Showing 96001 words to 99000 words out of 132946 words

Chapter 33 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1147

yatsunta, sai kawai ji yayi tace.

"Dan Allah zaka kaini gida kafin mu tafi?"

Muryarta ta fito ne tana rawa, tana rawa sosai ta yadda da ?yar ya gane me take cewa, ku.a ba shiri a lokaci guda ya tsayar da motar, Allah yaso ba gudu yake? har a lokacin ba, ya juyo ya kalle ta har a lokacin kanta yana ?asa,

"Me kika ce?"

Ya tambaya da sauri yana kallonta.

"Gidanmu, a can hanyar yake babu nisa, dan Allah ina so in ga Naani."

Ta sake faWa wannan karon hannayenta na rawa fiye da Wazu. Kuma kalmar Naanin ta haska a kansa da wata ma'ana da ya taba sanin cewa ya rike a cikin kansa cewar haka take gayawa mahaifiyarta. Don haka ba shiri yace.

"Gidanku? Anan garin kike dama?"

Ta daga kanta.

"Nan ne garinmu, da muka zo nayi zaton gida Hajiya tace ka kawo ni, sai kuma naga ba haka bane... Wanda ya nuna maka gidan da kuka je sunansa Nura, shima na san shi, a gidan da mamana take aure yake."

Ba shiri hannunsa ya kai saman kansa yayin da bakinsa yake a buWe, kuma a lokaci guda ya tuno da ranar da ya fara tambayarta sunanta da kuma inda take...

_"Sunan garinmu Yakura, a kusa da Kaduna yake."_

Haka ta fada muryarta tana rawa, sai kawai ya gyada kansa yace.

"Zainab kin san shi? Amma ya akayi baki yi magana ba shima kuma baice komai ba?"

Ta kai hannu ta share kwallar da ta cika idonta a lokacin, sannan ta girgiza kai har a? lokacin bata kallonsa.

"Bai gane ni ba, bai sanni sosai ba, lokacin da na tafi ma baya garin ance ya tafi ci rani."

Sai kawai ya haWiye wani abu da bai san sunansa ba a makogwaronsa yana kallonta, yana kallon yadda take sunkuye da kan ta da kuma yadda take share hawayen fuskarta, bai san kukanta na meye ba amma ya fahimci tsoro take ji, tsoron tambayarsa take yi don taje ta ga mahaifiyarta, shi Win da ba kowa bane har yanzu a rayuwarta, wani abu da yake ji kamar ya fi tausayi girma shi ke gilmawa a zuciyarsa a lokacin haWe kuma da mamakin yadda abubuwa ke kasancewa bi da bi a rayuwarsa.

Ya murWe kan sitiyarin motar suka juya, kuma yana tambayarta da kwatance har zuwa ?ofar gidan da a yanzu yaje tsaye yana jiran fitowarta, yana jiran yayin da kwakwalwarsa ke cike da lissafi da kuma tarin tunanin abubuwan da bai san adadinsu ba.

A karo na ba adadi hannunsa ya sake danna wannan lambar da aka bashi, kuma ta shiga har zuwa bugu na ?arshe kafin ta katse kamar kodayaushe, tunda ya tsaya a wajen yake kira, zai iya ?irgawa kiran ya tafi kusan sau goma daga lokacin da ya fara zuwa yanzu, sai kawai hannunsa ya shiga bangaren sako ya rubuta abinda ya san ko waye zai karanta ba zai dauki neman da yake yi masa da wasa ba.

Kuma sai da ya tura sannan tunanin ko bai kwafi lambar daidai ba ya haska a ransa, sai kawai yasa hannu a aljihunsa ya zaro wannan takardar, ya kalli lambar jiki da kuma wadda yake kira yaga daidai ne sai kawai ya du?un?une ta yayi wulli da ita gefe, yayi wulli da ita daidai lokacin da ?afafun wani dattijo suka fito daga cikin gidan.

Sanye yake da riga da babba ?ar ciki wadanda suke daban-daban, fuskarsa a murtuke take babu alamun fara'a ko kaWan, kuma da kallo Waya da yayi masa ya fahimci wanene shi, Mijin mahaifiyarta, mijin mahaifiyarta wanda tace shine sanadin tahowarta aiki, naganganu da kuma hoton wannan ranar da ya fara tambayarta sunanta ya sake dawowa cikin kansa.

