Showing 57001 words to 60000 words out of 132946 words

Chapter 20 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1144

#300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*13*

~~~~~~

_"If you want to keep a secret, you must also hide it from yourself."  George Orwell, 1984_


**

?afafunsa suka shigo cikin tangameman falon a hankali, kai tsaye ya shiga wuce tarin wajajen dake cikin falon har zuwa inda ya san zai sami mahaifin nasa, yana bi ta kan tausasan carpet Win dake wajen kala-kala har ya karasa wajen a daidai lokacin da idonsa ya shaida masa mutanen dake zaune bayan mahaifin nasa.

Mahaifiyarsa, matar mahaifinsa ta biyu mai suna Yagana, sai kuma shugaban ma'aikatan gidan Joshua, yana kallon yadda kayan Hajiya Yaganan ke ?yalli tare da na mshaifiyarsa a cikin fitulun wajen kamar masu shirin tafiya fadar shugaban ?asa.

Ya karasa da sallama sanda mahaifin nasa ya sauke jaridar dake fuskarsa sannan shirun da suka yi dukkaninsu ya tafi tare da amsawar sallamar daga mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa su kaWai yayin da Hajiya Yaganan ta shiga jefo masa hararar da sau Waya ya gani ya Wauke kansa.

"Barka da Safiya Abba."

Ya gaishe da mahaifin nasa yana zama kusa da Joshua.

"Yawwa mun tashi lafiya?"

Amon muryar mahaifin nasa ya fito babu yabo kuma babu fallasa.

"Lafiya kalau Alhmdlilah." Ya amsa kafin mahaifin nasa ya sake cewa.

"Ai ban san kana gari ba ma har akayi bikin ?annenka, sai yau da na tashi da ?orafin ka da aka kawo min."

Kafin ya amsa muryar Hajiya Yagana ta cika falon da cewar.

"?orafi? Ai ba ?orafi bane Daddyn su Amal, laifi ne yayi kuma shi kansa ya san da hakan."

Ta kira sunansa tana kebanta shi da ?a?an ta saboda Hajiya Mardiyyan dake zaune. Kuma maimakon mahaifin nasu yayi maganar katse shin da tayi a zancensa, sai kawai yace da Jawad Win.

"Me yasa ka korar mata ?an aiki har mutum uku Jawad?"

Jawad ya gyara zamansa yana fuskantar inda zancen ya dosa kafin yace.

"Ni ban san ?an aikinta bane, laifi suka yi min nace da Joshua ya kore su, kuma ko a karkashin wa suke aiki a gidan nan haka zan ce."

Alhaji Bashir ya gyaWa kansa alamun ya fahimta.

"Laifin me suka yi?"

Kai tsaye ya sake cewa.

"Wata yarinya suka ?onawa kayan sawarta gabadaya, sunanta Zainab."

Amsar ta fito da zare idon da Hajiya Mardiyya tayi a lokaci guda tana kallonsa da kuma kallon haushi dana takaicin da Hajiya Yagana ke jifansa dashi.

"Ita wannan yarinyar a ina take da har kake yanke wannan hukuncin saboda ita?"

Kai tsaye ba tare da wata shakka ba Jawad ya sake bada amsa, idanunsa na kallon adon carpet din dake gabansa, yace.

"Anan gidan take, ?ar aikin Maamah ce."

Wannan karon ba matan kaWai ba, hatta Alhaji Bashir din da kuma Joshuan dake zaune a gefensa sai da mamaki ya haska a fuskokinsu.

"Zainab Jawad? Zainab din dake wajena?"

Da alama Hajiya Mardiyyan dake tambaya bata shiryawa hakan ba, sai dai kafin ya bata amsa mahaifin nasa ya kawo tasa tambayar shima.

"Meye tsakaninka da ita kenan?"

Jawad ya girgiza kansa.

"Babu komai, I just like seeing her around me." ( Babu komai, kawai ina jin dadin ganinta a kusa dani ne.)

Ba wai sabon abu bane, duka wanda ke zaune a wajen hatta Joshua daya Webi shekaru a gidan, ya san hali irin na Jawad, halin kafiya, jajircewa, naci da kuma rashin boye ra'ayinsa akan abu, halin da tun a baya ya jawo rashin jituwa tsakaninsa da mahaifin nasa don ra'ayinsu ya banbanta sam kan gudanar da harkar mulkin da yake yi wanda ya faro tun daga matakin Chairman. Sannan kuma halinsa wanda ya dace da aikin da yake yi a office wanda ya jawo har ya samu babban mu?ami a ?ananun shekaru.

