Showing 108001 words to 111000 words out of 132946 words

Chapter 37 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1142

tare da matar dake gabansa kwata-kwata.

Har yanzu a gaban bishiyar motar take, bishiyar da ta shiga cikin wani Sari na rayuwarsa, Sarin da ya riga ya zama tambarin da a kodayaushe a kowanne waiwaye shi zai fara kalla a rayuwarsa.

?arfe shida na safiya, ?an mintuna kaWan bayan sallar asubahi lokacin da suka ?araso wajen, yana tafiya ne da karfin gudun da tun daga nesa wani magidanci dake tahowa akan keke daga hanyar shiga kauyensu ya hango ta, hasken fitilun gaba ya fara gani kafin kurar dake bin ta a baya ta cika idanunsa.

Ba shiri ya dawo da idanunsa kan gonakin dake gaba, gonaki kusan biyar dake dauke da sabbin shukoki da suka fara fitowa, kuma kafin ya gama lissafin abinda ke shirin faruwa, motar ta karaso ta zarce ta cikinsu da tsananin gudun da tayoyinta har dagawa suke saboda tudun kunya-kunya dake gurin, tana wucewa tayoyinta na murje shukokin da matukin cikinta baya ko ganinsu balle yaji alamunsu daga ciki.

Hannunsa akan sitiyarin suke kawai yana danne shi wajen kara nausawa ciki, dogwayen bishiyun da idanunsa ke gani kadai yake iya kaucewa bayan haka baya ganin komai, baya jin komai sai tarin maganganun dake tarewa a cikin kansa suna sake dawowa.

Maganganun dake sa wa tun yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa, yana jin huci da kuma dumin wani abu na ratsa kirjinsa zuwa cikin idanunsa, har ya daina.... Ya zama baya jin komai... Baya jin komai sai sautin muryarta dake fitowa daga cikin wadannan CD's din a lokacin da yake tsugunne a gaban? computer Abdurrahim.

Yana tuna kowacce kalma da ta shiga kunnensa yana tuna su bi da bi saman kwakwalwarsa na tsara masa su daki-daki a yadda al'amarin ya faru a yadda komai ya kasance... Sannan bayan haka daga can ?arshen kansa muryar Awwalu ce ke amsawa, dukkan bayanan da zai iya tunawa yaji lokacin da yake shaidawa su Baffa tarin abubuwan da suka daWe suna binne su a cikinsa.

Ya sani cewa zuwan Awwalun da kansa a wannan lokacin da kuma abubuwan da yake fada abu ne mai mutukar mamaki duba da tsawon lokacin da suka shafe suna nemansa, amma mamakin sautin muryar Mamin da kuma tarin abubuwan da dake fitowa daga muryar tata ya shallake dukkan wani abu a cikin kansa bayan hakan duk da cewar bayanan Awwalun wani abu ne?da ya ?ara basu dukkan tabbacin da zasu nema, don Allah ya sani zai iya ?aryatawa.

A wannan lokacin zai ce ba haka bane, zai ce dukkan abinda yaji karya ne... Zai yarda da dukkan wata hujja da zata gaya masa cewa impersonation Win Maminsa aka yi, Mamin da ya sani mai ?aunarsu ce, zuciyarta a buWe take ga kowa, ba zata taba ko iya hada hanya da wanda zai cuce su ba balle ta saka hannu, balle kuma ace itace ja gaba wajen faruwar munanan abubuwa da yawa a rayuwarsu....

Sai dai me? Bai ma yi wannan fatan ba, baiyi ma yi wannan tunanin ba aka tafi har zuwa gaSar da komai ya tabbata, komai ya tabbata ta sigar da basu da wata kafa ko kuma hujjar ?alubalantar abinda suka ji.

Kuma ba ga shi kaWai ba, ya sani dukkansu a yanzu dalili zasu so sani, dalilin da yasa tayi hakan, ta aikata tarin abubuwan da baya jin ko akan fatar bakinsa zai iya furta su, dalilin da yasa ta shigo rayuwarsu tun farko ma, dalilin da yasa basu taba ganin komai ba sai tarin murmushi da kuma dimbin kaunar dake nunawa akan fuskarta mai kaifi, kaifin da take amfani dashi tana huda zuciyoyinsu a tarun lokutan da ko sau daya wsni a cikinsu bai taSa waigawa yaga? makamin da hannayenta ke rike dasu ba.

