Showing 6001 words to 9000 words out of 132946 words

Chapter 3 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1156

don duk yadda zuciyarsa ke hassaso masa yadda zai dawo ya ganta, a yanzu ta wuce hakan, a lokaci guda kalolin rigarta dama yadda ta rigar ta zauna a jikinta suka Wauki hankalinsa, yaji wani abu ya motsa a cikin kirjinsa, sai kawai ya cije lebbensa yana murnushin kafin yace.

"Assalamu alaikum."

"Wa'alaikum salam."

Ta amsa a hankali tana sakin hannun ?ofar, ?afarta tayi taku biyu zuwa ciki amma sai ya cigaba da tsaiwa bai shigo ba, kuma har tana kokarin juya ciki jikinta ya bata cewa a tsaye yake don haka ta juyo ta sake kallonsa, yana tsaye a yadda yake, ya harde hannuwansa a ?irji yayin da wayoyinsa da kuma mu?ullin motar da ya rike ya fito ta kowanne gefe, mamaki ya nuna akan fuskarta don haka ta dawo ta tsaya kuma kafin tayi magana sai kawai yace.

"I'm sorry, ina neman wata ne mai suna Amina, ance min anan take, zaki ganta wata ?ar ?arama haka tana da idanu masu kyau, kuma ta iya murmushi."

Ba shiri murmushin ya suSuce a bakin Amina, murmushi da ya fito tun daga zuciyarta saboda da gaske ya bata dariya, yadda yayi da fuskarsa idan tare da wani ne zai rantse cewa da gaske kwantancen yake yi, kuma haka kurum sai taji wani abu a cikin ranta yana wucewa, don haka ta girgiza kanta a hankali tace.

"Bana jin na santa."

"Saboda me?" Muryarsa ta fito tare da godiyar biye masan da tayi.

"Saboda ni kaWai ce Amina anan, kuma ni duk ban kai yadda ka fada ba."

Ta sake faWa a hankali tana murza yatsunta. Ya kalli yatsun nata sannan yace.

"Zaki yi mamaki idan nace miki a yanzu kinfi ?arfin kwatance na ma, you look stunning Masha Allah."

Amon muryarsa na fitowa da zurfi.

Murmushin ta ya ?aru a lokacin da take kallonsa har yanzu da mamaki a fuskar ta, sai? kuma yayi saurin girgiza kansa kamar ya tuna wani abu sannan yace.

"I'm really sorry na manta ban tambaye ki ba idan Aminar da nake nema matar aure ce, kar in kwana a inda ban shirya ba."

Murmushin ta ya sake karuwa kafin ta Waga kanta sau biyu tana cije lebbenta.

"Ya Salam!" Ya faWa yana sakin hannayensa.

"Saurin me kika yi haka? Me yasa zaki yi aure tun yanzu?"

Sai da ta zare idanunta tana dariyar da bata san daga ina take fitowa ba kafin tace.

"Saboda me?"

A lokaci guda ya karaso, ya tako zuwa cikin falon, ya tsaya dab da ita sannan yace.

"Cox I want you, bai kamata ki auri wani ba, ko Allah ya san nine mijinki."

Sai da Amina ta cije lebbenta sannan ta rufe idanunta tana murmushi, kuma kafin ta buWe idon ya sunkuyo daidai gefen fuskarta yace.

"I apologize if this is a little bit forward, but you just look so.... Woww!"

Abinda taji kenan kafin taji ta a cikin hannayensa. Numfashinta ya yanke daga huhunta a lokaci guda, ?afafunta suka karbi hannayenta wajen rawa, zuciyarta ta sake komawa ruwa, ta sake komawa irin duniyar jiya, duniyar da take manta komai sai Ma'aruf kawai da irin abubuwan da yake nuna mata.

Ya tallafi fuskarta kaWan yana sawa ta kalle shi, don ko kaWan ta kasa rufe idanunta ma yanzu, idanunsa cikin nata yace.

"You are making my world so much more beautiful Amina."

(Kina kara ?awata duniyata Amina.)

Shikenan! Sai komai a cikin kan Amina ya sake rushewa, kalaman Hajiya Kilishi har ma dana Amma dake kokawar mi?ewa, dukkan wani abu mai hankali a cikin kanta ya shiga gaya mata cewar da gaske ne ba zata iya taba lafiyar Ma'aruf ba!

