Showing 120001 words to 123000 words out of 132946 words

Chapter 41 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1117

mijinta ya san da hakan... Ya san abinda ta tura Rukayyan yi a Niger kuma tare da ?awarta. Don haka bata ce komai ba har suka bar asibitin suka kawo ta wannan.

To a yanzu Ashraf din ya dame ta da tambayar wacece Hajiyan Sudan din da Rukayyan ke kira, ta gaya masa cewa itama bata san ta ba amma kallon da yayi mata bayan ta gaya masa hakan ta san ba na yarda bane.

Ta sake kallon Rukayyan, ciwonta da sauki ba kamar yadda suka zata a farko ba, mild stroke ne mutuwar barin jiki wanda likitoci suka tabbatar masu da cewar ba zai dauki lokaci ba zata warke ta koma daidai idan har za'a bi dokin da da kuma kaidojin da suka dace... Ita ta sani dama, ta san Allah ba zai jarraba su ta wannan hanyar ba, kyawun yarta haWe kuma kyawun jikinta wani abu ne da ba zai nakasa ba.

Don haka hankalinta ya dan kwanta ta yadda bata hango komai sai komawarsu Nigeria don su cigaba da jinyarta acan ba tare da asirinta ya tonu ba.

Lokaci ya nuna karfe biyu daidai yana tuna mata da sallar azahar din da bata yi ba, don haka ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala sannan ta shimfida slaya a gefen gadon ta tayar, zuciyarta cike da fatan kafin idarwar tata, Ashraf ya dawo tare da Ahmad din da yaje daukowa daga airpot.

Ai kuwa sai fatan nata ya karbu don a sallamar raka'a ta karshe su ma suka yi sallama suka shigo dakin.

Ta amsamusu a lokaci guda da ta fahimci rashin fara'ar dake kwance akan fuskarsu... Ahmad din ne ke gaishe ta yayin da Ashraf ya samu kujera ya zauna fuskarsa na numa tsananin bacin ran da ta dade rabon da ta ganshi a fuskarsa.

"Me ya faru? Wani abu ne ya faru kuma?"

Ta tambaya tana kallon dukkanninsu... Kuma Ahmad din dake gabanta bai ce komai ba sai kawai yasa hannu ya ciro wata takarda daga aljihunsa ya dora akan sallayar da take kai.

"Sakon da Daddy yace in kawo miki ne."

A lokaci guda zuciyarta ta buga a kirjinta, bata san meye a cikn takardar ba, bama tayi tunanin menene din ba, amma daga yanayin fuskokin yayan nata kadai ta san ba abu ne wanda zata so shi ba, dn hak ta yankewa kanta nisan taraddadin, ta mika hannunta a hankali wanda ke rawa ta dauki takardar, kuma tun kafin ta kai ga buWe ta, taji kwalla ta na neman cika idanunta yayin da kwakwalar ke gaya mata cewa ita ta riga ta karbi sakon tun kafin ma ya iso.

A rubuce a ciki,? Hajiya Nafisa ta tadda kalaman da sune abu na karshe da kunnen kowacce mace zai so yaji su daga sautin mutumin da take raba rayuwarta tare dashi!

***

_?addarar dake jiran labarin nan a gaba ya danganta ga amsar da Hajiya Kilishi zata samu daga bakin Wansandan nan...._

