Showing 69001 words to 72000 words out of 132946 words

Chapter 24 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1143

shekaru biyu, lokacin da naje wani aiki da Kilishi ta tura ni a Kaduna.

Lokacin ne naje har gidan matar, aka shaida min cewa ta rasu shekara guda da ta wuce, na tambayi zancen yaron sai aka ce min babu wanda ya sanshi, sai da nayi bayani sannan da kyar aka sami wadda ta shaida min cewar tun a washegarin ranar da na kawo shi aka sami wasu mutane da suka zo suka tafi dashi Abuja, da na ji haka sai kawai na share zancen na baro kauyen kuma ban kara bi ta kansu ba. Amma ina da tabbacin cewa da na kara bincikawa tsaf zan iya sanin inda yaron yake a Abujan."

Awwalu ya kai ?arshen dogon bayanin yana kallon fuskar Hajiya Salamatun da ko sau daya bata yi kokarin katse shi ba, kallonsa kawai take ui da idanunta da har yanzu basu canja ba, basu canja daga yanayin da suke tun a lokacin da ya fara magana ba har zuwa yanzu, kallonsa take yi kamar kalma guda kawai ya furta tana jiran ya fara bayanin ne.

Amma a cikin kanta hotuna ne kawai suke wucewa, hotuna masu tarin yawa, tun daga wadannan shekarun da Awwalun ya dauko, lokacin da ta haihun aka shaida mata cewar ta rasa danta, lokacin da ta rike gawar yaron a hannunta, lokacin da take jin wani daci na sauka daga makogwaronta yana mamaye dukkanin jikinta, har lokacin da aka raba ta da abinda take tunanin shine natan, da yadda ?anuwanta suka taya ta wannan bakin cikin da fuskar Kilishi da tafi kowa nuna alhinin hakan,da irin hidimar data sha akanta don ganin ta dawo daidai.

Da yadda jama'a hatta ysnuwanta suka dinga yabawa abotarsu, da yadda bayan shekaru biyu ta kamu da wata matsananciyar rashin lafiya bayan tayi barin wani cikin, rashin lafiyar data taba mata mahaifa, da hoton fuskar likitsn dake yi musu bayani a wancan lokacin cewa da wuya ne idan har zata sake hsihuwa a rsyuwarta.

Da tarin rigingimun da tasha da wannan mijin nata kafin ya sake ta da cewar ba zai zauna da juya ba, wani abu da ya zamo mafari kuma tushen tsanar maza a zuciyarta har ta kai duka aure biyun da tayi bayan nan ta kasa tsaida zuciyarta wajen hakurin zama musamman da mijinta na ?arshe Alhaji Shamsu. GaSar da har ta kawo ta cikin wannan rayuwar da take kai, rayuwar da tun iyayenta na da rai suke kokarin hana ta har suka koma ga mahallincinsu.

Ashe duk wannan abin, aminiyarta ce sila? Kilishi ce silar da kalolin rayuwarta suka bambanta da buri da kuma tarin mafarkanta na zama uwa kuma mata a gidan mijin da zata taso da nata ikon itama, ashe zalunci da kuma cin amanar Kilishi da kullum take yiwa hangen nesa ba'a kan kowa ya fara ba illa ita?

A lokacin ne ta rufe idanunta a hankali, tana jin zuciyarta na bugawa, da wani irin bugu da bata danganta shi da komai ba sai na cewar ita uwa ce yanzu, ita uwa ce... Ta zama wannsn uwar da a kodayaushe taje mafarki, Allah ya mallaka mata wannan dsnar ya dawo mata da matsayin da kubce daga hannunta tsawon shekarun da taje jin nauyinsu a kirjinta. Kuma abinda ta sani a wannan lokacin shine ko zata ga dan nata ko ba zata ganshi ba, zata yi abu guda daya ne da take jin kamar Allah ya bar mata numfashinta tsawon wannan lokacin don ta zama sanadinsa.

