Showing 81001 words to 84000 words out of 132946 words

Chapter 28 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1151

nasa ya bar garin Kano zuwa wajen da ya tabbata Kilishi ba zata taba riskarsa ba.

Kuma wannan ba shine babbar matsalarsa ba, ya san yana da ilimi da kuma takardun da zai iya neman aiki a koina, kuma ya san yana da yan kuWaWen da zai iya gina sabuwar rayuwar da zai fara a ko'ina, amma wannan ba shine burinsa ba, ba shine fatansa ba... Bashi da wani jin daWin da zai wuce ya ga faWuwar Kilishi, ya ga tarwatsewar ta tare da dukkan mafarkanta, yana so ko sau Waya ne Allah ya bashi damar da zai zama sanadin da Kilishi zata WanWani ko da rabi ne na irin ba?in cikin da ta shafe rayuwarta tana jefa al'umma a ciki.

Bayan sun shiga kwanar, motar ta tsaya a daidai gida mai bunun da akayi musu kwatance, kuma daga Hajiya Salamatun suka fito suna barin direban a ciki, kafafun Awwalu suka ?arasa da sassarfa ya ?arasa wajen wasu samari dake zaune a kofar gidan ya shiga yi musu bayanin abinda suka zo nema.

Akan idon Hajiya Salamatu wani saurayi ya mi?e ya shiga cikin gidan bayan yayi wa Awwalun bayanin cewa zaiyi masa iso da matar da suke nema, tana ganin yadda Awwalun ke juyowa yana kallonta daga inda yake tsaye, sai kawai ta juyar da kanta gefe guda ba tare da tace dashi komai ba, sharadi ne sun rifa sun yi sho tun kafin su taho.

Zata yafe masa,ba zata ce komai ba, ba zata ce komai ba,ba zata tona shi a gurin Kilishi ba, zata barshi yaji da neman hanyar tsira da rayuwarsa,komai zaiwuce kamar bai faru ba, niyyar taimakonta da yayi zata kore duk wani sharri da da zata iya shirya masa, amma idan har akasin hakan ce ta faru, komai ya tabbata zuwa gaskiya... to tabbas zata nunawa Kilishi wata sabuwar siffar cin amanar da a tsawon rayuwarta kaf! bata taba saninta ba.

Cikin abinda yake kasa da minti biyar, wannan saurayin ya fito yana faWin ance su shiga ciki.?Awwalu ya juyo ya sake kallonta alamun ta taho kuma bata ce komai ba har a lokacin ta gyada masa kai kawai.

Suka nufi ciki inda bayan sun wuce soron bunun ?atuwar haraba ce irin ta gidajen ?auye, akwai tarkace mai yawa wanda ya haWa da tarin tirame da kuma wasu abubuwan da baza su lissafu ba, ginin ?asa ne a ciki na Wakuna kala-kala kowanne na fuskantar junansu yayin da wasu suke daga can gefe, mata guda hudu suka tarar a tsakar gidan, uku da hijabi a jikinsu da alamun shigowarsu ce ta sa suka sanya sai kuma wata tsohuwa daje surfe daga? can gefe, dukkaninsu suka amsa sallamar su.

Wannan saurayin da ya shige gaba shi ya jagorance su har wani daki dake can karshe, kuma tun kafin su shiga suke jin muryar dake ciki na faWin.

"Maraba, maraba... Sannun ku."

Hajiya Salamatu ce ta fara shiga ciki kafin Awwalun ya biyo bayanta, Wakin bashi da girma sosai, akwai gado da kuma wasu kayan tarkace na kwanuka daga gefe, sai daga gaban gadon kuma aka shimfiWa wata sabuwar tabarma, matar tana daga gefe sanye da hijabi itama sai washe baki take yi tamkar ta sansu.

"Barkan ku dai, maraba..."

Ta sake faWa bayan sun zauna, Awwalu bai shigo ciki ba don ko takalminsa bai cire ba, tsugunnawa yayi kawai daga ?ofar Wakin yana amsawa kamar yadda Hajiya Salamatu ke yi.

"Ai Yakubu da ya shigo ya gaya min abinda ke tafe daku, yace bayanin Inna Hanne kuka zo nema ko?"

Awwalun yayi saurin gyaWa kansa da sauri.

