Showing 87001 words to 90000 words out of 132946 words

Chapter 30 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1124

tace ba zai Wauki lokaci ba komai zai fara, don haka zata saka ido ta gani, idan har komai ya tafi daidai, alkawarinta ba zai canja daga yadda ta faWa a farko ba."

Amma dake zaune a tsakar falonta tayi murmushi mai fadi kafin tace.

"Kar ki damu Amina, ki kwantar da hankalinki komai ya riga ya fara ai... Dama ita kadai muke jira!"


***

_Meye yake dab da taka kasar Nigeria?_

_Me kuke tunani zai zama jam'in dukkan waddanan gibin?_

_Kuna tunanin abinda Amma ke shiryawa yana da alaka da tonuwar asirin Kilishi?_

_Muna dab da faWawa cikin ramin dai...!_

_Kar ku manta da Jawad fa, tasa gudunmawar na nan tafe soon Insha Allah._

_Ku gaya min ?iyamar Kilishi ta tsaya!_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
#FararWuta.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*19*

_The fight between your heart and your mind is never easy..._

~~~~~~

"Mami..."

Sabon sunan da Hamida ta raWawa Amina ya ratso ta cikin hayaniyar kitchen din. Shigowarta kenan bangaren bayan ta gama aikin nata tuwon ta kuma gama waya da Amma, wayar da ta sanya ta farin ciki a lokaci guda, ya kore dukkan fargaba da kuma damuwar da Kilishi ta saka a ranta bayan ta bata maganin nan.

Zuciyarta ta wanku tas da tsarin da Amma ta fitar musu, tsarin da babu shakka duk wayo da kuma hange irin na Kilishi bai isa ya tsallake dabarar tasu ba, don kamar yadda Amman ta fada ne...

_"Na gaya miki takunta zamu bi Amina, da kifi ake kama kifi,kamun da baya ganewa har sai ya ji shi a cikin komar masunci... Idan kika bi irin takun da take bi, to kin riga ki gama tsallake tunaninta har abada._

_Tun kwanaki na gaya miki cewa na fara shiri akan hakan, na gaya miki yarinyar zata makance a idanun Kilishi ne kawai amma ba'a zahiri ba. Don haka tsarin da nayi shine akwai Wan gidan Baffa Saliyo abokin mmahaifinku na unguwar Sharada, kin gane shi?"_

Kuma a lokacin kwakwalarta bata sha wahala ba wajen hasko mata fuskar saurayin da Amman ke fadi ba, shine Babba a gidan abokin mahaifin nasu kuna kwanan nan ya kammala karatunsa na likita har ma ya samu aiki a asibitin malam Aminu Kano. Don haka ta gyada kanta da sauri tana gaya mata cewa ta gane shi.

_"Shi nasa aka kira min har cikin gidan nan Amina, sati guda da ya wuce, kuma yazo ya same ni da daddare har cikin falon gidan nan... Nayi masa bayanin komai ta sigar da ba zai fahimci cewa matsalar daga ina take ba amma kuma ya fahimci dukkan kudirina, kuma ya gaya min zai taimaka, don haka yanzu duk bayan kwana biyu zai dinga rubuto takardar magunguna daga adibiti na yara da suke shaida ciwon ido, a hankali, a hankali ana yin gaba yana kara rubuta cewa ciwon yana habba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ka._

_Maryam zata dinga kawo miki takardun duk bayan wani lokaci kina kai mata da cewar yarinyar ta fara ciwon ido... Rayuwar mace dabara ce Amina kuma Kilishi shaida kawai take nema a yanzu ba zahiri ba Amina, Kilishi tana wani matakin da ba zata saka ido akan al'amura ba yanzu, saboda ko ba'a faWa ba kin san binciken da suke yi akanta yayi nisa. Don haka a yanzu kamar tana kokarin tattare abubuwa ne don tayi ta gama karasa manufarta kawai._