_... haka kurum nake jin cewa kamar jibin nan ba zata karasa ba wani abu zai faru._

Kalaman Kilishi a dazu da suka yi waya ya dawo cikin kanta, tabbas ta yarda da kalaman Awwalu, ta yarda Kilishi kamar wani rabin shaidan be ya fado duniyar nan, jikinta ya bata wani abu zai faru tun kafin Awwalu ya shigo gidan nan tun kafin ita ta san komai.... Abinda kawai bata sani ba shine ashe ta hanyarta din, ta hanyar ita din da take gayawa karshenta zai fara.

Zaren labarin ya fara ne tun daga wannan ranar da tazo cikin gidan nan take gaya mata sauran tsarukan da take shiryawa, tun daga wannan lokacin da suke wannan dariyar take jin zuciyarta na yin wani iri akan al'amarin aminiyar tata duk kuwa da a sannan tana jin cewa ba zata taSa iya tona mata asiri ba, sai gashi ba'aje ko'ina ba a wannan Wakin, a wannan Wakin dai da suka zauna tare nan Win shi zai zama mafarin ?addarar da bata taSa lissafawa da ita ba.

"Na san da wuya ne ki yarda dani..."

Muryar Awwalu ta cigba da magana, sai kawai ta girgiza kanta a hankali tana katse shi, kuma tare da ta buWe idanun nata ba, kalamanta bakinta suka fito, sautinsu ya fito da wani amo a hankali amma kuma wanda ya karaWe falon...

"Ka kaini muje ?auyen Awwalu, idan har na tabbatar da abinda kake faWa, zan taya ka mu tonawa Kilishi asiri a idon duniyar nan...!"

Ta faWi haka a daidai lokaci guda da adadin mintunan kiran dake tafiya a cikin wayar Hajiya Salam???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?atu ya katse dib!

***

*No 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*

Karo na biyar kenan da Ru?ayya ke sake kiran nambar, amma da ya tafi kamar zai shiga sai ya katse kawai, ba sai wani yayi mata bayani ba, ta san ya rufe layinta ne daga shiga cikin wayar tasa, tunda dazu ta gwada da wani sabon layin ta kuma ya shiga, sai dai ba'a dauka bane.

Sai kawai tayi wulli da wayar kan gadon da take kai, ta tafi kamar zata fadi zuwa Waya karshen sai kuma ta tsaya bata karasa ba, hannunta ya dauko daya wayar tata dake gefe, ta sake lalubo nambar Jawad din a ciki, har zata sake danna nambar da niyyar kira sai kuma ta tsaya, wata zuciyar ta gaya mata cewa babu dalilin da zata cusa masa muryarta idan har ya nuna cewa baya so, sanin cuwon kai a rayuwa ma wani abu ne.

Don haka ta nufi bangaren rubuta sako, cikin abinda yake kasa da minti guda ta rubuta dalilin nemansa da take yi. Sakon ya tafi a daidai lokacin da mshaifiyarta ta turo kofa ta shigo dakin.

"Wani abu kike yi?"

Ba shiri ta girgiza kanta tana kallonta, sai ta gyada kanta sannan ta karaso ciki,da kowanne taku da take yi Ru?ayya na jin zuciyarta na bugawa sanin cewa bata da amsar abinda tazo nema din.

"Yazun nan muka gama waya da Hajiyan Sudan, ta gaya min cewa ta gama shirya komai tafiyar taku jibi ce."

Cewar Hajiya Nafisan va tare da ta zauna ba, daga kan gadon daga inda kafafunta suka lume gabadaya a cikin lallausan bargon Rukayya ta daga kanta sannan tace.

"Nima ta gaya min Maamah, Wazu da safe ta kira ni a waya ta ce min tayi settling komai sai tafiyar mu kawai."

"To kin fito da kudin?"

KuWin. Abinda take gudu kenan, tambayar da take gujewa kenan, kwanaki hudu kenan da mahaifiyar tata ta tuna mata da wasu kudi da ta taba bata ta ajiye mata a bankinta, kudade ne masu yawan da a yanzu ta manta ainihin lissafinsu, sai skayi rashin sa'a a lokacin ta samu matsala da bankinta na ajiyar kudi, don haka ba tare da tunanin komai ba ta bawa Jawad da cewar shi ya saka a Waya daga cikin bankunansa zuwa sanda zata tashi nema.

