Showing 51001 words to 54000 words out of 132946 words

Chapter 18 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1115

ta gyada kanta a hankali alamun ta ji kuma ta fahimta, shima ya gyada nasa.

"Good, now enter."

Bata ji me ya faWa ba amma dai ta san yana nufin ta shigo ne, sai duk da haka ta kasa motsi daga wajen ta tsaya a tsorace kamar wani zaiyi motsi ta juya da gudu ta koma.

Kusan minti guda taba tsaye a haka kafin muryarsa ta sake ratsa kunnenta.

"Zaki yi dana sanin tsaiwa anan, idan na taso."

Sautin muryar tasa ya fito iri Waya dana kwanakin baya, ranar da ya gaya mata cewar idan ta sake ta bayyana wannan sirrin nasa da taji, ba ita zai taSa ba, mahaifiyarta da ta baro a ?auye zai sa a lahanta.

Don haka abinda bata gane ba yanzu shine meye manufarsa kuma yanzu akanta?

Wani yawun da bata shirya masa ya wuce a bakinta sanda ta tuno maganar mahaifiyarsa, maganar da tayi sanadin kawo ta cikin wannan ?ullin.

_"Ki saka min ido akansa sosai, shi yasa nake aika ki kuma nake saka ki gyaran Sangaren sa, duk wani abu da kika gani daban a dakinsa ki kawo min, ko waya yake yi ko kuma yana tare da abokansa ki tsaya ki saurara, dole yana ?ulla wani abu na sani Zainab, don haka idan banji komai daga gare ki ba, matakin da zan Wauka zai shafi har iyayenki!"_

Allah ya sani a yanzu bata san meye mafitar ta ba, ta san dai kawai ko waye zai fassara halin da take ciki da Gaba kura, baya sayaki.


***

"Ina jinka..."

Tattausar Muryar Ma'aruf ta faWa a cikin office Win, a cikin wayar da yake yi zaune akan teburinsa, hannunsa Waya na kan wata ?atuwar jotter da yake rubutu akai. Daga cikin wayar muryar Yakubu ta cigaba da cewa.

"Na sami former address Win sa da komai ance anan gidan ya zauna directly da suka taho daga Kano, amma kuma satinsu uku a gidan suka tashi.

Kuma na fahimci kamar wani abun ne yasa suka tashi don ance min cikin dare suka bar unguwar babu wanda ya sani sai mutumin da suke hayar gidan a hannunsa, to shima jiya munyi kusan 3 hours tare ya rantse min da ubangijinsu cewa bai san inda suka tafi ba, sai dai ya san mai taxi Win da ya Wauke su daga nan unguwar.

To da safen nan munje gidan mutumin amma kuma sai matarsa muka tarar ta, gaya mana cewa wai wasu mutane sun dauke shi haya zai kaisu wani ?auye a can hanyar Uyo, kuma wai kwana uku zasu yi sannan ya dawo dasu,to da har naui niyyar daukar mai mota naje can sai kuma banga tunda ba dadewa zaiyi ba ai zamu iya jiransa don kwana uku kawai, amma what do you suggest?"

Ma'aruf yayi shiru yana kallon abinda ya rubuta, idanunsa ya haska da nazarin da kwakwalarsa ke yi, sai kawai ya ajiye biron hsnnun nasa sannan ya shafo saman kan hancinsa.

"Kar ka bi shi, ka barshi sai ya dawo din, and idan ya dawo din kayi duk yadda zaka yi ka samu wani bayani daga gare shi, Dan Allah Yakubu ko nawa yake bukata ka bashi kawai ko nawa yace."

"Banda dai ko nawa Ma'aruf, don ina gaya maka mutanen nan idonsu a buWe yake game da harkar kudi."

Ma'aruf ya girgiza kansa.

"Mani da wani choice ne yanzu a harkar nan Yakubu, wani abu ya sake faruwa da idan banyi tackling Winsu gabadaya ba ban san ya zan sami kaina ba, saboda haka I'm willing to give everything, wallahi zan iya bada komai nawa idan har zan samu wani gamsashen bayani daga ko waye, so kar ka ja dashi dan Allah."

"Baka da matsala, zanyi abinda ya dace... Ka tabbata dai kawai zaka biya ni a ?arshen komai."

"Ka san bani da matsala."

"Na sani, shi yasa ma na yarda zanyi maka aikin."

Da haka ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba.

