Showing 24001 words to 27000 words out of 132946 words

Chapter 9 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1138

basu tafi ba sai bayan da suka ci abincin dare, har Samira ta dawo daukan wayarta da ta manta tana ta korafin me yasa basu kirata ta taya su ba.

A yanzu fitowarsa kenan daga wanka yanzu tunda ya samu a dazu sunyi jam'in sallah tare dasu Ishaq.

Yana zaune daga bakin gadon dake dakinsa, safa yake kokarin sakawa a ?afarsa saboda sanyin da yake ji yayin da zuciyarsa ke kara hasaso dukkan abinda ya faru a yau yana ganin kamar? a wata guda akayi komai ba yau kadai ba.

Kofar Wakin ta buWe a hankali, ya juyo da kansa lokacin da Amina ta shigo hannunta dauke da wani dan madaidaicin tray a hannuta.

Tun bayan tafiyar kowa bai ganta ba, kuma tun a adibitin nan da ya farka yace ta kira masa Ishaq basu kara magana ba, jayan jikinta suka shaida masa cewa itama tayi shirin ba ci don doguwar riaga a jikinta wadda bara sauka sosai, ba, wani abu acikin kansa ya shiga gaya masa cewa yana missing wadannan siraran kafafun nata kamar me.

Ta karaso gabansa a hankali, idanunsa na kallon kowanne takunta, kaginnya maida su fuskarta.

"Yaya ka kara ji da sauki?"

Muryarta ta tambaya kamar wani abu dake tashi sama a hankali.

Kuma baiyi tunanin komai ba yace.

"Ke kike ta bani reason din da nake jin saukin ai."

Sai kawai tayi murmushi kaWan sannan ta tsugunna a gabansa, ta durkushe kafafunta daga ganinsa, hannunta ya buWe plate guda Wayan dake kan tray din tana fadin.

"Na san yanzu zaka iya cin wani abu ko?"

Bai amsa ba ta sake cewa.

"Inna Danejo tace kar in bari ka kwanta haka baka ci wani abu."

Ta karasa sanda ta saka cokali a cikin plate din hadadden potate din dankali da alaiyahun dake ta ?amshi a hancinsa.

Ta dago ta kalle shi, har yanzu idanunsa na kanta, kuma ga mamakinta sai taga kawai ya sauko kasan shima ya zauna daidai gabanta, sannan ya riko hannunta daya da bata rike plate din dashi ba, kamar koyaushe ya ratsa yatsunsa a tsakanin nata. Ta kalli hannun nata daya rike? ba tare da tace komai ba sannan ta Webo abincin ta shiga bashi, yana ci tana gaya masa yadda akayi kafin likitocin asibitin nan su sallame shi.

Kuma bayan sun gama ne yace ta dauko masa wasu magungunan gargajiya da ya taba siya ya ajiye a saman drawer dakin, kamar zata iya sai da taje gaban drawer sannan taga da saura dosai kafin tsawonta ya Kai, don haka ta shiga neman abinda zata taka, amma kafin ta motsa tajinsanda ya karaso daidai bayanta sannan kai tsaye hannayensa duka biyu suka zagayo ta kasan cikinta kuma kafin ya hade su waje daya tana jin irin rawar da suke yi alamun har yanzu jikinsa bai gama kwarin da zai tsaya haka ba.

Don haka bata san lokacin da ta juyo ta fuskance ba da sauri idanunta na haskawa da mamaki.

"Me yasa ka taso? Zan iya daukowa fa..."

Sai ya girgiza kansa yana sake rike ta a jikinsa.

"I want to talk to you."

Har yanzu ji take yi kamar basu gama tsayawa daidai ba don haka tasa hannunta duka biyu ta rike gaban rigarsa kadan tana cigaba da kallonsa, kuma bata ce komai ba ya cigaba.

"I'm sorry game da abinda ya faru Amina, I'm sorry for how you saw me, (Ki yi hakurin yadda kika ganni) Na gaya miki dama I'm a mess..."

Sai tayi saurin girgiza nata kan itama tana cigaba da kallonsa.

"You dont need to be, lafiya da rashinta ba mallakin kowa bace, Allah yana bamu ita ne a lokacin da ya ga dama ya kuma karSe ta a lokacin da yake so don wanke zunubanmu, saboda haka ba kaifinka bane, ba laifin kowa bane, don kowan bai wuce ya wayi gari shima an karbi tasa ta wata sigar ba.