Wani? Akwai wanin da ya dace ne bayan shi? Akwai wanin da ya kamata ace a cikin Winbin shekarun da ya rayu tare da ita ace ko sau Waya idanunsa ko kuma tunaninsa basu taSa haska masa wani abu da ya kamata ya Worawa ayar tambaya akanta ba?

Hannunsa Waya ya shiga cikin gashin kansa a lokacin da Wayan ke kara danne kan sitiyarin suna ?ara nausawa cikin dajin, a cikin hannunsa ya shake likitan da aks ce ya jagoranci ?ar karamar tiyatar da akace anyi mata an tabbatar da makantar idanunta, kuna ba'aje koina ba a cikin hannun nasa likitan ya gaya masa cewa ita ta nemi da yayi mata hakan ya fadawa kowa cewa ta makance bayan tayi masa alkawarin tarin wasu kuWaWen da ba zai iya ?in tayin ba.

Kuma daga idanunsa kaWai ya san ta sani, ta san ya san komai, tun kafin ma ya faWa shi yasa bata ce komai ba har yanzu, har suka ?araso wajen da bai manta hanyar ba, don ba zai taSa manta ta ba, yazo fiye da sau goma kuma a zuwan farko ne kaWai yayi bilinbituwar da ta Wauke shi awanni kafin ya iya gane ba wajen, bayan haka baya jin ko a mafarkinsa ya taSa kauce hanya.

A lokacin da suka ?araso, idanunsa sun? tsaya akan bishiyar da kuma gudun da motar ke yi a cikin hannunsa, yaji wani abu na yawo a cikin kansa kamar wancan lokacin, shekaru goma da suka wuce, lokacin da hannayensa dama duk wani abu mai tsini a cikin kansa suka kasa tsayar da motar dake nufar bishiyar da yake kallo a yanzu, da sanda suka tafi suka dake ta,?suka dake ta a yanayin ba zai taSa fita daga kansa ba...

Sai kawai ya danna birkin motar a yanzu da ?arfi, da ?arfin da ya fitar da sauti mai ?ara daga waje, ?arar ta karaWe cikin dajin zuwa nisan da ba zai iya kintata ba, kuma duk da karfin birkin, motar bata tsaya ba sai da taje dab da bishiyar, dab da ita sosai ta yadda bai fi tazarar taku biyu kawai ba a abinda ya rage

Tayoyin na tsayawa ya buWe ?ofar ya fito, ya fito ya buWe ta baya idanunsa na kaiwa kan Hajiya Kilishin da har yanzu bata kallonsa, kanta na juye daga gefe tana hangen wani wajen daban, da tafiyar da suke yi da ma karfin birkin da ya faru a yanzu babu daya da ya canja ta daga mazauninta, idonsa ya tsaya akan fuskarta, awanni kadan da suka wuce, awanni da basu fi kirgen yatsunsa ba, duniyarsa a tsaye take game da rashin lafiyarta, yana jin komai ya birkice masa yana jin rayuwar ba daidai take tafiya ba tun kafin ma ya san sakamakon abinda ya same ta.

Amma a yanzu gashi tsaye a gabanta sai dai a yanzu bashi Win bane, ba Ma'aruf Win da yake a jiya bane, ba Ma'aruf Win da yake a shekarun baya bane... Baya jin kansa a matsayin kowa da kuma komai, jin sa yake a wani sabon mutum daban, sabon mutum Win da babu komai a zuciyarsa illa tarin abubuwan da yaji ya kuma sani daga daren jiya.

A karo na farko, yaji wani abu kamar kwalla na shirin ziyartar idanunsa, sai kawai ya juya ya koma mazaunin direban ya juya ya buWe booth Win baya na motar... idanunsa suka tsaya akan rediyon motar yayin da yake jin zuciyarsa na girgizawa tamkar yadda yatsun hannayensa ke yi, sai kawai ya danna ya play buttun a jiki kuma a take sautin dake fitowa ya karaWe kowacce speaker dake cikin motar.