Ma'aruf ya ajiye wayar shima yana kallon rubutun da yayi a jikin jotter nan, bai san da yaya zai kira wannan bayanin na Yakubu ba, Nasara ko kuma akasin haka? Sai kawai ya koma da baya ya jingina da kujerar sannan ya rufe fuskarsa da duka tafukan hannayensa, fatansa guda Waya ne... Nan da kwana uku Yakubu ya iya samo wani kwakwkwaran bayani akan inda zasu sami Mr. Okafor.

"And guess what?!" (Ka canki wani abu!)

Faruq ya faWa da ?arfi yana banko ?ofar Office Win, sautin muryar tasa yasa shi Wagowa yana kallonsa.

"License daga wajen ?an sandan ya ?araso."

"Ka bari dan Allah." Ya fada yana kokarin tashi tsaye, ya ?araso ya mi?o masa takardar hannunsa da nasa murmushin shima.

Ya karSa a lokaci guda da idonsa ya shiga karanta abinda ke jiki.

"Ishaq ya aiko da nasu license din yau da safe, Wazu nayi printing dinsa, kaga mun hada komai kenan sai kawai mu fara aiki."

"And details din mutumin are ready?"

Ya tambaya bayan idanunsa sun bi dukkan rubutun jikin takardar da kallo har karshe,ya kuma tabbatar da dukkan abinda yake nema. Sai dai maimakon Faruq ya bashi amsar abinda ya tambaya sai kawai ya ja kujerar gabansa ya zauna, sannan yace.

"Naga alama hannunka a sake yake game da harkar nan, na dade ina gaya maka cewa ina son motarka, so yaushe zaka bani mu?ullinta?"

Ma'aruf ya girgiza kansa sannan ya koma ya zauna shima kafin yace.

"Zan iya bar maka gate Win gidana a buWe da kuma mukullinta a jiki, sai kazo da daddare ka Wauka."

"?arawo ka mayar dani kenan...?"

Maimakon ya bashi amsa sai yace.

"Dan Allah ka gaya min Faruq, bani da ha?uri akan wannan harkar ka sani."

Kuma sanin hakan yasa kai tsaye Faruq din ya ajiye zancen komai a gefe yace.

"Nayi convincing wannan mutumin ba RTL, wanda yaga saurayin da ya karbi kudin,wanda dai yayi mana bayanin kamanninsa, na gaya masa mun sami license Win ?ansanda da kuma na kotu, na gaya masa akwai tsaro sosai don haka ya yarda cewa zai bi mu yawon zuwa Prisons din mu nemi mutumin. Kaga babu ruwanmu da ma wani bayanin takarda,ya tabbatar min cewa yana ganinsa zai gane shi."

Murmushin da ya sauka a fuskar Ma'aruf a lokaci guda, irin murmushin da mutum baya shirya masa ne, irin murmushin dake fitowa tun daga ?asan zuciya a lokacin da farad daya mutum ya tsinci labarin mai daWin da bai taSa lissafinsa ba.

A yanzu tabbas ya yarda cewa zai kirga wadannan bayanai guda biyun da ya samu ne a matsayin nasara, don Allah ya sani har a ?asan zuciyarsa yake jin cewa watakila sun zo gaSar da zasu taka matakin nasara a tsawon shekarun da suka Wauka suna gwagwarmayar da bata da iyaka.

***

*?arfe huWu da rabi na yamma.*

A cikin Wakin Munaya, Amina tana tsaye a gaban mudubin Wakin kare da waya a kunnenta tace.

"Mun shiga cikin gida, ka taho ne?"

Muryarta ta fito a hankali, kuma duk da yaji ta Ma'aruf bai ce komai ba, yana kishingiWe ne kawai ta baya akan arm chair dake cikin office Win Faruq inda suka gama wani aiki.?

"Ka taho?"

Ta sake tambaya a hankali, duk da haka baice komai ba.

"Baka ji ba? Mun shiga cikin gida, na ?ulle gidan kuma."

Ya sake lumshe idanunsa kawai yana jinta, sakan daya, biyu ta wuce sai kawai tace.

"Sugar..."

Ba shiri yayi murmushi a lokaci guda sannan yace.

"Yanzu kike magana Doll, da ban san sa wa kike ba ai."

Ya jiyo ?arar murmushin ta a hankali daga cikin wayar.

"Shi yasa ka min shiru?"

Sai ya girgiza kamar tana kallonsa.

