Showing 66001 words to 69000 words out of 132946 words

Chapter 23 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1126

karanto adadin kayan da take lissafawa a ciki, bayan jotter akwai jug mai garai-garai yana Wauke da lemo kakar yalo tar da kuma kofinsa wanda?aka zuba lemon a ciki.

Ta kai ?arshe a wayar tata, sannan ta sauke wayar, kuma kai tsaye hannunta ya lalubo nambar Hajiya Kilishi wadda taji shigowar nata kiran a lokacin da take waya.

"Ina tare da mutane na ne ranki ya daWe..."

Ta fada kai tsaye bayan Kilishin ta Wauki waya daga nata Sangaren.

"Na sani ai shi yasa ban takura ba... Saratu ta kira ni da safe take gaya min cewa zasu dawo kasar nan kunyi waya?"

Hajiya Salamatu ta gyaWa kanta tace.

"Mun yi tun jiya, nake cewa komai labari ne, yaushe take ta daga hankalinta akan ya?i tafiya da ita gashi har ya dauke ta da ?a?an nata kuma zasu zo hutu."

Hajiya Kilishi tayi murmushi mai kama da dariya kafin tace.

"Da ta biyo ta hanya ta ba, a baya ta tashi hankalinta a banza, amma da ta fahimce ni ta ja da baya ta zama macen kanta ba gashi yanzu komai ya dawo hannunta kishiyar tata ma ta kama gabanta ba."

"Wallahi kuwa..." cewar Hajiya Salamatun kafin ta canja zancenta da cewar.

"Kin samu kayan ne?"

Hajiya Salamatun ta tambaya tana kurbar lemon hannunta.

"Wai sai Jibi zasu iso, abinda nake ta tunani kenan Salamatu, karo na farko da zuciyata ta kasa kwanciya akan wani abu, haka kurum nake jin cewa kamar jibin nan ba zata karasa ba wani abu zai faru."

Hajiya Salamatu tayi dariya kafin tace.

"Ki kwantar da hankalinki Hajiya, kin san hausawa sun ce aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, gangarar kawai kika zo shi yasa kike jin haka, ban da abinki ma daga ni sai ke fa muka san wannan abin da kike shirin yiwa Awwalun nan, kuma ni dai kin san ko yanka ni akayi baza'a iya fitar da sirrinki daga cikina ba ko?"

Kilishi ta gyada kanta.

"Na sani Salamatu, kawai ban san me yasa ba bana gane komai ne a yanzu sai na fara gamawa da Awwalun nan, Wazu munyi waya da Maigaskiya yace min yana office abubuwwa sun yi masa yawa, bai ce min komai bayan hakan ba amma na fahimci kamar binciken nan suke yi kuma sun gano wani abu Salamatu, da ba Awwalu na dora akan harkar nan ba da na bari ko sau daya ne dun ganni da tuni inaga abubuwa sun canja kala daga yadda nake kallonsu."

Salamatun ta girgiza kanta itama.

"Ki daina wannan tunanin, ki fuskanci abinda ya rage kawai bayan Awwalun, zancen yarinyar nan tasa Hamida sai kuma mutuwar shi mai gidan naku da har yanzu baki tsara yadda zata kasance ba."

"Na tsara komai Salamatu, zan gaya miki da zarar mun hadu, a yanzu bayan wadannan biyun kuma ina so da Amina idan ta gama yi min aiki akan yarinyar in raba ta da mai gaskiya itama, a fuskokinsu kawai zaki gane kamar rayuwa na tafiyar musu daidai, ba zan iya basu wannan farin cikin ba Salamatu... Ba zan iya barin Ma'aruf da wani abu mai haske a rayuwarsa ba, so nake har ?arshen rayuwarsa ya dauwama yana tunanin ni kaWai ce haskensa."

Hajiya Salamatu ta taSe bakinta kaWan kafin tace.

"Ba zaki canja tunaninki akan yaron nan ba Kilishi, amma wannan Win ma daidai ne, ai bai Wara daga cikin aikin ki ba, sai dai tsaya... Wane tabbaci ma kike dashi cewa har i yanzu yarinyar nan bata Wauke da wata hamidar ko kuma Hamidu?"

