Showing 48001 words to 51000 words out of 132946 words

Chapter 17 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1121

masa aikin kafin ta tunkari Amina da hodar da Awwalu zai karSo mata a lagos, don ta haka ne Aminan zata sami kwarin gwiwar yi mata aikin.

Da taga komai ya fara kuma, zata san ta yadda zata yi ta siya musu gida, wannan zai bawa Aminan ?warin gwiwar cigaba da yi mata aikin, sai kuma ta biya musu kudin aikin hajji ta kuma basu adadin kudin da zasu iya bu?ata, idan tayi hakan ta tabbata babu makawa Amina zata cigaba da yiwa yarinyar amfani da hodar har lokacin da idanunta zasu rufe gabadaya.

Ta gama wannan tsarin ta ajiye shi a gefe sannan ta jawo na Sangaren sauran adadin kudin da take son ta lahanta kamfanin Bakori dasu.

Gobe litinin, Ma'aruf zai koma aiki, ta san zai cigaba da bincike akan mutumin nan da ta tabbata yanzu an gaya masa kamanninsa kuma sun fara nemansa, baza su taSa ganinsa ba kamar yadda har yanzu basu iya gano inda wannan Mr. Okafor yake ba don haka a ajiye hakan a gefe, ta san Ma'aruf, ta san cewar wannan abin ba zai sa ya tsaya da aikinsa ba, zasu cigaba da aiki ne kamar wancan lokacin kuma suna cigaba da binciken su, don haka meye kwangilarsu ta gaba?

Ta jawo wani file ta buda cikinsa, ta dauko takarda ta karanta, sunan wani kamfani mai suna Rotel& Co ta shiga idanunta, sai tayi wani murmushi mai fadi, ta san kamfanin don lokaci bayan lokaci suna yawan yin aiki dasu Baffan, kuma basa wasa da harkar biya ko shi Baffan ya gaya mata.

Lissafinta yayi kwana zuwa wani lokaci na gaba, lokaci mai zuwa, lokacin da har su Ma'aruf zasu gama yi musu aiki azo gabar karbar kudi, idan zata lissafa ba zai fi cikin wata guda mai zuwa ba, don haka me zata yi a wannan lokacin da zai dauke hankalin su kudin su shigo hannunta?

Wace hanya zata bi ta karbi kudin kuma wace hanya zata bi ta fara karkato hankakin ?a?anta don ta sami wannan kudin ta san ta kassara kamfanin Bakori kenan har abada, babu ta yadda za'ayi su iya tasowa tunda bata sani ba amma zata iya rantsewa cewa a yanzu da ragowar kudin Ma'aruf zai yi amfani wajen karbar wannan kwangilar, to idan suma suka narke me kuma zasu sake samu suyi wani aikin.

Ta ajiye wannan lissafin a gefe ta shiga lalube a cikin kwakwalarta wajen neman mafita, a lokacin wani tunani ya haska a cikin kanta cewar zata iya samowa kanta hanya guda Waya da zata cimma wadannan abubuwan guda biyu, hanya daya da zata dauke hankalin kowa kudin nan su shigo hannunta kuma hanya guda da zata sa ko ?a?anta baza su ja da ita ba idan lokacin tafiyarsu yayi...

Hanya daya,

Daya kacal!

Jifan tsuntsu biyu da dutse daya...

Hanyar da zata ?arkare komai kuma zata kawo ?arshen komai...

Hanya Waya...

Jigo kuma ginshi?in komai...

Bango...

Meye Bangonsu?

Meye Bangon da zai jijjiga kowa?

Me zai rikito da komai?

Meye abinda zai taSa kowa ya Wauke hankalin kowa?

Meye zai taba har zuciyar ?a?anta su yarda cewa basu da wani zabi banda nata?

Idan har za'a je ?arshe, to dole ne ta tabo komai tun daga tubali.

Meye tubalin?

Meye mafari kuma ginshi?insu?

Meye Bangon da kowa ke jingina a jikinsa?

Baffa....!

Tabbas Baffa!

Alhaji Muhammad Mansour Bakori.

Mutuwarsa zata zo daidai da rikicewar kowa a gidan kuma daidai da samun nasararta!

Mutuwa...

Ta Wan tsaya tana nazari a cikin kanta amma kuma sai wani tunanin nata ya kore wannan nazarin, ta taSa sonsa ne? Tun da suke tare taba jin wani abu mai kama da son sa koda kuwa Wan burbushi...