_Me kuke tunani?..._

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*25*

_They tell you to be grateful for what you have, but you are also allowed to be sad for what you have lost..._


~~~~~

*Bayan watanni Shida.*

**
*Kano.*
*Central Prison.*
*03:00pm*

Ruwan ya cigaba da dukan rufin dakin da wani irin ?arfi fiye da kodayaushe. Karar tsawa da ake yi lokaci-lokaci tana cika iska da sautin da duk karfinsa baya disashe tarin surutun daje cikin dakin, tarin surutun dakin kurkukun wanda yake cike da fuskokin mata kala-kala. Manya -manya da yara farare da bakake, dattojai da yanmata wanda kowanne a cikinsu yake cigaba da rayuwarsa daidai kamar babu wanda yake da digon koda memory guda na wani abu daga bayan dogwayen katangar da suka zagaye su, kamar nan din shine mafari kuma farkon rayuwarsu, kamar basu san akwai wata duniya dake wanzuwa bayan su ba.

Rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kadan, wannan shine abinda Kilishi je maimaitawa a cikin kanta da fitowar kowacce rana da kuma faduwarta. Ta yarda rayuwa bata da adalci don babu abinda ke saka ta tsayawa, komai girmansa kuma komai kankantarsa ba abinda ke tsaida ita kamar dai ruwan daje zuba a yanzu, abubuwa suna cigaba da tafiya ne ba tare da wani ma yaje ko kusa da wajen da zai ji labarinka ba.

Damina ta dade da tsayawa ta yadda kusan kullum ake kwara ruwan dake daukar awanni, kuma a duk lokutan da ruwan ke sauka, Kilishi na samun waje ne dab da wata yar karamar taga dake can sama ta zauna, ta zauna tana kallon tasirin zubar ruwan da kuma nauyinsa da take ji a zuciyarta, tana ayyanawa kanta cewa hawayenta ne wannan ke zuba, don irin kukan da ya kamata tayi kenan tunda a kirjinta dama idanunta babu danshi ko kadan balle ayi tunanin hawaye.

Ta kan so ayi ruwan lokacin da suke fita waje don ta zauna a cikinsa ya sauka a jikinta, ya sauka akan fuskarsa ta yadda zata ji sosai kamar hawayen nata... Idanunta a tsaye kyam suna shsida kamannin da ta sani cewa ba nata bane, ba itace wannan Kilishin da tayi wata rayuwa da zata rantse da ubangijin da ya halicce ta babu wata mace a cikin kurkukun nan da tayi makamanciyarta.

Ba itace wannan Kilishin dake samun komai a zama daya da zuciya da kuma kwakwalarta ke sama mata mafita ba, sannan ba itace wannan Kilishin da ta shafe tsawon shekaru wajen gwagwarmayar samawa karshen rayuwarta tare da yayanta wata daddadar rayuwa da bata ko misaltawa ba.

A yanzu ita wata sabuwar halitta ce kawai, wata sabuwar halitta da ta rasa kowa kuma ta rasa komai, amma kuma zuciyarta ta kasa yarda ta karbi hakan, don idan ma zata yarda tana tunanin ya kamata ace ko da rabin mutanen duniya su jajanta mata, amma ba wai rayuwa ta cigaba da tafiya tamkar babu wani abu da ya faru ba.

_A tuhume ta akan kisan Wana kawai yallaSai..._

Tun da aka fara wannan tashin hankalin, wannan maganar ta Baffa ita kadai ce abinda ya fitar da hawaye daga idanunta bayan maganganun Ma'aruf, yace a ture dukkan wasu laifukanta a gefe, a tuhume ta kisan Jamal kawai wanda ta san yayi haka ne don ya tanadar mata wani abun daban.

Ko a lokacin da aminiyarta Salamatu ta baiyana a gabanta da tare da yanuwanta game da zancen raba ta da dan ta tsawon shekaru bata ji wsni abu sosai ba,don me take tunanin? Awwalu zai cigaba da lullube duk wani sirri nata da ya sani ne? Bakin cikinta daya ne ma da ya zamana akace Salanatun taga Wan nata, wani abu da duk da mamakin da ya bata sai da taji ciwonsa har cikin kirjinta.