Kilishi tayi murmushi mai fadi kafin tace.

"Na dade da bata magani Salamatu, kuma a yadda yarinyar nan ta yarda dani ba zata saba min alkawari ba, abinda zanyi musu ma idan ta gama yi min wannan aikin na Hamidan zai rufe musu ido ba zasu ga komai a rabuwar tasu ba daga iyayenta har ita din. Kuma yadda zan raba sun babu wuya, ni na san abinda zanyi, na san abinda zanyi yadda Mai gaskiya ba zai sake kallon yarinyar nan a duniya ba."

Hajiya Salamatu ta gyada kanta.

"Na fahimci har yanzu da saura a harkar nan Kilishi, shi yasa kika ce zuciyarki ta kasa kwanciya... Amma kar ki damu, tunda kin iya da tarin abubuwan da kika shallake a baya waWannan ma ba zasu yi miki wahala ba, ki cigaba da tsarinki kawai, ina garin nan har sai kaya na sun ?are, don haka kar kiji komai."

Da haka wayar tasu ta ?are.

Hajiya Salamatu ta Wauki jotter da kuma bironta sannan ta mi?e tare da wayarta ta shiga ciki tana barin jug Win lemon anan, kuma shigarta kenan bata ko yi minti biyar ba, wata ?ar aikinta mai suna Sadiya ta shigo, ta durkusa har kasa tace.

"Hajiya kinyi ba?o, yace wai mai karbar kaya ne shi yasa maigadi ma ya barshi ya shigo."

Ta Wan kalle ta tsawon wasu sakanni tana son tuna wadanda suka yi alkawari dasu a yau cewa za'a zo a karSi kaya, bata tuna Win ba don haka sai kawai tace.

"Je ki shigo dashi."

Ta tashi ta juya ta fita, idonta yabi ta da kallo har ta fita daga ?ofar falon nata da yake na biyu a jerin tsarin gidan.

Minti guda bayan haka Sadiya ta dawo, biye da ita Wani ne da bata ga fuskarsa a karo na farko ba kasancewar ya saka riga irin ta sanyi mai hula ya rufe kusan rabin fuskar tasa, don haka bata sallami Sadiya ba ta tsaya tana kallonsa, idonta akan kofin lemonta wanda ta baro a waje dake rike a hannunsa yanzu, kuma kafin tayi magana yasa hannu ya cire hular zuwa baya, a lokaci guda fuskar Awwalu ta baiyana a gabanta.

Yana murmushi ya kai kofin bakinsa ya kurSa, sai kawai ta Wagawa Sadiya hannu alamun ta sallame ta, Sadiyar ta juya ta tafi shi kuma ya karaso ya zauna a kujerar dake gefen tata.

"Me ya kawo ka wajena Awwalu?"

Ta tambaya fuskarta a hade tana kallonsa, da murmurshi a fuskarsa ya sake kurbar lemon sannan ya taso ya fuskance ta sosai yana rike kofin da duka hannayensa biyu.

"Ni ba mutumin banza bane Hajiya, na san ?awarki, na san Kilishi tun bata da komai a duniyar nan sai ku biyu ke da Wayar da bata magana Saratu... Yau sati guda kenan Kilishi bata kira ni ba, tun bayan da na karbo mata wannan hodar a Lagos, don haka dole na san akwai abinda yake faruwa kuma na san ba zan sami bayani a ko'ina ba sai a wajenki ko kuma wajen wannan Wayar yarinyar da ta shigo da ita cikin al'amarin.

Don haka zuwa nayi ki gaya min ta inda Kilishi ke shirin kashe ni..."

Hajiya Salamatu ta kalle shi tsawon sakanni, cike da mamakin yadda akayi yasha jinin jikinsa game da Hajiya Kilishin tunda ta gaya mata cewa bata bashi wata dama da zaiyi tunanin cewa tana shirin juya masa baya ba... Kuma ko mutumin da ta saka ya kusance shi mai suna Sadik bai bada damar da zai zarge shi ba har yanzu. Sai kawai ta haWiye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta.

"Ban san komai ba Awwalu, ka tashi ka fitar min daga gida."