Mutum Waya zuciyarta ke so, mutum Waya zuciyarta ta taSa russuna akansa, kuma mutum Waya ne ruhinta ya taba kallo da wannan sigar, Ma'aruf...

Amma kuma son nasa yazo mata ne ta haramtacciyar hanya, haramtacciyar hanyar da duk kaifin basira da kuma wayonta bata isa ta mallake shi ba. Da wannan karyayyiyar zuciyar take rayuwa a kodayaushe kuma da ita take ganin yadda wasu saSanin ita ke samunsa.

Shi yasa take yin duk abinda ta san zata faranta masa kuma zata zauna a zuciyarsa, kuma take kore dukkan wani abu da zai Wara matsayinta a ransa. Ta yarda da wannan, ta yarda iya shi kaWai zata samu, ta yarda shi kaWai ne nata, shi yasa take kare hakan da dukkan iyawarta.

Ba zata taSa bari wani abu a duniyar nan ya keta ta a cikin zuciyarsa ba... Duk sanda ta tashi tafiya kuma zata barshi ne da ragargajajjiyar zuciya irin tata ta yadda ba zai taSa samun wata dama da wani abu msi kyau zai sake tasiri a ransa ba.

Zata kashe mahaifinsa,

Zata nakasta ?arsa,

Zata kassara jarin kasuwancin da suke ta?ama dashi,

Zata raba shi da Aminar da yaga kamar hankalinsa ya fara karkata zuwa kanta.

Idan tayi haka, me ya isa ya sake ratsa cikin zuciyarsa kuma?

Dole ne kowa ya biya bashin rashin samunsa da ba zata yi ba.

Hannunta ya Wauki wani biro a gefe, a saman takardar Rotel&Co ta rubuta talatin ga watan yuli.

30th July.

Wasu abubuwan zasu fara kafin wannan ranar, wasu abubuwan kuma zasu faru ne a wannan ranar.

Abinda Kilishi bata sani ba shine, wani lokacin Bawa da hannunsa yake rubuta lokaci da kuma ?addararsa!

***

"Ni ba jahili bane Sadik, na gaya maka nafi shekara goma ina tanadi akan matar nan. Da ni take shirya komai, na san duk irin butulci da kuma cin amanar da take shiryawa makusantan ta, to ni waye da zan yi tunanin cewa zata ware ni?"

Awwalu ya faWa yana kallon abokinsa Sadik, suna zaune ne a tsakiyar falon gidan Awwalun, inda a kodayaushe Sadik Win ke zuwa suna hira.

"Me kake tarawa? Kana tunanin abubwan da kake tarawa sun isa su tozarta ta a idon mutanen nan, kai da kanka fa kake bani labarin irin yardar dake zuciyarsu game da ita."

Awwalu ya jinjina kansa, ya dauki kwalbar lemon dake gabansa ya kurSa sannan yace.

"Ina da CDs na recording Win bayanan da take yi min sun fi guda ashirin Sadik, dukka a cikinsu bayanai ne masu mutukar muhimmanci na abubuwan da tayi, a wayata nake recording sai in bayar a mayar min dasu cikin Cd, sannan ina dasu a duka computers dina ma.

Kuma na dade da sanin cewa sune sanadin arzikina, don ni ba mahaukaci bane da ina kallo zata sami waWannab ma?udan kuWaWen kuma in tsaya kawai ta gutsirar min wani abu a ciki? wane tabbaci ma nake dashi na cewar zata bani Win? So hanyarta take gyarawa kawai nima ina gyara tawa."

A lokaci guda Sadik ya Wuro wani zagi yana dariya, sannan ya jinjina kansa yana faWin.

"Sh*gen duniya! To amma baka tsoron idan kayi mata wannan barazanar ta saka a far maka kaima?"

Awwalu ya kalle shi sosai sannan yace.

"A wannan Sangaren matar nan daki?iya ce Sadik, don duk wadanda ka san suna mata aiki ni nake nemo su. Shi yasa nayi mamaki a yanzu da har ta sami wasu a Mexico tayi cinikin hodar nan dasu ba tare da na sani ba, kaga hakan ya nuna min cewar ta fara shirin juya min baya da ta sami wani connection Win.

Allah yaso dama zuciyata a tsaye take tun daga lokacin da ta shigo da yarinyar nan cikin wannan al'amarin, don na sani babu ta yadda za'ayi mu'amala mutum uku dole sai biyu sunfi jituwa... Kaga kenan da banyi wa kaina wannan tanadin ba ai na shiga uku."

