our story is different, labarinmu daban ne Doll, ni na san yadda zanyi handling Winki, na san yadda nake sace zuciyarki cikin ruwan sanyi..."

"Da gaske? Ta tamvaya.

"Ta yaya kenan?"

Muryarta ta sake fitowa a hankali tana kallonsa kuma maimakon ya bata amsa sai kawai taji hannunsa a bayanta, kusa da wuyanta sosai, kuma kafin tayi wani tunani ya zura hannunsa cikin wuyanta a hankali sannan ya shiga zana wasu abubuwa a gefen wuyan nata, jikinta ya shiga rawa sannan numfashinta ya fara haWewa, tayi niyyar sake magana amma ta kasa, sai kawai ta rufe idanunta a hankali gabaWaya tana saurarensa, har zuwa sanda taji wani abu kamar tashin zuciya da ya sata saurin ri?e hannunsa.

"Saboda me?..."

Muryarsa ta fito cike da ?orafi ba tare da ya fahimci dalilinta ba.

"Wai meye ban gani bane?"

Tambayar ta saka ta kyalkyala dariya, wata ?ar siriiyar dariya kafin ta ture shi gabadaya ta mi?e, ya bita da kallo daga kwancen da yaje yana cije lebbensa, ta dauki Hamida a hankali sannan tayi hanyar Waki tana cigaba da yi masa murmushi, kuma kafin yayi wani motsi sai wayarsa dake gefe tayi ?ara, ya mike zaune ya jawo ta daga kan centre table Win dake gabansa.

Nambar Yakubu da ta fito Saro-Saro akan screen din ta motsa zuciyarsa kafin yayi saurin danna wajen amsa kiran ya kara ta a kunnensa.

"Na sami mutumin, gashi nan a hannu na."

Shine abinda Yakubun ya fada kai tsaye bayan ya dauka.

Hannunsa ya shiga cikin gashin kansa a take kafin muryarsa ta fito fili.

"Ka ganshi Yakubu? Ka ganshi? Mr. Okaforn da gaske?"

Yakubun ya gyada kansa.

"Kwarai gashi nan ma Waure gabana, dashi da iyalinsa bakidaya... Kuma ya gaya min iya abinda ya sani, labarin mai tsawo ne amma yace sunan mutumin dake saka su aikin Awwalu.!"

Awwalu!


***

_Kuna tunanin Awwalun Kilishi ne??_

_Ku gaya min me ya sha kan Kilishi ne da har yanzu bata bawa Amina hodar nan ba?_

_Ina kuke hango tafiyar Jawad da Zainab? Allah yasa kar in shallake tinaninku!_=??

_Wannan tashin zuciyar na BabyDoll Win Sugar...?_=?
?=??


Littafin nan na siyarwa ne akan naira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login