Showing 78001 words to 81000 words out of 132946 words

Chapter 27 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1139

jin zuciyarsa ta saba da wannan banbancin sabon da baya jin a karo na biyu kuma zai bari ya sake rasa wani abu irin haka a rayuwarsa.

Tun kafin ya karasa shigowa Wakin ta mi?e hannayenta na ?o?arin fara rawa ri?e da rigar da ta Wauko a cikin ledar, ya cije lebbensa kaWan yana daurewa abinda ke ?o?arin tasowa daga zuciyarsa.

"Me yasa baki shirya ba?"

Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, ta girgiza kanta da sauri kafin tace.

"Ba komai, so nake in koma Wakinmu dama sai in shirya acan."

"You are not going back to that place..."

Idanunta suka tsaya akansa da kallon rashin gane abinda ya faWa duk kuwa da yadda take a tsorace, sai ya Wan kalli gefe alamun mantawa da hakan sannan ya sake juyowa.

"Anan zaki zauna, ba zaki koma can ba,idan akwai abinda kike bukata a cikin kayanki sai ki saka a dauko miki.."

Ai tun kafin ya ?arasa kwalla ta cika idanunta ta shiga girgirza kanta da sauri.

"Dan Allah kayi hakuri ka barni in tafi, wallahi Hajiya faWa zata yi min, yau ma tace za'a mai da ni gida kuma..."

"Babu inda zaki, idan kin warke zan kai ki gidan ki gansu sai mu dawo."

Ya fada yana sawa ta tsaya cak tana kallonsa, don hatta kwallar data taru a idanunta bata zubo ba.

"Ba dawowa zanyi ba idan na..."

"Dawowa zaki yi, 'Coz babu inda zaki je ki zauna a duniyar nan da ya wuce nan."

Ya faWi hakan kamar cikin tursasawa don har yanzu a tsaye take cak tana kallonsa, sai kawai ya shafo kansa da duka hannayesa biyu shima yana kallonta, yayi kokarin saita kansa sannan muryarsa ta saje fitowa.

"Babu abinda zanyi miki Zainab, wallahi babu abinda zanyi miki, baki ga har hijabi na siyo miki ba? I just want to feel you close to me... So nake kawai in dinga jinki a kusa dani. Shi yasa na tambayeki idan zaki aure ni saboda zan je har wajen iyayenki ne in nemi aurenki, babu ruwana idan ma akwai wanda suka tsara zasu baki Zainab, ko shari'a zan iya yi da kowa idan akace za'a hana ni aurenki..."

Ya faWa yana kallon yadda take kallonsa har a lokacin, a tsaye kyam amma kuma idanunta na haskawa da dukkan wata ma'anar tsoro na duniya kamar ma bata fahimce shi va, ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yace.

"Ko ke baki da zaSi yanzu Zainab, zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni."

Yana faWin haka ya juya yayi hanyar kofar dakin, sai dai taku huWu kawai ya tsayar da kafafunsa kafin ya ?arasa, ya juyo ya sake kallonta, tana tsaye yadda take har yanzu kamar tana jira ne wani ya taSa ta ta faWi, sai ya juyo ya dawo da saurihar gabanta, kuma bai jira komai ba ya janye hijabin kanta zuwa ?asa, gashin kanta da akayi wa wasu manyan kitso mai suna 'Doka' guda uku suka baiyana da jelarsu ?ar gajeriya a baya.

Sai dai shi ba ta su yake ba ma, hannyensa yasa duka biyu a wuyanta, yatsunsa dukkansu suka zagaye dan siririn wuyan nata har zuwa baya, dumin jikinta ya ratsa zuwa tasa fatar a lokaci guda da ta rufe idanunta gabaWaya, wannan kwallar da ta taru tana samun damar zubowa.?

Dukkaninsu suka sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya a tare yayin da Jawad ke kallon fuskarta yana ji kamar ya ?arasa da tasa ya haWe goshinsu waje daya, amma ya daurewa kansa ya haWiye wani abu a kirjinsa sannan muryarsa ta fito, a hankali cikin sautin da baiyi kama da wanda ya gama magana dashi yanzu ba.

"Maganin ki yana wajen dining, ki ci abinci ki sha, zan je wajen Maamah yanzu zan dawo, kinji?"

