Showing 75001 words to 78000 words out of 132946 words

Chapter 26 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1128

pancake da yayi taushi sosai guda uku.

A hannunta ta Wauko woven tray Win da ta jera komai akai tana barin flask Win ruwan zafin a kitchen din, kafafunta suka fita daga kitche Win har zuwa hanyar koridon Wakunansu, wata doguwar riga ce a jikinta ta atamfa, dinkin jikinta mysi kyau ne don ko ranar da ta fsra saka ts su Samirah sun yaba dinkin sosai, ta daura dankwalin kawai a gaban goshinta, bayan Waurin ya tokare da tudun gashinta mai laushi da yake a tsefe ya fito ko tawanne gefe ana ganin sa.

Fuskarta fayau take, don duk da halin da take ji suna ciki akwai murna kuma a ?asan ranta fal, godiya ga mahallicinta kawai take mikawa a cikin ranta, tana jin cewa kamar babu wani abu a duniyar nan da zai iya daukar irin farin cikin dake cikin zuciyarta.

"Assalamu alaikum..."

Muryarta ta faWa bayan ta murda kofar dakin nasa, labulayen da iska ke motsawa ta fara gani a idanunta kafin shi, yana zaune daga ?arshen gadon Wakin kusa da bedside drawer dake kunne da fitila akanta, hasken fitilar da shi kaWai ne a cikin Wakin, kasancewar labulayen windunan sun hana hasken ranar da ya fara fitowa a waje shigowa ciki kuma sauran fitulun dakin duka a kashe suke.

Faffadar kafadarsa da kuma bayansa su ke kallo ta yayin da kamar kodayaushe hannunsa daya na ri?e da wayar dake kare a kunnensa.

Taji kamar ya amsa amma bata tabbatar ba don maganar da yake yi ma bata jin ta sosai, kafafunta suka taka a hankali zuwa ciki kuma maimakon ta samu waje ta ajiye tray din hannun nata sai kawai ta tafi gabansa ta tsugunna gabaWaya da kayan a hannunta, idanunsa suka kalle ta kuma kafin ta gama tantance idan fushi yake yi ko akasin haka, sai kawai ya kamo hannunta guda daya ya ri?e shi a cikin nasa.

"Zuwa 11 na fito Insha Allah, ina ga muna da two hours kafin lokacin da zanje Wauko Abdurrahim..."

Ya fada a cikin wayar da ta san ba da kowa yake yi ba Faruq ne. Idanunta suk cigaba da kallonsa yana sauraren bayanin Faruq Win, ba ma sai yace mata ba, tana iya karantar cewa ransa a Sace yake a cikin idanun nasa da kuma yadda jijiyoyin gefen wuyansa ke fitowa suna motsi su kaWai, gashin kansa ma wani bayanin ne ?arara, gabadayansu a hargitse wasu sun dur?usa kamar zasu yi sujjada.

Sai kawai ta zame farantin daga hannunta ta ajiye shi a ?asa sannan ta mi?e zuwa gabansa ta zauna akan cinyarsa a hankali, da yatsan hannunta da bai ri?e ba tta shiga shafa gefen wuyansa a hankali kuma tana jin yadda makowagronsa ke tamkewa da taSawar da take yi, sai kawai ta karya wuyanta ta cusa fuskarsa ta gabaWaya a cikin nasa wuyan, tana jiyo muryar Faruq Win dake bayani tar daga cikin wayar.

"... Yaron bashi da hankali B, yana gaya min wai baya tunanin nambar ma wani ya taSa yi mata rijista? Akwai layin da yake amfani babu rijista ne?..."

Hannunta ya tafi daga wuyan nasa zuwa bayansa kuma a hankalin ta shiga zana masa harafan da ba lallai ta san ya fahimta a lokaci guda ba, don haka ta shiga yi tana ?ara sakewa... SORRY.

Har a lokacin kanta yana cikin wuyansa, tana jin yadda ko'ina a jikinsa ke amsawa da abinda take yi amna kuma bai ce komai ba, baiyi wani motsi ba ko kuma ya kalle ta tun bayan ri?e hannunta da yayi.

"Zan kira ka Faruk ina zuwa."

