Showing 126001 words to 129000 words out of 132946 words

Chapter 43 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1116

tsayawa waje guda da tunanin abinda ya farun, shima kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya mika hannu ya bude zip din briefcase din da ya shigo da it, hannun nasa ya zaro wani envelope da a lokaci guda ya sa zuciyart bugawa, yaba tuna mata da emwanda ta gani na karshe a hannunsa shi da Ahmad, na sakin mahaifiyar tasu.... Yanzu kuma me ya faru?

"Daddy ne zai yi aure Rukyya,ga kayin daurin auren nan, sati mai zuwa...!"

Ya fadi hakan daodai lokacin da Hajiya Nafisa ta shogo falon, sakon kuwa ya shiga kunnenta yana sa zuciyarta nugawa ta kuma tarwatse a kirjinta!

Rukayya ta hadiye abinda bata san sunansa ba a makogwaronta, shikenan! Kamar ita Mahaifiyarta tayi biyu babu akan mutum guda, ta rasa mahaifinsu ta sake rasa shi kamae yadda itama ta rasa Ma'aruf sau biyu a tata rayuwar... Da gaske Daddy yake kenan, da gaske ba zai mayar da ita gidanta ba...

Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce ka kiyayi zuciyar mai hakuri lokaci aka kaishi karshe.... Mahaifinsu mutum ne mai tsananin hakuri da kuma kawar da kai akan tarin abubuwa, shi yasa tun farko mahaifiyar tasu ta samu sake yin abubuwa da yawa da taga dama... Tunda sau da yawa ma zasu yi abu har su gama bai ma sani ba balle ya hana, baya takura musu baya takura mata, ko lokacin da tayi aure har biyu bayan Ma'aruf, yanuwansa sai da suka nuna bacin ransu na ganin bata wani dadewa take sake fitowa amma shi bai ce komai ba, bai yi mata ko ?orafi ba ba balle faWa.

Idan kayi laifin da zaka bashi hakuri ma wani lokacin ba ma sai ka furta ba, alamun niyyar ka kaWai kan sa ya yafe ma tun kafin ma kace wani abu... Don haka ba ita kadai ba, tabbas kowa ma ya sani cewa da gaske mahaifiyarsu ta kai shi ?arshen da ba lallai ne ya dawo ba.

A lokaci guda wata kwalla mai dumi ta gangaro kan kumatunta, tana tuna mata da tarin lokutan da suke cikin jin dadi da fantamawa son ransu... Rayuwa bata da adalci...

"Rukayya.."

Ashraf din ya sake kiran sunanta yana sska ta Wagowa a lokacin da Hajiya Nafisa ta karaso cikin falon ta dauki envelope din katin daurin auren tana dubawa, ta a duba sunan wata mai sa'ar da rayuwa ta zaSo ta wajen bata kyakkyawar damar da ita tayi rikon sagegeduwa da ita.

"Naga anyi posting daurin auren Jawad a facebook, kin sani?"

Kalaman suka tsayar da tunani dama numfashin Rukayya cak a lokaci guda... Taba jin wani abu na yawo a cikin kanta da bata san menene ba, jiri ya debe ta daga inda take zaune, kanta ya zagaya ya sake zagayawa a cikin Wakin kafin idanunta su dawo dashi kan Ashraf dake kallonta har a lokacin, sai kawai ta girgiza kanta da ?arfi a yanzu kwallar dake fitowa daga kowanne idonta tana tarwatsewa a iska...

Tabbas Rayuwa bata da adalci! Musamman ga mata irinta wanda basu da hankalin fahimtar cewa duk kwaSewar al'amari, namiji yana da damar tsame kansa ya bar macen a cikin rauninta wanda ba zai iya kaita ga matsayin wasu damar dashi zai samu ba...?

Zai barta a cikin ?uncin da zata zauna tana maimaita kalaman Rayuwa bata da adalci!


***

*Abuja.*
*New Horizon Street, Wuse 2.*
*05:30pm.*

Iska ta kaWa farin labulen ?aton windon dake manne da wani ?aton falo, wanda yake a saman benen gidan. Tagogin windon gabaWaya a bude suke, an wangale su ta kowanne gefe yayin da sassanyar iskar daminar da ake yi ke kada labulayen dake jikinsa kalar ruwan toka, kalar da ta dace da kusan komai na cikin falon da yake da sassaukan ado, (Grey &ash) sai kuma tsilla-tsillan abubuwan da suke kalar baki kamar sauran kayan electronics.

Mintuna basu fi goma kenan ba da Wauke ruwan samn da aka fi kusan awa guda ana zabga shi, don haka garin a lulluSe yake da duhun hadari da kuma na yamma wanda a lokacin ?arfe biyar da rabi ne.... Koina a jike yake sharkaf dauke da danshin dake komawa sanyi-sanyi yayin da bishiyun dake harabar wajen ke ta rangaji a cikin iskar na jin dadin yanayin da kuma jikewarsu.

Falon dogo ne wanda a can ?arshensa ya hade da wajen dining da kuma kitchen duk a ciki, iri Waya sak da tsarin gidajen turawa kamar yadda akayi ginin a haka tun daga waje.

Akwai matattakalar bene daga gefe wadda akayi kusan rabi na jikinta da gilashi fari kamar yadda mafiya abubuwa suke a gidan, matattakalar zata kai ka zuwa sama inda anan zaka tarar da kofofin manya-manyan dakuna guda uku masu dauke da hadddun toilets da kuma walk-in wardrobes...

A watannin farko da suka zo gidan, Amina zata rantse ta shafe fiye da wata guda kafin ta gam sanin komai na gidan ta kuma saba da tsananin kyawunsa da take gani. Har faduwa ta taba yi har kasa watarana data yi alwala ta fito daga toilet saboda tsabar santsin marbles din dake gidan wanda ko mai ta shafa a a kafarta tana jin kamar zata zame.