Kuma ga mamakinsa sai kawai ta Waga kanta sau Waya bata ?ara ba kuma har yanzu idanunta a rufe suke, ya cigaba da kallon fuskarta na tsawon sakanni idonsa na sauka akan siraran leSSenta yana jin yadda kwakwalar sa ke kokarin saita kansa daga abinda yake tunani kafin ya zare yatsunsa daga wuyanta a hankali.

Kuma bai ?ara cewa komai ba ya juya ya nufi hanyar kofa fitar, zuciyarsa na goge hoton ta da na mahaifiyarsa a cikin idonsa, Hajiya Mardiyya... missed call dinta ne a wayarsa kusan goma sha biyar, bayan wayar da suka yi sau hudu yana gaya mata inda suke da kuma sanda zasu dawo, yanzu ma ya tabbata bata ji shigowar motarsa bane da tuni ya ganta tazo.

"Jawad dan ub*nka a matsayin me ka dauki yarinyar nan ka kaita har wajen aikin ka?"

Haka take gaya masa lokacin da yace mata suna office tare.

Bata taba zaginsa ba, zai rantse bai ma taSa jin kalmar zagi a bakinta ba, sunansa kadai akan shafe watanni bata furta ba, a kullum kuma a gaban kowa shi baban ta ne, amma yau da girman sunan da take ji da komai ta haWa ta zage gabadaya.

Ya hadiye wani abu a ma?ogwaronsa lokacin da ya fita zuwa? waje gabadaya, haka kawai yake jin kamar ko ita bata isa ta shiga tsakaninsa da yarinyar nan ba.

Yana isa Sangaren nata kannenta ya fara tararwa tare da wasu cousins dinsu sun zo gidan, sun haWu akan wani katon tray da suka dafa wata tarin indomie da kifi a ciki, kowacce ta tattare kayanta sun baje suna ci ga wasu manyan-manyan jugs na zoSo a gabansu.

Gaisuwarsu ta amsa a cikin kansa cikin amo Waya na siririyar murya, kuma bayan ya amsa bai jira komai ba kafafunsa suka karasa zuwa hanyar koridon da zai tarar da dakin mahaifiyar tasa.

Kofar a buWe take, ya tura ta a hankali ya shiga ciki da sallamar da ta tsaya iya ma?oshinsa, sai dai idonsa bai gane masa kowa ba alamun bata ciki, kuma har ya juya zai koma lokacin da kunnensa ya jiyo masa muryarta daga cikin banWakin Wakin wanda kofarsa bata rufu sosai ba.

"Yanzu duk ba wannan ba Aunty Sadiya, mu fuskanci maganar nan, ina jin kamar zan iya komai don in gyara abubuwa su koma daidai, ba zan yi wahalar banza ba tsawon shekarun nan Aunty Sadiya, na kaWe idan har Jawad ko waninsa ya san cewar ba ni na haife shi ba....!"


****

_Yau na haWe muku lovebirds Win mu a Chapter Waya..._>?p?=?
?

_Ina kuke tunanin muna tafiya?_

_Kun san na saba wasa da tunaninku...=??_

_Ku shiryawa abinda ke shirin faruwa... Ku shiryawa alkawarin da na daWe ina daukar muku..._