Ta ?arasa tana nuna masa hanyar kofa, sai kawai ya saje wani murmushin yana kallonta, ya girgiza kansa sannan ya sake kai kofin lemon bakinsa, wannan karon ya shanye shi tas! Sannan ya Wago ya sake kallonta.

"Na gaya miki ni ba mutumin banza ne bane Hajiya, ina da abinda zaki miko min Hajiya Kilishi yanzu ba sai anje koina ba."

"Me kenan?"

Ta tambaya tana kallonsa cikin ido. Ya sake wani murmushin yana kallonta cikin ido shima kafin bakinsa ya sake motsi.

"Kina da labarin inda Wanki yake?"

Mamaki ya bayyana tar a fuskarta, mamaki irin wanda ke sauka a fuskar mutum lokaci guda, ba shiri bakinta ya furta.

"Wane Wan nawa?"

Awwalu yana sake wani murmushin da shi kadai ya san ma'anarsa kafin yace.

"?an da kika haifa tare da mijinki na farko, wanda ya mutu a asibiti ranar da kika haife shi!"


***

_Ku gaya min me yake shirin faruwa ne?_

_Me Awwalu ke shirin haddasawa tsakanin aminan guda biyu?_

_Me ya faru a wancan lokacin?_

_Me Amma ke shiryawa game da tsarin Hamida?_

_Su Ma'aruf zasu sami Awwalu kuwa?_

_Ta yaya kuke tunanin faWowar Kilishi zata fara?_

_Gashi tana ta lisaafo wasu sababbin tsarikan...=??_

_And yes! BabyDoll think they are Pregnant!=??.... Ta yaya ake Soye ciki ne wai=???_


Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*15*

*Ina mika ta'aziyyata ga al'ummar musulmi na rashin babban malamin da muka rasa a yau, Dr Ahmad Bamba BUK. Allah ya jimansa ya kyautata namu zuwa Ameen.*

~~~~

Awwalu ya cije lebbensa, kansa yana gyadawa... Gyadawar da shi kansa bai san yana yi ba, idanunsa sun canja, dun cika kuma sun yi fayau, suna tsaye akan fasashshen gilashin kofin dake gabansa, kofin da ya tarwatse tun daga lokacin da Hajiya Salamatu ta feWe masa biri har wutsiyarsa game da dukkanin shirin Kilishi akansa.

"... Haukata take shirin yi Awwalu, tace zaka ?are rayuwarka ne kana biyan bashin abinda kayi niyyar yi mata, ta shirya komai tare da abokin ka Sadik, zai saka maka maganin bacci ne a cikin wani abu da ka sha ka fita daga hayyacinka zasu Waure ka, akai ka cikin gidan gonarja da yake Janguza, anan zata je ta same ka, zata yi maka bayanin komsi idan ka farka sannan zata saka Sadik yayi maka wasu allurori a gabsn idonka, tace guda takwas ne, suna nsn tayi odar su zuwa jibi zasu iso, kuma bana tunanin zata bata wani lokaci idan har sun iso din, don tana da tarin wadu abubuwan da zasu yi bayan naka..."

A lokaci guda yaji wani abu na cika idonsa, kuma kafin ya lissafa dumin hawayen dake tahowa ya shiga saukowa kan kuncinsa... Yana jinsu, yana jinsu duna fitowa wani na bin wani, cikin gudun dake son kwatantawa da yadda zuciyarsa ke masa a wannan lokacin, cikin gudun da zaiyi daidai da rawar da yatsun hannayensa ke yi a gabansa.

"Babu abin hawaye anan Awwalu, abinda kuka yi kai da ita yafi karfin hawayen a wasu zukatan, ko ka manta suma wadancan mutane ne kamar ku?"

Hajiya Salamatun ta tambaya tana kallonsa kai tsaye a gabanta. Sakanni kusan biyar kafin ya girgiza kansa a hankali.

"Baki san komai ba Hajiya, baki san abinda nake ji ba, ba zaki iya kwatanta zuciyata ba watakila sai kin ji naki tukunna...Kilishi ta cuce ni, ta cuci dukanninmu, ta cuci tarin al'ummar da har yau bana hango kwakwkwaran dalilinta na yin hakan, na dade da dawowa daga rakiyarta, na dade da nadamar abinda son kuWi na ya jawo min, shi yasa na daWe da fara gyara rayuwarta.

Ba tun yau ba na san Sadik yaron Kilishi ne, na san ita ta aiko shi ya kusance ni tun daga lokacin da ta kula na fara canja mata, ina sane na biye masa na ja shi jikina kamar yadda take so kuma nake gaya masa dukkan sirri na, ina sane na gaya masa cewar na shirya kwace dukiyar da take tarawa kuma na tara hujja ta akanta, ina sane na gaya mata hakan don in san irin tunaninta akaina.

Amma ba wannan ne shiri na ba, don ko kudin da nake samu a wajenta na dade da daina cin su, suna nan a banki ina tara su don na san ba halali bane, bayan na gama karatu na sami aikin koyarwa a wata makaranta, da albashi na nake rike kaina bana taba wadannan kudin ko kadan.

Kuma nayi niyyar kawo karshen komai ne saboda na gaji, shi yasa na gayawa Sadik wannan maganar don in san in tsayar da abubuwa a tsakaninmu kuma in kawo karshenta. Kilishi ta cuci tarin mutane a duniyar nan Hajiya, ta cuci al'umma ta hanyar da bana tunanin ubangiji zai ?ona ta a wuta iri daya da ta sauran mutane, tayi abubuwan da idan ina tuna su a cikin kaina, na kanyi kokwanton idan har ba wani Sangare ne na shaidan ya sauko duniyar nan ba."

Ya juyo ya kalle ta a hankali, hawayen dake fitowa a idanunsa sun tsaya, sai shatinsu daya rage akan fuskar tasa.

Hajiya Salamatu kallonsa kawai take yi da abinda ba zata iya fassara shi ba a cikin kanta, duk abinda yake faWa game da Kilishi ta sani, ba tun yau ba ita kanta ta sha wannan tunanin a cikin kanta, tasha fada mata hakan ma cikin magana, amma daga wannan tunanin zuciyarta bata kara komai, tana Waukan komai dinne a matsayin labari kawai, bata jin wani emotion ko feeling na tausayi ko kuma na jin ciwon abun a zuciyarta, zata cigaba da harkokin ta ne kawai kamar babu wani abu da ya faru.

Don haka a yanzu ma ba wani abu taji ba, ita ba ta wannan take ba, zuciyarta na rawa ne tare da kuma hankoron bayanin da Awwalun ke shirin bata, bayanin da yayi mata alkawari kafin tayi abinda take jin kamar tasa hannu ne ta kashe aminiyarta tata a gabansa.

Kuma har yanzu zuciyarta bata gama kokwanto ba, bata gana kokwanton cewa idan har bs zata dsuki nasa bayanin ta kai mata ba, don Kilishi kamar wani barin ta ce, bata taba tunanin akwai wani abu da zai sa ta iya sarayar da sirrinta cikin sauki haka a duniyar nan ba, amma idan ta duba ba saukin bane, babu sauki a cikn soyayyar uwa ga danta, ga abinda ta haifa ko da kuwa bata taSa tunanin da wanzuwarsa anan duniya ba.

