Showing 123001 words to 126000 words out of 132946 words

Chapter 42 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1149

da ta gani ranar daurin auren nan, wani abu ne da ba ita kadai ba har dangin nata sunyi mamaki... Kuma a ranar ta sha kuka kamar me tayi kukan rashin mahaifiyarta sannan tayi kukan farin cikin da bata san irin yadda zata fallasa adadinsa a kirjinta ba, Tayi hamdala ta godewa Allah fiye da yadda zata iya kirgawa a lissafinta.

Bayan haka kuma tayi kukan fargaba na irin rayuwar da zata je ta tarar a gaba, don ta sani a yadda zata shiga rayuwar Jawad bata da komai kuma bata da iyaye tsayayyyu dole ne ta fuskanci wasu abubuwan daga mutanen dake kewaye dashi wanda na lallai suyi mata dadi ba... don ko a ranar daurin auren nan ta raina kansa a cikin kowanne bangare na yanuwansa sau dubu tana sakewa...

Kuma a wannan ranar ne aka basu ita suka taho Kano yayin tare da wasu yanuwan nata yayin da su Hajiya Mardiyya duka wuce Abuja. Sun taho tare da kuma tarin kayan da su Jawad Win suka kai wanda har a yanzu bata mayar da hankalinta wajen ganinsu ba kasancewar yadda aka dinga rububin kallon kayan a can garin nasu.

Kuma bayan sun zo ne suka tarad da gagarumin bikin da mahaifiyarsa ke shiryawa wadanda ta ga kamar sun fi karfin tunaninta, don kusan komai an gama shirya shi hatta kayan da zata sa an gama dinka su, sai bayan da tazo aka gwada aka ga wajen da yayi mata yawa sannan aka mayar aka daWa gyara su.

Kallon komai kawai take tana kuma kallon kowa tare da ita da yanuwan nata da suka zo kawai, an hada ta? da wata yarinya Ameerah da kusan ita ke jan ragamar komai nata, ita ta gaya mata dukkan shirye-shiryen da suke yi na cewar za'ayi walimar iyaye ne (mother's eve) a yau washegari da safe kuma za'ayi budar kai tare da yini sannan jibi zasu tafi can Abuja tare da Jawad din su kuma tari nasu Hajiya Mardiyya da suke shiryawa suma kafin a dangana ta da sabon gidan da ya kama kusa da wajen aikinsa.

Sai a lokacin da taji hakan ne sannan wani sabon kukan ya sake cike kirjinta, ta sani yanuwan mahaifiyar tata sunyi nasu kokarin, don da karo-karo da kuma gudumawa kala-kala aka hada mata kudi dubu hamsin bayan sadakinta da aka kawo na dubu hamsin din shima da cewar ta siya wasu kayan amfanin idan taje gidanta, ko da kayan kitchen ne a?alla ta dinga kallon wani abu da yake nata tunda sun sani cewa Jawad ya riga ya dauke musu komai yace zaiyi komai din ba sai sun wahalar da kansu ba.

Amma duk da haka a yanzu da tazo ta ganta a cikin tarin yanuwansa tana jin nauyin da zuciyarta ke ?ara yi da tunanin kowa yana yi mata wani kallo ne daban na cewar an kawo ta ba tare da komai ba kuma a yamzun ne masu niyya zasu kafa mata kahon zukarsu.

Idan Jawad da mahaifiyar tasa dake ta fara'a tana nan-nan da ita suna sonta kuma basa ganin aibunta, hakan baya mufin zadu iya rufe idon kowa daga ganin hakan. Don haka tun da suka zo a Warare kawai take, idan wani yana yi mata magana hannayenta har rawa suke, gani take kamar zasu daka mata tsawa ne kawai ta tashi ta fara aiki ba wai itace wadda suka taru dominta ba. Daga ita har yanuwan nata kuwa tunda dama itace karfin gwiwarsu a wajen, tunda suka fahimci a tsorace take shikenan su ma basu da ta cewa sai abinda akace.

A yanzu ta baro su ne acan gidan da cewar za'a tafi dasu wajen Partyn da idan an gama yi mata kwalliyar zata je ta same su acan. Ameeran tace mata Jawad ne zai zo ya Wauke ta idan an gama. Jawad din da tun a can garinsu ranar Waurin auren nan bata ?ara ganinsa ba kasancewar tunda suka zo gidan a cike yake da mata fal don haka bata ma san a ina yake ba.