_"Ka yi masa magana kawai Awwalu, na yarda zan bashi hakan, babu abinda ba zan bayar ba saboda wannan aikin... Ya kamata ka sani tun da har na kashe Jamal babu abinda ba zan iya ba akan cikar burina..."_

Tashin hankalin da ya daki tsakiyar kan Hajiya Kilishi a lokacin ba abu ne da zata iya misaltawa ba, tun daga lokacin da ta farka a daren jiya, lokacin da ta gama jin hirar dukkanin abinda ya same ta, ta daWe kwance a wajen tana tsara hanyar mafitar da zuciyarta ke sa?a mata, ta da yadda zata wanke kanta a idon kowa ta kuma fita daga ?ullin ?ansandan nan... Kuma tsarin nata ta tafi daidai a cikin kanta, ta ?irga komai ta fitar da dukkan hanyoyinta kamar yadda ta saba, hatta kuWin da zata kashe ta lissafa da kuma yadda bayan hakan tsarinta zai cigaba da tafiya daga inda ta tsaya.

Ta sami wani likita da ta farar-Waya ya amince da bu?atar ta jin makudan kuWin da a take tayi masa alkawari. Tana tuna murmushin da tayi bayan fitarsa, murmushin jin dadi da kuma jinjina wa kanta na yadda a kodayaushe mafita ke zywar mata, sai dai me? Ashe bata sani ba wannan murmushin shine na karshe da zata yi a wannan karnin watakila har ma da me zuwa a gaba... Don wadannan lokutan na jiya ta sani cewa har abada su zata lissafa a matsayin lokuta na ?arshe da suke daidai a rayuwarta.

Tana iya tuna maganganun da suka yi da Baffa kafin nan, sun shigo wajenta shi da Baba Usman, kuma dukkan maganganun da zasu kwantar da hankalinta su suka zanta, suna tabbatar mata da halin da kowa a can gida yake game da ciwonta da kuma cewar ta kwantar da hankalinta abubuwa zasu daidaita, wasu maganganu da suka ?ara saita hankalinta waje guda bayan tabbatarwar da tayi cewa abubuwa suna nan a yadda ta san su har a lokacin.

Sai dai tun daga lokacin da tayi ido hudu da Ma'aruf bayan ya shigo ya fizge bandejin da aka rufe fuskarta dashi, da kuma mutanen da ta gani a ?asa a kofar Wakin a lokacin ta fara fahimtar cewa tabbas abubuwa sun fara karewa mata, rayuwarta ta birkice a daidai ?arshen da bata taSa hangensa ba, kuma abinda Ma'aruf ya fada kai tsaye na cewar ta biyo shi yana kallon cikin idanun nata da zuwa wannan lokacin ta tabbatar da cewar an kai musu sakon makancewarta shine mataki na farko da ya fara tabbatar mata da cewar, rayuwa tana Wauke da mabanbantan kaloli kuma? ba a kodayaushe ne abubuwa ke tafiya kamar yadda Wan adam yake tsarawa a rayuwarsa ba.

"Babu kowa a duniyar nan, mu kaWai ne Mami... Babu kowa mu kaWai ne a wajen nan... Kuma na kawo ki ne don ki bani wata hujja kwakwara Mami, Me muka kasa baki a rayuwar nan? Me tasa zaki kashe Jamal? Me Hajiya tayi miki kika gurgunta kafafunta? Me Abdurrahim yayi kika dauke muryarsa?? Me yasa kike kwashe dukiyar Baffa?

Me zaki yi da ita Mami? Ina zaki je ina zaki kai ta? ?a?anki da su kansu kike rufe su da halaiyarki kike tarawa? Me zasu yi da ita Mami? Me suke nema a duniyar nan da basu samu yanzu ba? Me zasu nema ban gaba da ni ko Baffa zamu kasa Mami? Me yasa kike hukunta ni da soyayyar karya Mami? Me yasa kika sa na baki matsayi da kuma girman UWA a zuciyata? Me yasa kika kassara rayuwarmu kotawanne fanni Mami?...."

Muryarsa ta jero tambayoyin da dukkanin dauriyar da yake jin zai iya wajen saita kansa yayin da idanunsa ke kallon fuskarta,? har yanzu bata kallonsa kuma bata ce komai ba, baiyi tunanin zata yi magana ba dama don baya zaton idan za'a tara kalmomin duniyar na kaf zata sami wadanda zata iya kare kanta dasu, sai kawai ya juyar da kansa yana sake kallon bishiyar dake gabansu, a lokacin hawayen da yake dannewa suka sulala kan fuskarsa.

