Showing 36001 words to 39000 words out of 132946 words

Chapter 13 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1123

ri?e da wani abu da bata gani sosai ba, kuma tun kafin yace wani abu Hamida ta sake fadin.

"Daddy naku tuwo ne kai da Auntyn, ni bana ci shi yasa nake cin wannan."

"For real?"

Ya dawo da ganinsa kan Aminan, don shi har ga Allah ya manta da zancen tuwon da yayi.

"Da gaske na samu tuwon nan?"

Tana murmushin yadda yake tambayar ta gyada masa kai, sai ya zura hannunsa daya a cikin gashinsa yana kallonta ba tare da yace komai ba.

Sai kawai tayi murmushi ta mike zuwa wajen da ta ajiye food flasks din tana gaya masa cewa har da na dumame ma duk zai samu, yayin da Hamidan ta shiga tambayar meye Wumamen.

"Eeeewwwww!" Ta fada da karfi bayan Ma'aruf yayi mata bayanin.

Suka yi dariya dukkansu kafin Ma'aruf ya taso zuwa wajen da take zuba masa abincin, kamshin miyar ya ratsa hancinsa yana yaba girkin tun kafin ya kai bakinsa don ko daga yadda miyar bata yi mai sosai ba ma hakan ya burge shi, kamar ta san yadda yake son komai.

Ya tankwashe ?afafunsa a gabanta yana kallonta yana kallon yadda take zuba miyar, yadda take komai... Allah ya sani baya jin gar ya bar duniya zai taba manta wannan alkhairin na Mami na kawo masa Amina cikin rayuwarsa.

Wannan wani alkhairi ne da yake tunanin har a kabarinsa zai tuna shi.

****

"?arfe tara da rabi.*

Hamida tayi bacci a lokacin, kuma har a sannan Amina bata sami damar samun su Amma ba don wayar Baban shima bata shiga yanzu.

Ma'aruf ya shiga cikin gida wajen Baffa, kusan awa guda kenan, tun daga masallacin isha'i yace mata zai wuce. Ya gama cin abincin yayi santi kala-kala da tun tana daurewa har ta dinga dariyarta a fili, kuma bayan hakan ya gode mata lokacin da ta kwashe kayan zuwa kitchen.

A cikin kunnenta ya dinga raWa wasu abubuwa da ita kanta idan ta tuna yanzu sai ta runtse idonta don kunya, Ba wai maza ta sani sosai ba amma ta yarda Ma'aruf daban ne, shi da kansa yau ya gaya mata cewar baya ji, kuma itama ta yarda da hakan.

Babu wanda zai yarda zai aikata dukkan abubuwan da yake yi, idan ka ganshi a fuska very responsible and so stiff akan dukkan abinda ya yanke, amma yafi kowa sanin tarin hanyoyin da zai ruWa mace a lokaci guda.

Kamar kullum wajen da ya ri?e ta har yanzu tana jin kamar shatin yatsunsa a wajen, kamar lokacin da ya ri?e ta yatsunsa sun ?ona wajen ne sai a yanzu iska ke kaWawa tana son dawo da fatar tata daidai.

Ta ajiye abin sallar da ta idar da isha'i a lokacin, gyaran kitchen din da tayi ta kuma tsaya yiwa Hamida Brush da canja mata kaya tana gyangyadi shi ya cinye lokacinta sai yanzu ta samu na sallar.

Ta tafi zuwa gaban mudubi ta dauko wani kwando tana kwashe dukkan abinda ta san Hamida zata iya sawa a ido ko ta bata jikinta dashi, tana yi tana yabawa kanta yadda tayi kokari wajen kula da yarinyar da kuma sawa ta sake a gidan ysu daya kawai, Surayya na cewa sati guda, idan ta shigo gobe zata sha mamaki.

A lokacin ne kuma kofar dakin ta bude, ta dago da idonta ta cikin mudubin tana kallon Ma'aruf din da ya shigo, fuskarta ta haska da murmushi tana masa sannu da zuwa.

Ya karaso a hankali yana zuwa inda take, kuma ba tare da ya jira komai ba ya rungumeta ta baya, kansa ya sauka a gefe wuyanta sannan ya karkato da kansa gefe yayi kissing kumatun ta kafin yace.