"Rufe idonki..."

Mai kwalliyar ta fada tana dawo da ita daga tunaninta. Ta kuwa rufe idon zuciyarta na kiyasta adadin kudin da aka kadhe a wajen mai kwalliyar kada banda kayan dake cikin wani akwati dasu? Ameeran suka taho dashi.

?asa da minti talatin bayan hakan mai kwalliyar nan ta gama fente fuskarta a yanayin da ita kanta da rufe mata ido kawai akayi aka bude zata rantse cewa ba ita bace, Ameerah tare da sauran ?anmatan nan biyu suka taimaka mata ta zura doguwar rigar wani hadadden material kalar ja mai haske ta kasa, kalar ta dace sosai da kalar fatarta da take wani abu tsakanin fari da kuma brown, daga nan aka shiga daura gwaggwaron da bata san minti nawa aka shafe ana dora hawansa ba.

Lokacin da aka gama tsoro ne ya kamata sosai ganin kanta da tayi a mudubi, wani abu ya wuce ya sake wucewa a wuyanta lokacin da su Ameerah ke ta fadin Masha Allah suna daukar ta a wayoyinsu, ta kasa dauke idanunta daga mudubi koda na sakwan guda, ji take kamar ta tattaro dukkan mutanen da suka santa a hargitsenta don su taya ta shaida cewa ba itace wadda idanunta ke ganin mata ba.

"Ashe dai Yaya J ya san me idonsa ya gano masa."

Ameerah ta faWa tana saka ta murmushin da bata shirya masa ba. Dun dade a wajen, har akayi wa su Amirah tasu kwalliyar sannan mai wajen tayi ta Waukarta a hoto itama sannan wayar Amirahn tayi kara da sakon Jawad na cewar sun iso wajen, fabanta na dukan tara-tara su Amirah suka taimaka mata suka fita waje Bayan ta yafa wani mayafi shima kalar ja mai shara-shara.

**

"Eh munzo Wauko su yanzu, yanzu zamu taho."

Jawad ya fada a cikin wayar da yake yi bayan ya fito dafa cikin motarsa da ta tsaya a kofar wani gida da akace shine gidan mai kwalliyar dasu Zaunab suka zo. A yanzu haka ma da mahaifiyar tasa Hajiya Salamatun yake waya, da kyar yake jinta a cikin tarin kidan dake can wajen bikin inda kusan duka danginta ne gabaWaya ta tara, yanuwansa na Abuja kaWan ne a wajen, kusan maza ne ma kadai don su ma suna can Abujan da shirin yin nasu bikin da zarar sun koma.

Ya roke su, ya roki kowa a cikinsu Hajiya Salamatun dama Maaman (Hajiya Mardiyya) akan ba sai sun shirya wani gagarumin taro ba idan aka daura aure kawai aka bashi matarsa zai fi kowa jin dadi amma babu wanda ya yarda dashina cikinsu, kowacce tace tana da yanuwanta da dole ne su sani cewa tana bikin Wa, don haka a dole su suka ja tsawon watannin har aka kai yanzu wata na shida kafin komai ya tabbata.

Ya fahimci kishin dake tsakaninsu tun daga ranar da suka koma Abuja shi da Hajiya Salamatu da kuma wasu yanuwanta bayan dawowarsa daga wajen Zainab bayan kuma sun mika case din ?awar Hajiya Sakamatun da tayi sanadin komai wadda yaji suna kira da Kilishi, wani suna da yayi kama da orin wanda ya kan jina bakin Rukayya lokutan baya, sai dai bai rike komai ba sunan yana da alaka ne da zancen tsohon mijinta da baya son ji a lokacin.

Kuma a yanzun ma bai matsa ba ko kadan, ya san dai Hajiya Salamatun ta gaya masa cewa tuni matar dama tana gaban hukuma sanda suka kai ?arar, abinda ya sani kenan kawai har su saka ranar da ta maida su farin Abuja, zuwa cikin gidan da a ranar da ya fita ya barshi ko kadan baiyi tunanin dawowarsa a kusa ba, yana hango wucewar shekaru ne wanda kafin nan watakila ziciyar tasa ta iya hucewa game da abinda ya faru.