Don haka babu wani ja in ja, Alhaji Bashir din ya sake gyada kansa alamun ya fahimta sannan yace.

"Bayan haka babu wani abu?"

Kalmar wani abun a dun?ule ta fito, Wauke da tarin ma'anonin da kowa a wajen ya fahimce su, Jawad ya haWiye wani abu da bai san sunansa ba a ma?ogwaronsa, a wannan muhallin amsar sa mai tsafta ce ya sani, amma a wancan Soyayyen al'amarin na Ru?ayya, zai iya faWar amsar da zata sanya kowa sallallami a wajen nan, amsar da zai tozarta mahaifiyarsa ta mafi munin hanyar da ba zata taSa tsammani ba, wannan shine kadai rauninsa, shine kaWai rauninsa a duniya ya sani, kuma bai san ma ta yadda zai fuskanci hakan ba.

Wannan karon idanunsa na kan mahaifiyarsa dake kallonsa da tarin wasu abubuwa da ba zai iya fassara su ba yace.

"Babu wani abu Abba, babu komai tsakani na da ita."

Alhaji Bashir ya sake gyaWa kansa kafin yayi magana.

"Daga kai har yayyenka da ?annenka babu wanda nake takurawa a rayuwarsa kun sani, abu Waya ne kawai ba zan taSa lamunta ba shine hoto mara kyan da har zai iya taSa siyasa ta, saboda haka ina son labarin nan ya cigaba da kasancewa a yadda ka faWe shi yanzu Jawad.

Yarinya aiki take yi a gidan nan, kar ka shiga hakkinta, kuma kar ka shiga hakki na da naka na neman wani abu da ya Wara haka a tsakaninku, ko mai kyau ko kuma akasin sa. Ba zan lamunta ba wallahi!"

Shiru ya ratsa Wakin sabidya yadda muryar Alhaji Bashir Win ta fito cikin Wagawa da kuma hasala, wani abu da idan har ba a fagen siyasar tasa da yake ji da ita ba, da wuya ne kaga Sacin ransa irin haka, tsarinsa guda daya ne, yace a cikin iyalansa kowa yana da yanci da kuma damar yin abinda yake so, abu daya ne kawai ba zai taba lamunta ba, idan har al'amarinka zai shafi siyasar sa komai kankantarsa kuwa, balle kuma a yanzu da kujerar tasa ke girgidi kowa ya sani.

Sai dai duk wannan ba shi ya dami Jawad a wannan lokacin ba, ba shine abinda kwakwalarsa ke biyawa ba, kalamansa ne, kalaman mahaifin nasa na ?arshe masu dauke da ma'anar da ya kasa fahimta balle har ya ajiye su a gefe ya fuskanci ma'anar kallon da mahaifiyarsa ke masa a lokacin.

_... kar ka shiga hakki na da naka na neman wani abu da ya Wara haka a?tsakaninku, komai kyau ko kuma akasin sa..."_

***

?ofar falon ta buWe, ta buWe a lokacin da Jawad ke magana cikin wayar dake kare a kunnensa, dawowarsa kenan daga Sangaren mahaifin nasa ya shiga ansa kira daga wani shugabansa na wajen aiki da yake can babban branch dinsu na Lagos. Kuma bai Wago ya kalli kofar ba don ya riga ya san waye mai shigowar har ta ?araso ciki, kamar kodayaushe hannunta Wauke da? tray din kayan abincin da ya zama dolenta wajen kawowa.

"I'll see to it on Monday sir."

Cewar Jawad bayan ya fahimci dukkan abinda mutumin ke faWa ta cikin da wayar.

"Okay, so thank you for your time Mr. Kuliya."

"Thank you too sir."

"You are welcome."

Cewar mutumin kafin wayar tasu tazo ?arshe, Jawad ya ajiye ta a gefensa sannan ya dago yana kallon Zainab fin dake tsaye daga wajen Dining Win bayan ta ajiye ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kayan abincin, bai sani ba idan kyau tayi ko kuma akasin hakan, kawai dai ta ca'nja, don tana sanye ne da Waya daga cikin bunbula-bunbulan dogwayen rigunan da ya bawa wani direba a gidan yaje ya siyo mata jiya, wanda sai bayan ya siyo din sannan yaga wautarsa na bawa namiji ya siyo, don in banda yawo ba abinda take yi a cikin kayan, Khairat zai kira ya bata wani kudin ya san zata siyo wanda zasu yi mata daidai.