_Komai mai sauki ne idan har kun yarda dani._

_?ullin ba gab! da kwancewa._

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*??AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*17*

~~~~~~~

_Hope is a waking dream._ _ Aristotle_


***

"Yanzu duk ba wannan ba Aunty Sadiya, mu fuskanci maganar nan, ina jin kamar zan iya komai don in gyara abubuwa su koma daidai, ba zan yi wahalar banza ba tsawon shekarun nan Aunty Sadiya, na kaWe idan har Jawad ko waninsa ya san cewar ba ni na haife shi ba....!"

Haji Mardiyya ta fada tana dafa sink din daje gabanta a cikin banWakin, daga cikin wayar, yayar tata mai suna Aunty Sadiyan tace.

"Duk ba za'a kai ga wannan ba insha Allahu, yanzu dai kawai abinda nake so shine kiyi kokari ki samu ki raba shi da yarinyar kawai, idan har ta tafi sauran mai sauki ne.

Kawai lokaci zamu ja sai idan ya takura mu samu wani kauyen mu kaishi, da mun fan sunna wa wasu a cikin garin yan kuWaWe sai ya same su a matsayin iyauenta kawai ace masa ta mutu, kinga wannan dole ya hakura ai, komai fa dabara ne Mardiyya, rayuwar mace gabadaya akan dabara take tafiya, idan kika iya ta ina tabbatar miki babu ruwanki da tashin hankali akan abubuwa da yawa, kina daga zaune zaki dinga gyara matsololinki hankali kwance."

Hajiya Mardiyya ta gyada kanta.

"Na dade da haddace wannan karatun naki ai Aunty Sadiya, yanzu na aika a kirawo shi don haka ko yazo ma, ba zan nuna masa kai tsaye cewa ya rabu da yarinyar ba, kawai zan nuna raina ne ya baci ta yadda ba zai fuskanci komai....."

Kalaman ta suka gutsire a iska sakamakon juyowar da tayi a zacen nata, juyowar da tayi a lokaci guda kuma kai tsaye siffar Jawad ta shiga idanunta, yana tsaye rike da hannun kofar banWakin, yana tsaye yana kallonta? da tarin abubuwan da ba zata iya lissafa su ba a jikin idanunsa, tarin abubuwan da suka sa babu shiri wayar dake hannunta ta zame daga kunnenta ta tarwatse a ?asa!

***

A cikin tangameman Wakin baccin, Alhaji Bashir ya sauke wayar dake kunnensa daidai lokacin da matarsa ta biyu Hajiya Yagana, kwallin idanunsa kuma shalele duk a cikin matansa uku ke mi?o masa plate din data zuba abincin a ciki tun bayan farawar wayar tasa tsawon mintuna da suka wuce

Kallon da take masa wani kala ne, wani kala ne da duk sanda ta yin yake zabge shekarunsa da nata a zukatansu gabaWaya, lokaci ya ara musu wata dama da a cikinta suke WanWanar ruwan zumar da baya duba da yaro ko kuma babba.

"Ayi hakuri mana Shalele, aikin his excellency ne, ni ban isa ince ba zan saurare su a yanzu ba."

Ya fada yana kallonta da murmushi, sai ta turo bakinta kaWan alamun ba inda fushin nata yaje kafin tace.

"Kwana biyu ne an shiga hakkina da yawa ranka ya daWe, a lalace nayi kusan wata ban same ka ba, duk ranar da kwana na yazo sai tafiya ta taso ko kuma wani abu ya faru... Hatta su Amal sun fahimta."

Ya sake yin murmushi mai armashi yana kallonta kafin yace.

"Kar ki damu, wannan duk labari kike bayarwa, yanzu dai ba gani ba kuma ga ki? ai zance ya ?are kuma tsawon kwana ukun nan ni naki ne, ko office ba zan fita ba Yagana, idan ?asar ma kike son mu bari ki zabi inda zamu je mu kwana biyu sai mu dawo..."

Idanunta suka wulkito tana sake kallonsa yayin da dadi ke ratsawa har cikin zuciyarta, a duniyar nan bata da wani lissafi da ya wuce a kullum ta samu tarin hanyoyin kuntatawa kishiyoyinta, duk wani abu da zata yi su ji haushi shine kawai alkibilarta, don haka ta gyaWa kanta tana murmushi sannan tace.

"Garin masoya zamu tafi Daddy, (Paris) ina son inga hasken fitulun garin nan na haska min fuskar ka a idanuna...."

