Showing 63001 words to 66000 words out of 132946 words

Chapter 22 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1130

watarana, gwara ma ki gaya mata ba sunanki BabyDoll ba..." Ta dan yi shiru sai kuma tace.

"...Amma kuma ya iya zabar suna."


Dardumar dake gefenta Amina ta Webo ta cilla mata tana faWin.

"Ranki zai Saci wallahi...!"

Wayarta tayi kara a lokacin, Fatiman da take ta jira ce.

"Haba Fati, wai bokiti guda ake soya mana ne?"

Daga cikin wayar, a gaban ?awarta dake soyar waina Fatiman tace.

"Kin san mutanen da aka tsallake ake yi mana ne kike ta kwala min kira, to wallahi ko sun zo daukar ki ne sai sun tsaya mun ci wainar nan Allah."

"Wa ya gaya miki tun yanzu zan tafi? Ni kawai na ?agu ne, bakina sai tara yawu yake."

Fatiman tayi dariya tace.

"Ki cewa Wan Baban yayi hakuri, gani nan a hanya."

A lokaci guda kalaman Fatiman suka tafi cikin kan Amina dake zaune suka buga wani abu, wani abu da taji dirarsa har cikin ?irjinta, wani abu da yayi mata kama da tashin hankali a lokaci Waya, taji ma'anarsa na yin fadi a cikin zuciyarta tana so tafi karfin kalmar kokwanto.

Hannunta ya kai kan cikin ta a lokaci guda da kalmar Fatiman ta furta akan lebbenta, kwana biyu bata jin dadin jikinta sam, tana ta yin komai ne amma bata fahimta ba sai da ta fara jin tashin zuciya, haka kurum take ji kwana biyu bata son kamshin wasu abubuwa,ko a yanzu ma zogalen da Amma ke haWawa ne yasa ta kasa tashi taje wajenta, tun daga nan take jin cewa bata son ?amshinsa, sannan kuma yadda take ji kamar wani abu a cikin cikinta na rawa na jiran wainar fulawar da Fatiman ta tafi siyo musu, yafi karfin yadda take son wainar a kodayaushe.

Amma tsaya, haka da wuri komai yake faruwa? Kai tsaye kawai? Idan zata tuna lokacin da Aunty Ma'u ta sami cikinta na farko ba irin wahalar da ita da mijinta da kuma Amma basu sha ba.

Don ta kusa sati uku kwance a asibiti, kuma Amman ce mai kwana da ita a lokacin, to ta yaya ita yanzu tana zaune komai zai faru ba tare da ta ma sani ba? Sai kawai ta ture zancen Fatima a gefe ta mike ta fito daga falon lokacin da ta kula Amma ta rufe kwanon zogalen.

".... Suna gidanmu gabaWaya, zaki zo? Har da Barbie nake da."

Ta jiyo Hamida na lissafowa Hafsa kayan wasan ta yayin da take zare ido cike da Woki tana kallonta. Tana juyowa suka haWa ido da Inna dake kallonta tunda ta fito daga falon sai dai kafin tace komai Maryam ta fito daga Waki da hijabi tana fadin ta tafi.

"Ina zaki je?"

"KuSewa zata siyo anan bayan layi gidan su Aisha, ita kaWai ce ba'a samo ba a kayan naki."

Amma ta faWa tana jawo wata leda mai yalo da ba?i da aka cika taf da kullin bakaken leda.

"Ga Kuka anan, wannan kuma busashshen zogale ne ga yajin sannan ga dakakkiyar citta da tafarnuwa anan..."

Ta shiga lisaafin kowacce leda daga ciki yayin da Amina ke kallonsu, zuciyarta na bajewa da wani daWi da kuma ganin daraja ta girman Uwa, tabbas dole ne wanda ya rasa ta yayi kuka da idanunsa kullum a duniya, don ?arya ne ka sami mai kulawa da kai tun daga ?asan ruhi a duk duniyar sama da ita, sai dai kuma ubangiji kan Soye wasu tarin hikimomin nasa ga rayuwar wadanda ya karbi tasun, hukuncinsa daidai ne a kodayaushe.

?azu kafin ta tafi gidan kitson a hira kawai take tambayar idan har yanzu gidan wata mata mai suna Salamatu akan layin nasu tana sayar da kuSewa, tace duk bata dasu sai gashi har Amman ta tanadar mata komai a yanzu. Da murmushin da godiyar ba zata misaltu ba tace.