_Bayan haka kuma, idan kin lura al'adar Kikishi cewar bata da bin diddigi, da ta fahimci abinda take so ya faru shikenan kawai zata gama da wannan babin, na fahimci haka tun daga ranar da ta yi miki alkawarin tafiyar su Aminu India a lokacin da aka kira ta da bayanin Ma'aruf yana asibiti kafin ma ta ganshi.Don haka ki kwantar da hankalinki Amina, komai zai tafi daidai insha Allah."_

Kuma da wadannan kalaman hankalin nata ya kwanta, don kamar yadda Amman tace ne a yanzu hidimar dake gaban kilishi daban ce ita kanta ta lura, don ko a yanzu ma bata gidan tun dazu ta fita ba tare da kowa ya san ina ta tafi ba, wani abu da ya bawa kowa mamaki kenan, don da wuya ne idan ana hidima irin wannan ta sanya kafarta ta fita, hatta ?anuwan Hajiya Maimuna da suka zo kowa sai da yayi ta tambayarta ana sa ran dawowarta da wuri amma har yanzu.

Wani abu da a wajen Amina yayi mata daWi sosai, don a kullum tana son irin wannan tazarar ta dinga faruwa tsakanin Kilishi da kuma farin cikin ahalin gidan.

Sai da ta kammala komai a bangarenta sannan ta taho cikin gidan, inda anan ta tarar har wasu daga cikin ?anuwan Hajiya Maimuna sun iso ana ta hidimar tarar Abdurrahim Win da Ishaq yayi waya yace ya sauka gasu nan a hanya.

Basu yi waya da Ma'aruf ba tun dazu, bai kira ta ba kuma itama bata kara kira ba, don ta fahimci kwana biyu aiki yana yawan yi masa yawa, shi yasa bata so ta zama sanadin katse shi a komai, kamar yadda Amma ta gaya mata ne kamata yayi ta zama nutsuwar da zai dinga han?oro a duk lokacin da hankalinsa ke juyowa zuwa gida.

Don haka ko a yanzu ma da aka ce sun taho, bata kira shi ba ko kadan, aiki suke tayi na kokarin haWa miyar taushen da aka manta da ita kwata-kwata, anyi masar tun rana amma sauran sha'anin su Samirah ya mantar dasu miyar sai a yanzu sannan aka hadu gabadaya ake kokarin gamawa kafin karasowar tasu.

"Mami...."

Hamida ta sake kira sanda ta karaso gabanta da gudu. Amina ta juyo daga yankan alaiyahun da suke yi ita Munaya.

"Su Aunty Sahla sun ce dan Allah in tambayeki su canja min kaya?"

Ta fada muryarta na fitowa kamar haki alamun ta dade tana neman nata cikin mutanen gidan.

"Kaya Hamida? A ina suka sami wasu kayan?"

"Su suka Winka a School Winsu...!"

Ta faWa da sauri tana katse ta. Kuma kafin tayi magana Munaya tace.

"Wannan shirmen nasu zasu saka miki Hamida... wannan karkatacciyar rigar da suka dinka?"

Tana fadin haka Amina ta gane kayan da take nufi, don itama har wajenta suka shigo suka nuna mata da murnarsu, rigar bata yi kyau ba sam!

"Wallahi Aunty Munaya tana da kyau... Pink ce fa!"

"Hamida ki bari idan Dadynki yazo sai ki tambaye shi kinji? Zai fi so ki fara tambayarsa tukunna.."

Amina tayi mata wayo ta tsaya kanar bata yarda ba sai kuma ta gyada kanta sannan ta juya da gudu.

"Har yanzu ina mamaki da akace wai yarinyar nan tana da cutar rashin son mutane da yawa, gashi nan yanzu tagane kowa a gidan nan kuma ta saki jikinta."

Munaya ta fada tana kallo ta ta cikin ymgayaniyar sauran mutanen dake shige da fice a kitchen din du Mama Rabi, sai kawai Amina tayi murmushi tace.

"Bata son ta rabu da ita ne kawai, kin san Wa da uwa."

Munaya ta taSe dan karamin bakinta tana gyara zaman glass dinta tace.

"Ba wani kula fa take yi da ita ba, ba zuwa muke yi ba amma mun sani, atbfirst ma ba'a hannun ?ar aiki Yayan ya samo ta ba? Sai gashi kuma sun dawo da ita da kansu, sannan ko ita yarinyar ba kya ji tana nemansu."

