Showing 60001 words to 63000 words out of 132946 words

Chapter 21 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1125

ya fara yi shine jawo wayarsa. Hannayensa suka lalubo nambar Martha a lokaci guda.

"Ki duba min a kananun ma'aikatan dake aiki akwai wani Sani da ya mutu kwanakin baya?"

"Okay sir." Ta amsa da sauri fahimtar cewa shima saurin yake yi a cikin muryarsa, kuma daga inda yake zaune yana jin karar keyboard din computer ta da take dannawa, cikin abinda bai fi rabin minti ba tace.

"Akwai yallabai, sunansa Sani Madugu, wani danuwansa ne yayi reporting mutuwarsa wata hudu da suka wuce, kuma har an bawa iyalinsa garatutinsa wancan watan."

"Thank you."

Kawai ya faWa sannan ya ajiye wayar, idonsa ya sake dawowa kan Yakubu da kuma Mr. Okaforn dake jiran abinda zai ce ta cikin computer, zai so kwarai yace a sake shi ya tafi ga iyalansa amma ba zai iya ba, bayani kawai suka samu daga wajensa babu wata shaida ko kuma kwakwaran bayanin da zai kaisu ga wani abu har yanzu, don haka sakinsa zai zama tamkar saki na dafe ne wanda ba zai fara hakan ba.

Saboda haka yayi ajiyar zuciya mai nauyi kamar ta cikinta ne zai fitar da tarin abubuwan da yake jin nauyinsu a cikin kansa sannan yace.

"A cigaba da rike shi Yakubu, amma kar ku sake taba shi..."

"Sir pleeeease, pleeese sirrrr, abeg naaaa, help me sirrrr pleaseeeeee....."

Magiyar Mr. Okaforn ta sake cika oficce din a lokaci guda kafin Yakubu ya daga murya ya kira mutanen nan, kuma suka shigo a lokaci guda suka Wauke shi suka sake fita dashi yana ta magiyar yana rokon? Ma'aruf.

"Kar ka damu, duka iyalan nasa ma suna nan tare damu, zan cigaba da rike su har lokacin da kace, 'Cox ina da wani aiki da zsn yi anan garin ma."

Ma'aruf ya gyaWa kansa.

"Nagode sosai Yakubu it's a pleasure to work with you.? Zan sake turo maka da wasu kudin insha Allah to keep things going."

Yakubu ya gyada kansa shima sau biyu a jere sannan kiran ya katse. Ya katse a lokaci guda da sa?on Amina ya shigo wayar Ma'aruf dake gefe, ya dauko ta ya duba, abinda ta rubuta dan guntu ne.

"Sugar, zanje kitso dan Allah..."

Yana gama karantawa wani sa?on nata ya kara shigowa akai.

"Ba nisa..."

"Kusa da gidansu Fatima ne..."

Gidansu Fatima, wannan kawar tata da yake yawan ji tana faWa, dazu tare suka fito ya sauke ta s gidansu tare da Hamida kafin ya tajo office, shima ya shiga ciki sun gaisa da kowa, don saura kwana biyu kawai tafiyar mahaifinta da kuma kaninta Aminu zuwa India, har da kansa ya yiwa Mami godiya da yaji labarin cewa ita ta Wauki nauyin tafiyar, ?anuwanta ne ya sani amma haka kurum sai yaji kamar saboda shi tayi hakan, shi yasa shima a yanzu da yaje yayi musu irin tata kyautatawar wanda da kyar suka karSa, abinda basu sani ba shine, zuciyarsa na gaya masa cewa zaiyi tarin abinda yafi haka ma indai akan Amina ne.

Saboda haka kafin wani sa?on ya sake shigowa ya shiga typing amsar sa da take jira.

"Ki tabbatar an rubuta sunana a jikin kitson nan Doll."

Sakon ya tafi a lokaci guda tare da shigowar kiran Faruk, don haka ya fasa cigaba da rubuta abinda yayi niyya ya Wauka.

Muryar Faruk Win ta fito a lokaci guda da ya kara wayar a kunnensa.

"Muna High Prison, mun sami mutumin nan B, yana ganinsa ya gane shi, yanzu haka ma ya fadi duk wadanda suka saka shi ya fita daga Prison din suma an tafi za'a fito dasu don dukkaninsu ma'aikatan wajen ne."

"Alhmdlilah, Alhmdlilah, Alhmdlilah...."