Awwalu yasa tafin hannunsa duka biyu ya share hawayen fuskarsa sannan ya sake kallonta.

"Na san har yanzu kina kokwanton ki dauki maganata ki mayar mata, idan na gaya miki naki bangaren labarin, kwalwarki zata fahimta, watakila ko kadan ne, zaki ji irin abinda naji a zuciyarki, watakila hoton Kilishi zai iya canjawa a zuciyarki da siffar da kike kallonta."

Kuma bai bari ta ce komai ba ya cigaba da cewa.

"Shekaru talatin da hudu da suka wuce idan baki manta ba a lokacin kika yi aurenki na farko, watanni kadan da kuka kare karatun sakandirenku, ke kika fara aure a cikin ku ukun, kika auri Alhaji Ibrahim Shanawa, mai kudin da kowa ya sanshi a wannan lokacin.

Kuma a sannan ne amincina da Kilishi ya fara, don kamar yadda kika sani ni almajirin kakarta ne inda ta taso, a gidan nake aiki ana biyani da kuma bani abinci. Mun yi sabon da a wannan lokacin ta ksn gaya min yan kananun damuwarta, kuma tun daga lokacin auren naki, da taga irin kudin da aka kashe da kuma gidan da aka kai ki ta fara shiga damuwa.

Ta gaya min cewa duk a cikin ku ukun itace iyayenta masu karamin karfi, ta gaya min sanadin abotakar taku ma ya samo asali ne daga taimaka mata da kuke yi ta hanyar kudin makarantar da kuma sauran abubuwan bu?ata, saboda haka tace min tun a wannan lokacin tayi alkawarin samun dukiya itama,ta sa a ranta cewa zata yi kuWin da zata kere ku duka, amma a lokacin sai gashi bata sami komai ba ke kin taka wasu matakan nasarar kala-kala.

Taji zafin hakan a lokacin sosai ta hanyar da sai da ya zama a kullum tsakani na da ita bamu da wata hira sai taki, har ta kai tana gaya min cewa zata iya komai don ta tsayar dake daga cigaba da samun nasarar da tafi tata.

A haka har lokacin da kika sami ciki, zan gaya miki tayi ba?in cikin da duk duniyar nan bata iya nunawa kowa sai ni, kuma wannan shine mafarin lokacin da Kilishi ta fara jawo ni cikin zunubanta, a irin kuWin da take samu a wajenki tayi min alkawarin wani kashi idan har zan taimake ta, na yarda ba tare da na san abinda take shirin yi ba sai a watan da zaki haihu, ta same ni ta gaya min cewar ba zata iya jurar ganin kin samu magajin a wannan gidan ba, don haka tana son mu san yadda zamu yi mu kashe jaririnki bayan kin haihu kuma tun a asibitin.

Sai dai bamu sami wata mafita ba har zuwa ranar da kika haihun, ranar da aka kira ta cewa kina asibiti, a wannan ranar ne Kilishi ta sami mafitar da ta dade tana nema, bayan mun isa asibitin ni da ita ta sami hadin kan wata Nurse da ta yarda ta musanya miki dan da kika haifa da wani matacce na wata mata mai tabin hankali da wasu mutane suka taimaka suka kawo ta asibitin ganin tana nakuda.

Ta shaidawa mutanen cewa dan matar ya mutu kuma za'a bayar a binne shi a asibitin sannan ta dauko gawar jaririn ta kawowa mijinki da kuma yanuwanki, dan da kika haifa kuma ta danka shi a hannun Kilishi a blye ba tare da kowa ya gansu ba. Idan zaki tuna Kilishi bata asibitin a wannan ranar da kika haihu.

Ni da ita muka hayi mota muka fita har bayan gari tare da jaririn, a wannan wajen ta dage cewar mu kashe yaron, amma sai tausayinsa ya kama ni, ganin yadda aka dauko shi daga haihuwa, jikinsa duk jini don ko lokacin goge shi ba'a samu sosai ba, ana miko wa Nurse din shi bayan ta faki idon mutane ta canja shi da wannan mataccen, amma duk da haka baya ko kuka har muka isa bayan garin nan.

Saboda haka da kyar na shawo kanta ta bani yaron nan ta fasa kashe shi, nayi mata alkawarin zan dauke shi zuwa wajen da babu wanda zai taba sanin daga ina yake balle kuma asalinsa. A wajen ta bani kudin mota muka rabu, sai na kora wani abokina da yake almajiri shima na shaida masa komai,sai yabani labarin wata kanwar mahaifiyarsa dake aure a wani kauye yace min babu shakka ya san zata karbi yaron, fon haka muma tafi tare dashi.

A tasha muka sayi madarar jarirai na samu na bawa yaron da kyar, sannan muka hayi mota guda zuwa wani kauye a hanyar Kaduna, wani kauye da ake kira da Garun Albasu, amma yanzu ance sunansa ya canja zuwa Yakura, anan muka sami matar kuma kamar yadda Ila ya shaida min ta karbi yaron babu wani musu, nayi godiya sosai na bata kuWi daga na hannuna sannan muka juyo.

Bayan na dawo na jinjinawa Kilishi komai kuma ta yaba min, daga wannan ranar ban sake komawa ?auyen nan ba, ban sake tunawa da yaron ba sai bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login