*****

A cikin dakin, a cikin wayar, muryar Hajiya Kilishi ta ratsa da tsananin ya?inin dake fitowa daga zuciyarta.

"Mahaifinta shine a lissafi Awwalu, munyi wata ya shaida min cewa sun dawo Wazu, don haka gobe zai fita aiki ina so ka fara bibiyarsa tun daga safiya, duk inda zaije ka kasance tare dashi kuma a shirye, wa'adin lokacin zuwa yamma ne kamar na yaron nan. Idan har ban sami abinda nake so zuwa sannan ba, zaka ga umarni na."

Daga cikin wayar Awwalu yayi dariya mai cike da mamaki yace.

"Mutumin nan fa shine Wanuwanki Kilishi, ina laifin ki sake taSa wani daga cikin ?anuwan nata kawai? kuma shi bashi da wata matsala ma naga, let the man be! Ki duba iyalinsa ki kyale shi."

Ko bai ganta ba ya san ranta a hafe yake sanda tace.

"Tun yaushe muka fara la'akari da wani abu a cikin lamuran mu Awwalu? Ka amsa min kawai, bana bu?atar dogon surutu."

Sai ya sake kyalkyalewa da wata dariya mai armashi irin tasa sannan yace.

"An gama Hajiya, umarninki shine abin aikatawa ta!"

**

_Ku gaya min cewa Amina tana shirin kaimu ta baro..._

_Ko kuma laifin na Ma'aruf ne?_

_Ga dai mafita tiryan-tiryan Amma ta fitar, amma kamar Amina kuma kuna ganin cewa da matsala?_