"Tabbas, indai itace Hanne, to ita Win muka zo nema, wani Malam Tanimu ne ya kwatanta mana nan gidan yace ke ?arta ce zamu sami bayanin inda take a wajenki."

Matar da har a lokacin basu san sunanta ba ta gyada kanta sannan tace.

"Tabbas, ai da yake ta jima da barin ?auyen nan, tayi wani aure ne a can Hayin Shehu, wani kauye dake gabas da nan, hi isa?mutane da yawa ta Sace musu."

Hajiya Salamatu ta gyaWa kanta kafin tayi magana, maganar???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? da ta zarce ga abinda ya kawo su kai tsaye don har yanzu ita bata ga dalilin shigowar su gabaWaya da kuma tarbar da matar ke yi musu ba.

"Shi yaron yayi miki bayanin abinda ya kawo mu?"

Sai kuwa ta gyada kanta a lokaci guda da amon muryarta ya canja.

"E, yace nemanta kuka zo yi..."

"?auyen Hayin shehun kawai zaki kwatanta mana da kuma gidan wa zamu nema idan har mun je."

Awwalu ya faWa yana katse abinda take shirin faWa. Sai ta girgiza kanta a hankali idanunta na kallonsa, sannan ta faWi kalaman da yake gudu, kalaman da yake tserewa, kuma kalamai na ?arshe da zai iya tunanin ba da ransa akai idan har zai iya tare su daga fitowa daga amon kowanne mutum a duniyar nan.

Kanta ne yayi sama ya koma ?asa alamun gyadawa sannan sautin muryar tata ya fito fili.

"Haka ne, sai dai Inna Hanne ta riga ta rasu shekaru shida da suka wuce!"

***

?arfe shida na yamma, Awwalu ya buWe kofar falon gidansa, kuma bai jira komai ba ya shigo har ciki ba tare da ya ko cire takalman kafafunsa ba.

Ya wuce falon ya tafi har cikin Wakin kwanansa, inda ansn ma ma bai bata lokaci ba hannunsa ya janyo wani akwatinsa da yake yawan tafiye-tafiye dashi, ya shiga ya baWe drawer Wakin a gurguje yana kwaso gogaggun kayansa dake nibke a ciki yana jefa su cikin akwatin, kuma sai da ya tabbata ya kwashi fiye da rabi sannan ya rufe akwatin da ?yar ya sake jawo wata jaka irin ta matafiya daga ?asan wardrobe din.

Ya buWe zip Win cikinta ya tabbatar da tarin cd's Winsa dake ciki suna nan sannan ya wawuro wata computer dake ajiye kan bedside Win gadon ya cusa ta a ciki itama ya shiga ?o?arin rufe zip Win.

Wayardmsa da ya cillar akan gadon dakin ta shiga kara tana nuna wata sabuwar lamba, da sauri ya dauko ta ya kara a kunnensa.

"Eh nine, ni ne wanda ya kira ka yanzun nan... Dan Allah ka taimaka in samu ticket din nan... Eh, na Lagos... To shikenan ina son na Lokojan... Nagode ka samar min shi Win kawai, gani nan yanzu zan karaso."


Ta fadi dukkan wannan bayanin, zuciyarsa na rawa tare da amon muryarsa, burinsa da ma fatansa ya ta'allaka ne a tanzu kawai kan barin garin nan, babu iya kokarin da baiyi ba wajen kokarin fahintar da Hajiya Salamatu iya gaskiyarsa don ta yarda da dukkan bayanin da yayi mata, amma bata saurare shi ba sam! Hasali ma ta gaya masa ne cewar zata yi masa alfarmar rufe sirrinsa a wajen Kilishi don niyyar taimakon da yayi mata, kuma bata ko sake Wauko shi motar ta ba ita da direbanta suka juya suka tafi suka barshi tsaye a ?ofar gidan Bunun nan.

Haka ya fito daga cikin ?auyen nan ya samu ya isa tasha sannan ya Wauki shatar mota guda saboda tun akan hanya zuciyarsa ta gaya masa cewa bashi da isasshen lokaci da kuma kwanciyar hankali daga yanzu, gobe ne... gobe ne ranar da Kilishi ta gama tsarinta akansa, gobe ne dukkan wannan bayanan da yaji su a matsayin labari zasu tabbata idan har bai samarwa kansa mafita ba.