"Har guda nawa zan dinga samun wannan sannu da zuwan ne?"

Tayi kokarin tsaida numfashinta a hankali.

"Duk lokacin da ka fita ka dawo, kana da guda daya?"

Sai ya gyada kansa sannan ya ?ara karkata shi zuwa cikin wuyan nata, ba shiri ta damke kwandon nan dake gaban mudubin, tana jin kamar wannan karon kusan tayi yawa.

"Yaya jikin naka?"

Ta tambaya a hankali don ji take yi kamar har yanzu da Wumi a jikin nasa. Yayi shiru jamar ba zai amsa ba tsawon wucewar sakanni sannan yace.

"I'm sorry Doll."

Mamaki ya dan kamata.

"Na me?" Ta tambaya.

Sai kawai ya mike tsaye sosai ya juyo da ita tana fuskantarsa, sannan yace.

"Sorry da nake saki damuwa akaina."

Ya sunkuyo a hankali ya sake kissing daya gefen fuskar tata sanan ya sake cewa.

"Sorry da zuwan Hamida."

Ya sake kissing gefen bakinta.

"Sorry da dukkan flaws din da kika zo kika tarar a rayuwata."

Wannan karon saman bakinta ya sake kissing sannan ya Wan matsar da fuskarsa baya kaWan yana kallon idanunta yace a hankali.

"Sorry da na bata miki dukkan rayuwar da kike tunanin zaki samu idan kinyi aure..."

Kafin ya ?arasa, kafin ya sake cewa wani abu tasa hannunta da sauri ta rufe bakinsa sannan ta girgiza kanta.

"You don't have to be... Babu abinda na taba tsarawa a rayuwata a wannan stage din, babu wani hasashe da na taba yi, so dukkan abinda ke faruwa a yanzu shine duniyata kuma shine fantasy dina."

Ya rike hannunta da ta rufe bakin nasa dashi, yayi kissing cikin tafin hannun nata kafin ya janye shi a hankali.

"Ban gane ba Amina, ki kara yi min bayani sosai."

Sunanta da ya fito daga bakinsa da kuma yadda sautin muryarsa yake yasa jikinta yin rawa kadan, ta hadiye wani abu a makogwaronta har yanzu tana kallonsa sannan bakin ta ya furta.

"Ma'aruf Mansour Bakori, kai ne duniyata kuma kaine duk wani fantasy dina a yanzu, I really love you so much and I mean it."

Kuma da haka bata jira komai ba ta kara tsawon kafafunta tayi kissing gefen bakinsa kamar yadda yayi mata dazu,da farko bai ko yi motsi ba, yana tsaye ne kawai kamar baya numfashin amma tana kokarin maida kafafunta ta koma taji ya furta kalma guda biyu rak!

"Ya salam!"

Kuma da haka bai jira komai ba yasa duka hannunsa biyu ya jawo ta jikinsa.

"I love you." Muryarta ta kara fada a fuskarsa, yayin da a cikin zuciyarta take mika dimbin godiya ga mahallicinta jalla wata'ala daya kyautata rayuwar ta da mutum kamar Ma'aruf.

Kafin tayi tunanin komai, hasken dakin ya tafi gabadaya, kuma daga wannan gaSar bata ?ara gane komai ba, abinda ta sani kawai shine ta riga ta yiwa kanta alkawarin cewa da yardar ubangiji daga wannan lokacin, Ma'aruf ya daina sanin wani Sacin rai a rayuwarsa sai dai idan har abu yafi ?arfinta.

Dukkan wadannan matsalolin da yake fuskanta da sannu zata buWe masa su daya bayan daya, don in dai har a wajen Hajiya Kilishi matsalar take, tayi imanin zata warware masa su ne hankali kwance ba tare da ita kanta Kilishin ta fahimta ba kamar yadda Amma ta gaya mata a wayar da suka yi ta ?arshe.