Salamatu bata taba taya ta mugunta ko guda daya ba,hasali ma ta kan kushe mata wasu idan ta kawo su, amma duk da haka tare suka faro tafiyar tana gaya mata dukkan sirrinta da kuma abinda take ciki don haka ko yaya ne yaci ace itama ta karbi nata kamashon bakin cikin, ba'ace ita da Awwalun dai sune kadai zasu dandani zafin shari'ah ba.

A lokacin da dansandan nan yaki karbar tayin kudin da tayi masa, a lokacin da ya kalli nambobin da ta rubuta ya dago ya sake kallonta sannan ya girgiza kansa, a lokacin wata wuta ta kunno a cikin kirjinta, wata wuta dake zafi tana kona duk wani ragowar emotion da take dashi tana kuma kara zafin kunci dake cikin zuciyarta wanda karara yake nuna mata cewa da gaske ne tata ta kare babu wata sauran mafita kuma.

Daga wannan lokacin ta koma kamar wata gunki da aka sassaka ko kuma karfen dake motsi kawai, numfashi kawai take tana kallon tarin mutanen dake zuwa koyaushe wajen mata tambayoyin da bata ko fahimtarsu, ciki har da ?an jaridar da tayi zaton zasu watsa labarin nata zuwa kusufa-kusfar da zai sa duniya ta tsaya wajen jimanta mata, amma kamar yadda tace rayuwa bata da adalci, ba abinda ya faru!

Bata yi magana da kowa ba sai da akaje kotun sannan ta amsa dukkan tambayoyin alksli kai tsaye babu wani musantawa ko kuma kokwanto, tana bayar da amsar tana kallon idanunsu Baffa, Baba Usman, Ishaq, Abdurrahim da kuma tarin wadu yanuwanta da acikinsu har da mahaifin Amina, Alhaji Sulaiman.

To don me ba zata amsa ba, ai ba su kawo wanda zasu daure ta da jijiyoyin ta a jikinta ba, basu kawo wanda da yana wajen ta sani bakinta ba zai taba budewa ta amsa laifukan da aka zaiyano a cikin kunnensa ba... Ma'aruf!

Ya sani, ya san komai, ya san komai din da ya zamana ta san baya cikin haiyacinsa ma a lokacin, amma duk da haka da ace yana wajen, yana cikin kotun nan a lokacin da ake sauraren shari'ar, zata rantse da ubangijin da ya halicce ta cewa ko alkalin zai ce a kwantar da ita ana yankar naman jikinta Wai-Wai da Wai-Wai, ba zata taSa iya amsa wadannan laifukan a gaban idon Ma'aruf ba.

Amma har Baffa tana kallonsa ne kawai tana amsawa tare da tunanin abinda zai ji amma ba wai ita ba, har aka gama shari'ar aka yanke mata hukucin shekaru goma sha takwas bata jin ko da wucewar sakan guda taji nauyin wani daga vikin mutanen dake wajen nan.

A yanzu ma ?a?an ta kawai take tunawa, tana jin yadda rashin ganinsu ke Sangarar da wani abu a cikin zuciyarta, yanuwanta da yawa sun zo, musamman wadanda take yiwa alkhairi, wasu ma bata ko fita ganinsu saboda bata ga abinda hakan zai tsinana mata ba.

Don haka a yanzu rashin ganin yayan nata shine abu mafi tashin hankali da take fuskanta bata ko lissafin shekarun da zata kwashe a cikin wajen nan,don gani take kamar an fade su ne a kotun nan kawai, kamar an fade su ne kuma an rubuta amma baza su kasance a gaske ba... Gani take kamar zata iya fita, kamar idan ta yun?ura zata samu hanyoyin da zata fitar da kanta.

Amma matsalar shine har yanzu zuciyar tata ta kasa fahimtar komai a wajen na balle har ta fara tunanin hanyoyinta,? Baffa yana kassarata da wucewar kowanne lokaci a duniyar nan wajen hana ta ganin fuskokin ?a?an ta, ita Kilishi ce, mai zurfin tunani da hangen nesa, shi yasa a lokacin da yace a ture dukkan wani laifi a hukunta ta akan abu daya kawai ta zubar da hawayenta.

Shi mijinta ne, ta san halinsa tsawon shekaru,ta san yadda yake iya hukunta mai laifin dake hannunsa cikin salama ba tare da kowa ya sani va, hukuncinsa mai sanyi wanda zai daskarar da jinin jikinka hankali kwance yadda duk ihunka babu wanda ya isa ya ji ka, shi yasa yake da kai zuciya nesa a komai na rayuwarsa, da wuya kaga ransa ya baci akan wani abu don idan har ya bacin to shi kansa ya sani cewa hukuncin da zaiyi daban ne,ta san wannan... ta san wannan tun a shekarun farko data aure shi.