"Ki sake fada dan Allah, just say it once."

Tayi shiru kamar ba zata fada ba sai kuma tace.

"Sugar-Boofy..."

"Ya salam.."

Ya fada a lokaci guda yana dariya.

"Me gashina ya miki kuma?"

"Ba komai,yana maka kyau."

"Yana min kyau ko yana miki kyau?"

"Duka biyun." Muryarta ta sake fitowa a hankali tana jiyo hayaniyar dake tashi a can falon data baro.

Sai ya gyaWa kansa kafin yace.

"So yanzu ki gaya min, kwana nawa kenan da aka saka sunan?"

"Wanne suna?"

"Wanda kike fada."

Yana jiyo sautin wani murmushin nata kafin tace.

"Biyu, ko?"

Ya gyaWa kansa.

"Yes, biyu... Kenan ranar Asabar zamu yi suna?"

"Suna kuma?" Tambayar ta fito da mamakin dake nunawa a muryarta.

"Yes, idan an saka suna ba ana yanka rago baysn 7 days ba? Nima zan siyo bawa ranar Asabar mu yanka tare, kinga sunan ya tabbata kenan."

Sai kawai tayi dariyar dake fitowa mai dadi sannan tace.

"Baka gaya min ba, ka taho din?"

"You miss me that bad?"

Bata amsa ba yace.

"Shi yasa kika kira ni?"

Ta girgiza kanta.

"So nake in gaya maka muna cikin gida ne."

"Wajen Mami?"

Kai tsaye yayi tambayar da tun Wazu take dakon jiranta, sai ta girgiza kai tana cije lebbenta kafin tace.

"A'a muna wajen Hajiya."

"Baku je wajen Mami ba?"

Ta sake wani murmushin jin daWin nasarar da take fara samu ta wannan Sangaren, Waya daga cikin manya-manyan ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????takun da ta tsara a yanzu shine zata yi amfani da duk lokutan da Kilishi bata nan wajen kokarinta na haWa kan al'ummar gidan.

Kamar yadda Amma tace ne, kar ta taba bawa Kilishi damar da zata zarge ta don haka ta sani idan har ta fara yawan zuwa wajen Hajiya Maimuna a gabanta, dole zata iya bata wata damar da zata zarge ta da wani abun, amma idan har bata nan, to wannan ce damarta da zata yi komai ba tare da ta bawa ita kanta Kilishin damar ganin laifinta ba, tunda bata da hujjar da zata kafa a gaban kowa game da hakan.

Shi yasa a yanzu ta taho bangaren Hajiyar kuma ta kira har su Samirah ta hanyar dabarar cewa su koya mata wani cin-cin da suka dade suna bata labarinsa... Sannan tayi iya kokarinta da har Hamida ta saki jikinta da Hajiya Maimuna, a yanzu ma ta baro su ne Hajiya Maimunan na kokarin koya mata su alifun ba'un Win da tace mata bata san su ba.

Shi yasa ta kira Ma'aruf shima da dabarar da zai sa ya taho nan Win, don ta tabbata da kyar ne idan yazo gaishe ta tun bayan warkewarsa. Saboda haka kai tsaye ta girgiza kanta sannnan tace.

"Mami bata nan, mun shiga aka ce bata nan, shi yasa muka zo gaishe da Hajiya."

Ya gyaWa kansa kai tsaye alamun gamsuwa da hakan sannan yace.

"Ban taho ba, akwai aikin da zamu karasa da Faruq, ina tunanin sai bayan magriba ma tukunna."

Itama ta gyaWa nata kan.

"Allah ya kaimu, Allah ya baku sa'a. Zamu jira ka anan Win Insha Allah."

Ya san jam'in da ta saka yana nufin ita da Hamida ne, don haka ksi tsaye yace.

"Ni nace miki ku jira ni anan? I'm badly missing you Doll, ta yaya zaki hukunta ni da idanun Hajiya."

Tayi murmushi mai faWi tana kallon hannunta da yayi buWu-buWu da fulawa kafin tace.

"Ba hukunta ka zanyi ba ladan gaishe da ita zan sa ka samu."

Yayi murmushi a hankali.

"Na sani Allah ya saka da alkhairi, amma da gaske ina missing Winki, ki tsara sunan waWanda zaki kira tun yanzu, last time Amma kaWai kika yi ta kira..."

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un...."