Sadik ya jinjina kansa kafin yace.

"To me kake so? Fiye da abinda zata baka?"

Wannan karon dariyar ta Awwalu ce, ya ?yal?yala ta iya son ransa sannan ya dago ya kalle shi.

"Duka abinda ta tara Sadik, Duka!"

Ya fadi kalmar karshen yana daga murya.

"A irin abinda ta shuka, cin amana da kuma butulcin da tayi, bata cancanci taci kuWin nan ko ?wandala ba Sadik, ban ma san me zata yi dasu ba, matar nan ta tsufa sannan ?a?anta duka mata ne, ub*n me zata basu da zai fi ta aurar dasu, kawai dai an halicce ta ne da wani irin son zuciyar da ban san ta yaya zan misalta shi ba.

Ni namiji ne, yanzu zan fara rayuwata, aure zanyi in tara iyali, don haka ka gaya min wa yafi cancanta da wadannan kudaden?"

Sadik ya jinjina kansa yana cije lebbensa kafin yace.

"Kaine, kai zaka ci su, kuma nima dole in taya ka mu same su ko ta wace hanya ce, don nima in samu abinda zan samu!"


***

_Inaga a wannan babin mun samu amsar wasu abubuwa da muke nema tun farkon labarin nan._

_Bayan hakan, ban san ma me zan ce ba, ku san min ra'ayinku kawai..!=??_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
#FararWuta.
#FararWuta. Ko
#FararWuta.
#FararWuta.
#FararWuta.
#fikrawriters
#FararWuta.
#FararWuta.
#FararWuta.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*11*

~~~~~~~

_She will listen to your words, but your actions will say more._ _- Unknown_


**

*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*

A cikin ?atuwar harabar gidan wadda duk girman wajen ya cika taf da al'umma da koma motaci, baka jin komai sai tarin hayaniya, mata da maza ne fal da lokaci zai dauke ka da yawa wajen ?irga su ke ta zirga-zirga, kowa sanye da ?arshen akwatinsa sai ?yalli? kawai kake gani a kowacce kusurwa, musamman ga matan da mafiya kayansu wal?awa kawai suke a cikin fitulun compound Win, irin dai kayan da mafi yawan mata ke amfani dasu wajen halartar taron biki na dare, (Dinner).

Taron bikin ?a?a biyu?mace da namijin da ake gudanarwa a gidan wanda suka kasance ?annen Jawad din dake tsaye daga barandar Wakinsa a lokacin yana kallon hayaniyar mutanen dake?fita a jerin motocin dake layi, amma duk da haka kamar ba Wibansu ake yi ba, tunda a cikin tarin ?anuwansu kaf kowa ya tattaro ya dawo gidan da sunan zama har a gama bikin.

Kananun kaya ne a jikinsa daga wandon har rigar duka farare, kuma gama wayarsa kenan da Haro wanda ke ?ara gaya masa sababbin hanyoyin da ya sake samowa na yadda zasu kama Ma'aruf a hannunsu.


Hannunsa ya koma wajen kira ya sake danna nambar mahaifiyarsa da yake yi a cikin wayar amma har ta sake katsewa ba'a Wauka ba, karo na shida kenan daga 6uta har ?annensa biyu babu wanda ya Wauka, mukullin motarsa da ya bari a Sangaren nasu yake nema, don shima ba zai zauna ba, nan da minti talatin ya sani kowa ya bar gidan don haka shima yana da inda zai je ba zai zauna ba, dalilin fitowarsa kenan barandar ya tsaya ko zai hango Waya daga cikinsu yayi musu magana su kawo masa mu?ullin, amma babu alamarsu.

Ya ja tsaki a hankali sannan ya juya ya koma cikin Wakin, akan gadon ya jefa wayarsa sannan kai tsaye ya nufi kofar dakin, ya fita zuwa koridon dake kaiwa hanyar matatattakala ya sauka zuwa falon ?asa, a jikin falon daga can ?arshe akwai wata kofa dake fuskantar babbar kofar da za'a fita zuwa waje, ya buWe ta ya taka cikin koridon dake bullewa zuwa Sangaren mahaifiyar tasa, ya buWe a lokaci guda da hayaniyar wajen ta cika kunnensa.