"Ina wuni."

Ganin yadda yake kallonta ya sa ta furta gaisuwar da ta san ba amsawa zaiyi ba don bai taSa ba, amma kuma wannan bai sa ta fasa ba a kullum itama, sai kawai yayi ajiyar zuciya a hankali sannan yace.

"Ga wata jaka nan akan table din dauko ta ki zo."

Ta juya ta kalli jakar daga can gaban inda ta ajiye kwanukan, ta mika hannunta ta dauko ta sannan ta taho, ta karaso cikin falon a hankali har zuwa gabansa.

"Zauna." Ya faWa kai tsaye bayan ya karSa, kuma ta riga ta san me yake nufi don haka bata yi wani musu ba ta sami waje a daidai gaban nasa ta zauna.

"Maamah ta ganki kafin ki taho?"

Ya tambaya yana kallonta, sai ta girgiza kanta a hankali.

"A'ah, tun dazu ta tafi Sangaren Alhaji bata dawo ba."

"Wani ya sake miki wani abu a cikin gidan?"

Ta sake girgiza kanta a hankali tana kallon ?asa.

Ya cije lebbensa kaWan sannan ya buWe jakar ya dauko wani bandeji da kuma wasu kwalabe har da plaster, kuma bai sake cewa komai ba kawai ta ga ya sauko daidai gabanta shima, sannan yasa hannunsa kai tsaye ya janye ?asan rigarta kadan, kumburarriyar ?afarta da taji ciwo lokacin da plate din tangaran din nan ya fashe akanta ta fito fili.

"Just stay still." Ya fada a hankali ba tare da ya damu da ta gane ko bata gane ba.

Zuciyar Zainab ta buga a ?irjinta, mamaki ya ri?e ta a yadda take a zaune, sannan tsoro ya mamaye koina a ?irjinta, hannayenta suka shiga rawa, amma sai dukkan hakan ya tafi da saukar ruwan wani abu cikin ciwon nata, zafinsa ya ratsa har ?asan ruhinta ta yadda ba shiri ta runtse idanunta da dukkan karfin da zata iya tana jin yadda yake kokarin bajewa a ko'ina na jikinta amma duk da haka bata motsa daga yadda take ba har ya gama.

Ya Waga kafar tata a hankali ya naWe ta da bandeji bayan ya saka plaster sannan ya tattara sauran kayan ya mayar cikin jakar da ya bari akan kujera sannan ya juyo ya sake kallonta, itama shi take kallo yanzu, manyan idanunta sun buWe sosai akan fuskarta, kuma yanayin yadda yake zaune yayi kusa da ita sosai amma duk da haka bata yi ?o?arin matsawa ba kallonsa kawai take yi da tarin wasu abubuwa fal da bata san ma'anarsu ba a cikin kanta.

"Ni kike yiwa wannan kallon?"

Muryarsa ta fito a hankali shima yana kallonta, kuma muryar ta fito kamar ya daeo da ita cikin hayyacinta don babu shiri ta mi?e a lokaci guda jikinta ya hau rawarsa, sannan tayi hanyar wajen Dining inda ta san aikinta na gaba shine zuba abincinsa.

Sai kawai yayi murmushi a hankali sannan ya mi?e tsaye shima yana nufar inda ya ajiye wayarsa kafin yabi bayanta.

**

A cikin dakin Hajiya Mardiyya tayi wulli da dankwalin kanta akan gadon Wakin yayin da jikinta ke rawa tana rike da wayar hannunta kafin tace.

"Ki taimaka min Aunty Sadiya kizo gidan nan yau, tsoro na Allah tsoro na Annabi sce wannan yarinyar tana da ala?a dashi."

Daga cikin wayar yayarta mai suna Sadiyar tace.

"Baki da hankali ai Mardi, na daWe ina gaya miki har yanzu baki da wayo balle hangen nesa idan banda haka, me yasa zaki dauki yarinyar nan aiki? Tun farko da kika ji ance daga Garun Albasu take me yasa zaki rike ta har ki sakar mata kamar yadda nazo na tarar kina yi?