_"Mun riga mun gama haddace dukkkan wani takun matar nan Amina, don haka dasu zamu yi amfani daya bayan daya wajen kassara ta, ba zata taba tunani ba, ba zata taSa hange ba saboda tana da ya?inin hakan tunaninta ne ita kadai kuma saboda mun saka mata imanin cewa ke baiwarta ce, baki da wata mafita ko dabara sai tata kawai!"_

**

_Wannan shine takunmu na farko akan Kilishi... Shine takun farko! Gabatarwa kawai, introduction..._

_Shine play button na Game Win, don yanzu za'a fara wasan, yanzu komai zai fara, yanzu zaku san mene ainihin suna da kuma ma'anar labarin FARAR WUTA ( A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai!) Don Amina itace Farar wutarmu ba Kilishi ba kamar yadda kuke tunani tun daga farkon labarin._

_Amina itace FARAR WUTAR da Kilishi bata taba lisaafinta ba!_

_And Ehem ehem, kun kula cewa yau Ma'aruf muka ruda??_

=??=??>?#?

*Asuba ta gari!*

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*08*

~~~~~~

_I need you to tell me it's okay._ _-Unknown_


**

"Ma'aruf..."

Muryar Amina ta fito a hankali cikin shirun dakin a hankali, ?arfe bakwai da rabi ne na safiya, don tun bayan sun idar da sallar Asuba basu koma bacci ba. Kuma jin yayi shiru yasa a hankali ta dago da kanta ta kalle shi.

Idonta ya sauka akan fuskarsa, ya rufe idanunsa gabadaya kamar ya koma bacci amma ta san ba baccin yake yi ba, wani tunani mai daWi ya sauka a cikin zuciyarta na tunanin cewa daga daren jiya zuwa yau ya daWa tabbata shi mijinta ne don dukkan wahalar data sha ma da yadda take jin jikinta baya gabanta a yanzu, kawai zuciyarta na kara narkewa ne da tunanin dukkan abinda ya faru.

Daga yadda yake rike da ita kadai a yanzu tana jin cewa kamar a duniya kaf babu wani waje da zata taSa zama a killace sama da cikin hannayensa, musamman a yanzu da ya fara bata labarin rayuwarsa, tana jin yadda kowacce kalma da yake fada ke ratsawa cikin kanta har zuwa zuciyarta.

Rayuwarsa mai kyau ce, cike take da wani irin gata da kuma jin dadin da ita bata taba saninsa ba ma, don ko a tsakanin yan uwan nasa, rayuwarsa daban ce, Hajiya Kilishi ta kyautata rayuwarsa da wani irin gata da kuma jin daWin da a yanzu take jin zuciyarta na ?ara dasa aya kan wace irin ?auna ce wannan da zata so shi irin haka kuma ta dinga cutar dashi.

Sai dai bayan duk hakan kuma a yanzu yazo gabar da yake gaya mata labarin yadda ya rasa Wanuwansa Jamal, ya gaya mata yadda komai yake tsakaninsu, sha?uwarsu dama dukkan wani buri da kuma ?udirin Jamal Win bayan ya dawo daga karatu, a yanzu yana gaya mata lokacin da suka yi wata tafiya ne zuwa Bakori don Wauko Inna Danejo, kuma duk da bsi karasa ba, tunaninta ya gaya mata cewa a wannan lokacin ne wani abu ya faru, shi yasa bayan yayi shiru bata ce komai ba, tana jinsa kawai yana cigaba da wasa da yatsunta daga kasa bargon da ya lulluSe su, sai da shirun ya tsawaita tukunna sannan tayi magana.

Ya bude idanun nasa a hankali ya lumshe su yana cigaba da kallonta yayin da ita nata ke ware akansa. Kuma a hankali cikin rashin hasken Wakin muryar sa ta cigaba da cewa.

"Shi ya bani tu?in a lokacin, kuma abu na karshe da ya gaya min shine kar in kashe shi, bayan mun canja waje na hau titi bamu kara magana ba saboda ya shiga ansa call din wani abokinsa Liman, suna ta magaba ni kuma nayi focusing hankalina akan titin, wallahi wallahi banyi wani abu ba daidai ba, I was driving safely lokacin da abin ya faru."

Ya sske yin shiru, shirun da ba sai wani ya gaya mata cewar yana shirin gaya mata cewa yana shirin gaya mata dukkan memories din dake binsa shekara da shekaru bane.