"Madallah, Allah ya saka da alkhairi."

Amman ta amsa da Ameen sannan hannunta ya dauko kwanon zogalen nan ta mi?o mata, bata ko bude murfin ba, amma ?amshinsa ya tafi a tsaye har cikin hancinta, ba shiri ta juyar da kanta da sauri, sannan ta shiga girgiza kanta.

"Amma madallah, Fati zata kawo mana wainar fulawa yanzu."

Amman ta kalle ta na wasu sakanni kafin ta dauke kwanon tace.

"To ita zaki iya ci?"

Da murmushin ta ta kalle ta tace.

"Amma wainar fulawa ce fa."

"Wannan ma ai zogale ne kuma kina cin sa a da."

Fassarar da Amina ta yiwa kalaman Amma daban a cikin kanta, don haka a lokaci guda idanunta suka kaWa ta shiga sake girgiza kanta.

"Wallahi Amma ba wani abu nake nufi ba, kawai ji nayi bana son ?amshinsa, ya za'ayi in ?i ci haka kawai..."

Amman ta gyada kanta tana katse ta.

"Na sani ai, na san da lalurar shi yasa na tambayeki... Kin fada masa ma tukunna? Don ban ga alamun kun je asibiti ba?"

"Asibiti?..."

Amina ta tambaya kai tsaye tana kallon mahaifiyar tata, idan ka shigo a wannan lokacin ka kallesu, su biyu zaune akan tabarmar nan, zaka yarda an ?ir?iri wani mudubi ne dake zabge shekaru yana kuma ?ara du a lokaci guda, don kamarsu daya sak, yanayin sirantar jikinsu da idanun da hancin, dama yawan gashin kan mai laushi duk da na Amina ne kawai a buWe, banbancinsu kawai shine shekaru da kuma hasken fatar da Aminan tafi Amman a yanzu.

"... Lafiyata kalau fa Amma ba abinda ya same ni..."

Murmushin da Amman tayi shi ya katse ta daga sake magana, ta juya da kanta bata kalle ta ba sannan tace.

"Baki san kina da ciki ba?"

A lokaci guda tambayar ta janye Amina daga gangar jikinta, ta jita tana tashi zuwa wata sama mai nisa, tana barin gidan, tana batin unguwar, tana barin garin tana barin ?asar, tana barin nahiyar ma gabadaya... tana ganin kowa da kuma komai a cikin kanta kafin ta faWo a lokacin guda??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????, ta taho tun daga wannan lulukin a tsaye, babu wani hijabi har inda take zaune, kuma ?arar dirar tata ya cika kunnwanta bakidaya!


***

A cikin motar dake tafiya, Ma'aruf ya kalli Faruk dake zaune a gefensa bayan ya ajiye wayar da suka yi da wani jami'in ?an sanda yace.

"Yana da wayo Faruk, ko waye Awwalun nan yana da wayo, tunda har daga wadannan mutanen har Mr. Okafor bai taba waya tare dasu ba."

Faruk ya girgiza kansa yana komawa da baya ya jingina sosai da kujerar da yake zaune kafin yace.

"Shi yasa na gaya maka zama zamu yi sosai kawai mu fara sabon bincike, gobe dole ka fito early, sai mu ga ta inda zamu fara."

Dawowarsu kenan daga Police headquarters na Bompai inda aka garkame duka mutane hudu ma'aikatan prison din dake da sa hannu akan fitar wannan mai laifin, inda har a yanzu daga mutumin har da mutanen kowannensu ya tsaya akan rantsuwar wani mutumi mai suna Awwalu kawai suka sani akan al'amarin, a yanzu haka an sami nambar da suka yi magana da shi Awwalun a lokacin, an mika ta hannun IT department, kuma zuwa gobe suke sa ran samun bayani daga wajensu idan har za's iya tracking wani waje da za'a iya samun Awwalun ko kuma wani bayanin da zai ksi su gare shi.

Ma'aruf ya dunkule hannunsa akan bakinsa kafin yace.

"Kana tunanin mu shigo da Yakubu wannan Sangaren shima?"

Faruk ya girgiza kansa.