Sai gashi ya dawo a tsakanin lokacin da hannu ma zai iya kirga shi, ya dawo tare da wani abu da ya Waure tunanin kowa a gidan, don ba Hajiya Mardiyya kaWai ba, kusan duka al'ummar gidan a gigice suka taho bangaren mahaifin nasu jin labarin cewa Hajiya Salamatun da suka sani tsohuwar matar Kawu Ibrahim yadda kowa ke kiransa itace mahaifiyarsa.

Babu wanda bai santa ba, daga matan gidan har wasu da suka manyanta a cikin ?a?an gidan, kawai zumuncin ya lalace ne tun da ya dade da rabuwa da ita tun kafin rasuwarsa kuma ya auri wasu matan bayan ita sannan kuma dadin dadawa babu zuria a tsakaninsu.

Tun daga wannan lokacin labari ya gama zagaye danginsu gabaWaya, kuma maimaikon a samu shiri tsakanin Hajiya Salamatu da kuma Mardiyya sai wsni abu kamar kishi ya shiga tsakaninsu don kowacce tana ganin tana da nata ikon akansa.

Ko lokacin da suka tafi Yakura dukkaninsu sun je amma kowa da nasa tawagar ne. Ko yanzu Alhaji Bashir ya saka baki cewa su? Hajiya Mardiyya su zo nan Kanon, ma ta dage cewa itama uwa ce don haka ita ya kamata azo a samu. Sai kowa ya rabu dasu a hakan, Alhaji Bashir ya gaya masa cewa lokaci ne amma komai zai daidaita a hankali.

"Ka kira su kuwa? Time yana ta tafiya..."

Haro dake tsaye a gefensa ya faWa, kuma kafin ya amsa sai ga kiran Hajiya Mardiyya ya shigo, ba shiri yayi murmushi yana girgiza kansa kafin ya bawa Haro amsa.

"Na kira Ameeran, tace gasu nan fitowa.."

Haro yayi murmushi yana kokarin gyara hular kansa sannan yace.

"Ai sai ka gaya min in gyara Malam."

"Haro, na gaya maka yarinyar nan ba kalar ka bace, yes tana da wayewa amma ba irin taka ba."

Haron ya juyo ya kalle shi, bayan ya kalli sauran abokan nasu ya tabbatar hankalinsu baya kansu.

"To ni an gaya maka mai irin wayewata nake nema? For real? Kana tunanin kai ka samo mai nutsuwa shikenan ni bani da hankali zan auri yaran titi ne? Malam idan zaka bani support kawai gwara ma kayi..."

Kafin ya bashi amsa wani kiran Hajiya Mardiyyan ya shigo sai kawai ya ?ara a kunnensa da murmushi yana faWin.

"Maamah wallahi jibi zamu taho..."

Daga cikin wayar Hajiya Mardiyya ta kyalkyale da dariya alamun farin cikin da take ciki kafin tace.

"Na sani Babana, kira nayi in gaya maka cewa na aika an sake Wauko wasu daga cikin yanuwanta don ance min mutum goma sha biyar ne kawai anan, sunyi kaWan ita kanta yarinyar tana bu?atar yanuwanta..."

Murmushi ya sake yi yana cije lebbensa don ya san tayi hakan ne kawai saboda Hajiya Salamatu... Daga haka ta cigaba da bashi labarin shiryen-shiryen da suke yi wanda a ciki baya hango komai sai tarin gajiyar da shi dama Zainab Win zasu fuskanta, Kawai babu yadda zai yi ne yce da waninsu ya fasa.

A cikin saurarenta da yake yi, yaji muryar Haro yana fadin.

"Here goes my chance..."
( Ga dama ta nan...)

Don haka yayi saurin juyowa a lokaci guda da idonsa ya nuna masa wata tsantsareriyar halittar da tayi kama da Zainab din dske amsa sunan tasa a yanzu...

Watakila ya fara yarda da idear shirye-shiryen bikin nan....

**

Lokacin da su Zainab suka fito ?ofar gidan, daga can gaba kadan suka hango motoci guda biyu da suka tsaya yayin da mutanen ciki ke tsaitsaye a waje suna jiransu, Jawad na tsaye daga tsakiyarsu yana waya, idonta ya sauka akansa lokaci guda da numfashinta ya tsaya a kirjinta yana sawa ta manta da nata kyan da tayi gaba Waya.