Ya karba din tun a lokacin kuma ya ajiye, sai dai daga shi har ita sunyi mantuwa da hakan ta sigar da bata sake tunawa ba sai a yanzu. Sai a yanzun da mahaifiyarta ta gaya mata cewa ta fito da kuWin dasu zasu yi komai, shi yasa a yanzu bata san ta yaya zata fara yi mata wani bayani ba da ta san ba fahimta zata yi ba, don haka ta gyaWa kanta da sauri sannan tace.

"Anjima zan fita Mamah, anjima zan dauko su gabadaya."

Sai ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan tace.

"Yau Daddynku zai dawo kin sani, ki saki jikinki ki nuna masa kin hakura a yanzu da zancen Hamidan, idan ba haka ba kuma zai Wauki matakin da zai lalata mana al'amari kin sani. Kuma kar ki sake ko da wasa ki bari ya san da zancen tafiyarki, ni na san abinda zan ce masa."

Sai tayi kokarin fito da wani guntun murmushi daga siririn lebbenta sannan ta gyada kanta.

"Ba zan yi komai da zai kawo matsala ba Mamah kin sani, idan nayi haka na san kaina na Sata."

"Sannan duk wanda ya kira ki da zancen Hamida kice musu kawai ta fara zuwa wajen mahaifinta ne hutu. Kar ki kara komai daga haka."

"Me yasa ma sai an gaya musu hakan Maamah, ba dai daga Sangaren Daddy bane masu tambayar, ni babu wayar wanda zan daga."

Hajiya Nafisa tace.

"Na gaya miki ne ko da zaku yi magana da wani..."

Bata karasa ba wayar hannunta ta shiga kara, don haka ta dauka ta kara a kunnenta sannan ta juya ta fita daga Wakin taiba magana, Rukayya ta bi ta da kallo, wani abu ya zarce a makogwaronta, ta san halin mahaifiyarta sarai, ba son dukkan wata mu'amala da ta danganci Ma'aruf take ba, kawai tana yin komai ne saboda ita kawai don haka idan har zata yi saken da za'a kasa samun kudin nan akan lokaci,komai zai iya tsayawa m, zata iya yin wasa da damarta ta ?arshe a yanzu.

Ta jawo Waya wayar tata ta duba tarihin asusun da take dashi a yanzu na banki, kudin ciki basu fi rabin abinda Hajiyan Sudan ta nema ba, babu mai bata kudi a cikin ?anuwanta ta sani, Ashraf ne kadai zai iya kallonta da wannan rahamar amma shima a yanzu wannan fetsararriyar matar tasa da baya yin komai sai da shawararta ba zata bari ba.

A wajen mahaifinta ne kadai zata iya samun wani abu amma shima ta sam wanda bai taka kara ya karya ba, don tunda yayi ritaya ya shiga hsrkar buga-bugar kwangila baya son fitar da kudi sam wanda hakan halinsa ne tun a baya, kawai suna da wadatar da ba'a ganewa ne... Kuma hakan ba daya daga cikin wani babban dalili da yasa mahaifiyarta ke dagewa kan ta auri mai kudi, don su samu ta wani Sangaren tunda ita mai son busasha ce.

Ta dafe kanta da duka hannayenta biyu, yatsun hannayen nata na shiga cikin gashin kanta, Jawad ya sha bata kudi, yasha bata kudin da tana tarawa ta san ta wuce wannan lissafin a yanzu, amma bata karba din ne da hujjar cewa ba lada take nenya a wajensa ba, don ta yarda da cewar mu'amalarsu na tafiya ne saboda haka take so, saboda ita take amfani dashi ba shi ba, saboda kuma bata son ya kalle ta da wani ?as?anci ko na kaWan.

Tayi ajiyar zuciya a hankali tana sake kallon text Win da ta tura wa Jawad, ita kanta ta sani a bayan wannan neman da take masa kuma akwai wani abu kamar damuwa, damuwar da bata san dalilinta ba, a baya ta danganta hakan ne da shirunsa kawai, amma idan har zata yiwa kanta adalci ta san akwai wani abu ksmar kewsrsa a can kasan ranta, kawai tana danne shi da tarin dalilin da take bawa kanta a kullum.