Dariya da Alhaji Bashir yayi wannan karon mai sauti ce, dariya ce dake fitowa tun daga cikin zuciyarsa, kuma har ya buWe baki zai yi magana lokacin da kararrawar (doorbell) Sangaren gabaWaya ta Wauki ?ara, sautin ta ga mamaye ko'ina da amon da zaka san tabbas ba an danna ta ne sau Waya ba.

"Waye wannan kuma..."

Hajiya Yagana ta furta tana ?o?arin danne zagin da taji ya biyo bakinta. Kuma kafin ta karasa wata karar ta sake biyo baya, Sai kawai Alhaji Bashir dake gefe yayi murmushi yace.

"Je ki buWe ko waye na gida ne ai."

Kamar ba zata tashi ba, don sai dai ta kirga wasu sakanni zuciyarta na biya tsinuwar dake tafiya ga ko waye a bayan kofar nan kafin tayi kwafar da ita kadai taji ta ta mike, ta mi?e sanda Alhaji Bashir ke fadin.

"Zan same ku anan falo."

Kafafunta suka dauke ta zuwa cikin falon da shi zaka fara tararwa bayan ka fito daga Wakin, ta wuce ta isa ga falo na karshe a bangaren sannan ta kama handle din makekiyar kofar ta buWe bayan ta murda mukullin, kuma fuskar wanda ke tsaye daga wajen, fuska ce da ta sake bakanta ranta a lokaci guda, tasa zuciyarta matsewa a kirjinta... Wai har yaushe Jawad ya fara shiga rayuwarta ne? A kodayaushe ita mantawa take dashi ma a lissafin dukkanin ?a?an gidan don ko zama a gidan bai cika yi ba, to don me yasa yanzu zai dawo ya saka ta a gaba kuma?

Tayi niyyar gaya masa magana amma sai yanayin fuskarsa ya tsaida ita, don duk da ba wani sanin halinsa tayi sosai ba, ta sani cewa bata taSa ganinsa a irin yanayin da yake yanzu ba, fuskarsa fayau take yayin da idanunsa ke haskawa da wani abu da bata san meye ba, sai kawai ta saki kofar sannan ta juya ciki ba tare da tace dashi komai ba.

Ta juya daidai lokacin da Alhaji Bashir ke fitowa, nasa idanunsa shima suka sauka akan Jawad din dake shigowa, yana kallon yadda bai ko cire takalman kafarsa ba, balle ya rufe kofar da ya baro a bayansa.

Kuma ga mamakin Hajiya Yagana, tana juyuwa da niyyar biyo bayansa su dawo cikin falon sai kawai ya Waga mata hannunsa guda.

"Ki shiga ciki Yagana, zan shigo."

Ita kanta ta sani cewa a yanayin Jawad din,?babu ta yadda za'ayi ya faWi abinda ya kawo shi a gabanta, bata jin ma ko da gaishe da mahaifin nasa ne zai yi idan har tana wajen, don haka bata ce komai ba sai kawai ta juya ta koma ciki, kuma ta shiga cikin ba tare da ta rufe ?ofar Wakin gabaWaya ba.

Alhaji Bashir ya ?araso cikin falon ya samu waje ya zauna, kuma sai da ya zauna Win sannan Jawad ya ?arasa ?arasowa cikin shima, ya sami waje a daidai jikin kujerar dake fuskantarsa ya durkushe har ?asa kan lallausan carpet Win dake shimfiWe a wajen.

Alhaji Bashir ya kalli yadda ya zaune a gabansa, idanunsa na cigaba da nazarin fuskarsa, zai kafa hujja da cewar tunda yake bai taSa ganinsa a irin wannan yanayin ba, don haka sai kawai ya ajiye wayoyinsa da ya fito dasu a gefe sannan ya kira sunansa.

"Jawad, me ya faru?"

Muryarsa ta fito ne a hankali, cikin wani amo irin na manya, irin na manya a lokacin da suka fuskanci wata matsala game da ?a?ansu ko kuma duk wani wanda suka san zai iya samun mafita daga gare su.

Sai dai abinda Jawad Win ya buWi baki ya fada a wannan lokacin, wani abu ne da ya shallake dukkan tunani da kuma hasashen Alhaji Bashir, wani abu ne da idan za'a tattaro dimbin abubuwan dake kansa a jera sunya tabbata ba za su taba kaiwa ga magana irin wadda ya fada a wannan lokacin ba...

"?an sanda zasu zo gidan nan, nan da minti kaWan Daddy, babu wanda zasu taSa kuma babu wanda zasu kama, kawai so nake ta gansu ta tsorata ta gaya min gaskiya, tace ni ba Wanta bane ba ita ta haife ni ba, don haka so nake ta gaya min su waye iyaye na kuma meye asalina... Wannan kawai nake so in sani Daddy!"