"Kawai naji sitiyarin ya ?wace daga hannuna ne sannan naga motar tana wullawa akan titin, ina jin salatin da yake yi amma ni ban ma san me nake cewa ba, hannunsa yana ta kokarin ya kama sitiyarin amma juyin da motar ke yi yasa buguwa kawai muke yi kotawanne bangare, lokacin da motar ta sauka daga kan titi ta nufi cikin daji, daga ni har shi babu wanda yaga karyayyiyar bishiyar dake gabanmu har motar ta dake ta, ta dake ta daidai saitin inda Jamal yake da karfin da yasa ta faso ta cikin gilashin ta soke a ko'ina na kirjinsa."

Ya sake yin shiru, idanunsa na kallon tsakanin girarta guda biyu yayin da suke haskawa da wani irin abu da Amina ta kasa tantance shi a lokacin, sai kawai ta Wago da hannunta daya da bai ri?e ta dashi ba zuwa gefen fuskarsa, a hankali dogwayen yatsunta suka ratsa tsakanin gefen fuskarsa da kuma wuyansa, wani abu da yasa ya sake lumshe idanunsa nasa kafin ya sake cewa.

"Likitocin sunce zuciyarsa ta fasa a lokaci guda shi yasa tun a wajen ya rasu..."

Bata ce komai ba ya cigaba.

"Ya rasu yana kallona Amina, idanunsa akaina suka tsaya har lokacin da jama'a suka karaso suka rufe motar ana kokarin fito damu, don tankin mai ya fashe tana shirin kamawa da wuta, ba'a iya fito da Jamal ba sai da aka sare reshen bishiyar nan daga jikinta, aka fita dashi dasu a jikinsa.

Ban ma san ta yaya aka zaro ni ba, na san dai kawai ban ?ara fahimtar komai ba bayan hakan sai farkawa nayi na ganni a asibiti, and that was the beginning na farawar ciwo na, I was depressed, emotionless and even out of my mind."

Taga alamun ya haWiye wani abu a ma?ogwaronsa sannan ya cigaba.

"Kusan haukacewa nayi a wannan time din Amina, bana gane komai bana fahimtar komai, wannan ranar ita kadai take ta maimaitawa a cikin kaina, tun daga safiyar da na ganshi zaiyi tafiyar, har tahowarmu mu, da maganganun da muka yi da kuma yadda hatsarin ya faru.

Su Mami, kowa da kowa sunyi mutukar kokarinsu wajen tallafa min Amina, musamman Ishaq, Ishaq yayi mutukar kokarin da ban ma san adadinsa ba Amina, kusan shi kaWai yake tare dani a kodayaushe, dashi muka yi ta yawon zuwa asibiti a London, shi yake tare dani a gida kodayaushe, su Mami suna zuwa duba ni amma ba kodayaushe ba, ina samun support dinsu da tarin addu'o'i.

A cikin wasa muka yi magana da Jamal cewa zan iya canja rayuwata zuwa tasa idan har wani abu ya faru, amma duk da haka bayan naji sauki sai naji ba zan iya rayuwa a matsayin Ma'aruf da wannan nauyin ba, saboda haka sai na ajiye dukkan wani buri na a gefe na fara sabuwar rayuwa.

Tun ina yaro burina ne in zama likita, kafin accident din na sami admission a wata makaranta a lokacin amma bsyan na warke ban sake bi ta kan admission din ba na dage wajen canja makaranta dama course din gabadaya, Baffa ya iya kokarinsa don hana ni amma na gaya masa cewa in dai ba karatun business ba ba zan yi karatun ba gabadaya, a lokacin ne Mami tasa Ishaq ya dawo wajenmu bayan rasuwar iyayensa muka tafi London tare muka yi karatun.

Bayan wannan abubuwan da na canja a rayuwata suna da yawa Doll, this isn't me, mafi muhimmanci shine wannan matakin da nake kai, burin Jamal shine ya karanci harkar kasuwanci kuma ri?e ragamar kamfanin Baffa kamar yadda nake yi yanzu."

Ya sake yin shiru yana kallon yadda ta kame gabadayanta, har yanzu hannunta na kan fuskarsa,babu abinda take sai numfashi da kuma jiran ya cigaba.

"Kin fahimce ni Doll, kina ganewa?"