Shine abinda ya fito daga bakin Amina babu shiri kuma ba tare da ta sani ba tana saka Waya hannunta ta rufe bakinta don bata san me zata ce ba bayan hakan, Ma'aruf yayi dariya sosai yana rufe idanunsa sannan ya sake cewa.

"Kar ki damu BabyDoll, da mun fara Printing kema zaki fara taya ni wannan hirar."

A lokaci guda yaji Wib, wayar ta katse.

***

*?arfe shida da rabi na yamma.*

A cikin duhun magaribar, Hajiya Kilishi ta gyara zaman ni?abin fuskarta tana kallon mutumin dake tsaye a gabanta, ta jinjina kanta a hankali sannan tace.

"Recording muryata yake yi?"

Sadik dake tsaye ya gyaWa kansa da murmushi yana kallonta.

"Tabbas, da bakinsa ya gaya min cewa yana da Cd's sun fi guda ashirin da yake nafe muryarki sannan kuma yana dasu a kwamfutocinsa gaba Waya, sannan ma ya gaya min duk hanyoyin da zai bi yaci galaba akan ki."

Murmushin da ya sauka a fuskar Kilishi a lokaci guda, irin murmushin da mutum baya shirya masa ne, irin murmushin dake fitowa tun daga ?asan zuciya a lokacin da farad daya mutum ya tsinci labarin mai daWin da bai taSa lissafinsa ba. Sai kawai ta gyaWa kanta a hankali tana cigaba da murmurshin sannan tace.

"Aikin ka yana kyau Sadik! Ka cigaba da bibiyarsa ka cigaba da kasancewa amininsa, ai bamu samu komai ba tukunna!"


***

_Kuyi ha?uri, ku jira faWuwar Kilishi, ?addarar labarin nan tayi al?awarin wanke muku zukatanku insha Allah. Mu bita dai zuwa talalar da ubangiji ke yiwa ire-irenta a doron ?asa. Sakayyar mai girma ce insha Allah._

_Wai me Ma'aruf yake nufi da Printing ne?_=??

_kun fara kaunar labarin Zainab da Jawad?_

_Ku gaya min Awwalu ya shiga uku.!_=??>?#?