Shi yasa zuciyarta take rabewa da kowanne motsawar lokaci idan ta tuna hakan, idan ta tuna yadda rayuwar kowa ke cigaba da tafiya babu ita kuma kamar ba'ayi ta din ba, don yanuwanta sun gaya mata cewa har sake gini anyi a gidan an rushe bangarenta.

Mamakin yadda rayuwa ke juyawa dan adam baya a lokaci guda shi ke dada cinye ta, kamar badu saba ba, kamar ba itace mai yarje mata komai ba, kamar ma bata santa ba, ace komai ya ?are a lokaci guda? Komai din da zai hada har da ya'yanta, banda wannan tarin dukiyar da ta shafe shekaru tana ajiyarta, shi yasa a kullum take fada tana karawa rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kankani....

Tana zaune ne kawai a yanzu ba tare da wata mafita ba, abu biyu kawai take hasashe shine watakila idan har ta mike da ?arfinta da kuma dabararta ba lallai ne ta kai wannan shekarun da aka gindaya mata a kotu ba, amma kuma matsalar shine bata da karfin, a kullum kuma a kowanne wayewar farin Allah Baffa yana kara kassarata ne da hukuncinsa na hana ta ganin yayanta... Shi yasa duk yadda ta kai ga ture wani tunani a zuciyarta tana ji kamar zata yarda dashi akan cewa.

Karshen tika tika dole TIK ne! Dole ne ta yarda cewa komai ya kare mata, kuma dole nrme ta yarda da abinda Ishaq ya kalli cikin idanunta ya fada mata a ranar da za'a kawo ta gidan nan...

*'Wata shari'ar sai a lahira Mami...!'*

Rugugin tsawar da ake yi ya cika iska a lokacin, walkiya ta haska tar ta kuma haskawa a cikin duhun hadarin, sai kawai ta sake Waga idanunta tana kallon zubar ruwan ta cikin tagar Wakin, ta cikin hayaniya da kuma dararrakin mutanen dakin, kuma ba tare da tayi zato ba a lokacin wata guntuwar ?walla ta cika idanunta tana gangarowa kan fuskarta, wannan shine karo na uku da taji dumin hawaye a kan fatarta, kuma wannan lokacin shine karo na farko da tambayar da? ta?i bari ta yiwa kanta tun a zamanin farko ta Warsu a cikin zuciyarta... Wannan tambayar da take gujewa, tambayar da bata taSa lissafa ta ba balle ta yi tunanin matsayinta na Kilishi zai kai ta ga yinta....

Ta yaya zata mayar da rayuwarta baya shekaru goma da suka wuce?

Dana sani....! Yau Kilishi ce da dana sani!

Dana sani a lokacin da komai ya kure!

Dana sani irin wadda kowanne musulmi ke gudu a duniyar nan!

Dana sani tun ta duniya kafin a je ga ranar da ?afafunta zasu dur?ushe a gaban ubangijin da shaidan ya janye hannunta ga barin umarninsa!

Abinda Kilishi bata sani ba ma shine kamar yadda Ishaq ya faWa ne... Wata shari'ar sai a lahira!

Hakki yana rama kansa ne cikin halaye biyu... Tun a duniyar da kuma lahirar dake jiran kowanne bawa!

Zata karbi abinda yake nata a yanzu, kuma zata karbi abinda yake nata a can, ga rayuwar kurkukun da bata fara ganin komai a cikin ta. Gata nan... ita Win ce dai Kilishin da take ce, da lafiyarta da karfinta har ma da tunaninta da komai da take takama dashi, kuma a cikin duniyar da take ganin ita da ita aminan juna ne ta kowacce hanya, sai gashi tasirin wasu katangogi kaWai!

Tasirinsu kaWai ya hana mata dukkan abinda take takama dashi da kuma iyawarta, tasirin shari'ar duniyar kaWai, ba ma akai ga mutuwa ba, balle kwanciyar kabari ko kuma tashi a gaban Mahaliccin da ta bijirewa da dukkan iyawarta!


***

*Kano.*
*Mai ?a?a Street, Bawo Road.*
*04:30pm.*


_So here we stand in our secret place_
_Where the sound of the crowd is so far away_