_"Waye ya kawo ki nan?"_

_"Abokin babana ne."_

_"Ina baban naki?"_

_A hankali tace._

_"Ya rasu."_

_"Ina babarki?"_

_Sai da ya lura ta hadiye wani abu sannan tace._

_"Tana nan, matarsa ce ita yanzu."_

_Kalaman suka daki kirjinsa da wani abu da bai san meye ba, amma dai ya san nazarinta yake yi, nazarin shekarunta da ya kasa ?iyasinsu._

_"Ita me yasa bata hana shi kawo ki ba?"_

_Sai ta sake dagowa ta kalle shi, idanunta na nuna wani abu da ya kasa tantancewa, idan ma tunani take cewa muryarsa ta fito da damuwa ne, zai goge mata hakan yanzun nan._

_"Bashi da kirki, Naani baza ta iya hana shi ba."_

Wadannan maganganun suka dawo cikin kansa a lokaci guda, a cikin sakannin da mutumin bai kai ga karasowa inda yake ba, don haka zuciyarsa ta Wauke shi ta ajiye shi a wani mazauni na daban daidai lokacin da mutumin ya ?araso har zuwa gabansa ya tsaya kuma kai tsaye tambayar bakinsa ta fito.

"Yawwa, nace kaine Jawad Win?"

Jin haka yasa shi gyara tsayuwarsa kadan sannan ya amsa, yana ?o?arin ture abinda ke cikin ransa.

"Eh ni ne, Barka da fitowa."

Sai ya gyaWa kansa ba tare da ya amsa ba sannan yace.

"Ni ne mahaifin wannan yarinyar Zainab da ka kawo..."

Ya faWa yana kallonsa don yaji me zai ce, amma baiyi maganar ba sai kawai ya cigaba da kallonsa, don haka shima ya cigaba.

"Ta gaya min tare kuke daga can gidan da take a Habujan... To an gode madallah zaka iya tafiya yanzu."

Kallonsa kawai Jawad yaje yi daga inda yake tsaye yana jin maganganun na shiga cikin kansa suna fita ta Waya gefen,kuma sai da ya kai karshe sannan ya girgiza kansa.

"Nima nagode Baba, amma a yadda na sani mahaifinta ya rasu, kuma ni ban kawo ta ne don ta zauna ba, hasalima wani abu daban ne yazo damu nan kafin in san cewa anan mahaifiyarta take."

Mutumin ya sake kallonsa a sheke sannan yace.

"To ni nake auren mahaifiyarta kuma shi din wanda ya haife ta abokina ne don haka ka gaya min ta yadda ban zama mahaifinta, sannan a wane hurumin zamu sake daukan yarinya yanzu mu baka? Tunda dai ta zo gida ba shikenan ba, dama ita Deluwa da ta kai ta ai ta gaya mana cewa uwargijiyar tata,ta gaji da halinta tace zata dawo da ita gida..."

Jawad ya sake girgiza kansa yace.

"Ba gajiya suka yi da ita ba, zasu dawo da ita ne kawai saboda ni, saboda sun fahimci cewar ina son in aure ta, kuma da gaske nake ba da wasa ba..."

Dariyar da mutumin yayi ita ta katse shi daga kasa ?arasawa, ya tsaya a lokaci guda yana kallonsa.

"Ai Zainaba tana da mijin aure tuntuni, itama ta san da wannan zancen, tun ubanta yana da rai muka hada su da Wan waje na Nura, baya zaman gari ne shi yasa itama muka tura ta don ta tara kuWin kayan aikinta kafin ta dawo...."

Nura, Nura. Nura.... Sunan ya Warsu a zuciyar Jawad tare da hoton saurayin da suka sauke daga farkon garin yanzu, wannan saurayin da yake sanye cikin wasu dukunannun kaya riga da wando yana washe baki a lokacin da ya mi?a masa dubu biyu, sai kawai ya girgiza kansa yana kallon mutumin, wannan wani abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, ba zai taSa faruwa ba koda kuwa bayan babu ransa... Zainab tasa ce, tasa ce har abada, me yasa kowa baya ganin tambarin hakan da shi yake gani a tare da ita?

Ya sake girgiza kansa ya a kallon mutumin kafin yace.

"Kayi hakuri Baba, amma bana tunanin a yanzu kana Waya daga cikin mutanen da zasu hana ni aurenta, saboda..."