Insha Allah abinda ya same ka kaffara ne ga wasu abubuwan da ba lallai ka san dasu ba ma. Don haka daga kai har mu ba abinda zamu yi da ya wuce addu'a kamar yadda kowa da ya taru anan yayi tayi maka..."

Tayi shiru tana kallonsa kafin ta karasa a hankali.

"... abinda kake bukata kenan."

Taji hannayensa sun sake rike ta sosai kafin ya karadso da fuskarsa a hankali ya dora goshinsa akan nata.

"Ban san me zan ce miki ba Amina, duk abinda kike yi, duk kike fada yana wuce dukkan tunanina, bana jin a duniyar na bayan Mami akwai wanda yake fahimtata yanzu sama dake."

Ambatar sunan Hajiya Kilishi da yayi yasa numfashinta yin rawa kafin ta? rufe idanunta a hankali, tana jin nasa numfashin shima na sauka akan fatarta, sai kawai ta tatraro dukkan dauriyarta tace.

"Nima bana son kowa yafi ni fahimtarka, nafi son na zama mutum ta farko da zaka nema a kowanne lokaci walau na Sacin rai ko farin ciki."

Bata sani ba ko kallonta yake yi amma taji sanda ya kara rike ta a jikinsa yana gaya mata dukkan wasu kalaman godiya, sai kawai ta ture dukkan wani tunanin a cikin kanta a lokacin ta mika hannunta daga saman kirjinsa zuwa bayan wuyansa, ta rike shi kwatankwacin yadda shima ya rike ta. Wani abu da ya bashi mamaki don taji sanda ya dantsaya a cikin hannayen nata kafin ya kira wannan sunan nata a hankali.

"Doll..."

Kafin tama yi tunanin amsawar yace.

"Wannan ma yana daya daga cikin amsata na ranar?"

Ya rufe bakinsa daidai sanda ta daga kanta alamun amsa, taji yayi wani murmushin mai sauti sannan ya matsar da fuskar sa kadan daidai saitin kunnenta ya rada abinda a lokaci guda ya sata dun?ule yatsun kafarta akan tiles din dakin.

"I want to kiss you again dan Allah..."

Ya faWi hakan sannan ya janye fuskarta daga tata, yayi baya sosai yana kallonta. Amina taji lebbenta ya shiga rawa tare da hannayenta sai kawai ta ?ara tsawon kafarta?a lokaci guda, ta kai fuskarta daidai gefen tasa kuma ba tare da jiran komai ba tayi pecking gefen kumatunsa.

Ta sake jin sautin murmushinsa kafin ya kara sunkuyowa cikin fuskar tata ya kwaikwayi sak abinda tayi yayin da take jin murmushinsa akan fatarta, kuma sai da ya matso dab da bakinta sannan ya tsaya, wani abu da yasa a lokaci guda ta buWe idanunta tana kallonsa.

"I want to ask you something? (So nake in tambaye ki wani abu.)

Kafin ta amsa yace.

"Naga kin fara kwarewa a wannan karatun, shekarar ki nawa? 'Cox I don't want us to stop, bana so mu tsaya kuma bana so a kama ni da laifin child abuse."

Amina bata san lokacin da bakinta ya subuce da wata irin dariya ba, ta rufe idanunta gabaWaya sautin dariyar na fitowa tare da tsananin kunyar da maganganun dake lulluSe ta.


****

_Wani abu yana shirin konewa anan.=??>?p?>?)?_

_Ina kuke tunanin Hajiya Kilishi ta tafi ne?_

_Me suka shirya ita da Awwalu?_

_Ru?ayya da mahaifiyarta sun samu nasara, Hamida ta koma wajensu, kun tuna mataki na biyu a tsarinsu?_

_Yaya kuka ga kokarin Amina na farko wajen hada kan gidan Alhaji Muhammad Mansour Bakori?_

Sai naji dukkan sharhinku..>?p?=?
?=?O?