"Yakubu ya iya aiki B, amma ka san yana da nasa matsalolin... Yana aikin ne tare da mutane da yawa kuma ban san me yasa ba amma haka kurum jikina yake bani cewa neman Awwalun nan yana bukatar sirri, sannan ya gaya maka cewa akwai aikin da yake yi yanzu haka shi yasa har zai cigaba da kula da wannan Mr. Okaforn, ka ga we have no time da zamu jira shi kenan.

Kawai kaje gida ka huta, gobe early in the morning mu san ta inda zamu fara kafin mu sami bayani daga IT members din, zan taho da ?an bayanan da na hada sai mu gani."

Ma'aruf ya gyaWa kansa sau biyu kafin yace.

"Gobe Abdurrahim zai dawo and I think ni da Ishaq zamu dauko shi daga airport, but insha Allah zamu yi komai."

"Wow! Allah ya kawo shi lafiya..." Cewar Faruk Win kafin ya cigaba.

"Da safe kafin in kira ka, munyi magana da mutanen Rotel&co (kamfanin da zasu yi aiki dashi na gaba) na gaya musu ranar da muka yi fixing zamu zauna dasu... Amma yanzu da wannan abubuwan da suka taso, ina ji kamar a kira su mu ?ara Wagawa..."

Ma'aruf, ya sake girgiza kansa.

"Let them, zamu iya Insha Allah Faruk, kar ka manta duk wannan fafutukar da muke yi Baffa bai sani ba, so abinda kawai zai sani shine idan muka tsayar da aikin mu, har zuwa karshen shekarar nan fa bamu da wata kwangila a gaba, wannan ce damu kawai, may be idan muka yi aiki mai kyau, zamu iya sake wani contract da wasu."

"Haka ne."

Cewar Faruk Win kafin wayarsa ta fara ?ara, ya dauka ya kara a kunnensa ya shiga waya da makanikensa wanda zai zo ta dauki motarsa data mutu a ?ofar Prison din nan da suka fara zuwa.

"Canja ta zanyi kawai Aminu, kawai dai a fara gyarawa mu gani tukunna..."

Faruk Win ya? shiga magana, sai kawai ya dun?ule hannunsa guda dunkule akan bakinsa yayin da har a lokacin yake kallon titi.

Wani iri zuciyarsa ke masa, wani iri yake ji a dukkanin jikinsa gaba daya, kowannan tukin ymda yake yi ji yake kawai kanar a cikin wani zagaye yake tafiya da idan suka yi gaba suna sake, tunanimsa yq kasa hango masa waye wannan Awwalun da kuma dalilinsa na kassara su, yadda yake amfani da kwakwalwa dana kudinsa don ganin kawai ys tarwatsa su.

Zai rantse har da Allah dalilin wannan abin bai taru kawai akan kuWi ba, dole akwai wani labarin dake ?ar?ashin komai.

A haka har suka karasa kofar gidan Faruk din ya sauke shi.

"Ka huta sosai B dan Allah idan kaje gida, ka barwa gobe komai, let your mind rest."

Abinda Faruk din ya fada kenan bayan ya fita ya tsaya daga wajen motar, kuma da ya kalle shi sai yaga kamar yana kallon mudubi ne wanda ke hasko masa irin tarin gajiyar dake tattare dasu, idanun Faruk din kadai sun kada kamar nasa, don banda ruwan da suka siya bayan sunyi salkar La'asar babu wani abu da ya shiga cikinsu a tsayin ranar yau din.

Sai dai kafin ya buWe baki ya bashi amsa, kofar falon gidan daga can barandar dake fuskantarsu ta buWe, yara biyu mace da namiji suka fito da gudu suna ihun.

"Daddy! Daddy!"

Kafin matarsa ta baiyana itama ri?e da hannun karamin Wansu Aarif wanda ya fara tafiya, sai kawai yayi masa murmushi sannan ya ja motar zuwa can gate inda maigadin dake tsaye bai rufe ba kasancewar ya gaya masa yanzu zai iso. Da a yau bashi da inda zai je ya huta gajiyarsa kamar Faruk, baya jin zai iya hana ciwonsa tashi kotawacce hanya.


*

Siraran hannun Amina suka kwankwasa kofar bandakin a hankali, idanunta na kallon tiririn daje saman ?ofar inda wajen glass ne maimaikon katakon dake kasa.

"Come in..."

