Showing 18001 words to 21000 words out of 132946 words

Chapter 7 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1137

take kallo har a jikin Faruk yanzu, to kuwa ta tabbata bata da kalaman da zasu wanke ta ko a gaban waye.

"Ka ce bai ji ciwon sosai ba ko?" Sai a wannan lokacin muryar Mamin ta shiga kunnenta, tana tambayar Faruk din da ya gama amsa wata waya wafda da alama fuk akan abinda ya shafi al'amarin ne.

Ya daga kansa sau daya.

"Ba sosai ba, na wancan mutumin ne yafi yawa, tun a can muke fatan Allah yasa bai fasa masa ido ba, don dukansa yayi tayi Mami, yana cewa a kyale shi ya kashe wai yana da sakon da zai bashi."

"Inalillahi wainna ilaihir raju'in... Bari na kira Baffa."

Ta faWa amon muryarta na fitowa da tsananin damuwar da babu wanda zai kasa shaida hakan, Amina ta bita da kallo baya ta juya ta bar wajen, kuma a wannan ya lokacin ne wata Nurse dake cikin Wakin da suke jira a kofarsa ta fito, hannunta dauke da farantin kayan dressing wanda ya cika fal da tarin auduga mai jini.

Idanun Amina ya sake bin hannunta da kallo har ta Sacewa ganinsu, abinda take ji a ranta yayi yawa a lokacin don haka sai kawai ta dam?e hannayenta biyu duka waje daya ta a shirin kore kwallar dake taruwa a idanunta. Munaya wadda suka taho tare da ita ta karaso daga fitar da tayi tana gama waya da Hajiya Maimunan da ta sake kira tana tambayar halin da ake ciki.

Taji sanda ta zauna a gefenta bayan tayi sallama da Hajiyan don haka ta juyo ta kalle ta.

"Za'a barmu mu ganshi yanzu?"

Sai ta girgiza kanta.

"Wallahi ban sani ba, amma ko sun ce ma ai inaga Mami ce kadai zata shiga."

Idon Amina ya nuna da mamaki kafin ta tambaya.

"Saboda me?"

"Saboda idan yana wannan yanayin bai kamata aje kusa dashi ba, Mami ta fada mana hakan tuntuni."

Bakin Amina ne ya bude a lokaci guda, mamakin dake idonta ya karu tana kallonta.

"Waye yake kula dashi kenan?"

"Yaya Ishaq ne, yawanci ma ba anan suke zama ba, akwai asibitin da yake ganin likita a London, can suke tafiya sai ya sami sauki tukunna. Amma lokaci kadan ne, da mood din nasa ya dawo zaki ga koma daidai."

A lokaci guda sai taji hankalinta ya kasa Waukan maganganu da Munayan ke faWa, kallonta kawai take yi yayin da take jin kamar kwakwalwarta na washewa, komai yana gogewa, don bata san yadda zata dauki wannan al'amarin ta ?ara akan sauran tarin abubuwan dake kanta ba.

Tunaninta ya kasa lissafa wace irin zuciya ce da Hajiya Kilishi, a kowanne irin ma'auni na duniya ta rasa a wanne iri za'a dora zuciya irin ta Kilishi tayi kama da ta mutane... Abubuwan da ta aikata a rayuwarta kaf idan za'a tara su waje Waya bata jin duk raunin imanin mutum a duniyar nan za'a sami wanda zai kalla bai ji zuciyarsa ta motsa ba.

Ta shigo cikin rayuwar mutanen nan da ?arfi da yaji, ta gurgunta mahaifiyarsa, ta ?wace shi daga gare ta, ta shuka tarin ?ananun abubuwa a cikin rayuwarsu da watakila ita kanta ba zata iya lissafawa ba, kuma duk da bata sani ba tana tunanin wata?ila itace sanadin ciwon nasa ma amma duk wannan bai ishe ta ba sai ta da?ile shi kuma a dukkan Sangare na kulawa irin wannan.

Bata san irin ciwon Ma'aruf ba, bata san komai game dashi ba, amma tayi imani cewar babu wani ciwo a duniyar nan da baya bukatar kulawa, ko da na hauka ne kuwa, to ta yaya za'a ce ayi nesa dashi a lokacin da yake tsananin bukatar kulawa?