Taji ya faWa a cikin wayar muryarsa na fitowa wani iri, kuma tana jin wayar ta tsinke sai ta ?arasa da fuskarta daidai kunnensa tace.

"I'm sorry Sugar, dan Allah kayi hakuri."

Muryarta ta fito da sautin da taji da ace dare ne zata iya tayar da hasken taurari su haska masa fuskarta sosai don ya fahimce ta, ta fadi hakan sannan ta janye kanta a hankali zuwa baya tana kallon fuskar tasa, kallonta yake yi kawai babu alamun zai ce wani abun amma duk da haka tana iya jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar tata.

Komai fushin da zaiyi da ita, bata jin zai karasa har cikin zuciyarsa, ita mai rangwame ce akanta ta sani, sai kawai tasa tafin hannunta duka biyu ta rike kowanne gefen fuskar tasa.

"Ba fushi nake yi ba, me yasa kike bani hakuri?"

Ya yanke shawarar fada muryarsa na fitowa da wani irin amo da bai yi nata dadi ba, amon da yasa babu dalili a lokaci guda taji hawaye ya cika idanunta, bai fahimce ta ba har yanzu, bai fahimci dukkan bayanin da tayi masa ba, bata taSa tunanin kuma zai ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kasa fahimtar tata irin haka ba.

Zuciyarta ta matse da tunanin irin fassarar da yayi mata tun kafin ma ta sani, tana jin wani abu na narkewa a cikin jikinta kamar ?arfen da ake ?onawa a cikin wuta, wannan ya?inta ne ta daWe da gayawa kanta hakan, babu wanda ya san wannan manufar tata a duniya bayan shi, ko Amma bata furtawa ba, shi kaWai Win ne ta san ya zama dole ya sani kuma shi kaWai take tunanin zai fahimce ta su rufawa junansu wannan asirin duk da bai san komai ba, amma idan har yana yi mata wani tunani na daban nasarar me taci kenan?

Sai kawai ta girgiza kanta tana cigaba da kallonsa.

"Da zan iya zan tattaro komai a duniyar nan Sugar, zan tattaro du gabaWaya in jera a gabanka don su zama shaida cewar ba zan taSa yin wani abu da na san zai bata ranka ba, so nake kawai ka fahimce ni, ba zaka gane yanzu ba na sani, kuma lokacin da zaka gane Win ma na tabata ba sai na sake yi maka bayani ba.

Ro?on ka kawai nake yanzu ka bani haWin kanka, bayan shi bana son komai Ma'aruf, kaine inuwata kuma kaine tallafi na, bani da wani mai kare ni a duniyar nan da ya wuce kai, bani da wani da zan dogara dashi a duniyar nan bayan ubangiji da ya wuce kai, kuma ba zan taSa daina godewa Allah ba da ya kawo min kai cikin rayuwata a lokacin da ban tsara ba kuma ban taba tunani ba, I will always love you in a way that I will never hurt you..."

A yanzu bata jin wannan kwallar data taru a cikin idonta, wani abu take gani a idanunsa take kuma ji?a jikinta kamar kwarin gwiwar da ya sata ?arasa maganarta.

"Zamu haifi babyn nan cikin kwanciyar hankali insha Allah Sugar, babu abinda zai faru, ka cire tunanin komai a ranka dan Allah ka yarda dani, kamar yadda kake yarda da Faruq Win nan."

Sai kawai ya girgiza mata kansa a lokaci guda sannan yace.

"Kar ki taSa haWa kanki dashi Babydoll, matsayinki da nasa daban ne a cikin zuciyata, there's no way ma da kuka zo kusa."

Ya fadi hakan yana matso da ita jikinsa, kusa dashi sosai ta yadda take jin ?arar bugun zuciyarsu ya haWe waje guda akan zare guda, sanyi da zafi, mai nauyi da mara shi da kuma siririn da ya yake haWewa cikin dan'uwansa.

"Na yarda dake Noor, na yarda I'm just curious ne, abubuwa be suke neman haWe min haWe min waje Waya matsalar office da kuma..."

Ya faWa hannunsa na kokarin lalubo zip din rigarta a hankali, wani abu da yake son wasa dashi a kodayaushe. Sai kawai ta girgiza mata kanta a hankali.