Don haka a yanzu zai dauki dukkan wasu abubuwansa masi muhimmanci ne ya var garin nan, idan yaso daga baya,zaiyi magana da dillalin da zai sayar da gidan ya kuma Waukar masa sauran kayansa... Burinsa da fatansa kawai shine ya bar cikin Kano a yau, yayi nisa daga inda Kilishi zata iya samunsa kafin yayi nisa daga gare ta gabadaya, nisan da ba zata taba iya samunsa ba, don idan har shi baiyi nasara akanta ba, to kuwa ba zai taba bari ita tayi akansa ba.

Bayan ya ajiye wayar ya zaro wallet dinsa ya kalli adadin kudin ciki da kuma tarin cards Winsa na banki, ya tabbatar komai yana nan daidai sannan ya sake mayar da ita aljihunsa.

A hannayensa duka biyun ya Wauko jakar ya kuma ri?o akwatin da guda Waya, ?afafunsa na sassarfa ya fito daga Wakin ya sake biyowa ta cikin falon ya nufo hanyar fita waje inda motarsa da ya bude ke jira, sai dai da taku biyu kaWai ya rage tsakaninsa da kofa lokacin da abin ya faru...

Kofar falon ta buWe da wani irin ?arfin da yafi na hankali, kuma a cikin sakanni biyun da suka biyo baya, idanun Awwalu suka Waukar masa hoton mutanen da suka fado ciki...

Ya san su, ya gane shigarsu, kayan jikinsu da kuma yanayin yadda suke rufe ba tun yau ba, ba kwanan nan ba, a shekaru masu yawa da suka wuce, shekaru goma da suka wuce.... Sai dai kafin kwakwalwarsa ta tariyo masa inda ya san su da kuma a ranar da ya gansu Waya daga cikinsu ya karaso da saurin da suka faWo gidan dashi ya buga masa wani dogon abu da yake ri?e dashi.

Wata tsawa tare da wani farin haske suka ratsa kunnuwa da kuma idanun Awwalu a lokaci guda! Yaji kamar ruwa na bi ta bayansa, kamar yana sulalewa zuwa wata duniyar daban, taji sanda kafafunsa suka yi rawa suna durkushewa a wajen, kuma kafin idanunsa su tafi su rufe gabaWaya, yaga sanda da yawansu ke shigowa cikin gidan suna yanyame shi.


****

"Kun gama?"

Ma'aruf ya tambaya a cikin wayar dake kare a kunnensa yayin da yake zaune cikin daga office din Faruk.

Amina dake tsaye ya gaban mudubin dakinta ta daga kai kafin tace.

"Eh yanzu ta fita, ta gaya min duk abinda zan dan kiyaye ne kuma tace babu wani abu tunda anui scanning a asibitin babu wata matsala, kuma nace mata babu abinda nake ji."

Ma'aruf yayi shiru yana kallon tarin takardun dake gabansa da kuma Faruk Win dake can jikin windon office Win yana waya, an kammala dukkan wani binciken da gidan waya je yi akan lambar da suka samu ta Awwalu, sun sami tarin bayanin da tun dazu ake turowa Faruk Win yana printing dinsu daga computersa, a yanzu abu Waya kawai suke jira, so suke yi a turo musu da address din inda yake wanda aka samu daga cikin wayarsa tare da wani shekaru uku da suka wuce yana bayanin canja gidan da yayi.

Yaron da zai turo musu da report Win hakan ne ya tafi wani meeting tare da sauran shuwagabannin su, don haka tun Wazu Faruk Win ke rike da kan waya yana jiran dawowarsa tare da kuma samun wasu bayanan daga sauran ma'aikatan wajen.

A gabansa kuma tarin takardu ne na meeting din da zasu shiga da kamfanin Rotel&co gobe, kwangilarsu ta gaba... Babu yadda Faruk bai yi dashi akan su daga ranar zaman nasu ba amma yace masa A'a dole zasu ajiye komai a gefe su yi hakan, don baya son bawa Baffa kowacce irin dama da zaiyi tunanin cewa suna kasawa a wani abu, sannan su kansu kamfanin sun samu kwangilarsu ne da kyar, akwai tarin kamfaninnika da yawa da suke neman samun yin aiki dasu don tabbas kowa shaida? ne cewar biyansu ya banbanta da na wasu kamfanikan da yawa.