_You take my hand, and it fees like home_
_We both understand, it's where we belong..._

An dauke ruwan, amma har yanzu garin da danshi, iskar da take kadawa mai sanyi ce, Zainab tana jinta akan fatar ta da kuma wuyanta yayin da mai kwalliyar dake gabanta ke ta aikinta na fente fuskarta, sassanyar wakar qmwestlife ta queen of my heart kuma na tashi daga cikin Mp3 din studion...

"Kiki, miko min brown liner nan..."

Mai yin kwalliyar ta fadawa wata yarinyarta dake gefe, Zainab ta bude idanunta bayan Aysha ta juya karbar liner, idonta ya gane mata wata ita din daban a cikin mudubin dake kallonta, wata kyakkyawa mai kama da ita din da da take ganin kamar ba ita ba, powder da aka saka da komai ta bi fatar jikinta tsaf ta kwanta tana fito da kowanne tsini da lankwasar sa, musamman hancinta da taga ya ?ara tsawo fiye da yadda da ta sanshi, ga kwsllin da ya fito da idanunta tar yana shaida hasken ?wayar cikinsu.

Gabanta ya fadi ya kuma faduwa hannunta yayi nauyi yayin da surutun da yan mata biyun dake bayansu ya cika kunnenta, ds kuma muryar Ameerah dake waya can gida akan a kawo mata takalminta da ta manta.

Can gida, can gida yana nufin gidan Hajiya Salamatu mahaifiyar Jawad da kusan komai na harkar bikin da ake yi yake hannunta da kuma yanuwanta.

Watanni shida kenan da Jawad ya same ta a cikin tashar nan, watanni shida kenan da rayuwarta ta canja, don tun daga wannan lokacin tun daga wannan ranar abubuwa suka fara sauki a rayuwarta, Jawad ya mayar da ita har gida can wajen yanuwan mahaifiyarta, inda baya nan aka sha artabu tare da mijin mahaifiyarta akan cewar ya barta ta Sata, babu wanda ya nuna masa cewa tana can hatta dansa kuwa Nura, sai da hankalinsa ya tashi ya fita daga haiyacinsa bakiWaya ya tabbatar ana shirin kaishi kotu sannan yazo ya bada hakuri.

A lokacin ya san tana wajensu, kuma ga mamakin kowa sai ya faWi maganganu san ransa sannan ya tashi ya tafi.? Kuma tun daga lokacin tun daga lokacin da hankali sa ya fara kwanciya, sannan Jawad din ya koma Abuja ya dawo bayan wasu kwanaki, sai ya zama babu abinda ake yi sai maganar bikinsu wanda ba'a samu wata matsala da yan'uwan mahaifiyar tata ba wajen amincewa.

Kuma sai bayan nan ne sannan ya shaida mata dukkan abinda ke faruwa a tasa rayuwar, abinda ke faruwa tun a lokacin da ya Wauko ta daga Abujan nan game da rikicewar rayuwarsa da kuma yadda Allah taimake shi ya samu mahaifiyarsa a cikin ?an?anin lokaci, dama babban abin manakin na cewar tsawon rayuwar tasa da ya shafe tun daga yarinta a gidan yayan mahaifinsa? yayi ta ba wai a wani waje da yake bare ba.

Ta daWe tana ma?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 makin kasancewar hakan, sai dai duk mamakinta bai kai na yadda har a lokacin Jawad ya dage akan aurenta ba, don har a cikin yanuwanta daga mazan har matan waWanda basu furta cewa tayi sa'a ba kadan ne...

Ita kanta ta sani, ta san hakan ne kawai suna tuna mata ne da irin sa'ar da tayi, shi yasa bata da wa ta cewa a dukkanin abinda ake yi, don ta sani bata da wani gata a yanzu idan ba Jawad ba, ko su yanuwan nata da suke faram-faram da ita don? na doki ne da kuma tausayawa rashin mahaifiyarta da tayi da kuma wahalar da ta sha a hannun mijin mahaifiyar tata, sannan bayan haka ma ta sani cewa da yawa suna mutunta ne kawai saboda ganin Jawad Win.

A can garin nasu aka daura auren, yanuwansa da yawa sun je har dasu Hajiya Mardiyya daga can Abuja da kuma dangin sabuwar mahaifiyar tasa, don haka fadar tarin mutanen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login