"Saboda me? Nace saboda me? Ita bata gaya maka da al?awari akanta bane tuntuni? To bari in gaya mska kaf dangin uwarta babu wanda ya damu dasu da nace zan auri uwar tata ma gode min suka yi don babu wanda yake bukatar nauyinsu sai ni da nace na ji na gani.

Dangin ubanta kuwa babu inda zaka same su, ko wuka ka dora akan uw*r tata ba zata iya gaya maka ba, daga ci rani yazo arewa bai koma ba... don haka bari in gaya maka babu wanda yafi ni iko da Zainaba a yanzu a duniyar nan don haka ka kama hanya ka bar min kofar gidana, ta gode da alherin da kuka yi mata acan da kuma wanda kayi niyya.

Yarinya ta dawo gida ba fitowa zata yi ba, kai bari in ?ar?are maka ma ita da sake fitowa daga gidan nan sai idan zata tafi gidan ?ana, Win mahaifiyar tata ma da take ta?ama da ita, ta mutu yau kwanaki takwas kenan!"

"Ta mutu yau kwanaki takwas kenan!*...

WaWannan kalaman sune ?arshen abinda Jawad yaji kafin fuskar Zainab da kuma tunanin halin da take ciki a yanzu ya cika idanunsa bakiWaya!


*****

"Aunty... Aunty... Aunty."

Amira Wiyar Yayar Hajiya Salamatu wadda ke yawan ziyartar ta idan tana gari ta faWa tsaye daga bakin kofar dakin baccinta. Tana sanye ne da wata matsatstsiyar riga fitted gown data bi fukkan lunguna da kuma tudun jikinta yayin da ta sangala Wan karamin mayafinta daga gefe Waya na kafadar, daya hannunta navrike da jakarta da take ?ar mitsitsita kamar ita.

Hajiya Salamatu ta yaye bargon da ta lulluSe jikinta dashi, ta Wago kaWan tana kallonta ta gefe.

"Na tafi." Cewar Amiran.

"Yau ma da karatun ne?"? Ta tambaya muryarta na fitowa a disashe.

"Eh Aunty, 2-4 ne lectures din, za'ayi na 4-6 ma amma ba zan tsaya ba."

Sai ta gyaWa kanta.

"Daga can zaki wuce gida?"

Ta gyada kanta.

"Eh, amma idan kina gari zuwa jibi zan dawo."

Sai ta mike zaune a hankali kafin tace.

"Ina nan, bana jin daWin jikina, bana tunanin zanyi tafiya kwanan nan..."

Ta Wan tsaya kadan tana kallonta kaWan.

"Momi me ya same ki wai? Sadiya tace jiya ko abinci baki ci ba..."

"Na sha fruits, bana jin daWin jikina ne kawai Amira, kije sai kin dawo."

Kuma daga hakan Amiran ta san cewa babu wani bayani da zata sake yi mata don haka sai kawai ta tabe bakinta kaWan cikin siririyar muryarta tace.

"Bye-bye."

Sannnan ta juya tana jan hannun kofar da siraran hannunta da kusan dukkaninsa yake a waje. Hajiya Salamatu ta sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ta dafw kanta da duka hannayenta biyu.

Bata jin dadi, abinda take fadawa kowa kenan tun a kwanakin da suka wuce,haka take gayawa kowa, daga wadanda suka kira ta don cinikayyar kaya har ma da wasu daga cikin ?an uwanta.

Kuma ba karya tayi ba, da gaske bata jin dadin, bata ji dadi tun daga wannan ranar da Awwalu ya furta mata maganar da ta darsa wani irin fata a zuciyarta, wani fata da ya zabge tarin shekarunta na duniya, ya mayar da ita zuwa wani lokaci na can baya, lokacin da take Wauke da cikin Wanta, lokacin da take jin abinda kowacce uwa ke ji a lokacin da? abinda ke cikinta ya kusa karasowa duniya, wannan han?oro da kuma Wokin, zata rantse irinsa take ji tun daga ranar da Awwalu ya bata sabon fatan da bata taSa lissafawa dashi a rayuwarta ba.

Ta mi?e a hankali bayan ta yaye bargon dake jikinta, wayarta da ta ajiye akan mudubi ta jawo tana kunna ta, 10 missed calls daga wata sabuwar lamba ya nuna tar akai, sai kawai ta ajiye ta sannan ta nufi toilet, minti kusan ashirin a ciki tayi wanka hade da wanke bakinta sannan ta fito.