"Babu ruwan gidan nan da office my Ranger Handsome, ka bani damar da zan sa idan ka dawo wajenmu kaji kamar wata duniya daban ka shigo, kamar mun koma Mars ne mun bar musu duniyarsu da hayaniyarsu."

A lokaci guda murmushi ya suSuce a fuskarsa yana kallonta.

"Really BabyDoll? Kamar me kenan?"
Ya tambaya yana Waga mata gira Waya, sai ta cije lebbenta na ?asa alamun tunani kafin tace.

"Zamu zama iyaye nan da watanni masu zuwa..."

"Alhmdulilah." Ya katse ta yana gyaWa kansa.

Bata tsaya ba ta cigaba.

"... Kuma yau muka sani, yau aka gaya mana... So let's celebrate!"

Ya ?ara gyaWa kansa murmushinsa na ?ara yawa, yayin da a cikin kanta take godewa Allah ganin yana dawowa yanayinsa na Ma'aruf Win ta.

"We should BabyDoll, me kike so muyi yanzu? I think ina da two hours kafin in fita."

Ya fada yana Wora goshinsa akan nata, hancinsa na taSa saman nata.

Ta sake cije leSSenta tana kallonsa sannan ta girgiza kai, duka fuskarsu ta girgiza a tare.

"Yanzu lokaci yayi kaWan, kayi breakfast ka fita, celebration Win zai fi daWi da daddare."

A lokaci guda hannunsa ya tsaya da taSa zip din rigarta da yake yi, ya janye fuskarsa daga tata yana kallonta sosai, da idanunsa da take jin kamar yana sace ruhinta daga jikinta, har a lokacin da murmurshi a fuskarsa yace.

"Tabbas zai fi daWi sosai Babydoll..."

Ta gyada kanta itama.

"Zan nemo restaurant hadadde wanda suke da fitulu sosai 'cox we are going to take pictures na tarihi wanda zasu zauna har tsawon shekar...."

Bata ?arasa ba lokacin da Ma'aruf ya kyalkyale da dariya yana Wora kansa a gefen kafadarta ta dama.

"Menene? Me ya faru?"

Ta tambaya tana murmushin da bata san na meye ba yayin da hannunta ke kokarin? Wago da fuskarsa. Tana jin yadda jikinta ke girgizawa da dariyar da yake yi.

"Na kasa ganewa, wai menene?"

Ta ?ara faWa sanda tayi nasarar dago da kan nasa, ya kalle ta sosai yana girgiza kansa kafin yace.

"Babydoll da kika ce celebration kuma kika ce da daddare, abinda nake hangowa daban..."

Bata san lokacin da ta ture shi ba tana kiran sunan sa, sunansa gabaWaya.

"Ma'aruf Mansour Bakori..... ka dinga tunani irin na mutane a cikin kanka dan Allah."

Ta fada tana ?o?arin mi?ewa, bata je koina ba kuwa ya jawo ta suka koma kan gadon gabaWaya.

"Zo ki koya min irin yadda ake yi tunanin mutanen..."

Abinda ya faWa bayan hakan ya saka ta kyalkyala dariya tana cusa kanta a cikin wuyansa, abinda ya cigaba da faWa kuma ya sata faWin.

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un... Ma'aruf!"

Dukkaninsu suka kyalkyale da dariya, kuma abinda dukkaninsu basu sani ba shine, za'a Wauki wata tazara mai tsawo kafin sake faruwar irin wannan ranar a rayuwarsu!

****

*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*

Ta san dakin, amma idanunta suna kallonsa ne kamar bata taSa ganin sa ba, idan ma akace ta ?irga bata san sau nawa zata kirga adadin data share kuma ta gyara shi ba, shi kaWai ne a ?asa bayan falon, kuma tasha tambayar kanta dalilin da yasa aka hada shi har da komai da komai alhali mai wajen baya amfani dashi ko kaWan.

Bayan haka kuma zuciyarta tasha hasko mata yadda zata ji daWin kwanciya akan gadon da yake dakin, don kalar labulayen cikinsa da kuma zanin gadon Wakin da suke suke dukka kalar yalo, suna faranta zuciyarta haka kawai, tana jin kalar na shiga idanunta da tasirin da take jin kamar tana samun ?ancinta ne a ciki, kamar zata samu wani fiffike da zai mi?ar da ita sama ta tsaya da kafafunta irin yadda take fata a kullum.