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*05*

~~~~~~~

_If it's not you, it's not anyone._ _- Unknown_

***

*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*

*?arfe tara da rabi na safe.*

A cikin harabar gidan, daga can gefe inda akayi shuke-shuken wasu bishiyu dama fulawowyi, Jawad ya shafo kan hancinsa da daya hannunsa wanda baya rike da wayar da yake yi kafin yace.

"Na gaya maka naga motar, daga can gefen inda muke ta tsaya kuma ni naga mace da namiji a ciki, fuskokinsu ne kawai ba zan iya tantance maka ba."

"Babu ji, wannan mai sauki ne in dai har ka tabbatar number motar da ka faWa daidai ne. Zanyi kokarin nemo bayani akan plate din sai muyi tracing , tunda na san dake zuwan nasu yana da alaka da dalilin rashin zuwan Ma'aruf wajen."

Jawad ya gyaWa kansa a hankali yana cije lebbensa.

A jiya bayan sun shiga Kano, tsarinsu ya tafi daidai, sun yi komai kamar yadda Haro ya tsara kuma ma sun isa wajen da suke saka ran? ganin Ma'aruf inda zai hadu da wadannan mutanen, sai dai? sunyi tsawon jiran da har mutanen suka zo babu Ma'aruf din babu alamarsa, kuma suna wajen har lokacin da motar mutanen ta juya suka bar wajen.

Kuma sai a yanzu Jawad ya tuna da motar da suka wuce akan titin kafin su sami wajen tsayawa, don haka ya kira Haron a waya yanzu yake gaya masa, don a jiyan bai ko bari ya kwana a Kano ba yayi booking jirgin dare ya dawo gida,yana da abubuwa da yawan da ba zai iya wasa da lokaci wajen kuSucewaru ba.

"Kar ka damu J, ai ba ?asar ya bari ba, muna da lokaci muna dashi mara adadi, wannan opportunity din ma don naga yayi kusa ne nace muyi amfani dashi kawai, amma yanzu damar ta fara Jawad kai ma ka sani."

Ya gyada kansa.

"Na sani, na san akwai lokaci Sadiq, fata kawai nake ne kar Rukayya ta shammace mu."

Haro yaja tsaki a cikin wayar.

"Haba Jawad, a cikin kwakwalwar wannan dakikiyar yarinyar har akwai abinda zata yi ne da zai fi namu?? Kawai ka cigaba da harkokin ka, ba za'ayi dedewar da kake tunani ba insha Allahu, su kuma WaWannan mutanen zan saka a nemo mana su insha Allah."

Da haka suka gama wayar, Jawad ya kalli mintunan da duka gama fitowa a jikin screen din kafin ya kashe ta ya zura a aljihu, yayi abu guda biyu da ya Wanawa tarko a safiyar yau bayan dawowarsa, saura na ukun wanda har cikin zuciyarsa yake jin tasirin faruwarsa, game da yarinyar nan, ?ar aikin nan.

Jiya bayan ya fito ya gan ta a wajen nan kuma ya tabbatar da cewar taji dukkan maganganunsa da Haro, baiyi mata magana ba, bai ce komai ba, don ko Haron baya son ya san hakan, abinda zuciyarsa ta gaya masa shine dole ya san yadda zai yi ya rufe bakinta kawai don baya hango yadda alakarsa da mahaifiyarsa zata kasance idan har koda wasa ne ta fadi hakan a gabanta.

Ya zura wayar a aljihu, sannan kai tsaye ya fito daga wajen ya nufi hanyar da zata zagaya dashi baya zuwa Sangaren masu aikin gidan, bangaren dashi kansa gida ne guda mai ?atuwar haraba da kuma shuke-shuke, ba zai iya tuna rana ta karshe da ya taka kafarsa zuwa wajen ba, kawai dai ya san kafin su kai ga tarewa a gidan da suka zo gabaWaya tare da mahaifinsu da kuma sauran ?anuwansa maza, sun zagaya koina har nan kuwa.

"Good morning sir... Good morning."

Wasu ?an aikin guda biyu dake shanya tarin kayan wankin yara suka tsugunna suna gaishe shi, ya gyaWa kansa alamun amsawa sannan ya tsaya yana kallonsu, ya rasa ma me zai ce musu saboda ko sunan yarinyar bai sani ba, ya san dai ya taba ji Mamah ta taSa kiranta a gabansa, watakila fiye da sau Waya ma amma baya jin zai iya tunawa.