Don haka ko yaya suka basu wata dama, kai tsaye zasu iya tuntubar wasu su manta da zancensu, fon haka ya dage cewar dole su tsaya kan alkawarinsu, amma kuma duk da
Wadannan tarin ayyukan dake gabansa tunaninsa ya kasa mantawa da matarsa da kuma sabon al'amarin da suke ciki, gani yake kamar ba haka bane, kamar abinda ita da kuma asibitin nan suka gaya musu ba gaskiya bane, ba don komai ba sai don yadda abin yake iya tsakaninsu kawai har yanzu.

Lokacin da yana tare da Rukayya, lokacin da ta sami ciki, zai iya cewa shi da Malam sani direba sune na ?arshe a sani, don yayi tafiya a lokacin har aka kwantar da ita a asibiti ta kwana babu wanda ya kira shi a cikin ?anuwanta tunda ita tana bacci a lokacin, sai da safe da Mami zata je asibiti wajenta sannan ta kira shi tana gaya masa, a lokacin suka ji tare da Malam Sanin da zai kaita.

Kuma Allah ya sani a wancan lokacin da zuciyarsa ta riga ta gama sarewa da al'amarin Rukayya, don baya jin ko sau daya ya taSa nuna damuwa da abinda ke cikin nata, ya san dai ya bata dukkan kulawar da zai iya, bayan haka bai damu ba da dawainiyar cikin ba kamar ita, kamar itama da a lokacin bata Wauke shi a komai ba.

Sai a ranar da Hamida tazo duniya, ranar da ya ri?e ta a hannunsa sannan wannan ?aunar da iyaye ke ji a lokacin da suka kalli gudan jininsu ta mamaye komai, ta rufe wasu abubuwan ta kuma bude tarin wasu a zuciyarsa, tarin wasun da duk karfin da suka yi basu iya saita rayuwarsa daidai a lokacin ba, don ?aunar da yake bukata, zuciyar da yake bukata ta fahimce shi tafi tafi karfin ?ar karamar dake bugawa a kirjinta.

Amma wannan karon, haka kawai yake jin kamar komai daban ne, tunda rayuwarsa ta canja, yana cikin nutsuwa da kuma kwanciyar hankalin da yake ji hannayensa zasu iya buWewa su ri?e wani abun fiye da wanda yake iya kokarinsa wajen kula dasu a yanzu, shi yasa haka kurum bayan yazo office Win ya kira wata likita dake aiki a asibitinsa na can Abuja, ya kira ta yace taje gidan ta sake duba ta tunda sunyi magana tace masa tazo Kano ita da Familyn ta hutu.

Saboda haka ya sake gyara zamansa yana zura hannunsa cikin gashin kansa kafin yace.

"BabyDoll kin tabbata babu abinda kike ji?"

Amina ta girgiza kanta a hankali tana neman wajen zama daga bakin gadonta.

"Ba abinda nake ji da gaske, kawai kamshin wasu abubuwan ne suke damuna ka sani..."

Ya gyaWa kansa yana kallon Faruk Win da a yanzu ya tafi can gaban teburinsa yana? karanto wasu lambobi daga cikin wayar tasa zuwa?cikin wayar dake kare a kunnensa.

"Kiyi list dinsu gabaWaya ko menene we are getting them out of the house da zarar na dawo... Kinji."

Ta cije lebbenta taba murmushi, don list Win farko da ta fara hangowa kusan rabi na turarukan da yake amfani dasu ne, sai kawai ta gyaWa kanta sannan tace.

"Insha Allah Sugar."

Yayi shiru na wani lokaci, itama tayi shiru bata ce komai ba, tana jin muryar Farouk din dake magana daga cikin wayar.

"Kina son wani abu?"

Ya tambaya a hankali yana katse shirun, sai ta girgiza kanta kamar yana kallonta kafin tace.

"A'a."

"Ni ina son wani abu..."

"Wani abu me?" Ta tambaya tana cije lebbenta sanin halinsa, amma sai taji yace.

"Dan Allah ki min tuwo yau..."

Tuwo. Kalmar ta dira akanta duk da yadda ya fade ta a hankali, ba wani jin daWin jikinta take ba, kawai daurewa take tana gaya masa babu komai tunda ta san tarin ayyukan dake gabansa da kuma abinda yake fuskanta. Bata tunanin ma zata so kamshin kowacce miya da zai ce yana so.