Brown shadda ce a jikinsa da kuma dark brown hula, yayi kyau ya gyara fuskarsa sannan tsawonsa ya sake fitowa, sai ta kasa yarda, ta kasa yarda cewa wai a yanzu matsayinta da nasa ya zarta na yadda ta san shi, a yanzu shi din mijinta ne, mijinta shine wanda ya rufe idonsa daga kowa da kuma komai ya zabe ta a cikin tarin mutanen duniyar nan alhali bata da kowa kuma bata da komai.

Sai kawai kwallar da bata shirya mata ba ta cika idanunta tana gangarowa kan fuskarta, yayin da sauran mutanen dake kewayensu suka shiga maganganun da ko kadan ba jinsu take ba, shi din kawai take kallo kamar tana son nemo dalilin sa na aurenta akan fuskarsa, kamar tana so taga wani abu da rayuwa ta tauye masa har ?addara ta hukunta shi da aurenta alhali yana da tarin dama a duniyar nan.

"Idan kika cigaba da tsayawa kina kallonsa haka, zan tafi in maye gurbinki yanzun nan..."

Ameerah ta raWa a kunnenta daga gefe, wani murmushin da bata shiryaemwa ba ya sake sauka a bakin ta, ta juyo tana kallonta idanunta cike taf da hawaye, sai kawai ta gyada mata kai tace.

"Alhmdlilah ake cewa..."

Ta gyada nata kan itama sannan a hankali bakinta ya furta kalmar.

"Alhmdlilah."

"Ai gasu nan sun fito ma, Masha Allah..."

Muryar Waya daga cikin abokan Jawad Win tasa su juyowa daidai lokacin da Jawad din shima ya juyo har a lokacin wayar kare a kunnensa.

Idanunsu suka hadu waje guda kuma maimakon taga mamakin rashin gane tan da take zato a fuskarsa, sai kawai yayi wani murmushi mai fadi yana cigaba da kallonta, murmushin da ya mamaye fuskarsa gabaWaya yana sa nata lebben talewa itama har a lokacin da ragowar ?wallar dake cikin idanunta.

"Alhmdlilah..!"

Bakinta ya sake furtawa a lokacin da kafafunsa ke tahowa gabanta, idanunta kuma na hango mata wata kyakkyawar dake jiranta a gaba...

Tabbas Rayuwa me adalci ce... Bata saka alkhairi da mugunta!