Itace kalmar dake fitowa daga bakin Ma'aruf tunda yaji abinda Faruk Win ya faWa na farko. Ya mi?e tsaye a lokaci guda ya fito daga kujerarsa ya dawo tsakiyar office din hannunsa a cikin gashin kansa yayin da zuciyarsa ta kasa tsaida kanta waje guda a tsakanin murnar wannan nasarar da kuma taraddadin abinda yake shirin tambaya.

"Ya gaya maka wani abu Faruk? Any clue na su waye mutanen da suka sa shi aikin kafin yaje ya karbi kudin?"

Ya tambaya muryarsa a tsaye kyam!

A can bangaren,Faruk ya girgiza kansa yana kallon hayaniyar dake faruwa a gabansa wadda ma'aikatan Prison Win suka tayar na Cewar baza'a tafi da ogansu ba kasancewar har da sa hannunsa al'amarin,tarin ?an sandan da suka zo dasu na ta ?o?ari wajen hana su haurowa inda su suke tsaye ana shirin fito da mutumin, sai ya girgiza kansa a hankali sannan yace.

"Ko waye Awwalu ya shiga uku Ma'aruf, don gayen yace min mutum daya ya gani da ya saka shi aikin, shi ya bashi wallet dinka da wayoyinka ya kuma fada masa duk abinda zaiyi, kuma yace sunansa Awwwalu."

"Awwalu." Ma'aruf ya furta ba tare da ya san ya fada ba.

"Awwalu." Ya sake faWa a hankali.


****

"Awwalu."

Hajiya Kilishi ta faWa tana kallon Aminiyarta Hajiya Salamatu.

"Ni Awwalu zai yaudara ya mayar mara hankali Salamatu? Wai har ni Awwalu yake kokarin cin amana a harkar nan?"

Ta sake faWa amon muryarta na fitowa cike da takaici. Suna zaune a cikin falon gidan Hajiya Salamatun ne,inda bayan su kaya ne fal na sabbabin atamfofi da kuma lesuna tsibiri-tsibiri an zube su kamar banza kasancewar dawowar Hajiya Salamatun kenan daga ?asar da take yo siyayyar kaduwancinta.

Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.

"Wannan ai ba komai bane Kilishi, ki duba fa ki ga yadda kike cin amanar wadannan mutanen dake tare dake, to har dan abokin aikin ki wanda kullum yake ganin abinda kike yi ya kwaikwayi hakan sai kiji wani zafi? Kamata yayi ace daman kin dayde da shirya masa.

Kilishi dake kallonta tace.

"Maganganunki sunyi zafi Salamatu, amma haka ne, tabbas abinda kika faWa haka yake, wannan ba komai bane don Awwalu ya nemi ya bauWe, daWin shine na daWe ina shirya masa dama, kuma a tunaninsa ya koyi irin taku na yana shirya hanyarsa bai san cewa sawun giwa ya take na rakumi ba kuma ko a gidan giya akwai babba, sannan sama tayi wa yaro nisa sai dai ya Waga kai yayi kallo."

"Wannan haka yake, nice ta farko da zan fara yi miki wannan yabon bayan ke Kilishi, yanzu ki gaya min a ina kuka tsaya tare dashi."

Kilishi ta kurbi lemon hannunta tana kallon Salamatu ta cikin gikashin kofin, kuma bata ajiye ba sai da ta shanye shi tas sannan tace.

"Tun daga ranar da ya kawo min hodar nan daga lagos bai sake ce min komai ba nima kuma ban kira shi ba, dukkan abinda yake ciki ina jinsa ne ta hanyar wannan Sadik din dana tura ya zama abokinsa a kwanakin baya, saboda haka na riga na daWe da gama shirya masa, yanzu jira kawai nake yi ya nunawa Sadik inda ya tara Cd's din da yake Waukar muryarta, ya riga ya ganoinda computers din suke, da mun samu Cd's din, zan sa ya ?ona komai ne gabaWaya sannan inje in fuskance shi.

Zan gaya masa dukkan shirinsa da na san yana yi da kuma yadda akayi na kama shi, kafin in aiwatar da nufi na akansa."

"Me zaki yi masa?"

Kai tsaye Salsmatun ta tambaya tana wulli da wani leshi dake kan cinyarta zuwa cikin kayan dake baje a dakin.

"Haukata shi zanyi Salamatu, ba zan kashe shi ba, Haukata Awwalu zanyi ta yadda zai kare rayuwarsa yana biyan bashin cutar da yaso yayi min."