Muryar Ma'aruf ta faWa daga ciki, sautinta ya fito lazily kamar yadda yanayinsa yake tun lokacin da ya shigo, ta tsaya kamar ba zata bude ba sai kuma tasa hannunta daya da baya ri?e da Wan karamin towel din da ta ri?o, ta murda handle din a hankali, kofar ta rabu da wata ?ar siririyar hanya amma sai ta kasa karasa buWewa, ta tsaya rike da handle din kawai tana shakar daddadan dimin dake fitowa hade da ?anshin sabulunsu.

Baifi sakanni biyar ba Ma'aruf yaja kofar daga ciki ya buWe ta gabadaya, yana tsaye daga shi sai towel din dake jikinsa na wankan da yayi, gashin kansa a jike yake gabadaya ya barbaje wasu kuma sun manne da fatarsa, tana kallon idanunsa da suke a lumshe sosai don kusan rabinsu je kawai a buWe kanar mai jin bacci, sai kawai ta karaso ta rufe takun biyun dake tsakaninsu, tasa towel din hannunta akansa sannan ta shiga goge masa gashin a hankali da duka hannunta biyu.

Ya rufe idanunsa duka biyun a lokaci guda da hannayensa suka zagaye ?ugunta yana rike ta sosai a jikinsa... Yana jin yadda siraran yatsunta ke motsi a cikin gashin nasa ta jikin towel Win. Sai kawai tayi Wage da kafafunta ta ?ara tsawo daidai shi sannan ta dora goshinta akan nasa, ta janyo hannayenta daga saman towel din ta zura su ta kasan sa, numfashinsa ya kara nauyi akan fuskarta sanda yatsun nata suka shiga cikin gashinsa gabaWaya, tana jin yadda ya ?ara ri?e ta a jikinsa, Wumin jikin nasa da kuma ?amshin sabulun na mamaye ta gabaWaya.

"Are you feeling better?"

Muryarta ta fito a hankali, a hankalin da shi kansa da yake jikinta can kasa yaji ta sosai.

"Abinda nake ji yafi karfin Better Babydoll, you are healing me..."

Kalaman suka sata murmushi, suka kuma bata kwarin gwiwar yin Wage da kafafunta a hankali kafin tayi kissing dinsa, bai ce komai ba da farko sai da yaji da gaske take sannan bakinsa ya furta.

"Damn it!"

Da haka ya sake ri?e ta sosai a jikinsa yana tuna mata da banbancin dake tsakanin abinda zata iya da kuma wanda shi zai yi, tsawon mintuna kafin ta janye zuwa baya a hankali tana kallonsa.

"I love you." Muryarta ta fito kamar wadda ta tsaya a tsakiyar gudu.

"I love you too Noor."

Ya fada tasa muryar?hankali kwance. Sai tayi murmushi mai fadi jin sabon sunan da ta samu kafin a hankali ta janye towel din daga kansa ya fado zuwa wuyansa sannan ta saka hannunta na dama ta shiga gyara gashinsa zuwa baya a hankali.

"Da zan iya tsaida lokaci zan tsayar da wannan daren yayi ta sake faruwa Sugar, har sai ka dawo daidai, sai na tafiyar da gajiya da kuma damuwarka gabadaya, this is our own happy place, ni da kai kawai."

Ta fada idanunta na kan gashin nasa da kuma yadda take gyara shi, ya sake rike ta a hannunsa kafin ya gyada kansa a hankali sannan muryarsa ta fito.

"Nima haka BabyDoll, I wanna see the sun rise on your skin kullum, amma kar ki damu da nayi settling abubuwan da ke gabana we're going on a honeymoon, somewhere far away, just me and you." (Da na gama da abubuwan da dake gabana zamu tafi yawon amarci, wani waje mai nisa daga ni sai ke kawai.)

Ta gyada kanta tana kallonsa da murmurshi a fuskarta, sai ya sake cewa.

"Yaya kika bar su Amma?"

Su Amma, sunan ya tuna mata da gida da kuma dukkan abinda ya faru a can, sai taga kamar taje wata duniya ne ta dawo, rayuwarta a can da kuma a wannan gidan tana da tarin banbanci, a gidansu a gaban iyayenta da kuma ?anuwanta, ita Amina ce, Aminar da kowa ya sani Aminar da ita kanta ta san kanta a ita, amma idan ta dawo gidan nan sai taji ta koma wata daban, wata suruka a gidan ?an gayu da kuma Wan gayun mijin dake sawa taji kamar sune ma'aurata mafi sa'a a duniya, bata jin kanta a komai sai a matsayin Babydoll din da yake kiranta. Fuskar Hajiya Kilishi ce kawai mai ruguzo da ita tana tuna mata cewa ba'a aljanar duniya take ba.