Amma ya zata yi? Ba kullum ne zata fyskanci abinda take so a cikin auren ba ma ta sani, ta sani a cikin kanta cewa wannan matakin da suke ciki mai wucewa ne ma, yau da gobe tafi ?arfin komai, rayuwar ba tatsuniya ba ce ba, ko a tatsuniyar ma akwai lokacin da abubuwa basa tafiya daidai, tana lissafi da ranar da zata zo Ma'aruf zaiyi mata abinda zai ?ona ranta, tana lissafi da ranar da zata fara fuskantar irin hakurin da kowacce mace ke yi a gidan aurenta, saboda hakan shine auren shi yake mikewa ya cigaba da haifar da fahimtar juna da kuma sha?uwa a tsakani, idan har babu hakuri a ginshikin aure, da tabbas duk wani nau'i na jin dadin duniya ya ?are.

Saboda haka sai kawai ta gyaWa kanta a hankali sannan tace.

"Insha Allah Sugar, kayi aikinka ka dawo, muna nan muna jiranka da tuwonmu a ?ofa..."

Tana jiyo murmushin da yayi mai kama da dariya.

"I love you so much Noor..."

"Love u too."

"Ki saka min wannan rigar kafin in dawo."

"Wacce?"

Ta tambaya girarta biyu na gadewa waje guda alamun bata gane ba.

"Wadda ba sai na sha wuya ba..."

Dariyar da ta kyalkyale da ita ta katse sauran maganganunsa, yayi shiru yana juya biron hannunsada nasa guntun murmushin shima.

"Da gaske nake."

Sai ta girgiza kanta sannan tace.

"Kar ka damu, zaka so wadda zan saka fiye da wadda kake tunani ma..."

Ya girgiza kansa a lokaci guda

"The day is rough Babydoll, and you are making me go crazy..."

(Ranar yau sai a hankali Babydoll, kuma kina kara rikita ni....)

Amina ta cije leSSenta a hankali tana murmushi, kuma sanin halinsa da abinda zai iya faWa a gaSa, yasa tayi saurin yi masa sallama, wayar tasu ta ?are da hakan.

A daidai lokacin da Ma'aruf ya sauke wayar daga kunnensa daidai lokacin da Faruk ya tsaya a gabansa yana mi?o masa takardar dake hannunsa, kuma murmushin dake kan fuskarsa shine abu na farko da ya fara shaidawa Ma'aruf abinda bai furta ba.

"Mun same shi Ma'aruf, ga address dinsa nan, ka shirya mu tafi... ko waye wannan Awwalun yau dubunsa ta cika!"

***

_Su wa kuke tunanin sun kama Awwalu?_

_A wane lokaci kuke tunanin su Ma'aruf zasu isa gidansa?_

_Tare da mutanen nan?_

_Ko bayan sun tafi da Awwalun?_

_Ina Kilishi?_

_Kuna tunanin Hajiya Salamatu ta hakura da zancen dan ta?_

_Ta yaya Jawad zai gano mahaifiyarsa?_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
#FararWuta.
#FararWuta.
#FararWuta.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*18*

~~~~~~

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka, ina mika ta'aziyyata da kuma jaje ga dimbin al'ummar musulmi da ma jama'ar Kano game da tashin hankalin da muka fuskanta a cikin satin nan na kisan gilar da aka yiwa ?ar ?aramar yarinyar da bata da laifin komai a duniyar nan, ina rokan Allah ya bawa iyayenta ha?urin rashi, Allah ya ?ara kare mu da iyalanmu, Allah kuma ya kawo mana karshen dukkan tashin hankalin da muke ciki lafiya. Ameen.*


***

Motoci guda huWu zaka fara gani a ?ofar gidan kafin idanunka su lura da cewar kofar motar guda Waya a bude take hade da mukullinta a jiki.

Don a lokacin da suka tsaya, tunanin Ma'aruf da kuma duk wata nutsuwarsa tayi kaura daga cikin kansa, fatansa kawai shine su sami mutumin da suka zo nema a cikin gidan nan, Awwalu!

"Nan ma baya nan...!"

?an sanda na ?arshe da suka dawo daga bayan gidan suka fada suna shivowa cikin falon inda dukkaninsu ke tsaye, sun duba koina a gidan sun duba koina, kuma hasashen Ma'aruf na cewar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login