"You want something sir?" ( Kana bukatar wani abu ne yallabai?)

Daya daga cikin ma'aikatan ta faWa, sai dai kafin ya buWe bakinsa yayi magana idonsa ya hango masa ita, ta karyo kwana ta shigo wajen, hannunta dauke da wani katon farin nokiti da ta ciko kayan miya a ciki, ko daga nesa ya san bokitin yayi mata nauyi daga yadda yake kokarin rinjayarta ta gefe guda.

Sai kawai ya juya ya nufi wajenta, kuma har ya taho bata lura dashi ba sai da ya iso daidai gabanta tukunna, da farko idanunta basu shaida shi sosai ba, watakila ko bata taba zaton ganinsa a lokacin kuma a wajen bane, amma a lokaci guda sai idanun nata suka haska da tsananin mamaki da kuma fargaba.

Yana ganin yadda ta saki bokitin da sauri zuwa kasa kafin itama ta bishi kasan ta durkushe kan gwiwoyinta sannan tace.

"Ina kwana... Barka da safiya."

Duka kalar gaisuwar guda biyu shi kaWai, kuma har ya buWe baki zaiyi magana sai idonsa ya kai kan wasu mata daga ginin dake gabansu sun le?o ta window suna hangensu, wani tunani ya gifta a cikin ransa don haka sai kawai ya maida kalaman da yayi niyyar faWa yace.

"Me kuka dafa a bangren Mamah?"

Tambayar ta shiga kan Zainb da tsananin mamakin da ya fi na farko, don ta tabbata ba abinda ya kawo shi kenan ba, ya za'ayi ya bato bangaren ya taho tun daga can har zuwa nan don ya tambayeta kawai abinda aka dafa? Mutumin da idan hr ba fita zai yi ba kowa ya haddace cewar baya tashi sai rana ta mi?a, amma ?arfe nawa yanzu? Tara da mintuna...

Ta yaya ne ma yake mata magana muryarsa a ?asa, ta zata ai idan har ba tare da mahaifiyatsa yake ba baya iya magana babu hantara.?Sai tayi saurin hadiye abu a bakinta sannan tace.

"Ba'a gama abincin duka ba, an dai yi wasu."

Ya gyada kansa.

"Ki debo wanda aka gama ki kawo min."

Da haka bai kara cewa komai ba yayi gaba. Zainab tabi bayansa da kallo gabanta na faduwa kafin ta mike a hankali.

Kuma minti goma bayan hakan,? ta kwankwasa kofar Wakin nasa Wauke da farantin kayan abincin, kallon da sauran manyan ?an aikin gidan suka dinga binta dashi bayan ta gaya musu inda zata kai abincin.

"Shigo."

Muryarsa ta fada daga ciki, kuma karo na farko ta murda hannun kofar ta shiga, dakin kamar yadda ta zata ne, ?ato mai cike da hadaddun kayan kamar na sauran ?anuwansa mata, sai dai har gwara nasu ma yafi kyale-kyale akan wannan da komai tsilla-tsilla ne. Yana zaune daga gaban gadon dakin a tsakiya, ya dora hannayensa kowanne akan cinyoyinsa yana kallonta, kuma da yatsu biyu kawai yayi mata alamar cewar ta karaso.

Ta taho Win, amma muryarsa ta tsaida ta.

"Koma ki rufe kofar."

Gabanta ya sake faduwa, amma babu yadda ta yi ta koma Win ta rufe ta a hankali sannan ta sake juyowa, tana ta tahowa bai ce ta tsaya ba, kallonta yake yi ta sani amma ita idanunta na kan farantin.

Sai da ta karaso nesa dashi kadan sannan ta tsugunna ta ajiye farantin a saitin gabansa, kuma kafin ta mike kamar yadda daga shi har ita suka san shine abu na gaba ya sake magana.

"Zauna."

Ta hadiye wani kullutun abu a makogwaronta sannan ta gyara tsugunnon nata a hankali alamun ta zauna Win, tambayarsa ta gaba ta kada ?a?an hanjinta a lokaci guda.

"Daga ina kike?"

Sai ta dago ta kalle shi.

"Nace daga ina aka kawo ki?"

Ya sake maimaitawa, ya sake maimaitawa yana fadada tambayar da ta riga ta fahimta din kuma ta san ina take dosa.

"Sunan garinmu Yakura, a kusa da Kaduna yake." Muryarta tana rawa.

Ya gyada kansa.

"Waye ya kawo ki nan?"

"Abokin babana ne."

"Ina baban naki?"

A hankali tace.

"Ya rasu."

"Ina babarki?"

Sai da ya lura ta hadiye wani abu sannan tace.