Amma yau da take tsaye a cikin dakin rike da ledar kayan dake hannunta bata jin dukkan waWannan abubuwan, bata jin komai, zuciyarta fayau take kamar fuskarta.

_"Zainab zaki aure ni?"_

Sune kalaman dake maimaitawa kawai a cikin kanta, amonsu take ji yana ratsa ko'ina na tunaninta, tana ji kamar sha?uwar data kwace mata a lokacin zata sake dawowa, don sha?uwa kawai ta dinga yi yayin da idanunta ke ?ara zarewa akansa, kuma bai sake cewa komai ba sai kawai ya kai hannunsa ya shafa kansa sannan ya juya ya bar wajen.

Bai sake cewa da ita komai ba har suka gama dukkan abinda za'ayi a asibitin ya karSo mata magani, binsa kawai take yi tana so ta tsayar da sha?uwar da ta kasa tafiya, ya barta a mota ya shiga wani waje da ta kula cewa magunguna ake sayarwa, kuma bayan ya dawo ne ya shigo motar ya miko mata robar ruwa har a lokacin bai sake cewa da ita komai ba.

Tana tuna yadda ta shanye ruwan gabadaya kasancewar ba wani girma ne dashi ba amma har a lokacin shakuwar bata tafi ba, sai kawai taga ya sake miko mata wata robar daga cikin ledar maganin, a lokacin har sun fita daga cikin asibitin sun hau titi. Kuma ga wani mamakinta ba gida suka taho a lokacin? kamar yadda ta zata ba, idan zata tuna ma taga sanda suka wuce hanyar gidan suka tafi kai tsaye har wajen aikin sa.

Wajen da ya ?ara rikita ta, ya kara sawa ta raina kanta ta san cewa ita ba komai bace a duniyar nan, tun daga waje ginin wajen?ya daki zuciyarta har suka shiga ciki, don bai bata wani zabi ba yace ta biyo shi, suka tafi har office din wata mata da taji yana kira da Aunty Mary, dattijuwa ce amma kuma arniya, ta saka kayan da basu matse kayion jikinta ba sannan tayi kitson ?arin gashi.

Tana da tsananin fara'a da kuma kirki, anan yace ta zauna zai je ya dawo, kuma bayan ya tafi haka tayi ta mata magana duk da ta fahimci ba ganewa take sosai ba, don idan ma zata gane Win, taraddadin dake cikin zuciyarta na tunanin Hajiya Mardiyya da nemanta da za'ayi ba zai barta ba, a haka ta zauna cikin tunani da tsoro har sanda wani ma'aikacin wajen ya shigo rike da leda mai dauke da abinci da kuma magungunan da aka siyo.

_"Hajiya ga shi yace ki ci abincin kuma ki sha magungunan."_

Tana tuna fuskar mutumin da ya kira ta da Hajiyar, zata iya rantsewa zai kai sa'an mijin mahaifiyarta da ta baro a gida, amma kamar bai ga kankantar ta ba ko kuma dogon hijabin data zura wanWanda basa shaida wani abu na Hajiyar da ya kira ta.

Matar nan da kanta ta gaya mata cewa lokacin sallah yayi, ta buWe mata banWakin cikin office Win ta shiga tayi alwala sannan bayan ta fito ta shimfida Wankwalinta akan carpet din wajen tayi sallah, haka ta zauna idanunta na cigaba da zarewa har sanda ya dawo, kuma a lokacin kallonsa kawai tayi taji shakuwar Wazu ta dawo, haka ta dinga yinta tana kokarin boyewa har suka koma motar kuma ya sake miko mata wani robar ruwan ba tare da yace komai ba, wani abu da duk rikicewarta sai da ya saka ta murmushi a lokacin.

Sun dawo gidan jikinta na rawa kamar yadda zuciyarta ke yi na tarin abinda ta san zata tarar, abinda ke jiranta wanda kwakwalarta ta kasa hasaso mata shi, amma bai ko bari tayi hanyar wajensu ba yace ta biyo shi bangarensa.