"Haka ne." Amina ta fada a hankali idanunta na hasko mata hoton wannan layar, da kuma fuskar matar da aka aiko takanas har cikin gidanta, har yanzu basu sake cewa komai ba, basu sake yin wani abu ba, bata sani ba ko ha?ura suka yi ko kuma suna shirya wani sabon shirin ne, zata so idan har ma basu ha?uran ba su cigaba da Waga musu ?afa har zuwa lokacin da abubuwa dake gabanta a yanzu zasu yi sauki, don haka gudun kar Munaya ta cigaba da maganar yasa ta tsokane ta da cewar.

"Ina fata dai kin ajiyewa Yaya Ishaq nasa special abincin?"

Kuma murmushin da Munayan tayi yasa ba shiri ta taya ta itama.

Da misalin ?arfe tara daidai na daren, motoci guda biyu na Ishaq da kuma Ma'aruf suka shigo gidan, a lokacin sun kammala komai, jiran ba?on kawai ake yi,bakon da sai a yau Amina ta fahimci irin kewarsa da al'ummar gidan suka dade suna yi bakidaya,a da yadda kowa ke harkokinsa ba'a zancensa sai jefi-jefi sai taga kamar basu saba dashi bane ko makamancin hakan, amma yanzu ko zuwan wasu daga cikin yanuwan Hajiya Maimuna kaWai ya tabbatar mata da matsayinsa a zuciyarsu.

Tana kitchen ita da wasu ?a?an Yar Hajiya Maimuna sanda suka shigo gabadayansu bayan sun baro bangaren Baffa inda nan suka fara danganawa dashi. Taji yadda falon Hajiya Maimuna ya ruWe da hayaniyar murna kala-kala wadda bata ko gane me ake cewa.

Hannunta ri?e da farantin da aka jera kofunan kemo suka fito tare da sauran, kuma a lokaci guda idanunta suka lalubo Abdurrahim din, fari ne, fari ne sosai duk da bai kai Jamal din da take ganin hotonsa a wajen Ma'aruf ba, sannan yana kama da Ma'aruf din sosai, yanayin idanunsu da sumar gashin kansa da shima ya tara, sai murmushi yake yi zaune a kusa da Hajiya Maimuna dake kan kujera yayin da kowa ya yanyame shi da sakon gaisuwarsa.

Ma'aruf na tsaye daga bayansu ri?e da Hamida wadda ta makalkale shi, idonta ya kai kansu sanda Hamidan ke lalubo kunnesa tana rada masa wani abu da ta san ba zai wuce zancen rigar ba, a idanunsa kaWai ta fuskanci tarin gajiyar da ba sai ya furta mata ba.

Sai kawai tayi masa murmushi ta karaso cikin falon suka gaisa da Abdurrahim din, bata ji muryarsa sosai ba amma taji kamar ya amsa da 'Lafiya' a hankali, kuma da yake bai santa ba shikenan abinda tace sannan ta juya kitchen din da niyyar dauko wayarta, a lokacin Hamida ta taho da gudu zuwa gabanta.

"Mami, Daddy yace inje a saka min kayan kuma yace dan Allah shima ki zo ki canja masa kayans..."

Hannunta tasa da sauri ta rufe bakinta don da ?arfi take maganar sannan ta juyo tana kallon Ma'aruf din da ya juya yana yiwa Ishaq da ya shigo a lokacin magana, ta yaya zai gayawa yarinya wannan maganar?

Hamida bata jira taji me zata ce ba ma ta fita daga hannayenta ta tafi wajensu Sahlan da sa?onta tana murna, a lokacin ne kuma taji muryarsa yana tambayar Surayya da tazo wucewa.

"Ina Mami?"

Tambayar ta fito daidai lokacin da wani al'amari ya faru daga can falon Baffa, inda yake zaune a gaban talabijin Win dake ci a gabansa yana kallon labaran NTA na ?arfe taran dare, a hannunsa guda robar robb ce da yake shafawa a ?afarsa ta hagu.

Zuciyarsa a cike take da tsananin murnar dawowar Abdurrahim, a kowanne dare da kuma wayewar garin Allah fatansa baya wuce ganin iyalansa sun haWu waje guda, a kodayaushe yana daga cikin addu'arsa cewar kar Allah ya Wauki rayuwarsa ba tare da ya ga haduwar iyalansa waje guda ba, duk da cewar ya san akwai wani giSin da har abada ba zai taSa cikewa a zuciyarsa da ma ta sauran al'ummar gidan ba... Jamal.