Farkon zuwanta gidan tana ganin komai ne daidai, tana sha'awar mu'malarsu da komai sha?uwarsu na mata yawo a ido kodayaushe, amma sai a yanzu take ganin tarin ramukan dake gewaye dasu, sai yanzu take fahimtar cewa ba daidai komai yake tafiya ba kamar tunaninta.

Mutane ne su masu hankali, ?an boko kuma masu ilimi, amma Kilishi ta dauke su gabaWaya ta sanya a wani rami da babu mai iya haurowa, tana daga sama sai iya amon muryarta da kuma umarninta kawai suke ji, suna yin dukkan abinda ta furta ba tare da sun sani ba, ba tare da sun san ma me saka su ba. Taji zuciyarta ta matse a lokaci guda wani abu a cikin kanta yana gaya mata cewa wannnan yana daya daga cikin abubuwan da zata fara canjawa.

Tana jin Munayan na cigaba da waya da wata classmate dinta a lokacin, tana jin suna tattauna wani abu da ita ba fahimta take yi ba har sanda Mamin ta dawo, ta shiga gayawa Faruk?da ya dawo cewar yaje gida ya canja kayansa, don mutanen dake wajen duk wanda zai wuce sai ya kalle shi, amma yace mata bari likitan ya fito tukunna su ji abinda zai ce, don har ga Allah baya jin zai iya tafiya ba tare da ya san halin da ma'aruf ke ciki ba.

Zuciyarsa ta yage har karshe tun daga lokacin da yaga yadda yake rike Ma'aruf a wajen nan yana yi madmsa magana amma babu alamun ya a gane shi alhsli yanzu-yanzun nan suka rabu lafiya, lokacin da al'smarin Daniel din nan ya faru a Office zuciyarsa tana bada wani kamashon laifin ga Daniel din, yana ganin har da laifinsa wajen tunzura Na'aruf din, amma abinda ya gani yau, yafi karfin dukkan wani tunaninsa.

Don haka yana tsaye har lokacin da Ishaq ya bude kofar wajen ya fito, kayan jikinsa kalar maroon ne amma duk da haka ana ganin inda ya samu nasa rabon Sacin jinin shima.

"Ishaq me ake ciki? Me suka ce?"

Mami ce ta fara jero tambayoyin cikin za?uwa. Kuma da muryarsa a hankali? kamar kodayaushe yace.

"Mami ki kwantar da hankalinki, ciwonsa ne dai ya tashi, dama munyi sa'a ne kwana biyu mood din nasa ya saisaita, kuma ban san me ya tada shi yanzu haka a lokaci guda ba. Sai dai na yi musu duk bayanin da suka bukata kuma sun bude file sun rubuta hakan, yanzu an bashi alluran bacci yana hutawa."

"Abinda zasu iya yi masa kenan?" Ta tambaya.

Ya gyada kansa.

"Mami ai ko irin magungunan nasa na basu dasu anan, guda daya kawai aka samu, so na gaya musu zamu taho da na wajenmu zuwa gobe su kara duba su tukunna, ina tunanin insha Allah iya nan komai zai tsaya, ba sai mun koma? London ba. Don allurar da suka yi masa ma iya ta zuwa gobe ce."

Hajiya Kilishi ta gyaWa kanta alamun fahimta sannan ta sake furta kalmar inalillahi wainna ilaihir raji'un fuskarta na nunaea da abinda za'a kashe wani akansa cewar damuwa ce.

"Likitan ya fita, yanzu zasu kaishi Wakin da zai huta, sunce nambar dakin C0-9."

Mamin ta gyaWa kanta.

"Zamu je mu ganshi kafin mu tafi...."

"Mami zan zauna."

Babu zato muryar Amina ta katse abinda Hajiyan Kilishin ke shirin fada. Dukkaninsu suka juyo suka kalle ta a lokaci guda, wani guntun mamaki ya haska a fuskar Hajiya Kilishi kafin tayi saurin kore shi da murmushi.

"Toh shikenan, sai ki zauna zuwa gobe."

Ishaq ya gyaWa kansa shima.

"Zanje in Wauko masa wasu kayan da za'a canja masa don waWannan na jikinsa sun Saci. Sannan zuwa gobe zan dauko reports dinsa gabadaya na asibitin don na san familyn wancan mutumin zasu iya shigar da kara, dole ne mu sami backup a hannu."