Yana jinsa ne fanko, kamar wani ya zazzage dukkanin abubuwan da ya sani da kuma abinda yayi mu'amala dashi a rayuwarsa, kamar wani ya shafe dukkan tarihinsa komai ya zame masa sabo, yana jin kamar bai san ina ya nufa ba bayan nan, kamar bashi da wani takamaiman wani abu da zai sake yi a rayuwarsu, sai kawai ?wallar dake danne a idanunsa ta fito tana gangarowa kan fuskarsa.

Kuma a lokacin ne dukkaninsu suka jiyo jiniyar motocin ?an sanda dake tahowa daga bayansu, motocin guda biyu ne yana hango su tun daga can nesa ta gilashin motar suna tahowa, daga gefensu motar Faruk ce ke tahowa, sai kawai ya sake juyo da fuskarsa ya kalli Hajiya Kilishin da har a lokacin take zaune bata motsa ba.... Kuma sai a sannan ne idonsa ya gane masa hawayen dake gangarowa kan fuskarta...

Wani abu da ya saka shi murmushi a lokaci guda kafin ya sake juyawa, dogwayen yatsun hannunsa suka rufo kofar motar yayin da dayan ya murda mukullin mitar yana kunna ta.

"A tunanina, nan wajen shine mafari Mami, shine mafarin dukkan wani abu da kika dade kina ?ulls mana, daga kan Jamsl kuka fara, don haka daga kansa zsmu tsaya."

Yana faWin haka bai jira komai ba ya ?arasa tayar da motar sannan ya danne kanta, a lokaci guda ta figa da tsananin ?arfi kai tsaye tana nufar Bishiyar nan....

Kuma ta cikin gilashin dake gaba idanun Ma'aruf na kan fuskar Mamin da ta Wago tana kallonsa fuskarta shaSe-shaSe da hawaye sanda motar ta karasa ta daki bishiyar da wani irin ?arfin da karasa ta karade ko'ina!

?arar da ta sanya Faruk taka nasa birkin motar sannan ba tare da jiran komai ba ya buWe kofar motar ya tafi da gudu zuwa wajen, sauran ?an sandan dake bayan motoci biyu suka diro da nasu saurin suka rufa masa baya!

***

*NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*


"Basu kira ba har yanzu?"

Hajiya Nafisa ta tambaya da idanunta da suke a zare tana kallon Wan ta Ashraf wanda ke rike da waya a hannunsa, a cikin falon da suke akwai Ahmad ma, yana zaune daga cikin kujerun falon yana hannayen sa duka biyu dafe akansa yayin da yake sauraren Ashraf Win dake ri?e da waya yana amsa kiran mutane daban-daban Win da suke fatan su isa ga abinda suke nema... Rukayya.

A yanzu bincike da kuma dukkan hasashensu ya kai ga abinda suke nema, an basu tabbaci na cewar Hoton da suka gani Rukkayya ce kuma a cikin gawarwakin da aka fito dasu daga wata mota dake nufar wani kauye a can kasar Niger.

Idon Ahmad ya koma kan mahaifiyarsu, Hajiya Nafisan dake ta zarya a cikin falon idanunta shabe-shabe da hawayen dake fitowa wani na bin wani akan fuskarta.

Ashraf ya girgiza kansa sannan yace.

"Bai kira ba Maamah, kiran da nayi masa kusan na biyar kenan ya ce suna hanya, bana don inyi ta kara kiransa..."

Hajiya Nafisa ta girgiza kanta.

"Ka kira shi Aahraf... Ka sake kiransa, ya san al'amari irin wannan ai, ya san ba zamu iya jira ba, dole ne hankali ya tashi...."

Ahmad dake zaune ya girgiza kansa.

"Maamah ki jira yanzu zasu isa kar muyi abinda..."

"Kar muyi abinda me? Kar muyi abinda zamu tashi hankalinsu? Saboda kai naka bai tashi ba? ?aruwarka tana can a halin da babu wanda ya sani amma kai kana zaune babu abinda ya shafe ka?"

"Babu abinda ya shafe ni? Babu ya shafe ni zaki ganni anan Maamah? Ni na tura ta Niger din ko kuma idan Allah ya ga damar Waukar ta zan iya wani abun da zai hana ne...?"

"Ahmad..."

Ashraf ya katse shi yana juyowa kansa. Sai kawai ya mike tsaye.