Amma kuma bayan hakan a yanzu, karo na farko sai taji cewa kamar an ?ulla wani zare ne da ya haWe waccan duniyar tata da wannan, kalaman Amma, bata tabbatar ba, ba wai bata yarda ba... Kawai kokwanto ne a cikin kanta har yanzu...

Kokwanton da ta kasance a cikinsa tun daga wancan lokacin, don bata sake cewa Amma komai ba, basu sake maganar ba gar suka taho, kawai dai kowa ya san yanayinta ya canja, tunanin ya cika kanta, tunanin da a cikinsa babu komai sai na yadda zata gayawa Ma'aruf hakan, fon a tsarin da tayi, a tsarin da tayi na kokarin boyewa kowa, kowan da Hajiya Kilishi ta zamo sila babu Ma'aruf, hasalima shine daya hannun da zai talkafa mata wajen cimma dukkan abinda ta tsara din, tsarin da ko Amma bata san shi ba...

Amma kuma tun kafin tazo gaban nasa, sai ta rasa ta yadda ta yadda zata iya harhado kalaman da zasu tashi ma'anar da zata gaya masa, ta kasa tunanin konai, tana jin kwakwalarta dama zuciyarta fayau, don haka ko a yanzun babu abinda ta iya cewa sai kawai ta shiga bashi labarin gidan nasu da kuma yadda Hamida ta sake da ?anuwanta.

Har ya shirya suka koma falo inda ya cika cikinsa da abincinta kafin Hamida ta cika kansa da nata surutun, har suka yi bacci, tana rungume a jikinsa tana jin numfashinsa a hankali kafin ya koma mai nauyi alamun gajiyar dake jikinsa tafi ?arfinsa.

Har Asuba da tayi, ya fita masallaci ya dawo ya same ta akan tata sallayar, tana zaune gaban Mahaliccin data idar da ibadarta yayin da zuciyarta ke karanto tarin addu'o'in da basu da ?arshe.

Daga bayanta ya tsugunna akan gwiyoyinsa, sannan ya zuro hannayensa duma biyu ya kara su a bayan nata, ya tsayar dasu yadda ta yi wa nata wajen addu'ar sannan ya Wora haSarsa a saman kanta.

Tayi murmushi a hankali tana jin ?amshin sabon turaren da ya fesa a jikin sallayarta na shigar mata har cikin kai, ?amshin mai sanyi ne, amma ita tana jin ?arfinsa har cikin kanta, ta kai ?arshe a addu'ar kuma yana ganin ta motsa hannunsa ya haWe su da nasa gabaWaya suka tafi kan fuskar tata.

"Ameen ya Allah Noor."

Ya faWa daga saman kan nata sannan ya juyo da ita gabaWaya tana fuskantarsa, a lokacin ne ta rasa dukkan wani tunanin kanta, yadda yake kallonta a cikin duhun dakin ya warware dukkan wani lissafinta,? a lokacin ne bakinta ya furta abinda ya zama mafarin bude wata sabuwar rayuwa a tsakaninsu.

"Ma'aruf..."

Bakinta ya furta sunan ba tare da ta san ma me ta fada ba, kuma kafin ya amsa sauran kalaman suka biyo baya, bi da bi, wani na tunkude wani akan lebbenta.

"I think we're pregnant....!"

( Ina tunanin muna da ciki...!)


****

*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
*Gidan Hajiya Salamatu.*


"Kar ki damu Hajiya, gobe-goben nan zan sako miki su a mota, an riga an haWa sun cika cif, laces guda talatin da biyu ne, atamfa arba'in, sai materials Win guda takwas Nylon da kuma cotton guda goma..."

A cikin wayar dake kare a kunnen Hajiya Salamatu take wannan bayanin, tana zaune ne a barandar gidanta, daga ?asan rumfar yayin da iskar yammar ke kadawa a kowanne Sangare na harabar gidan.

A gabanta akwai wani dan karamin tebur da ta ajiye jotter da kuma biron da take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login