Wayarsa tayi ?ara daga kan kujerar da yake jingine a bayansa, ya mi?a hannunsa ta gefe ya dauko ta, sabuwar lamba ce da b sant ba don haka ya Wauka yasa a speaker...

Muryar wani dattijo ta fito daga cikin wayar a lokaci guda.

"Barka da dare yallabai... Ina magana ne da Alhaji Muhammad Mansour Bakori?"

"Barkanmu dai, Eh Ni ne Mansour."

Ya faWa yana ajiye robar robb Win dake hannunsa... Kuma kalaman da suka biyo, kalamai ne da babu shiri suka tsayar da duk wani tunani a cikin kan Baffa.

"Ranka ya daWe suna na DPO Umar Nasir, matarka Hajiya Kilishi tana nan tare dani!"

***

*Washegari.*
*?arfe shida da rabi na safiya.*

Motar na tafiya ne a wani irin yanayi da Zainab ta ?asa gane gudu Jawad ke yi ko kuma akasin sa, idanunta na manne da titin dske gabansu yayin da take ji zuciyarta na bugawa a kirjinta da sautin da zata iya rantsewa cewa yana iya jinsa daga inda yake zaune.

Hannnusa ne guda akan sitiyarin motar ya danne shi da ?arfin dake baiyana a ido, yayin da ?afafunwansa ke ?ara take motar suna shillawa akan titin da bata san ina zai dangana dasu ba. ?arar sautin shigowar kira a wayarsa yafi ?irgen da zata iya tunawa, bai Wauka ba, bai kashe kiran ba ko ma wayar gabaWaya, yi kawai take tana sakewa kamar ?arar motar agaji,(ambulance).

Ta hadiye rawu a cikin ma?ogwaronta a hankali tana sake matse yatsunta a cikin hijabin dake jikinta, wannan dogon hijabin sabo da ya bata, shi ta saka tayi sallar asubahin yau, sallar da tana sallamewa Jawad ya shigo dakin, kuma bai jira komai ba yace ta taso ta biyo shi.

Bata san me yake nufi ba, bata san ina zasu ba don haka ta taso ta biyo shi Win zuwa cikin falon da komai yana nan kamar yadda yake a jiya, kayan abincin dake kan dining suna nan har a sannan babu wanda yabi ta kansu, bata ko buWa su ba tun a jiyan, daga su har ledar magungunan da yace mata taje tasha suna nan a wajensu.

Don babu yadda za'ayi ?afafunta su iya dauko ta daga inda ya bar ta a jiyan zuwa cikin falon, tasirin maganganun da ya gaya mata kafin ya fita su suka manne ?afafunta a inda ta tsaya kuma suke ta maimaitawa a cikin kanta, maimaitawar da duk zagayen da tunaninta ke yi ya dawo a waje guda yake tsayawa, waje gudan da har a yanzu da garin Allah ke kokarin wayewa abubuwan da ta gane a ciki basu da yawa, don bayan ma kankantar tasu, ita shaida cewa ko giyar wake aka taru aka sha a garin tunaninta baya hango kasancewarsa.

Aure ba ?aramin abu bane ta sani, ana yinsa kullum, cikin kowanne sati na duniya, amma duk da haka yana da wani irin girma da kuma darajar da ubangiji ya Soye a cikinsa, shi yasa har kullum yake kamar ba?o a zukatan al'umma, idan za'a gama yau a fara wani gobe, na goben zai zo ne da wani sabon farin ciki da kuma doki a zukatan masu yinsa.

Aure abu ne da rayuwar mutum ke tafiya gabadaya akai, rayuwar da zata mamaye farko har zuwa ?arshe na kwanakin ka a duniya, shi yasa har yanzu bata ga dalilin Jawad na cewar zai aure ta ba don bata ga wani abu da take dashi a duniyar nan da zai iya hada rayuwarsa da tata ba.

Bayan haka ma, ita bata jin cewar tana sonsa, zuciyarta ta riga ta gama tsorata da tarin abubuwa, tun daga rayuwar da ta baro har zuwa wadda take yi a yanzu, sannan shi kansa tsoronsa ya fara dasawa a ranta, tsoron da a yanzu bata san ta yaya zata iya juya shi ya koma wani abu daban ba....