Salamatu ta gyada kanta tana taSe baki kafin tace.

"Shi kuma Sadik din fa?"

Kilishi tayi shiru tana nazari kafin tace.

"Sadik irin mutanen da basu da ra'ayin kansu ne Salamatu, kuma daga Ghana yake kin sani saboda haka wani kaso kawai zan bashi ya koma kasar su, da ya koma ya cigaba da shaye-shayensa shikenan bani da wata matsala dashi na sani."

Salamatu ta gyada kanta tana murmushi sannan ta sake cewa."

"Victoria Island dai na can na jiranki Kilishi, kafin ki kammala komai na tabbata an gama gine-ginen nan."

Girgiza kanta kawai Kilishi tayi kafin tace.

"Bar wannan zancen tukunna yanzu Salamatu, jikina ya bani cewar Ma'aruf ya dage akan binciken kamfanin nan nasu, bai ce dani komai ba amma na fahimci hakan ne kawai, shi yasa na tsayar da komai nake son inyi in gama da Awwalu akan kari.

Tunda kin san indai har sun sami mutanen nan duk abinda zasu samo zai kaisu ne kawai ga Awwalun tunda shi kadai suka sani, kin ga idan na kammala abinda zanyi dashi kafin su nemo shi, zasu je su same shi ne a haukace, haukan da ba zai taSa warkewa ba. Daga nan sai in dawo in fuskanci batun yarinyar nan da kuma Baffa, yadda zan tsara mutuwarsa a ranar da kudi na gaba zasu shigo kamfanin."

Dariyar da Hajiya Salamatu ta kyalkyale da ita tana debo wani zagi wata iriyar dariya ce da babu shiri Kilishin ta shiga taya ta itama, muryoyinsu suka karaWe falon cikin wani irin amo mai Wauke da tsananin nishadi da kuma ta?ama, ta?amar da a cikinta Kilishin ke jin kanta zuwa wani mataki da take jin cewa bata da takwara a duniyar nan.

Abinda bata sani ba shine, al?alami ya riga ya bushe akan wata ?adddara da zata wanzu cikin kwanakin da take lissafawa kanta da wani labari da yasha banban da wasi?ar da zuciyarta ke biya mata!

Kuma zaren labarin ya fara ne a daidai wannan lokacin kuma a cikin wannan dakin!

***

_Wanne irin sirri kuke tunanin Hajiya Mardiyya na Soyewa akan Jawad? Kuna tunanin sirrin yana da alaka da halayyarsa?_

_Sannan ta ina kuke tunanin labarin Jawad da Zainab yana da ala?a da Sangaren su Kilishi?_=??

_Ma'aruf ya tattaro kowanne Sangare na matsalarsa, kuna tunanin ya fara taka matakin nasara?_

_Ga kuma tsarin da Hajiya Kilishi ke yi tun kafin su kai ga ?arshen binciken nasu, matar nan A ce!_=??

_Amma ya kuke tunanin hakan zai kaya??_

_Ina gaya muku BabyDoll din Sugar ta tanadar mana wani surprise mai daWi a babi na gaba._=?
?=?
?>?p?>?p?

_Muje zuwa!_=??

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*14*

*Tarin Addu'o'in ku da kuma fatanku na alkhairi na Waya daga cikin abinda ya farfaWo dani, bani da bakin da zan ce Nagode, don ina ji kamar kalmar tayi kadan in dora ta a mizanin goriyar tawa... sai dai ince Allahu ya saka muku da alkhairi ya kyautata rayuwarku ta duniya da kuma lahira.*