***

*?auyen Garun Albasu ( Yakura).*
*12:15Pm.*

Awwalu ya gyara zamansa a gaban motar da suke ciki, motar dake tafiya cikin wani tsukin lungu na ?auyen da suka shigo kusan awa gyda da ta wuce, kuma a wannan lokacin suka shafe suna faman tambayar gidan wata mata mai suna Hanne kamar yadda Awwalun yace itace wadda a wancan lokacin ta shaida masa cewar yaron da yake nema yana can Abuja, kuma a cikin awa gudar an kaisu ga gidajen mata masu sunan Hanne fiye da goma, kowacce Awwalu yana fadin ba ita bace da zarar ta fito.

Lokacin da suka shigo cikin kauyen kai tsaye ma yace zai iya gane gidan da ya sami matar a wancan lokacin, amma tun kafin tafiyar tayi nisa, canje-canje da kuma sabbin tsarin da aka samu a koina ya shaida masa cewar abinda ya sani a wadancan shekarun da kuma yanzu daban ne, don haka suka shiga tambaya, tambayar da ta kaisu ga lissafin mutane kusan tara kafin a samu wanda ya faWa musu cewa matar ta daWe da barin garin amma akwai wata Talatu da zata iya basu labarin inda take.

Tun a hanya Hajiya Salamatu ta sani cewar zai iya yiwuwa matar ta mutu, zai iya yiwuwa su zo su sami labarin wucewar wasu shekaru da mutuwarta, ace musu ta rasu tare da labarin abinda suka zo nema, abinda shine zai zamo ginshi?in canjawar rayuwarta da ma ta adadin wasu masu yawa.

Amma bata san me yasa ba a yanzu zuciyarta ke gaya mata cewar bai kamata ta biyewa Awwalu rana tsaka ba, bai kamata ta yarda da wani daban akan aminyarta da suka shafe tarin shekaru tare ba, waWannan shekarun da a cikinsu baza ta taSa cewa ga rana guda da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, kokwanton kawai guda daya ne... idan ta tuna cewa sauran mutanen da take azabtarwa wanda suma haka zasu buWi baki su ce.

Sannan kuma har yanzu Awwalu bashi da wata shaida, bashi da wata shaida ko guda Waya da zata tabbatar mata da dukkan labarinsa, zai iya yiwuwa yazo yayi amfani da ita ne don kawai ya sanarwa kansa mafita, idonta ya sauka akansa daga gaban motar, shi kansa ba abin yarda bane, shekara nawa ya shafe yana aiki tare da Kilishin, shekaru nawa yayi yana taya ta wajen kuntata rayuwar wasu? Me yasa bai taSa tuba ba sai a yanzu? Shekaru sun fara ja masa amma ko aure bai taSa tunanin yi ba, bashi da wani mutunci ko kuma wani abu kwakwkwara da rana tsaka kawai zata yarda dashi.

Sai dai idan har bata yarda da Awwalun ba, to tabbas kuwa ba zata yarda cewa?Kilishi ba zata iya aikata abinda Awwalun ya faWa ba.

Lungun da suke bi a yanzu wani Wan tsuki ne da ba don direban nata yace zai iya bi ba, zata ce su fita su tafi a ?asa ne, don a yanzun ma dukkan mutane da kuma samarin dake zaune sai da suka mike suka dage bencinan da suke zaune akai don bawa motar waje, idanun kowa na binsu da kallon rashin sani kamar yadda suke gani a koina duk inda suka tsaya tambaya.

"Wancan kwanar ce, yaron yace kwana ta farko zamu karya."

Awwalu ya fada yana nunawa direban kwanar dake damansu, zuciyarsa fayau take a kirjinsa, yana jin kamar allon kirjin nasa baya Wauke da komai, kamar iska ce kawai ke yawo a cikin gangar jikinsa da take fanko, yana jin yadda bugawar zuciyar ke amsawa a cikin kunnuwan shi.

Rayuwarsa gabaWaya a yanzu ta ta'allaka ne ga inda zasu je da kuma abinda suka taho nema, nasararsa da akasinta tana ga irin amsar da zasu tarar ga tambayarsu, idan har bai samu gamsaahshen bayanin da zai tabbatarwa da Hajiya Salamatu ba, bai san me ya kama ba, bashi da wata mafita ko zaSi illa ya tattara komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login