Garun Albasu ?auye ne, mutanen cikinsa ba wani yawa ne dasu ba, idan har ma yarinyar nan ta kasance ?aruwarsa wani abun mamaki ne?"

Hajiya Mardiyya na faman girgirza kanta tace.

"Ba zai yiwu ba, ba zai taba kasancewa ba, dan Allah Aunty Sadiya kizo mu zauna akan zancen nan...!"


***

*Kano.*
*Bakori Enterprises.*
*10:30am.*

"Ina Faruk Win yake?"

Yakubu ya tambaya ta cikin screen Win computer dake gaban Ma'aruf wanda suke video call ta jiki, Ma'aruf ya girgiza kansa kafin yace.

"Baya nan, ya tafi wani aiki ne."

Yakubu ya gyaWa kansa yana cije leSe.

"I wish yana nan, da na nuna masa proof na kokwanton da yake yi akan aikina."

Ma'ruf ya gyaWa kansa kusan sau biyar a jere.

"Ya sani Yakubu, ai munyi maganar dashi tun sanda ka kira ni, let's just get straight to the point dan Allah, ina yake?"

"Ka kwantar da hankalin ka yanzu zasu shigo dashi, bana garaje a aikina ka sani,ko so kake yi yazo a sigar da ba zaka sami wata amsa ba?"

Ma'aruf ya haWe tafukan hannayensa biyu akan fuskarsa sannan ya fitar da iska ta bakinsa, kusan awa guda kenan da Yakubun ya kira shi cewa zai haWa shi da Mr. Okaforn ya tambaye shi duk abinda yake so ta wayar video call kafin su yanke hukuncin abinda zasu yi dashi.

Kuma tun a lokacin suke magana da Yakubun ta wayar ba tare da ya ga Mr. Okaforn ba don kamar yadda Yakubun yace ne yana hannun wadanda zasu lallasa shi ta hanyar da ba zaiyi taurin kai ba.

Tunani kawai yake a cikin kansa na yadda zasu sami karin bayanin da zai kai su ga ko waye wannan Awwalun da ya faWa, kuma ko a ina yake, don a yanzu haka har an fitar masa da list din duk wani ma'aikaci dake karkarshin kamfanin nasu mai suna Awwalu, da wadanda suka yi aiki suka bar wajen har da ma wadanda applying kawai suka taba yi ba'a dauke su ba tukunna.

Ance idan rakuminka ya bata ka duba har cikin tulu, a yanzu ya koyi buWe idanunsa sosai wajen nema, maganar da Amina ta fada masa na cewar su nemi mutumin nan har a cikin prison ta bude tarin wasu abubuwa da yawa a cikin kansa, ta sa shi ya daWa fahimtar cewa bai kamata yayi limiting nemansa a iya wani waje guda ba, watakila tun farko abinda yasa suke ta zagaye suna dawowa kenan... Da wannan tunanin yake ?ara godewa ubangiji a kodayaushe da ya azurta shi da mace kamar Amina a cikin rayuwarsa.

?ofar dake bayan Yakubu a cikin videon ta buWe a lokacin, wasu mutane biyu suka shigo, dogwayen jikinsu kawai ya gani kafin Yakubun ya juya yaga mutumin da suke rike dashi.

Kuma ba don ya tabbatar da cewar Mr. Okaforn da suke jira ne za'a shigo dashi ba, zai rantse ba shi bane wannsn saboda fuskarsa ta kumbura gabaWaya, idanunsa sun shige a fuskar tasa sannan hancinsa da bakinsa na fitar da jini. A lokaci guda ya shiga girgiza kansa yana kallon Yakubun.

"This is not what I ask of him Yakubu, ( ba abinda nace kuyi masa ba kenan) mutumin nan yana da iyali..."

"Just ask your questions."

( Kawai kayi tambayoyin ka.)

Cewar Yakubun yana katse shi, daidai lokacin da mutanen nan biyu suka ajiye Mr. Okaforn a gaban camerar sannan suka juya suka fita.

Ma'aruf ya haWiye wani abu a ma?ogwaronsa yana girgiza kansa sanda Mr. Okaforn ya shiga magiya yana haWe hannayensa biyu cikin kuka. Sai kawai yayi karfin halin saita muryarsa sannan ya shiga magana da turanci.