_To wace matsalar kuka zaba?_

_Ta Amma dake cikin mafitar?_

_Ko kuma ta Kilishi da zata biyo baya?_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*02*

~~~~~~~

_The act of love is Confession._ _- Unknown_


**

*Shekaru Goma da suka wuce.*

*?arfe takwas na safiya.*

A bakin titi ne, daidai bayan dogon banki wajen da Babu mutane sosai musamman a safiya irin haks, motar da Hajiya Kilishi da kuma Awwalu take tana daka fake a gefen titi an zuge duka gilasanta da bakin tint mai duhun gaske, don musamman don wannan fitar Hajiya Kilishin tace da Awwalu yaje ya saka tint Win.

A cikin motar, Kilishin taja tsaki tana kallon agogon tsakiyar dashboard kafin tace.

"Mutanen nan sun fara vata mana lokaci Awwalu, saninka ne fa ko Baffa bai san na fito ba."

Awwalun dake gaba mazaunin direba ya gyada kai shima yana kallon titin yace.

"Ki bari kawai, ni kaina ina da aji ?arfe takwas Win nan, kuma wallahi mai muhimmanci ne."

"Aji?" Da mamaki a fuskarta ta tambaya.

Sai ya juyo ya kalle ta.

"Au na manta ban gaya miki ba, na koma makaranta fa, Bayero na samu ina yin English saura shekara Waya ma na gama."

Kilishi taji ranta ya kara baci, har tana shirin bude baki tayi masa korafin ta yadda har ya shekara biyu a University ba tare da ta sani ba sai kuma taga meye damuwarta a ciki? Rayuwarsa ce, zata hana shi ne idan har hakan ba shafarta zaiyi ba, kuma ma tun asali ta san Awwalu mai son karatu ne, don tun yana yaro farkon zuwansa almajiranta da kudinsa yasa kansa a makaranta har ya gama firamare kafin daga baya kakarta ta shiga tallafa masa, kuma shekaru biyu bayan ta gama shima ya fita daga sakandiren, don haka karatunsa bai kamata ya dame ta ba.

Ta juya tana kokarin kallon wani mai teburin shayi daga can nesa dadu dake ta kokarin hada wutar itacensa, amma itacen ya?i bashi hadin kai duk kuwa da iskar sanyin da ake hurawa a lokacin. Ba shiri taji murmushi ya subuce a bakinta, zuciyarta ta cika da jin dadin yadda dattijon ke ta goho yana firfita wutar, tana son irin wannan abin, tana son taga wani nata wahala akan neman bukatunsa har sai zuciyarsa ta ?e?ashe ta daina rauni, shi yasa ko kallo bata cika yi ba, don bata ganin amfanin yadda mutane ke tsara finafinan su cewa mai kirki ne zai ci galaba a kodayaushe.

Taja tsaki bayan wutar ta kama babu daWewa, ta dawo da idonta cikin motar tana ?o?arin lalubo wayarta, sai kuma ta tuna ai ta kashe ta don kar ma a neme ta, kuma a daidai wannan lokacin sai ga wata mota katuwa ?irar jeep Prado tazo ta sha gabansu, nesa kadan tayi fakin ta tsaya.

"Ina ga gasu nan Hajiya."

Cewar Awwalu yana kallon motar.

"Fita zanyi kenan?"

Ya gyaWa kansa.

"Ai bana tunanin shi ne zai fito."

Sai ta kuma jan wani tsakin.

"Mutanen nan suna cin alfarmarta da yawa Awwalu, ba don dole Jamal ya bar duniyar nan ta hanyarsu ba, bubu abinda zai hana ni zaba musu irin tasu ?addarar su ma."

Awwalun ya juyo yana kallonta.

"Ha?uri zaki yi Hajiya minti biyar ne ba su isa su sake ganin fuskarki ba har abada, harbin tayar mota tana gudu ba aikin kowa bane banda irinsu da suka san duk wani tactis na abin...."

Bata ko jira jin ?arshen zancen nasa ba ta sauke nikabin da ta daura a fuskarta sannan ta janyo wata ?ar madaidaiciyar jaka dake gefenta tare da wata farar takarda ta bude kofar motar ta fita.

Kanta tsaye ta isa wajen motar ta tsaya daga daidai ?ofar baya, kuma daga inda Awwalu ke zaune yana hango sanda aka zuge gilashin ita kuma tasa hannu ta sake Wage nikabin nata.

Wani mutum ne zaune a ciki, fari tas dashi irin farin da yake komawa tamkar zabiya, sannan ilahirin fatarsa kaf, koina akwai wani Wigo-Wigon bakin wani ciwo da ya fito ya warke. Idanunsa na sanye da wani katon gilashi ba?i ta yadda ba'a ko ganin kwayar idanunsa, a lokaci guda yayi wani murmushi da ya baiyana jerin ha?oransa wanda rabinsu suna rufe da ?arfe ne irin wanda ake cewa hs?orin makka kalar ruwan gwal don haka sun haska tar a cikin hasken safiyar.

"Barka da zuwa Hajiya, sai ha?uri da irin aikinmu na gaya miki ni bana mu'amala da jakada, shi yasa kika ganni nima da kaina."

Hajiya Kilishi bata yi murmushin ba, tana kallonsa idanunta a tsaye tace.

"Tun da har ka ganni anan ai ka san wannan maganar ta wuce kuma."