Kafafunta sai da suka tsaya cak jin hakan yayin da wani shiru ya ratsa ta tana jin yadda komai ya Wauke a cikin kanta amma bayan yayi gaba ya sake juyowa ya kalle ta da wadannan idanun nasa sai kawai ta kasa cewa komai ta biyo bayan nasa suka shigo har bangarensa, ya buWe mata kofar wannan dakin ya bata ledar kayan dake hannunta a yanzu yace ta shiga ta shirya.

Ta shirya. Shiryawar da bata san ma'anarta ba har yanzu, kallon Wakin kawai take yi kamar a cikinsa zata samo amsoshin da take nema.

Ta tsugunna a hankali har ?asa, ta buWe ledar hannunta ta zaro kayan ciki, wata farar riga ce mai tsawo da kuma laushi, akwai wani dogon wando kakar adon jikinta pink, sannan da hijabi fari tas wanda ta san zai kai mata ne har ?asa, mamakin inda ya samo kayan ya kamata, Allah ya sani bata san me yake nufi ba, bata gane komai ba har yanzu, so take kawai ya barta ta fita ta samu Hajiya Mardiyya ta gaya mata duk abinda ya faru ta kuma ro?e ta gafara, don ?wakwalarta na shaida mata cewa itace gatanta ba Jawad da al'amarinsa ba.

Kusan minti talatin tana zaune a kasan carpet Win Wakin ta jingina bayanta da jikin gadon yayin da kwakwalwarta ke ta faman lissafin wucewar lokaci tana jira yazo ya sallame ta tafi, kuma saboda gajiya da kuma zazzaSin da bai gama barinta ba har a lokacin, sai ta fara gyangyadi zaune a wajen har zuwa sanda aka kwaknkwasa kofar dakin, sau biyu kawai kafin kofar ta buWe.

Idonta ya sauka akansa tana ?o?arin wartsakewa, yana tsaye sanye da wata jallabiya ba?a, hasken fatarsa ya ?ara fitowa sosai alamun wanka yayi, yayi shirin da ita bata yi ba.

Jawad ya tako har ciki yana kallonta, da alama inda ta tsaya bayan ya barta a dakin a wajen ma ta zauna, Babu alamun ta matsa ko'ina, me yasa take so ne ta kara masa matsala bayan tarin abubuwan da yake fuskanta?

Shi kaWai ya san yadda ya daurewa kansa yayi aiki a office yau, zai rantse da Allah bai taSa ganin tsoro a idanun kowacce mace a duniyar nan ba kamar yadda ya gani a nata lokacin da ya tambaye ta idan zata aure shi, shi yasa ko da ya barta a Office din Aunty Mary, sau biyu yana kiranta yaji idan tana nan bata gudu ba, wannan shakuwar kaWai da ta dinga yi tayi yawo a cikin kansa ta yadda da ?yar ya goge ta yayi aikin dake gabansa.

Da gaske yake, da gaske yana ganin zai iya aurenta shi yasa har ya tambaya, don bai taba jin wani abu da ba zai taSa kasancewa ba sai a lokaci?da Mamah ta gaya masa cewar wai aure iyayenta zasu yi mata, ya sani bashi da iko akanta fiye dasu ko ma wani a duniyar nan, amma a lokaci guda yaji cewar babu mahalukin da ya isa yasa hakan ta kasance, babu wanda zai bari yayi nasarar dauke ta daga gabansa, shi yasa a lokaci gudan ya yanke shawarar tambayarta idan har zata aure shi.

Don a wannan lokacin yana ji kamar idan ta amsa shikenan komai ya tabbata, shikenan ta zama tasa sun kaucewa dukkan wasu abubuwa.

Burinsa kawai ya cigaba da wayar kowacce safiya yana ganinta a gefensa ko da ba zai iya taSa ko yatsanta ba, ya riga ya fahimci a yanzu rauninta yake so, shine babban abinda ke jan hankalinsa akanta, wannan rauni da kuma rikicewarta da suke banbanta masa ita da Rukayya, Rukayya mai ji da kanta da kuma ta?amar tsayawa da kafayrta a kodayaushe, komai nata yayi hannun riga da Zainab, shi yasa tun a farko zuciyarsa ta fara tsayawa akanta don yana neman duk wani abu ne da zai sa ya manta da Rukayya a lokacin.

Da lokaci ya cigaba da tafiya kuma sai yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login