Sai kawai ta mike tsaye iskar dake shigowa daga winfon dakin na kada lallsusar rigar baccin da 'ke manne a jikinta, idonta ya ksi ksn siffarta acikin mudubin Wakin, waye zai taSa cewa tayi aure har da haihuwar ?a? Ai ko don kyawunta ta san ba zata taSa asara ba, shi kansa Ma'aruf Win bata son zubar da ajinta a wajensa ne shi yasa ba za ta tunkare shi ba.

Taso ganinsa lokacin shari'ar nan amma tunda har abubuwa sun canja, jiran nasa ne a yanzu, shi zai jira har zuwa lokacin da zai kasa lissafa asarar da yake yiwa kansa, tayi murmushi a hankali, siraran lebbenta suna talewa, da ta samu Ma'aruf ko meye a cikin tata zuciyar zai manta da Jawad shima.

Sai kawai ta kada kanta tana sake yin baya da gashinta sannan ta nufi bandakin dake cikin Wakin.


***

*Abuja.*

"Bata da lafiya kamar yaya?"

Jawad ya tambaya tsaye daga kofar Wakin, yana kallon wata yarinya mai suna Kristy dake tsaye tana gaya masa hakan.

"Eh Yallabai, baya da lafiya tun jiya bai fita ba, as a matter of fact ma snce ne yau zata tafi gida."

Yarinyar da ta fadi haka cikin gurbatacciyar hausarta jin ceqar tambayar da yayi matan da Hausa ne, ya cije lebbensa yana kallonta, wani tunanin ya gifta a cikin kanta na sakanni biyu, tun jiya bai ganta ba ance masa tana aiki sai wata banzar inyamurar aka aiko ta kawo masa abincin da bai ci ba don mukullin mitarsa ya dauka ya bar gidan kuma bai dawo ba sai dare, a yau ya farka ne babu tunanin komai akansa sai na son ganinta, to kuma ta yaya zai zo ace bata da lafiya? A cire ma maganar tafiyarta a gefe, wannan bai san dashi ba kuma babu ta yadda za'ayi ya faru.

Don haka bai jira komai ba sai kawai ya gyaWa kansa sannan yayi gaba zuwa hanyar dakin dake bayanta.

Ba shiri yarinyar ta juya ta bishi da kallo, idanunta na zarewa da tsananin mamakin ganin ya nufi hanyar kofar shiga dakunan wajen, idan aka cire lissafin cewa tunda take bata taba ganin wani dan gidan walau mace ko namiji ya shigo bangaren nasu na masu aiki ba... Babu ta yadda kuma za'ayi ace an samu wani da ya shiga har cikin dakunan nasu... Saboda haka da ita da sauran ?an aikin dake harkokinsu a harabar wajen, suka bi bayansa da kallo har sanda ya taka kafarsa zuwa ciki.

Wajen dogo ne yana Wauke da kofofin dakuna kusan biyar don haka yaja ya tsaya ba tare da ya san inda zai shiga ba, muatan dake wajen duk suka tsugunna a lokaci guda suna gaishe shi, idanunsu na nunawa da mamakin da ba sai sun furta.

"A ina Zainab take?"

Ya tambaya kai tsaye cikin harshen turanci don ya san babu wani karin bayani, du duka sun san wacece Zainab din tunda babu wata bayan ita, ta farko ce ta nuna kofar dakin dake gabansu tana fadin.

"She's inside here sir..." (Tana cikin nan ranka ya daWe.)

Zainab na kwance akan katifarta daga can karshen dakin, ta kudundune a cikin hijabin sallarta, jikinta yayi zafin da babu makawa ta san zazzaSi take yi, amma ko kaWan ta san wannan ba damuwarta bace, taraddadin dake cikin ranta daban ne, kalaman da Hajiya Mardiyya ta kira ta jiya ta gaya mata su ke ta yawo a cikin kanta...