Faruq ne ya fara gyaWa kansa kafin yace.

"Allah ya kaimu, I need to talk to you please kafin in wuce." (Ina so muyi magana kafin mu wuce.)

"Okay toh muje." Cewar Ishaq din suna yin gaba.

"Kin tabbata kina son ki zauna?"? ?

Munaya ta tambaya tana kallon Amina lokacin da wata Nurse ta karaso tana mikawa Hajiya Kilishi wasu takardu na Wakin da aka kai Ma'arf Win, kuma tana jin wani abu kamar damuwa na yawo a cikin muryar tata.Sai ta gyada kai tana kallon hannayenta.

"Babu abinda zai faru Munaya Insha Allah, bai kamata a barshi shi haka shi kaWai bane ba."

Hajiya Kilishi ta juyo ri?e da takardun nan a hannunta ta mi?owa Munaya su.

"Munaya je ki fara dubo mana dakin gamu nan."

Wannan karon muryarta ta fito da sanyi kalau, kamar na iskar wajen dake hurowa daga A.c, kuma Munayan bata yi tunanin komai ba ta mike tsaye ta karbi takardar amsawa da Toh.

Hajiya Kilishi ta bita da kallo har ta bace a dogon koridon wajen sannan ta juyo ga Aminan da har yanzu kanta ke sunkuye a kasa tana wasa da yatsun hannunta.

"Naji dadin abinda kika yi fiye da tunaninki Amina, na baki wannan aikin ne don in gwada hankali da kuma tunaninki ba wai don ba zan iya ba kin sani, kuma ba zan boye miki ba zuciyata ta yaba da irin hikimarki, musamman a yanzu da nazo naji cewa daga Mai gaskiya har wadannan abokan nasa basu san komai ba, shi kansa bai san cewar ya sha magani ba balle har ya dora zargi akanki.

Na san zaki iya Amina, na san zaki iya tun daga ranar dana fara ganinki a duniya jikina ya bani hakan, shi yasa nayi amfani da Aminu na zaburar dake don ki fahimci cewa zaki iya din ba tare da kin bata min lokaci ba, amma kamar yadda na nuna miki ne, komai zai wuce kamar ba'ayi ba, zan sa ki manta da abun da ya faru dashi kwanan nan insha Allah.

Shima Ma'aruf din zai tashi, kwana biyu ne dama wanda kafin nan na gama dukkan abinda zanyi akan RTL, don haka abu daya nake so dake yanzu, ki rage wannan damuwar dake kan fuskarki, kin riga kin shigo cikin tsarina Amina, kuma ni bana tafiya ina barin shaidar takuna a baya, ina wucewa ta cikin sahara ne ba tare dashi kansa yashin wajen ya san na taka ba. Kin fahimce ni?"

RTL! Sune kalaman da Amina ta fara rikewa a cikin kanta kafin maganganun Amma su gufta cikin kanta.

_ki ?as?antar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba..._

Me ya same ta ne? Me take shirin yi? Tayi saurin tambayar kanta, tayi komai, ta samu yardar Kilishi a yau kadai tun ba'aje ko'ina ba, sannan kuma a yau din tana neman tayi wasa da haka? Yawu ya zarce cikin ma?ogwaronta babu shiri, Amma bata nan, hasali ma zata iya kirga iya lokutan da ta taba ganin Hajiya Kilishi a rayuwarta, amma kamar ta karance ta ne tsawon shekaru, dukkan maganganunta suna zuwa akan kowacce gaSa na tunanin Kilishin. Saboda haka sai tayi saurin girgiza kanta sannan tace.

"Mami, damuwata ba akan abinda ya faru take ba, tunanin nake yi idan har da gaske kike game da abinda kika fada akan Aminu, ina son ?anuwana fiye da komai Mami, kuma zanyi komai kamar yadda kika fara gani yanzu indai akansu ne, shi yasa nake ta fatan samun saukin sa kamar yadda kika fada."

Ta fadi hakan bayan ta Wago tana kallonta, kuma ga mamakinta sai kawai tayi murmushi mai kyallin dake tabowa har cikin idanunta kafin tace.

"Kar ki damu Amina, kin riga yarda dani amma baki gama tabbatarwa bane, abinda nake so kawai shine ki kwantar da hankalinki, duk wata gaggawa bata Sullewa ga nasara, don haka mu bi komai a hankali. Ina tabbatar miki da sannu zaki fahimci wacece Kilishi da kuma hukuncinta!"