*Nagode da tarin ?auna.*

~~~~~~

_I'll hold you when things go wrong..._
_I'll be with you from dusk till dawn..._
_Baby, I'm right here... -ZaynMalik & Sia._

***

Hannun Inna dake ri?e da cokali ya juya wani kwadon zogalen da yaji kuli-kuli da kuma su tumatir daga can tsakar gida inda take zaune yayin da a lokaci guda da Amina dake zaune a gWaki ta sauke wayar hannunta daga kunnenta.

Idonta ya tsaya akan Amman yayin da kalamanta na yau suka shiga dawowa cikin kanta. A dazu bayan fitar Baba, sun fi ?arfin awa guda suna magana, magana sosai irin wadda tun bayan tafiyarta basu yi irinta ba kasancewar wannan ba'a waya bane ba, sun sake tattauna tarin abubuwan da suka gudana a baya sannan ta gaya mata cewar ta cigaba da rike Hamida hannu biyu kafin ta ga abinda su Rukayya ke shirin sake shiryawa, wanda har a yanzu ta jaddada mata da cewar kar ta bari Ma'aruf ya sani.

"... Ki cigaba da tafiyar da al'amarin gidanki kan turba mai kyau Amina, daga shi har yarinyar kar ki basu kokwanton wani abu yana faruwa daban tare dake, ki barshi yaji da matsalar wajen aikinsa da yake fuskanta yanzu, kuma kar ki taSa tambayarsa wani abu idan har ba shi ya gaya miki ba, don tambaya hanya ce mai ce mi?ak?iya ga zargi... Don haka ki kyale shi da dukkan wata tambaya da ta shafi binciken da yake yi, kwanciyar hankali shi yafi bu?ata daga gare ki yanzu, idan har muna bu?atar wani bayanin, akwai hanyar da zamu samu abinda muke nema daga gare shi, zai faWa miki duk abinda kike so ba sai ma kin tambaya ba."

Tana tuna yadda ta dinga juya maganganun a lokacin, yadda Amma ta gata mata dukksn hanyoyin da mace zata bi idan har tana son samun amsar wani abu daga wajen mijinta, ba tare da shi kansa ya fahimci tambayar tata da kuma abinda take nema ba.

"Rayuwar mace gabaWaya dabara ce da kuma kissa Amina, idan da har bayan ibada kowacce mace zata Wauki waWannan abubuwan guda biyu ta ri?e su a kowanne fanni na rayuwarta, da tabbas mata da yawa zasu sami rabin aljanarsu ta duniya."

"Kin san ranar nan kuwa Jamila tazo nemanki?"

Maryam dake zaune a gefenta ri?e da Hamida wadda ta Wane kan cinyarta tana zana mata fulawa da abin Rani ja kan fararen hannunta ta fada.

Amina ta kalle ta, tana tuno Jamilan da take fada, wata ?awarta ce da a islamiyya ce da babu gaira ba dalili ta tsiri daina yi mata magana, har Amma sai da ta shiga cikin al'amarin a lokacin wajen tambayarta abinda ya faru amma tace babu komai.

"Da gaske? Me tace kuma?"

"Wai taji labari ance kinyi aure ne shine tazo yin murna, wai a rakata inda kike ku gaisa."

Amina tayi murmushi tabya jinjina kanta alamun mamaki kafin Maryam din ta cigaba.

"Amma tace wai ai sai ta saka rana tazo a raka ta, shine ta karbi nambar wayar Amman wai zata kira, ni kuwa na bata wrong number, ranar da ta gaji ta tako ?afarta tazo, kwanciya zanyi ince bani da lafiya?"

"Saboda me?" Amina ta tambaya tana dariya.

"Dan Allah ki rako ta ko kuma ki bata namba ta, kinga ai a kawo karshen gabar tata."

Maryam ta girgiza kanta tace.

"Wallahi Yaya wannan yarinyar ba mutunci ne da ita ba, haka kurum taje ta jawo miki wata matsalar..."

"Haba dai, ai bata isa ta jawo min wani abu da yafi karfin wanda nake ciki ba Maryam, tunaninta bai isa yafi na mutanen da nake tare dasu ba."

Ta fadi hakan fuskar Kilishi na haskawa a cikin kanta.

"Bata sake yi kiranki ba har yanzu?"

A dazu da suke magana da Amma haka ta tambaye ta, ta girgiza kanta kafin tace.

"Bata sake yi min magaba ba tun daga lokacin Amma, na kula kamar kwana biyu hankalinta ya rabu ne kan wani abun, tana yawan fita sannan bata maida hankali kan abubuwan gidan sosai."

Amman ta gyada kanta a lokacin sannan tace.

"Watakila ta fahimci binciken da suke yi ya fara doso ta ne, watakila kuma tana da tsarin wasu abubuwan bayan sha'anin yarinyar shi yasa tayi miki shiru.