"Babu wani abu kika yi min ba Zainab, Allah ya sani naji dadin zama dake da kuma aikin ki. Tafiya zanyi zuwa wata kasar kuma zan debe tsawon watanni shi yasa nake ganin ya dace ki koma gida, tunda babu wanda zaki zauna kina yiwa aiki, kuma babu amfanin zamanki cikin kabilun nan, gobe zan saka direba ya mayar dake har garinku, ga kaya nan cikin wancan akwatin duk naki ne, ga kuma kudi nan isassau zan bawa Hajiya Mairo da ta kawo ki ta kaiwa iyayenki, nace ta roke su ayi miki aure Zainab, kar su sake tura ki wani wajen gwara ki tafi dakin mijinki ke ma ki samu kwanciyar hankali...."

Tana tuna kowacce kalma da ta faWa har yanzu a cikin kanta, tana jin nauyinsu da kuma irin razanarwar da suke yiwa zuciyarta... Komawarta gida a yanzu kamar yana nufin zuwa karshen rayuwarta ne ta sani, babu ta yadda za'ayi mijin mahaifiyarta ya yarda cewa ba wani abu tayi aka dawo da ita ba, idan kuma har yaji wannan sa?on na cewar ayi mata aure ta tabbata za'ayi Waya ne cikin biyu, ko dai ya karSe kuWin ya sake tura ta wani wajen ko kuma yayi mata auren da wanda ranta ba zai taba so ba kuma a wajen da zata wahala.

Tana kwance tana hango fuskar mahaifiyarta, Allah ya sani bata san me ta fito nema ba, ta san ba wani yanci ta taho samu ba amma haka kurum zuciyarta na jin cewa kamar zata koma ne da wani abun da zata samawa mahaifiyar tata sauki, kamar zata koma da wani abu da zai cire su daga kangin wahalar da suka faWa tun bayan mutuwar mahaifinta... Sai gashi mafarkinta dama burin nata yana shirin bajewa a iska, ba zata koma da komai ba sai wannan jakar da Hajiya ta nuna mata, jakar da ta san ko meye a ciki bai kai ya canja rayuwarsu ba.

Daga yadda take kwancen tana jin hayaniyar sauran matan dake zirga zirga a waje, ita kaWai ce a cikin dakin, kuma tun jiyan ?an kadan ne a cikinsu suka kula da yanayinta kuma tunda suka tambaye ta tace musu bata da lafiya shikenan babu wanda ya kara bi ta kanta, amma gwara su sau dubu akan Waya Sangaren data baro, inda anan anfi samu wanda suka tsane ta kuma suke mata mugunta da gaske.

Ta rufe idanunta a hankali tana jin yadda yadda zuciyarta ke rawa a jikinta, taradaddin barin wajen ne kawai ke kamata, yana ?arawa akan halin da take ciki. A lokacin kuma taji muryoyinsu daga waje suna gaisuwa, kowa yana fadin?barka da zuwa yallabai, don haka ta bude idanunta da sauri cike da mamakin da bsi je koina ba wanda idanunta ya sauka akan mutumin da ya shigo cikin dakin, zuciyarta ta buga a ?irjinta.

Jawad, Jawad ne tsaye daga bakin kofar taba sanye da wasu kaya bakake, irin kayan da yake sawa a kullum wanda ba manya ba, wadanda suke zama a jikinsa daidai, kansa har da hula wadda ta dace da kayan, sannan a hannunsa akwai mukullin motar kamar fita zaiyi, Allah ya sani tun a jiya ta manta da lissafinsa kwata-kwata, taraddadin da take ciki har shi ya haWa ya shanye baki daya.

Kafin tayi wani yunkuri ya karaso har inda take, kafafunsa da takalmi na bi ta kan katifun sauran ?an dakin da basa nan, yayin da gefen idonta ya Wauko mata yadda wasu? suka shiga lekowa ta kofar dan karamin dakin wani abu da ya haddasa rikicewarta a lokaci guda don ta san ta riga ta shiga uku kenan a wajen mutane da maganganu kala-kala, jikinta ya shiga rawa a karkashin hijabin yayin da idanunta suka zare a kansa, amma babu alamar ya kula da hakan ya tdugunna a daidai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login