Bayan ta shirya ta ?walawa Sadiya kiran ta kawo mata abinda zata karya sannan ta koma kan wayar tata ta Wauko ta, ba tare da tunanin komai ba hannun ta ya danna wannan lambar da ta tarar da kiran nata...

Ta shiga har sau biyu ta tsinke ba'a dauka ba, don haka bata sake kira ba, sai dai kafin ta kai ga ajiye wayar wani kiran ya shigo, lambar Salma ce ?ar gidan Kilishi, mamaki ya Wan kamata kafin ta Wauka, ta kara ta a kunnenta haWe da sallama.

"Salma kuna lafiya?" Bakinta ya furta hakan kai tsaye.

"Aunty Mami tana asibiti, bata cikin hayyacinta tun jiya.!"

Sa?on ya fito tare da bugawar zuciyarta a lokaci guda, ba shiri ta karonto salati tun daga farko har karshe a bakinta.

"Gani nan Salma, gani nan zan zo gidan yanzu."

Ta faWi hakan tana jin sauran hayaninyar dake tashi a cikin gidan kafin Salma ta kashe wayar,cgirman sakon na lulluSe zuciyarta, har yanzu Kilishi aminiyarta ce, bata samu wata hujja da zata yi watsi da ita ba har yanzu, Awwalu baiyi nasara ba... Tana son ta ?aryata shi duk da cewar zuciyarta tafi son ta bashi gaskiyar, amma har yanzu ba komai, bata da wani abubda zai nuna mata gaskiya ko akasinta...

Ta sauke tata wayar daga kunnenta daidai lokacin da idonta ya kai kan wani sakon da bata lura dashi ba sai a yanzu, sa?on text message ne, daga wannan lambar... lambar da ta kira a yanzu ba'a dauka ba. Idonta ya sauka akan harafan sa?on, harafan da suka canza rayuwarta da na duniyarta a lokaci guda!

_Assalamu alaikum, an bani wannan lambar ne da fatan zan samu bayanin wata mata mai suna Hanne, iyaye na nake nema a wajenta, please idan sa?on nan ya shigo contact me._

***

?arar iskar dake kadawa ta shiga idanun Awwalu a lokaci guda da mutumin dake tsaye akansa ya kwance ?ullin da aka rufe fuskarsa dashi.

Ya rufe idanunsa saboda tasirin iskar da kuma na ?asar dake tashi a wajen yayin da mutumin ya sunkuya yana kokarin kwance wayar da aka ?ulle hannayensa da ita ta baya, jijiyoyinsa suka saki bayan an kwance hannun ya shiga mutsikka su duka a lokaci guda, sannan ya murza idanunsa kagin ya buWe su a gaban motar dake fake a gabansa.

Ya kalli kowanne gefe a inda suke, cikin daji ne mai fili gaba da baya, bishiyun da yake iya hange tsilla-tsilla ne.

Ya juyo da kallonsa zuwa cikin motar dake gabansa ?irar Odessy sabuwa, idonsa ya sauka akan ?antaron dake zaune a kujerar tsakiya wadda aka zuge zuwa baya, gajeren wandon da yake sanye dashi tun jiya shine a jikinsa har yanzu, sai kuma ba?ar T-shirt.

Yasa hannu ya zare gilashin fuskarsa sannan ya kalle shi.

"Ni ba Wan i*ka bane Awwalu, ba zan zauna tare da kai ba alhali na san ?an sanda suna nemanka ba, ina da ?ura a lamurana, idan na bari mutanen nan suka risko ni ba zan ji dadi, don haka ga ka nan na sake ka... Idan kun gama daidaitawa dasu, idan har baka mutu ba zan dawo gare ka don haka ka tanadar min kuWina kafin nan!"

Yana faWin haka yayi wani guntun murmushi sannan yaronsa ya rufe kofar motar ya zagaya zuwa gaba ya shige, cikin abinda yake kasa da minti guda motar ta tashi... Suka bar wajen suna tayar da ?urar da ta bade fuskar Awwalu baki Waya.

Sai dai wannan ba shine abinda ya dame shi ba, ba shine tunaninsa ba... tunaninsa Waya ne, he's free at last! Don haka ta ina zai fara??