***

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*26 (Final Chapter)*

_Madly is the way I love you, forever is how long it will be...!_

~~~~~

Mintina goma da dauke ruwan, aka kwsnkwasa kofar gidan, Rukayya dake jingine akan doguwar kujerar falon ta kalli gefe inda ?ar aikinsu ke zaune tana kallon Tvn dake aiki a Wakin, ganin bata nan ya dan bata mamaki don ko kadan bata ji lokacin da ta tashi ba.

"Jummai..."

Muryarta ta kira ta a hankali tana ?o?arin gyara zamanta, sai dai da alama Jumman tayi nisa a cikin gidan da ba lallai ne ta jiyo ta ba, ?arar doorbell din ta sake cika dakin, sai kawai ta mika hannunta a hankali ta jawo ?arfen da take rikewa wajen tashi da kuma tafiya dashi, hannyenta da har yanzu ke rawa suka damke jikinsa a hankali kafi ta tattara dukkan ?arfinta akai ta iya mikewa.

Ta mike daidai lokacin da Jumman ta dawo tana fadin.

"Hajiya gani nan, koma kiyi zamanki.."

Ta koma din a hankali ta zauna yayin da Jumman tayi gaba ta bude kofar, kuma da yake kujerar da take zaune itace daidai saitin kofar, sai ya zamana Jumman na buWewa hoton ?aninta Ashraf ya shiga idanunta a lokaci gyda da gabanta ya fadi zuciyarta ta buga a kirjinta, ba wai ganinsa ne ya haddasa hakan ba...

Don kusan kullum yana zuwa duba du ita da mahaifiyar tasu tunda suka tare a gidan, kusan koyaushe ya tashi daga aiki nan yake faraboyowa kafin ya wuce gidan nasa, don haka yanyin fuskarsa a yanzun shine ya tsorata ta, wani yanayi ne da rabon da ta ga irinsa a tare dashi tun a lokacin farkon ciwonta, sanda suna Niger kafin ma ayi transfering dinta zuwa asibitin da tayi kusan jinyar watanni biyu a cikinsa anan Nigeria, lokacin da ta farka ta tarar da sakon dashi da kuma Ahmad suka kawo na saki tsakanin iyayen nasu.

Wani abu da tunda ya faru daga su Ashraf din har ?anuwansu suke ta fafutukar neman yayi hakuri ya mayar da Hajiya Nafisan amma duk yadda akayi, duk kokarinsu baya sauraren kowa yace ya riga ya yanke hukuncinsa, tunda har zata iya rufe idanunta akan saSon Allah ta kuma tura ?arta har wata ?asa wajen neman magani don biyewa bukatun duniya, to tabbas bai ga amfanin zamansa da ita ba.

Ita kanta Rukkayan sau Waya yaje ya duba ta a asibiti, a ranar a gaban Hajiya Nafisan ya bata hakurin kuskurensa ma cewar bai bata uwa ta gari ba a matsayinta na ?arsa sannan yayi fatan cewa abinda ya faru zai zama izna gare daga yanzu wajen gane tarin laifukan da ita kanta tare kuma da mahaifiyar tata suka taya ta aikatawa.

Sannan ya gaya mata cewa ta dawo wajensa da zama duk ranar da aka sallame ta tunda duk wata dawainiya da tsadar asibitin ma shi yake biya amma bayan an sallane tan, sai wannan tausayin da ubangijinke halittawa tsakanin ya'ya da iyayensu musamman ma Uwa... Ya hana ta juya baya ta koma wajen mahaifin nata.

Ashraf ne ya kama musu wannan gidan acan hanyar Tarauni suje zaune, kuma anan? mahaifiyar tata tayi jinyarta tare da yanuwanta dake yawan zuwa akai-akai suna taya su kwana, a yanzu ta sami sauki sosai har tana mi?ewa tsaye kuma maganarta ma ta fara fitowa sosai.

Sai dai har yanzu bata koma Rukkayyan da take a da ba, bata koma wannan kyakkyawar Rukayyan dake ji da kyan da take ganin ta hanyarsa zata iya samun komai a duniyar nan... Komai din da bai hada da Ma'aruf ba, wanda hakan sho ya rude ta wajen biuewa kowacce irin shawara da mahaifiyarta tata da ?awarta Hajiyar Sudan suka kawo, tunda ko a karon farko ta sani cewa da ?yar ta same shi a rayuwarta.

An kawo Hameeda kusan sau uku tazo ta? duba ta daga can gidansu Ma'aruf din da a yanzu Baffa ya aiko an shaida musu karara cewa yarinya ta dawo hannunsu tunda su suka kawo ta da kansu amma lokaci bayan lokaci za'a dinga kawo ta suna ganinta, kuma itama yarinyar ko kadan bata nuna tana sha'awar zama ba musamman ganinsu a wani sabon gidan ba inda ta saba ganinsu ba.

Sannan kamar kusan kowa, sun ji labarin abinda ya faru a gidan su Ma'aruf game da Hajiya Kilishi, tayi mamaki amma ba wani sosai ba don tun lokacin da ta zauna a gidan dama ba wani shiri suka yi sosai ba, don haka ta yarda duk abinda aka fada din zata aikata. musamman da su ma suke ji da tasu matsalar sai basu wani daukaki abin sosai ba.

Ashraf ya shigo a lokacin da wannan yanayin na fuskarsa, yanayin da ba ita kadai ba hatta Jamilan da ta buWe masa kofa a hankali ta rufe sannan ta juyo ta fita daga falon tana basu waje.

"Sannun da zuwa, ya aikin?"

Rukkayan ta faWa a hankali tana kallonsa bayan ya ajiye jakar hannunsa.

"Alhmdlilah, bata nan?"

Ta san wa yake nema don haka ta girgiza kanta.

"Tana wanka yanzu zata fito..."

Ta fada sai kuma ta sake cewa.

"Me ya faru?"

Don zuciyarta ta kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login