Allah ya sani ya rasa tunani irin na mahaifiyarsa, a kullum kawai yana Wora alhakin Wabi'unta da rashin karatun ta ne, don labari ne da kowa ya haddace shi cewa irin fulanin dajin nan ce mahaifin nasa ya auro ta, idan ba haka ba bai ga dalilin da zai sa itama tayi tata gayyar har kuwa da ?an kwana ba don ana bikin ?a?an kishoyoyinta.

Ya shiga cikin falon inda mutane da yawa suke, suna ta gaishe shi ya amsa sama-sama don kaWan daga cikinsu kawai ya sani wanda sune manyan, wata yayar mahaifiyar tasa ta tsayar dashi suka yi magana akan aikin da take son ya samowa danta a wajen aikinsu kafin ya shige kai tsaye zuwa Wakin mahaifiyar tasa.

"Wallahi kinyi kyau, babu wadda ta isa tayi miki kallon raini a cikinsu, babu wadda zata yada miki maganar cewa ba kya fantamawa kamar su."

Abinda ya fara ji kenan yana fitowa daga bakin wata Aunty Nana kafin hoton mahaifiyar tasa ya shiga idonsa, ta saka wata doguwar riga ta lace da zai rantse da Allah babu wajen da yatsa Waya zai zauna ba tare da taSa tarin dutsunan dake ?yalli ba, sai wal?awa suke suna haske kota'ina.

Ba shiri ya haWe ransa a take sanda mutanen Wakin ke kiran sunansa da korafin tun safe suke nemansa.

"Naje aiki ne."

Shine amsar da yabi kowanne su dashi bayan gaisuwa.

"Mamah mukullin motata nake nema."

Ta tambaya kai tsaye sanda ya isa gabanta, sai tayi murmushin da ya nemi karya zuciyarsa a lokaci guda, murmushin da yasa ba shiri duk wannan haWe ran nasa yabi iska.

"Haba Babana, yanzu ba zaka ce nayi kyau ba...?"

Yasa yatsansa daya ya shafo kan hancinsa, sannan yace.

"Mamah kinyi kyau... Kinyi kyau sosai."

Sai kuma ya kara da.

"Sai dai na so don ra'ayinki kika yi wannam kwalliyar ba don wani ko kuma wasu ba."

Murmushin da take bai bar fuskarta ba tace.

"Ka kawo min mata ka gani wanda zanyi don kai bashi da iyaka Babana, har sai ka rufe idonka."

Murmushin da bai shirya ba ta sake saka shi kafin ya gyaWa kansa yace.

"Allah ya kaimu, key Win motar yana wajenki?"

Daidai lokacin da Zainab ta shigo dakin a lokacin, hannunta dauke da wani katon kwando, yana jin yadda sauran Aunties Win nasa na Wakin suka samu damar korafin jiran bikin nasa da suke yi suna faWin so yake yi su haWa shi da ?annensa su Khairat tukunna, amma hankalinsa baya kansu tun sanda ta shigo dakin, hannunta na Wauke da wani ?aton kwondo da ta ciko kayan da bai san na menene ba dasu, idonsa ya bita da kallo sanda taje har can ?arshen Wakin ta bude wardrobe tana saka kayan.

"Zainab anyi namu wankin?

Wata ta tambaya a cikin mutanen dakin, sai ta Waga kanta da sauri tana murmushi tace.

"Eh suna cikin dryer ban ?arasa dasu ba, amma yanzu zan kwaso."

Wata da ya san sunanta Aina'u tace.

"Kafin mu tafi ki kwaso min kayan da kika kai mota Wazu, na fasa barinsu anan."

Bata amsa ba wata tace.

"Zainab an karSo min sa?on kuwa?"

"Yanzu zan karbo Aunty, ban samu lokaci bane tun dazu."

Sai ta gyaWa kanta tace.

"Babu komai, ai kina kokari ma, tun safe kike tsaye."

Daga inda Hajiya Mardiyya ke ?o?arin lalubo mukullin motar Jawad Win tace.

"In dai Zainab ce ai ba daga nan ba,bata zama sam."

Duk maganganun da ake yi idanun Jawad na kan yarinyar, yana kallon yadda take saka kayan cikin wardrobe da sauri da kuma yadda hannayenta ke rawa, wani abu ya gifta cikin zuciyarsa da bai san menene ba.

Ta gama saka su tazo wucewa daidai lokacin da Hajiya Mardiyya ke miko masa mu?ullin motar, kuma bai ji me take cewa ba kawai ya karSa sannan yabi bayan ta, suka fita daga Wakin tare.