Amina ta kalle ta da nata guntun murmushin da a dole ya sauko kan sannan ta daga kanta kawai.

_Ina tabbatar miki idan kika tsallake? matakan farko Amina, komai zai zo miki bi da bi kuma saukake, yardarta kawai muke nema a yanzu._

Tabas! kalaman Amma gaskiya ne, gwara da ta daure zuciyarta ta bi umarninta, don tun a yanzu? ta fara fahimtar cewa babu wahala juya tunanin Kilishi,

Taji zuciyarta na ?ara yarda da kalaman Amma na cewar kissa da dabara sune makamin kowacce mace a duniyar nan, ba namiji kadai ba, hatta mace ?aruwarta yanzu zata ci galaba akanta da waWannan abubuwan duk kuwa da irin takama da ikonta, ya danganta kawai daga yadda macen ta yarda ta bude kwakwalarta, ta yarda cewa Allah ya halitta mafitar kowacce matsalarta a cikin kwakwalwarta, kuma idan ta dogara dashi? ta yarda cewar zaki iya Win, shikenan ta rusa dukkan wata katanga dake gabanta.

Kuma lokacin da suka isa Wakin, kwata-kwata su Mami basu fi minti biyar ba suka tafi bayan Mamin ta furta kalmar Allah ya sawwake sau daya, wadda ta san itama ta fada ne saboda Munayan dake tsaye, wadda ita kuma ta kasa dauke idonta daga kan Ma'aruf din tun bayan shigarsu, tana kallonta har sanda suka zo fita sai da ta waiwayo ta sake kallonsa.

A wanan lokacin ne kuma zuciyarta ta kasa iya auna irin don da Hajiya Kilishi ke ikirarin taba yiwa Ma'aruf, duk da cewar ita kanta shaida ce, tana kaunarsa ta wata siga da babu mai iya kwatanta ta cikin hankali, don babu hankalin da zai yarda da so da kuma cuta a lokaci guda, ta yaya za'a yarda tana sonsa amma zuciyarta bata jin komai wajen cutar dashi? Ita gabadaya saninta dashi na yaushe ne, amma da yaya ta daure zuciyarta ta aikata komai kuma yanzu yaya take ji a ranta?

Sai ta matsa a hankali zuwa gaban gadon bayan fitarsu, kuma da kowanne taku tana jin kamar tana tafiya ne da nauyin laifukanta a gabansa, laifukan da a yanzu zuciyarta ke shan alwashin gyaransu ta duk hanyar da ta san zata iya, tunda ta riga ta fara yin mai wuyar.

Kafafunta suka tsaya a gaban gadon tana kallon fuskarsa, kuma yanayin yadda fuskar tasa?tayi so innocent ya daki zuciyarta taji tana ?o?arin hadiye wani abu da ya kasa barin makogwaronta.

Wasu abubuwan suna faruwa ne ba'a yadda bawa ya tsara su ba, wasu nasarorin suna samuwa bayan ka daure zuciyarka wajen aikata wani abu da kake da yakinin samun nasararsa a gaba.

Gashin kansa a barbaje yake sosai, sannan fatar bakinsa ta rabu da ?aruwarta ta yadda tana iya jin fitar numfashinsa ta duka hanci da baki daga inda take tsaye, sai ta tsugunna a hankali idanunta na cigaba da kallonsa.

Kuma bata san ta yadda zata hana kanta ba sanda hannunta ya sauka akan gefen fuskar tasa, yatsanta daya ya taho a hankali daga gefen fuskarsa zuwa karshe, kumatunsa ba cikakken bane kuma ba ramamme ba kawai dai wani abu ne a tsakiyar hakan, da sauri ta janye hannunta ganin ta karasawa kusa da bakinsa sannan ta mike tsaye.

Wayarta da ta ajiye akan kujerar dakin tun bayan shigowarsu taje ta dauko, missed din Amma har guda biyu ya shiga idonta. Bata san lokacin da ta kira va don wayar ta shiga silent,kuma dama ko bata kira din ba, ita take shirin kira don tun safe ya kamata ace sunyi wayar amma hayaniyar dawowar Inna Danejon nan ta Wauke hankalinta.

"Assalamu alaikum."