***

_Ta ina kuke tunanin kowa a wannan babin zai fara?_

_Ta ina Kilishi zata fara?_

_Ta ina Jawad zai fara?_

_Ta ina Hajiya Salamatu zata fara?_

_Sannan ta ina Awwalu zai fara?_=??

_Wai ina Rukayya ne??_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*??AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*21*

_Sin makes its own hell, and goodness its own heaven.-Mary Baker Eddy_

~~~~~~

?arar tashin jirgin ta ragu a cikin kunnen Jawad, yana jin yadda tafiyar jirgin ke ?o?arin daidaita a sararin samaniya, yana jin kamar kafafunsa na bin gudun jirgin ne zuwa garin da suke dosa, yana jin yadda tasirin tazararsa da Kaduna ke yagewa a jikinshi, zaren na yin tsawon da bai san ta yaya zai kwatanta shi da wani sunan ba face cewar yana barin Zainab ne a baya, yana barinta a cikin halin da bai sani, halin da bai ko iya ganin fuskarta ba balle ya iya kintata halin da take ciki.

Sai kawai ya koma da baya ya rufe idanunsa, yayin da a hankali bi da bi abinda ya faru awannin da suka wuce tsakaninsa da Nura ya shiga dawowa cikin kansa.

*

"Karya yake..."

Abinda Nura ya fada kenan?yana kallonsa a lokacin da yake tsaye a gabansa. Shi din da ya dawo ya sake nemansa lokaci kadan bayan rabuwarsu, don a tunaninsa tun bayan lokacin da suka sauke shi sun dade da barin garin, sai gashi cikin abinda yake kasa da awa guda kiransa ya sake shigowa wayarsa da tambayar yana ina? Kuma bai bata lokaci ba ya shaida masa inda taken duk da mamakin da ya kama shi, wajen da cikin abinda yake kasa da minti goma yazo ya same shi.

Tun kafin ya tsaya ya hango motar don haka ya taho ya iske shi a daidai jikinta bayan ya fito.

A wannan lokacin Nura zai rantse da Allah duk da ya dade da sanin halin mahaifinsa ba karamin mamaki ne ya sake lulluSe zuciyarsa ba lokacin da Jawad din ya shaida masa abinda ke faruwa.

Farko, yayi mamaki sosai da ya kasance yarinyar ta zama Zainab Win da ya sani cewar a kwanakin nan an rasa zaman lafiyar gidansu saboda ita, ya san ya kalle ta a lokacin da ya fara haduwa dasu amma baiyi mata kallon da zai gane wacece ita ba don a tunaninsa matarsa ce, matar aure ce, matar da babu dalilin da zai sa shi kare mata kallo, don duk buWewar idanunsa duk irin tarin zunuban da yatsunsa zasu lissafa ya aikata a rayuwarsa babu harkar mata a cikinsu, a kodayaushe a kowanne hali yana daraja mata, yana basu ?ima da kuma darajar da ya san Allah ya halitta su da ita, don haka mace ko wace iri ce ba saka ta a ransa.

Mamakinsa na biyu akan mahaifinsa ne, mamakin yadda kai tsaye ya haWa ?arya irin wannan don kawai ya kore alkhairin da ya san cewa ba zai shafe shi ba... Don halin da yake ciki bashi da alaka da zuwan Jawad ko rashinsa kwata-kwata, kawai yayi hakan ne don son zuciya da kuma ?o?arin kuntatawa yarinyar da ko maraicinta ba zai kalla ba don ya sassautawa rayuwarta.

Satin sa biyu da dawowa garin lokacin da mahaifiyarta ta rasu... Ya dawo ya tarar bata da lafiya kuma zai rantse kafin mutuwar tata akwai ranar da kunnensa yaji?tana ro?on mahaifin nasa akan ya dawo mata da ?arta don tayi jinyarta, wanda sai a sannan shi ya tuna cewa ma tana da ?a guda daya da tsohon mijinta, kuma a lokacin ne ya fahimci inda yarinyar take don da kunnensa yaji mahaifin nasa na gaya mata cewa idan yarinyar ta dawo bai san kuma da wanne kudi za'a dinga samu ana siyo mata magunguna ba don shi bashi da shi.

Rigimar da ake ciki kuma a gidan ta fara ne tun bayan rasuwar mahaifiyar tata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login