Kwandon da ta juye kayan ne a hannunta tana ta ratsawa ta cikin mutanen dake Wakin har waje, hannayensa duka cikin aljihun wandonsa yana bin bayanta har suka fita wajen, tayi kwana zuwa hanyar inda Wakunan kwanan su suke,kuma bai tsaida ita ba har suka fara shiga wajen suka bar hayaniyar mutanen nan a baya sannan ya kira sunanta.

"Zainab."

A lokaci guda ta tsaya cak kafin ta juyo da sauri, idanunta suka zare a lokaci guda da ganinsa, tasirin mamakin ganin nasa ya haska ?arara a fuskarta kafin ya lura cewa rawar da hannayenta ke yi sun ?aru. Sai kawai ya taho ya ?araso dab da ita ya tsaya. Hasken fitilun wajen ya nuna masa yadda fatar bakinta ta bushe sosai ksmar yadda ya hango.

"Kinci abinci?"

Ya tambaya kai tsaye yana kallon ta, bashi take kallo ba ta sunkuyar da kanta ?asa kawai, kuma jin tambayar yasa babu shiri ta shiga Waga kanta da sauri, Waga kan da a cikinsa ya fahimci cewa amsaawa kawai take don ta tsorata amma hakan ba gaskiya bane.

Sai ya ja tsakin da bai shirya masa ba, ?ararsa ta fito ?arara, sannan yana kallonta ya sake maimaita abinda ya fada.

"Ba wasa nake miki ba, nace kin ci abinci?"

Wucewar sakan daya ,biyu kamar ba zata amsa ba sai kuma ta girgiza kanta a hankali alamun A'a. Ya cije lebbensa yana gyada kai sannan yace.

"Biyo ni."

Ya fada ba tare da ya matsa ba, ta Wago ta kalle shi sannan ta girgiza kai har yanzu idanunta na nunawa da tsoro.

"Akwai aikin da zanyi da yawa, su Hajiya suna ta jira na, dan Allah ..."

Bata ?arasa ba saboda tasirin yadda idanunsa ke kallonta, kuma ganin ta dakatar da kanta da kanta yasa shi lumshe idanunsa a hankali sannan ya juya, har a lokacin hannayensa sanye cikin aljihunsa, ya juya ya fara tafiya.

Zainab ta kalli bayansa, yadda ?aramar rigar ta fito da fadin kafaWunsa, zuciyarta ta kara nauyi a ?irjinta, sai kawai ta haWiye wani abu a makogwaronta sannan ta bi bayan nasa itama.

Ta cikin mutanen nan suka wuce, tana tsayawa nesa dashi kadan duk sanda ya tsaya magana da wasu, kuma kusan sau biyar yana juyowa ya tabbatar idan tana bin nasa har suka ?arasa Sangarensa, ya buWe kofar da mukullin da ya zaro a aljihunsa sannan ya shiga ciki yana barinta a buWe.

Ta sake yin karfin halin danne zuciyarta kafin ta taka kafafunta ta karasa zuwa ciki, har yanzu tana ri?e da wannan kwandon, hannunta ya saki kofar bayan ta shiga cikiba tare da ta rufe ba, kuma har ta yi taku biyu a ciki taji muryarsa a cikin kanta.

"Koma ki rufe kofar."

Ta juya gefen da taji muryar, wajen kujerun falon dake gefe, yana kwance akan guda Waya three-sitter dake fuskantar Tv ya mike kafafun sa.

Sai ta juya a hankali ta koma, ta tura kofar a hankali har ta rufe, amma kuma sai ta kasa juyowa, ?afafunta suka tsaya a wajen, hancinta na sha?ar daddaWan kamshin air freshener da ta fesa da kanta yayin da hannayenta ke rawa ri?e da wannan kwandon.

"Ki ajiye wannan abin ki shigo ki ci abinci "

Ya faWa ba tare da ya bata damar shawara da zuciyarta ba, sai ta juyo ta sake kallonsa, shima ita yake kallo daga yadda yake kwancen.

"Wallahi akwai abinda zanyi da yawa, suna jirana kuma... kuma Hajiya zata min faWa, al?ur'an..."

"Me?" Ya katse ta a lokaci guda yana kallonta.

"Me kika ce?"

Ba tare da ta fahimci abinda yake nufi ta sake cewa.

"Alqur'an faWa zata yi min..." Rantsuwa ta sake fitowa daban da yanayin fuskarta, babubta yadda wani zai ce ma ita ta fada. Sai kawai ya girgiza kansa.

"Kar in sake ji kin fadi wannan rantsuwar. Bana so, kar ki sake faWa."

Ta hadiye yawu a makogwaronta sannnan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login