Muryar Amman da ta fito a hankali kuma cikin sanyinta kamar kodayaushe tasa ta jin kowacce tsigar jikinta na tashi, tasirin al'amarin na da kuma abinda tayi na kara kamata, ta rufe idanunta a hankali kafin ta iya tattaro dauriyarta ta fara? gaishe ta, wanda bayan hakan ne dukkan sauran hirarsu ta biyo baya.

Hirar da a cikinta kalaman Amman da kuma umarninta ya kara inginza zuciyarta, suna buWe mata wani sabon kwarin gwiwar da bata san tana dashi a baya ba!

***

*Washegari.*
*07:30am.*

"Doll..."

Muryar ta shiga kunnenta a hankali, ta jiyo amonta kamar daga can nesa, kamar a cikin wani fili da ita take ?arshensa muryar kuma tana daya karshen, don haka bata motsa ba ta tsaya a hankali tana saurare ko zata kara jinta,bdon bata yarda cewar wanda take tunani zai kira ta da hakan a halin da yake ciki ba. Ilai kuwa bayan sakan daya biyu kuwa sai amon ya sake cika kunnenta da wannan sabon suna da a duniya kaf ta san mutum daya ne ya taba gaya mata.

Babu shiri ta bude idanunta, amma hasken da ya shiga cikinsu a lokaci guda ya hana ta ganin komai, sai da ta maida shi ta rufe tasa hannunta ta mutsikka sannan ganin nata ya dawo daidai, a cikin Wakin asibitin nan ne, don kafar gadon da take fuskanta itace abu na farko da ya tuna mata cewa tana kwance ne akan carpet din dakin tun bayan da tayi sallar Asuba kuma ta gama yiwa Ma'aruf dukkan addu'o'in da Amma ta shaida mata jiya a wayarsu.

"Doll..."

Muryar Ma'aruf da ya kira ta yasa idonta ya kai kansa a lokaci guda, yana kwance irin yadda take ta gefe daya a saman gadon, idanunsa duka a buWe suke kallonta.

Mamaki ya ratsa ilahirin jikinta gabaWaya don bayan dawowar Ishaq jiya da daddare yace mata likitocin sun ce ba lallai a yau ma a samu ya farka ba don allurar tana da karfi sosai, sai kuma ta tuno addu'o'in da tayi har bacci ya dauke ra, a lokaci guda tajintana kara yabawa ?udira da kuma ikon ubangiji, don haka ba shiri ta mike zaune kuma bata jira komai ba ta ja ?afafunta ta ?arasa gabansa.

"Why are we here?" (Me yasa muke anan?)

Ya tambaya amon muryarsa na fitowa a hankali yayin da yake kallonta, gashinsa a barbaje kamar yadda yake tun jiya sannan idanunsa ke lumshewa alamun fada yake yi da kansa wajen bude idon. Tausayinsa da ta kwana dashi a cikin zuciyarta ya sake tasowa a ranta, taga idonta na? nuna mata cewa kamar ya rame daga jiya zuwa yau kaWai.

Tasa hannunta a hankali ta gyara dankwalinta da yayi baya da yawa, ta jawo shi ta rufe gashinta sannan tace.

"Baka da lafiya, jiya su Ishaq suka kawo ka."

Taji muryar tata ta fito kamar wani yana karta farce akan katako don haka ta shiga kokarin yin gyaran murya kadan sanda ya girgiza kansa a hankali.

"I don't want to be here." (Bana son zama anan.)

Ta daga kanta a lokaci guda.

"Tohm, bari nayi wa Nurses din magana su zo sai mu tafi gida."

Ta fadi haka da niyyar mikewa amma a lokaci guda ya kamo hannunta, taji yatsunsa da suka dauka dsuka da sanyin A.cn sun ratsa sun nad hannun nata, numfashinta ya dan katse a kirjinta kafin ta dawo ta tsugunna akan gwiwoyinta sanda idanunsa sun sake rufewa.

"Kar ki kira su."

Bata ce komai ba, yayi ?o?arin sake bude idonsa sannan yace.

"Ina wayata?"

Tambayar tasa a lokaci guda ta tuna abinda Faruk ya fada a jiya cewa an dauke duka wayoyin nasa har dasu wallet, don haka sai kawai tace bata san inda take ba, ya sake yin shiru yana kallonta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login