Kilishi tana da tsari, ta san me take yi... Wasu abubuwan take saitawa kafin ta waiwaye ki, ba zata baki aikin a lokacin da ta san hankalinta baya kanki sosai ba, watakila kuma tsuntsu biyu take neman jifa da dutse Waya, abu biyu zata haWa a lokaci guda. Ba lallai ki iya sani ba, amma idan kin ga alamar wani abu ki gaya min watakila zamu iya samo wani abun a cikin takunta."

Ta gyada kanta a lokacin sannan ta Wago ta kalle ta sosai kafin tayi tambayar da ta daWe tana ci mata rai a zuciyarta.

"Amma idan har ta kawo maganin ta yaya zanyi amfani dashi? Lokacin da muka yi magana kince komai zai faru amma kuma ba abinda zai faru? Kince a idonta kawai Hamidan zata makance amma ba a gaske ba."

Murmushin da Amman tayi mai fadi ne a lokacin kafin tace.

"Kar ki damu, har na fara wannan shirin Amina, na gaya miki takunta zamu Wauka kamar yadda muka fara yanzu, zamu shammace ta ne ta hanyar da take shammatar mutane, ta hanyar da take ganin tata ce itace mai ikonta, don haka ki bari lokacin yazo zaki san komai, nafi so a yanzu ki tsaida hankalinki akan gidanki tukunna, nan ne Sangare mai girman da yafi kowanne bukatar tallafawarki a yanzu."

"Wani abu kike ciki yanzu a gidan?"

Tambayar Maryam ta dawo da ita duniyar zahiri, sai tayi saurin girgiza kanta.

"Ina nufin tunaninta bai isa yafi na mutanen gidan da yanayin wayewarsu da komai ba, na gaya miki yadda su Samiran nan suke, yanayin rayuwarsu ta banbanta da namu ta hanyoyi da yawa."

Ba tare da ta fahimci komai ba Maryam tace.

"Shi yasa bana son zuwa ai, kin san ni duk inda za'a wulankanta ni ko a raina ni ba son zuwa nake ba, wallahi ko da su Amma suka tafi Jigawa kai Aminun nan da muka je gidan Kawu Mallam baki ji yadda na dinga ji ba, na tsani a dinga min iko da abu."

Sanin wannan halin nata sarai yasa Amina bata ja zancen ba tace.

"Allah ya taimake ki kar Baba ya miki irin nawa."

Sai ta girgiza kanta tace.

"Wallahi ba zan iya ba Yaya, ba zan taba iyawa, nifa kinga ko kayan gidanki da na san da yawa nasu ne, zasu sa zuciyata ba zata nutsu wani ya shigo ya gaya min magana...Don ma dai Hajiya Kilishi ce, da sauki ta saba mana alkhairi, shi yasa ma banji komai sosai ba ko a wannan tafiyar dasu Baba zasu yi."

Amina tana murmushi tace.

"Allah ya shirye ki Maryam."

A wajenta dukkan wannan abin da take faWa tatsuniya ce kawai, don bata san tarin kalolin da rayuwa ke haskawa Wan adam ba.

Daga haka idonta ya jai waje inda Amma ke zaune da kwano a gabanta da kuna Hafsa da ta shigo a lokacin daga islamiyya tana tambayar.

"Har yanzu su Yaya suna nan?"

"Wai ina Aminun yake ne ma?" Amina ta tambaya.

Maryam ta tabe bakinta tace.

"Abokanansa ai ba sa kyale shi tunda ya dan ji saukin nan, yanzu zaki ji sallama sun shigo sun gara wheelchair din sun fita dashi musamman yanzu da suka san jibi za'ayi tafiyar nan."

Kafin Amina tace wani abu Hamida dake kan cinyar Maryam din ta taso da sauri tana nuna mata kunshin da aka gama da murnarta.

"Babydoll yayi kyau?"

Wani abu ya ratsa cikin kan Amina, ta rasa ta yadda zata yi yarinyar nan ta daina kiranta da haka, Ma'aruf ya vuvi kwakwalarta da yawa, kuma kagin ta amsa idon ta ya gano mata Hafsa, sai kawai tayi wajen da sauri tana fadin,

"Aunty Hafsa come look, zo ki gani me aka min
..."

Mamaki ya kama dukkaninsu. Maryam ta gyada kanta tace.

"Ina gaya miki Hafsa ta ?ar rashin mutunci yarinyar nan, yanzu wai daga zuwanku har ta san ta gaya mata sunanta Aunty Hafsa...? Bari Adam yazo kuma mu ji Uncle Adam."

Dukkaninsu suka yi dariya Amina na fadin,

"Ni na san kamar fuska kawai muke yi da Hafsa ai, amma ina zan iya da halinta."

Maryam tana mikewa tace.

"Yarinyar nan zata kunyata ki a cikin mutane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login