Sai ya Waga mata girarsa daya cikin duniyanci irin nasa sannan ya nuna jakar hannunta yace.

"Sune wadannan?"

Sakan Waya biyu tana kallonsa hankalinta na kokarin danne takaicin dake yawo a zuciyarta kafin ta Wago jakar ta miko masa, ya kuwa karSa ya zura ta cikin motar sannan ya buWe, idanunsa suka yi nazarin kuWin dake ciki.

"Kince yau da misalin karfe tara zai fita sannan shi kadai ne a motar ko?"

Ta gyada kanta sau Waya sannan ta mika masa wannan farar takardar hannun nata.

"Ga lambar motar koda wancan text Win ya gige."

Ya karbi takardar ya kalla sannan ya sake Wagowa? ya kalle ta.

"Hajiya zan so ace babu magana biyu a cikin wannan al'amarin namu, zamu ?irga kudin nan idan sun cika zaki ga aiki, idan kuma akwai matsala, to kuwa za'a sami matsalar da gaske."

Sai da ta Wauke kanta gefe cike da takaicin yadda yake mata maganar sannan tace.

"Idan kuma har babu matsalar ta yaya zan tabbatar da cewar zaku yin?"

Ta dawo da idonta kansa lokacin da yake sake wani murmushin.

"Tabbaci kike nema?"

Bata amsa ba, shima kuma bai jira amsar ba, sai kawai ya Waga yatsansa Waya a iska yana cigaba da murmushi.

Kuma bata gama tunanin me Ke shirin faruwa ba lokacin da ta wata irin ?ara ta ba?unci iska, tsananin karfin ?arar yasa duk dauriyarta sai da ta firgita, kafafunta suka yi baya yayin da tasa hannayenta duka biyu ta toshe kunnuwanta lokacin da idonta ya kai kan wasu maza da suka juya da gudu bayan sun karyo kwana, sannan ta hango wannan mai shayin ma ya kwanta a gaban teburinsa yana kakkarwa, tabbas ?arar ta bindiga ce ba wani abu ba.

"Wannan shine tabbacinki Hajiya, yarana basa wasa da aikinsu, hannu kawai nake Wagawa shikenan duk abinda nace zai wakana ko akan waye kuwa."

Bayaninsa yazo daidai da lokacin da idonta ya sauka akan tayar motarsu ta gaba, gabadaya ta dagargaje ta kuma wargaje a lokaci guda, motar ta tuntsira tayi gefen titi, yayin da Awwalun dake ciki ke kokarin buWe kofarsa don ya fito kar ta kara hantsilawa dashi.

"Na barki lafiya."

Ta sake jin muryar mutumin kuma ko kafin ta juyo ta kalle shi, direbansa yaja motar sun yi gaba da wani irin saurin da har sai da tayar motar ta gurzu da titi ta bada wata irin ?ara.

Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Hajiya Kilshi karo na farko a wannan safiyar, tabbas ta bakin Awwalun ne, mutanen nan sun iya aikinsu, rainin hankalinsu ne kawai a gefe. Taji murmushin nata na sauka har cikin zuciyarta da tunanin cewa ba za'a samu akasi ba, a yau Jamal zai bar duniyar nan, ai ta gaya masa... ta gaya masa lokacin da ya juya mata baya zai tafi.

_"Na so zan yi dukkan shirina in bar cikinku ba tare da na taba wani ahalin Baffa ba, nayi maka katanga mai yawa Jamal, na daWe ina kange ka daga sharrina, amma ka rufe idonka ka tsallako ka iso... Ina jiye maka takaicin barin duniya da ?uruciyarka, ina taya ka alhinin barin duniyar nan a lokacin da ya kamata ka fara cin ganiyarka, don daga yanzu ni da kai, mutane ne da baza su taSa iya rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba."_

Ta sake wani murmushin tana cije leSSenta, zata so ace zai tuna wadannan maganganun nata a lokacin yake bin ruhinsa da kallo zuwa sama. Awwalu ya karaso wajenta?a lokacin da nasa murmushin shima, fuskarsa na Wauke da yanayin da ko bai furta ba ta san me zaice.

_"Me na gaya miki? Mutanen nan zasu iya aikin ki."_

Sai kawai ta juya ta kalli motar tasu a lokacin da Jama'a suka fara taruwa suna ?o?arin zagayeta.

"Zaki yi waya a kawo mana wata motar ne?"

Ya tambaya, ta girgiza kanta.

"Baka da zurfin tunani Awwalu, ta yaya hatsarina zai zo rana daya dana Jamal? Tsaftataccen aiki nake yi a kodayaushe ka sani, bana yin sajacin da zan bari ko da Wigon baki da zai kawo zargi a zuciyar wani na."

Awwalu ya gyaWa kansa yana cigaba da wani murmushin kafin yace.

"Na yarda dake wallahi Hajiya."

""Kaje ka siyo wata tayar, a daura sai mu tafi."

Kuma wadannan kalaman nata na lokacin sune tushe, shine sanadin faruwar wasu abubuwan da har a yau ba'a warware su ba, don Awwalu ya dauki tsawon lokaci kafin ya iya samo sabuwar taya da kuma mai daurata kasancewar safiya ce lokacin, don haka kafin su koma gida matafiyan nan sun tafi.