"Komai zai koma daidai idan har ka bamu hadin kai akan dukkan abinda muka tambaye ka, ba zan bari su sake taSa ka ba, za'a maida kai gida cikin iyalanka lafiya, hatta ?arka Mary zan yafe mata laifin da tayi min akan ?ata, kuma ba zamu sake tuntubarka bayan nan, zaka cigaba da rayuwarka cikin kwanciyar hankali idan har ka fada min dukkan abinda ka sani Mr. Okafor."

Kuma bai bashi damar da zai tsaiwaita godiyar da ya fara ba yace.

"Ina jinka."

Babu musu balle tirjiya Mr. Okafor ya gyada kansa da sauri alamun zaiyi hakan kafin muryarsa dake cike da kuka ta fara magana cikin nasa yaren na Pidgin English.

"Kamar yadda ka sani Yallabai ni mai shara da goge goge ne a kamfaninka,to watannin baya da suka wuce, sai wani abokin aikina mai suna Sani ya same ni da labarin cewa ya samo mana hanyar da zamu yi kuWi mu daina wannan bautar, ya gaya min cewa akwai wani mutumi mai suna Isa, bayarbe ne amma kuma musulmi, yana harkar computer hacking da duk wani abu da ya shafi harkar technology na yanzu.

Rana Waya yazo yace min wai wasu mutane sun same shi da rokon cewa zasu bashi miliyan daya idan har ya shiga ofishinka ya samu wasu nambobi a cikin computerka, to shi bai san harkar komai na computer ba shine yazo ya same ni yace zai bani rabin kudin dubu dari biyar idan har na taya shi aikin, ya gaya min sau Waya cewar sunan mutumin da ya saka su aikin shi da Isa Awwalu amma bayan nan bai kara gaya min komai akansa ba.

Kuma sai a ranar da nake da aikin gyaran ofishin naka ne sannan muka yi waya da daya mutumin mai suna Isa, shi ya kwatanta min inda zan shiga a computer taka in kwafo wasu security numbers wanda sune na account din kamfanin, kuma na sami sa'a har naje na samo nambobin ba'a kama ni ba.

Kuma Sani ya gaya min cewa da wannan nambobin suka yi amfani akayi hacking account number kamfanin har aka turo muku da alert din ?arya alhali kuWin sun tafi ne zuwa wani account daban, kuma sunyi haka ne ta hanyar da ko banki baza su gane balle idan kun je ku sami wata gamsashshiyar amsa daga gare su.

Bayan mun gama aikin da sati Waya sai shi abokin aikin nawa ya kawo min kuWi dubu dari kawai yace min wai shima basu bashi yadda suka fada ba, amma idan sun bashin zai ciko min. Daga nan bai ?ara yi min mgna har tsawon lokaci kuma na tuntube shi amma yaki saurarata.

Ni kuma hakan sai nayi kokarin Waukan matakin da zan tsorata su su bani kudina, shi yasa naje na sami sbokin aikin ka Yallabai Faruk na gaya masa cewa ina da masaniyar abinda ya faru, nayi recording hirar mu a wayata sannan naje na sami abokin aikin nawa Sani da niyyar in nuna masa hakan.

Sai dai ina zuwa gidansa na tarar ya mutu har ana jana'izarsa. Sai na tsorata na dawo gida, bayan kwana biyu sai Isa ya kira ni da cewar inyi hankali watakila wadanda suka kashe Sani suna da alaka da wadanda suka samu aikin nan, a wannan ranar ne kai kuma kazo gidana Yallabai, sai dai bamu samu munyi magana ba ka dauki wannan yarinyar ka tafi.

A washegari kuma na tsinci labarin mutuwar Isa shima, shi yasa ba shiri na haWa iyalaina muka gudo nan garin ranka ta daWe, kuma nayi maka rantsuwa da kabarin babana tun daga wancan lokacin ban ?ara jin wani bayani daga kowa ba ranka ya daWe."

Mr. Okafor ya kai ?arshe a lokacin da Ma'aruf da kuma Yakubun suka cigaba da kallonsa, kallon da Ma'aruf ke yi masa daban ne, kallonsa yake yana kuma saurarensa da dukkan wani abu mai hankali dake jikinsa, kwakwalarsa na fahimtar kowacce kalma dake taruwa tana fitar da jimla guda a bayanin nasa, kuma bayan ya kai ?arshe, abu na farko da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login