_"Ko ke baki da zaSi yanzu Zainab, zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni..."_

Ta rufe idanunta a hankali tana tuna sanda suka iso wajen motar tasa yace mata ta shiga, a lokacin ne kafafunta suka tsaya waje guda cak! Ta tsaya daga daidai bayansa tana tambayar ina zasu tafi? Ina zai kaita a wannan safiyar ba tare da Hajiya Mardiyya ta sani ba ko kuma ta bata izini.

Abinda tayi dana sanin tambaya kenan tun daga kirgen wancan lokacin har zuwa yanzu, don yadda ya tsaya a gabanta ya rike hannayenta duka biyu da iya karfin da take tunani nasa ne, ya gaya mata cewar baya son? baya son sake jin muryarta kawai tayi dukkan abinda yace, da wani yanayi ne da zata rantse bata taSa gani a fuskar wani mahaluki ba, don sandan hannayenta duka biyu suna zafi da tasirin ri?on da yayi mata. Shi yasa bata ?ara cewa komai ba har a yanzu da suka yi nisa cikin tafiyar da bata san ina ne ?arshen ta ba.

Zuciyarta na faman bugawa ne cike da tsoron irin tarin laifin da yake kara mata a wajen Mahaifiyarsa, Hajiya Mardiyyan da tun a jiya ta bata umarnin haWo kayanta don ta maida ita garinsu, da kuma Deluwa matar da ta kawo ta gidan, don bayan rashin mutunci Dekuwa gar azaba tana yiwa duk yarinyar da ta kai gidan aiki ta gudu...

Tunaninta ya tsaya a lokacin da motar ta tsaya kusan a lokaci guda, kusan a lokacin gudun da tasirin hakan yasa tayoyinta gaba daya suka fitar da wata ?ara da ta cika kunnuwan su da suke ciki ma, kuma kafin Zainab ta sake wani tayi wani tunani ya Wauki wayarsa da har a lokacin ke ?ara ya jona da wata waya dake jikin motar.

"Jawad, Jawad... Jawad..."

Muryar Aunty Sadiya ta cika speakers Win dake cikin motar a take, daga bayanta hayaniya ce mai yawa ke tashi yayin da sautin kukan da babu shakka na Hajiya Mardiyya ne ke barazanar fin muryar tata karfi. A lokaci guda Zainab taji cikinta ya hautsine.

"Jawad kana ji na? Kana ina? Ina ka tafi?"

Tambayar ta shiga kunnen Jawad da sigar rainin hankali, ina ta tafi? Ina suke tunanin zai tafi bayan inda suka gaya masa?

A daren jiya har wajen ?arfe biyun dare ana case din da yake gani da jin sa tamjar a mafarki, bayan ya shaidawa Alhsji Bashir komai, shi da kansa ya karbi wayar hannunsa, ya kira ?ansandan da shi ya kira ya tsayar daau daga zuwa gidan. Sannan shi da kansa ya kira mijin Aunty Sadiya yace ya kawo ta gidan a lokacin, bayan haka, ya kira dukkan sauran ?anuwan Hajiya Mardiyyan da suke a garin yace suma yana bukatar ganinsu, kuma cikin abinda bai haura awanni biyu ba dukkaninsu su huWu suka hallara, mata biyu da yayyensu maza biyu.

Hajiya Mardiyya itace ta karshe a kiran Alhaji Bashir din, alokacin ta kira wayar Jawad dake rile a hannunsa fiye da kirgen mai kirga, don tana ta nemansa a cikin gidan, bangaren Alhaji Bashir Win ne kawai bata zo ba don watakila tana tunanin bata da kwarin gwiwar fuskantarsa a wannan lokacin, amma sai gashi kafafun nata sun kawo ta, kuma a lokacin da ta shigo tayi arba dasu, ?anuwanta har su hudu cikin wannan dare da kuma shi da Alhaji Bashir Win dake mata kallon da babu bukatar asarar kalmomi, sai gashi ta samu kwarin gwiwar ?arasowa har gaban nasu.

Kuma a jiyan yaji komai, yaji dukkan wani bayanin daga bakin ita da kuma Aunty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login