Ya yanke shawarar tambaya, sai tayi kokarin Waga kanta a hankali tana son tayi maganar amma ta kasa, ta kasa don bata ma san me zata ce ba, ya gyada kansa shima ba tare da ya damu da jin abinda zata fada din ba, kuma tana ji yana cigaba da wasa da hannunta kafin yace.

"Bani na kashe Jamal ba Doll, ni na san bani na kashe shi ba don haka bayan abubuwa sun fara tafiya daidai sai na fara bincike akan wannan accident din, kuma sai da na shekara uku ina bin wannan hanyar ina tuntubar mutane kafin na samu wasu mutane biyu da suka tabbatar min cewa wasu mutane ne suka harbi tayar motar mu a lokacin da nake tu?in, da silencer suka yi amfani a bindigar ta yadda babu wanda yaji wata ?ara sai kawai ta fashewar tayar.

Bayan nan, nayi iya binciken da zan iya don gano mutanen da suka yi wannan aikin, ina living rayuwata ina kuma yin binciken don ban taba amma duk hanyar da na bi bata Sullewa bana samun komai, kuma duk lokacin da hakan ya faru I felt emotionally high, sai ciwona ya tashi, sai inji komai ya tsaya, abu kadan yana bata min rai kuma idan ran nawa ya baci bana jin ina son komai sai tsananin yadda zan iya wanke kaina a wajen Jamal.

Kuma abu daya ne kawai yake zuwa kaina cewa zan iya aika masa da sako, shi yasa duk wanda ya bata min rai, sai inji ina son in kashe shi kawai, in kashe shi in bashi sakon cewa ya gayawa Jamal abinda ya faru bani na kashe shi ba, this is crazy! I'm crazy na sani Amina, na san banbancina da mahaukaci a irin wannan lokacin bashi da yawa, amma wallahi hakan ne kaWai abinda nake so shi yasa nake tunanin idan har na samo wanda suka yi abin nan watakila zan iya jin sauki a raina."

Amina ta hadiye wani abu da bata san sunanshi ba a ma?ogwaronta, tana jin yadda maganganun ke zagawa cikin kanta kowanne da tarin ma'anar da yake fitowa da ita, kowanne da nauyinsa kuma kowanne da tasirin da yake zama dashi a zuciyarta. Kuma bata sab lokacin da hawaye ya cika a idanunta ba sai zubuwarsa taji a gefen fuskarta.

"Wannan ciwon shine dalilin rabuwata da Rukayya, ta bata min rai a ranar da nima nawa ran yake a bace, so bana cikin hankalina sanda na karbi Hamida daga hannunta tana Baby lokacin nayi wulli da ita, ita kuma nayi mata dukan da ba don Allah ya kawo Ishaq a lokacin ba ban san me zai faru ba.

Ba zan Soye miki ba Amina, duk yadda nake jin zuciyata na sakewa dake wallahi ina tsoron ranar da ciwona zai iya tashi akan ki, shi yasa lokacin ayrenmu na aika miki da wannan takardar don ki fasa, bana son in sake abinda nayi tare da Rukayya ..."

Ya kara kallonta sosai, yana kallon idanunta da suka cika da kwalla kafin ya ?arasa.

"... Na yarda ?addarar haduwa dake itace bata sa na mutu ba tun a wancan lokacin, sabida haka idan har wani abu ya same ki ta dalilina yanzu, na tabbata wannan karon nima mutuwa zanyi, don ba zan taSa iya sake wata rayuwa a duniyar nan ba idan har na kara sanadin rasa abu nsi muhimmanci irinki..."

Wadannan kalaman suka tada tsigar jikinta a lokaci guda, taji wani abu ya ratsa tun daga zuciyarta har zuwa bayanta. Sai kawai ta sake matso da kanta cikin jikinsa sosai, tana rike da fuskarsa har yanzu ta shiga girgiza kanta a jikin fuskarsa.

"Babu abinda zai sake faruwa, babu abinda zaka yi min Insha Allah, babu wanintashin hankalin da zai kara samunka, sauran da suka faru ma, sun faru ne saboda haka Allah ya tsara komai ya kasance, amma Allah ba zai kara kawo su cikin rayuwarmu ba insha Allah, all I care is that ba kai ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login