"Tana nan, matarsa ce ita yanzu."

Kalaman suka daki kirjinsa da wani abu da bai san meye ba, amma dai ya san nazarinta yake yi, nazarin shekarunta da ya kasa ?iyasinsu.

"Ita me yasa bata hana shi kawo ki ba?"

Sai ta sake dagowa ta kalle shi, idanunta na nuna wani abu da ya kasa tantancewa, idan ma tunani take cewa muryarsa ta fito da damuwa ne, zai goge mata hakan yanzun nan.

"Bashi da kirki, Naani baza ta iya hana shi ba."

Kalmar Naanin da ta fada ya fahimce itace mahaifiyarta don haka kai tsaye ya sake tambaya

"Yaya sunanki?"

Wannan karon da mamakin da yafi nasa ta kalle shi, bai san sunanta ba? Bai san sunanta ba yake tambayar labarinta?

"Sunana Zainab."

Sai ya sake gyaWa kansa yana kallonta.

"Zainab, I know you heard us...."

Maganar tasa ta katse tuna cewar a banza zai yi bayanin ko ta cigaba.

"Na san kin ji mu ranar nan, kinji duk abinda muka fada ni da wanda yazo...."

Ta riga ta sani dama, tasan zancen da zai yi mata kenan, ta san ta shiga uku, ta san karshen rayuwarta a gidan nan tazo tun daga wannan lokacin, Allah ya sani tana jin daWin zaman gidan nan fiye da sauran gidaje biyu da tayi aiki dasu a baya saboda yadda mahaifiyarsa ke kyautata mata, amma tun daga ranar da ta ci karo dashi har ta zuba masa miya a kaya, tun daga ranar hannayenta suka fara lissafin kwanakin barinta gidan, sai gashi ta samu talalar wasu watannin kafin shekanjiya ta tabbatar mata cewar wa'adin kwanakin nata yazo karshe.

Don haka taji yadda iska ta wuce cikin busashshen makogwaronta kafin ta tattaro dukkan karfinta ta daga kanta sau daya.

Jawad ya gyaWa nasa kansa shima.

"Good. Shi yasa na kira ki nan."

Ya fadi hakan sannan ya gyara zamansa.

"Ba zaki so in zama abokin babanki na biyu ba Zainab balle kuma har in fi shi, don ina rabbatar miki zan iya kuntata rayuwarki fiye da yadda bakya tunani idan har kika zabi yin wasa dani.

Abinda kika ji sirrina ne, kuma duk da babu yardata ya iso gare ki, na baki amanarsa a yanzu, kuma in so ki barshi a cikin ranki, ki barshi kamar yadda yake a tsakanin mu yanzu, idan har shiga kunne na biyu musamman kunnen mahaifiyata Zainab..."

Yayi shiru yana cije lebbensa kafin ya fadi abinda yasa ta zare idanunta a lokaci guda ta dago tana kallonsa, hannayenta dama ilahirin jikinta gabaWaya suka shiga kakkarwa yayin da idanunta ke haskawa da tsoron da bsta lissafa dashi ba?? a duk wani lissafinta na ukubar rayuwar da take tunanin fuskanta!

****
*Kano.*
*No. 58 Mafara Street, NNDC SharaWa Quaters.*

*?arfe Goma na safe.*

A cikin dakin, cikin uwar dakin Hajiya Kilishi ta dubi kawarta Hajiya Salamatu wadda isowarta kenan a wannan safiyar bayan fitar Mama Rabi wadda ta shirya musu abun motsa baki fal a wani katon faranti.

"Kinyi min nisa da yawa Salamatu, china tayi min nisa tunda ni ba harkar social media din nan nake yi ba. Na kulla abubuwan da yawa wanda babu tayawarki a ciki balle har mu kai wa tufkar ?arshe mai daukar ido."

Hajiya Salamatun ta cire dankwalinta ta ajiye shi a gefe, mikakken gashin kanta da yasha gyara ya shiga nuna maikonsa cikin hasken dakin kafin tace.

"Ni iyaka ta dake ai shawara Kilishi, wasu ma ba Wauka kike ba idan na fada, to don me zaki yi kewata? Yanzu kawai ki gaya min me ya faru? Me ya faru daga inda na barki."

Hajiya Kilishi ta juya idanunta tana murmushi sannan ta kalli aminyar tata dake zaune daga bakin gadon dakin tace.

"Abubuwa da yawa Salamatu, don haka mu kyale ?ananan ma a gefe, mu fuskanci manyan.

Na riga na gama da yarinyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login