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
#FararWuta.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*12*

~~~~~~

_ You don't always have to make sense of it all, sometimes you just follow your happiness._ _-Unknown._

***

*Bayan wasu kwanaki.*


"Ayiryiryiryiriiiiiiiiiii.....!"

Wata tsohuwa ta rsngaWa guda a lokaci gyda da jama'ar dake dawowa daga wajen daurin auren suka shigowa gidan, mazs ne fal samari da dattijai suna ta sauka daga motocin dake shigowa suns parking a harabar compound din, kusan kowannensu sanye da fararen kaya sai fara'a suke yi yayin da ksmshin turarensu ke gaurate iskar wajen yana haduwa dana matan dake waje suma cikin kwalliyarsu da kuma wadanda ke fitowa don tarar angwaye biyun dake zagaye fal cikin abokansu.

Kidan algaita da kuma kirari ga angwayen dama guda kawai kake ji a tsayar hayaniyar da wani baya jin wani.

Daga cikin morarsa wadda yayi parking a can gefe bayan ya shigo gidan, Jawad ya tsaida idonsa akan screen din wayarsa yana kallon lambar da har a bayan kwakwalarsa bai taba tunanin ganin kiranta ba.

Barbiee ( Rukayya.)

Missed call daya ne, daga shi babu kari balle kuma sako ya biyo baya, ya cije lebbensa a hankali, mamaki yake na yadda skaui har yanzu nambarta take cikin wayarsa s tunanimsa ya goge tun a ranar da ya baro waken da suka hadu na karshe, amma kuma sai ya tuna cewar yayi saving nambar tata ne fiye da sau biyar a wayar tasa da garafai daban daban.

Don haka kai tsaye tafi zuwa kan nambar, ya danne ta ya goge, sannan ya koma vikin layin contact din nasa, ya nemo dukkan harafan da yayi saving nambar tata ya goge su gabaWaya.

_"... Ka taimaki kanka ka manta?dani Jawad.."_

Haka tace, haka ta gaya masa, dune harafan da suka fi kowanne Wagawa a cikin maganganun da ta fada masa, sune harafa da a kowacce rana zuciyarsa ke maimaita masa su fiye da kirgensa, kuma tun daga wannan lokacin zuciyar tasa ke neman abun da zai sa ta manta da ita din, kuma Allah ya sani ya gwada tarin abubuwan da bai san iyakarsu ba tun daga wancan lokacin a ciki har da ?udirinsu shi da Haro na shirin daukar fansa akan Ma'aruf, amma duk cikin tarin abubuwan nan, babu wanda yake jin yana tafiya har cikin zuciyar tasa kamar yarinyar nan.

Tsanar da yayi mata mai yawa ce a kwanakin baya, amma yanzu baya jin hakan ko kadan, wani abu yake ji da bai ma gama lissafa shi ba, abinda ya sani kawai shine, duk sanda zai gan tan zai ji kawai yana son ta cigaba da kasancewa a wajen, shi kadai ya san yadda abinda ke zuciyarsa ya dinga bin iska shekaranjiya daya tsare ta taci abincin nan a Sangaren sa, kuma bai san me yazo kansa ba sanda ya ri?e hannunta ya maida ita baya lokacin da take kokarin fita shi kuma ya hango wani Wanuwansu Ahmad da yazo zai shigo Sangaren nasa.

Ba abinda zai faru don ya ganshi da ita, ba abinda ya isa yace, amma haka kurum yayi saurin kamo hannunta ya dawo da ita ciki, kuma itama hango shin da tayi yasa bayan ya dawo da ita, ta shige bayan ?ofar ta tsaya jikinta na rawa.

Kuma bayan ya sallami Ahmad din ma da kyar ta fito, ta tsorata sosai bai san me yasa ba, watakila shi yasa tun wannan lokacin bata kara bari sun haWu ba, tun wancan satin ske bikin amma sau daya ya ganta kawai daga windon dakinsa taba hoye dawani yaro sannan ga wata yarinya kuma a hannunta tana yi mata wasa.

Kwankwasa kofar gilashin motar da akayi ya katse tunaninsa, ya juta yaga wani ?aninsa ne Mukhtar, sai ya zuge gilashin ?asa a hankali, tarin hayaniyar wajen ta shiga kunnensa a lokaci guda.

"Nace dan Allah akwai mutanen da zaka Wauka a motarka ne?"

"Zuwa ina?" Ya tambaya da mamaki.

"Wajen reception din, yanzu da angwayen sun fito za'a juya ai."

Sai kawai ya girgiza kansa.

"Bana jin zan je, sai dai in baku motar."

"Thank you so much bro, su Na'im zan dauka dama wallahi na rasa mota."

Da haka ya fito, ya mi?o masa mukullin motar sannan ya nufi cikin gidan, a ?a'ida bangarensa ya kamata ya tafi ya kwanta don tunda aka fara hayaniyar bikin ya manta yaushe rabon da ya samu wani isasshen bacci ba, amma haka kurum tunaninsa ya gaya masa cewa ya tafi bangaren mahaifiyarsa ya nemi abinci, babu mai kawo masa a cikin wannan hayaniyar, ba tunawa dashi zasu yi ba ya sani.

Ya isa Sangaren yana fara cin karo da kanmensa mata da kuma tarin kawayendu fal a falo, har yanzu ya kasa lissafin yadda kowa ke dokin wannan bikin, shi mutun daya kawai ya gaiyata wani Wan office Winsu, shima ba gayyatarsa yayi ba akan table dinsa ya ga katin yace masa shima yana da Waurin aure a masallacin kuma a ranar don haka zai zo, kuma bai ganshi ba ma.

?awayen su Khairat din suka hada baki wajen sirranta muryoyinsu su suna gaishe shi, ya amsa jai tsaye sannan ya nufi wajen wasu cousins din nada mata dske wajen dining, a cikinsu har da Ibrahim wanda aka yi masa maganar ya nemo nasa aiki, bayan sun gaisa da kowa suka shiga magana da Ibrahim din akan interview din da zai zo yayi, yana fada masa abubuwan da ya kamata ya duba.

Kuma sanda Ibrahim din ke masa wani bayani ne ta fito daga dakin, Zainab... Hannunta dauke da wani ?aton tray da ta ciko tarin plates da kuma cokula a ciki.

Ta yo hanyar cikin falon alamun fita zata yi, daidai sanda wata mata da bai san wacece ita ba ke cewa.

"Zainab har yanzu kina nan? Kowa ya shirya ke baza ki je ki shirya ba gashi har ?an Waurin aure sun dawo..."

Da murmushinta a fuska tace.

"Maman Nasir yanzu zanje, kwanukan nan na tsaya debowa idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login