"Me nayi? Nayi laifi ko? Ni kullum mai laifi ne a gidan nan, Ru?ayya ce ta tafi yawon barbadancinta har Niger amma ni da nake zaune anan nine mai laifi?"

Ashraf ya girgiza kansa fuskar sa Wauke da tsananin Sacin rai? muryarsa a sama yace.

"You are crazy! Baka da hankali Ahmad me yasa kai a kullum kan ka kawai kake gani? Me yasa baka taba considering mutane a kowanne hali da ake ciki?..."

Sai kawai Ahmad Win ya mi?e, shima cikin daga murya yace.

"Saboda nima babu wanda yake considering dina a gidan nan....!"

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un!"

Hajiya Nafisa ta faWa tana komawa da baya ta zauna akan kujerar dake bayanta.

"Da wanne zan ji Ashraf?? Da wannan halin da muke ciki ko kuma da fadan da zaku fara? Inalillahi wainna ilaihir raji'un!..."

Ta rufe bakinta daidai lokacin da kiran waya ya shigo cikin wayar Ashraf din, hannunsa na rawa ya Wauka ya kara a kunnensa, Hajiya Nafisa ta taso da sauri ta tsaya a gabansa yayin da Ahmad ya koma ya zauna yana kallon fuskar Ashraf din.

"Eh, eh ita ce.."

Ya fada yana gyada kansa, yayin da hannayen Hajiya Nafisa ke rawa akan fuskarta tana sauraren sa. Ashraf ya sake cewa.

"Eh ita ce Yallabai..."

Sai kuma ya gyada kansa yace.

"Alhmdlilah... Okay toh... Mun gode sir, mun gode mun gode...."

"Me ya faru? An ganta? Sun ganta? Tana da rai Ashraf?"

Tun kafin ya sauke wayar Hajiya Nafisa ke jero waWannan tambayoyin, kuma ga mamakin kowannensu sai kawai ya gyaWa kansa sannan yace.

"Sun ganta, tana da rai Maamah, tana asibitin a kwance..."

"Alhmdlilah... Alhmdlilah."

Dukkaninsu su biyun suka faWa a lokaci guda yayin da Ashraf din ya shiga girgiza musu kansa amma babu wanda ya lura dashi a cikinsu, sai kawai ya kira sunan mahaifiyar tasa kai tsaye.

"Maamah..."

Ta juyo ta kalle shi da sauri, idanunta a zare dauke da wani sabon fatan da a yanzu ya sani cewa maganarsa zata rusa shi ne har garinsa.

"Maamah sun ce ta samu paralysis (mutuwar Sarin jiki)!"

***

*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
*Gidan Hajiya Salamatu.*

"Wallahi Sister Maryam muna gidan har yanzu, abu ne kamar wasa, shekaru kusan talatin da wani abu sai yau Allah ya baiyana shi.. "

Cewar wata dattijuwa da take ?aruwar Hajiya Salamatu wadda suke kira da Aunty Bilki. Zuwansu gidan kenan a safiyar yau da suka tashi da labari mai daWi mai kuma cike da dimbin al'ajabi na cewar ?aruwar tasu ta samu danta bayan tsawon wasu shekaru, Wan da duniya da ma kowa a cikinsu ya riga ya bada tabbacin cewa ya koma ga mahaliccinsa tun a ranar da yazo duniya.

Sai a gashi a cikin ?an?anin lokaci kawai, a cikin wasu kwanaki da hannu zai lissafa su labarin ya canja, Wan da yake natan na asali ya baiyana a raye tare da kammanin da ko bashi da hujjar labarin da ya bayar wanda yayi daidai da na Hajiya Salamatun, kowa a cikinsu zai shaida ya kuma gasgata cewa shi Win da gaske Wanta ne na asali, don kamarsa Waya da mahaifinsa sak! Mijin da ta fara aura Ibrahim Shanawa, komai nasu iri Waya ne ta yadda babu wanda ya isa ya musa hakan.

Su kusan biyar ne ?an uwanta suka zo a yanzu, harda guda biyu da suke a Abuja, tun a daren jiya da ta gaya masu suka yi booking jirgi a safiyar suka taho... Kuma a cikinsu babu wanda ya ?aryata hakan saboda sun zo ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ne sun iske tarin hijjojin da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login