"Mami, Ya Ma'aruf ya shigo yace ya kira wayarki a kashe, yace idan kin dawo in gaya miki ya bi Ya Jamal zuwa Abujan, zaku yi waya idan kin dawo."

Kalaman da Salma ta faWa mata kenan bayan ta koma gida da misalin karfe goma saura na wannan safiyar.

Kuma a tarihin rayuwar Kilishi kaf! Idan zata misalta kalmar tashin hankali, zata kwatanta ta ne da wannan ranar, ranar da zuciyarta ta buga a kirjinta, kafafunta suka zube gar a ?asa yayin da idonta ya shiga hasko mata gawar Ma'aruf din da bata tsara a lissafinta ba tare da ta Jamal!

***

*Present Day.*

"Halima."

Alhaji Sulaiman dake zaune a cikin Wakinsa ya kira sunan matarsa dake shirin sa kai ta fita bayan ta ajiye masa flask din ruwan zafin da ta dafa a dawowarsu yanzu da safen.

Tsintsiya ce a hannunta wadda ta dauka don zuwa? ta kara share falo inda aka kwantar da Aminun, taso ace tun jiya su Maryam sun zo sunyi sharar kafin su dawo, amma haka kurum ta kasa kiran iyalan gidan Kawu Malam inda su Maryam suka tafi da wannan umarnin, tana da kawaici akan ?a?an ta kowa ya sani, abinda mutane basu sani ba shine tana ajiye wannan kawaicin a gefe idan har aka zo gabar da za'a cutar mata dasu.

A kofar dakin ta saki tsintsinyar sannan ta juyo ta dawo ciki, don daga yanayin amon muryar Baban ta san magana ce mai muhimmanci zasu yi.

Ta sami waje gefensa ta zauna yayin da idanunta farare irin na Amina sak ke kallonsa, kallo na saurare da kuma jiran umarni.

"Jiya na hango ki kina waya da ?arki."

Ta gyada kanta sau Waya bayan ta gane cewa Amina yake nufi.

"Akwai wata matsala ne da take fuskanta a gidan?"

Mamakin tambayar tasa ya kamata, sai kawai ta sunkiyar da kanta kasa a hankali, a shekarun zamanta dashi kaf! ya sani ko da sau Waya bata taba zuwa ta bashi labarin wata matsala ba walau ta danginta ko kuma ta wani da ya shafe ta ba kuma shima baya taba tambayar abu makamancin hakan ba sai idan har zancen ne yazo a dole su fade shi, don haka abinda ba'ayi a baya ba, ba za'a fara shi yanzu ba.

Amina yarsa ce, ta san yana da hakki akanta amma a tunaninta ya riga ya gama taka rawarsa akanta, yayi ruwa yayi tsaki wajen kaita rayuwar da babu ta hanyar da bata kalubalance shi ba. Shi da kansa ya fada cewa ba zai iya tuna ranar da tayi masa musu akan wani abu ba, amma bai ko duba wannan kawaicin nata na tsawon shekaru ba, da yake shi namiji ne ya rufe idonsa ya juya mata baya, ya dora yar tasa a wani mizani da dole nasa umarnin zata dauka.

A yanzu anyi hakan, komai ya wuce ba tare dacta nuna fushinta ba, kuma gashi sun fara fuskantar kalubalen da ta guje musu shi, to don me yasa zai tambaye ta kuma?

Ta fahimci har yau Sulaiman bai gama buWe halayenta ba, don da ya san wacece Halima da bai Sata bakinsa ma wajen tambaya ba, bata gori, bata cewa 'dama na fada...' zata yi iya kokarinta ne a farko don ganin ta kawar da matsala daga karasowa gare ta, idan kuma ta kasa, sai ta fara shirin tunkararta ta hanyar da zata iya kawar da ita, wannan shine babban abinda ke ri?e da zaman lafiyar gidanta dama zamanta tare dashi. Shi kansa idan zai tuna yana da zafi da kuma zuciya a lokacin kuruciyarsa har zuwa aurensu, amma da wannan halayen nata ta canja shi a lokacin da bai ma sani ba.

Don haka sai ta gyara zamanta kawai a hankali sannan ta girgiza kai.

"Babu wani abu, wata yar matsala ce kawai tamu ta mata."

Ya kalle ta tsawon wasu mintuna kafin ya sake kiran sunanta.

"Ina fata a yanzu kin daina ganin laifina Halima, don kowa shaida ne daga ganin yarinyar nan an san tana cikin nutsuwa."

Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Amma, mazan kenan! bata jin har abada za'a zo lokacin da kwakwalwar kowanne namiji zata bude game da al'amarin mata, suna ikirarin sun san komai a kullum, amma tarin abubuwan da ake lullube su a ciki suna da yawa, wanda hakan na Waya daga cikin abubuwan dake juya duniya, don da zasu san kowacce kissa da dabara irin ta matan to da zaman auren ma zai gagari kowa ce ?abila a duniyar nan.

Tun a lokacin da aka jawo kayan kefen Aminan kallo Waya tayi wa akwatunan da aka zuba kayan kwalliya zuciyarta ta Warsa mata wani abu da sai a yanzu take ganewa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login