Watansa hudu kenan a ciki, amma komai yana nan da kyallinsa kamar sabo, hatta kayan kitchen wanda su tafi komai tabawa a gidan balle kuma sauran dakunan da ta kan yi kwanaki biyu ma bata leka ba. Hatta doguwar kujerar falon da Ma'aruf kullum yake kwanciya akai bata taba nuna alamun nauyinsa na nunawa ba, ko kuma tace nauyinsu tare...

Daga cikin falon, Amina na tsaye a jikin sink din dake tsakanin drawers na kitchen din, ta kunna fanfon tana wanke wani farin kwano data dauko yayin da sassanyar iskar daminar ke shigowa tana kada ?an kananan gashinta da suka taso sama saboda laushinsa, babu dankwali akan nata sai gashinta da ta daure da wani yalon ribbon, rabon da ta taje shi ma kusan kwanaki biyu kenan.

Rigar jikinta wata loose T-shirt ce ta maza fara kal wadda bata fi rabin cinyoyinta ba, ta tattare duka hannayen rigar zuwa gwiwar hannunta yayin da maSallan sama ma bata gama rufe su ba.

Ta juyo daga jikin sink din ta dawo kan worktable din dake tsakiyar wajen, ta shiga yanka albasar kanana a cikin wani farin kwano... A lokacin ne wayarta tayi ?ara daga can kan Centre table din dake tsakiyar kujerun falo, da saurita ajiye wukar kafafunta suka dauk ta zuwa can, siraran tafin kafar nata na bi ta kan santsin marbles din dake wajen har ta sauka zuwa falon wada ya danyi kasa da matattakala biyu kawai.

?afarta ta shiga cikin tattausan carpet din da? yake kalar grey, kamar kullum yatsun kafarta suka lume ciki kafin ta kara wayar a kunnenta da murmushin da ko mutumin bai tambaya ba zai canki waye mai kiran.

"Amma... Barka da yamma."

Ta fada da murmushi bayan sallama. Daga Waya bangaren, Amma tayi nata murmushin itama tana kokarin dauke kwanon dambunta da Hamida ke kokarin dauka sannan ta amsa.

"Barkanmu dai, kun yini lafiya?"

Amina ta gyada kanta.

"Alhmdlilah Amma lafiya kalau."

"Ya jikin naki? Ya nasa jikin shima?"

Ta cije lebbenta tana zama akan hannun kujerar dake gefenta, wata iska mai ?arfi ta shiga kaWa ta tana ratsa ?ar rigar jikinta tana shiga koina.

"Alhmdlilah Amma dukkanmu da sauki, da sauki sosai."

"Ga Hamida nan an kawo ta yau tazo zata hana ni cin abinci..."

Cewar Amman tana sawa fara'ar dake fuskar Amina ta karu a lokaci guda.

"Hamida tazo?"

"?azun nan da safe aka kawo ta, Abdurrahim ne yace zuwa goben zai zo ya dauke su gabaWaya har dasu Maryam su zo taren ku. Dambun shinkafa muka yi yau, shine ta hana kwanon kowa sa?at! Yanzu suka gama ci tare da Adam ta dawo kan nawa kuma n tsoro nake kar yayi mata yawa ya bata mata ciki, tunda har a rama Babanku yasa aka saka.'"

Amina tayi dariya.

"Ni ban san yaushe ta koyi haka ba, da fa idan bata san abu ba bata ci kwata-kwata..."

"Hajiya ma haka tace, ranar da suka yi Amala a gidan wai da kyar aka samu ma ta dandana, amma yanzu gashi mu ban t kasa ko zama."

Daga cikin wayar tana jiyo maganganun Hamidan tana fadin a bata da kuma na Hafsa tana cewa ta Wauko plate su ake zubowa tare."

Amina tace.

"Allah Amma nima raina ya biya tun daga nan, dambun nan naki daban ne ai, a gas kina yi ko a mangal?"

Amma tace.

"A mangal ne, Babanku kuma kafin ya fita da safe cewa yayi wai yafi son naki wanda kike hadawa da rama... Shine na bawa Adam ya siyo muka saka kar ya dawo ya sake min gori."

Amina ta bude bakinta kadan tana dariya.

"Baya ci sosai fa idan nayi, Amma kin manta har cewa yayi baya son tsaminta..."

Kafin Amman ta amsa daga cikin wayar Muryar Maryam dake shirin fita daga Wakin tayi magana da karfi tace.

"Missing Winki yake yi kawai..."

Amma tace.

"Ai nima naga alama, don ko da safe da zai fita sai da ya sake tambaya yau din zaku taho kuwa.."

Kwalla ta cika idanun Amina a take yayin da murmushin ta ya ?aru.

"Ni tawa kewar tafi taku Amma, ni kadai na san abinda naji a cikin watannin nan."

Ta fadi abinda ya canja akalar hirar tasu a lokaci guda. A lokaci guda da Amma ta gyara wayar a kunnenta sosai kafin ta tambaya.

"Wannan duk ya wuce yanzu Amina, tunda ga dawowar nan tazo, abinda kawai nake so ki bani tabbaci shine kin tabbata dai babu wata matsala har yanxu ko? Ya gama jin sauki gabaWaya?"

Wani abu ya zarce wuyanta a lokaci guda... Yaji sauki? Ma'aruf yaji sauki? Tana da tabbacci?

Tambayoyin da har take yiwa kanta kenan a kullum wayewar garin Allah tunda ya gaya mata cewa da gaske Win yu zasu koma, don ba sai wani ya gaya mata ba ta sani, duk abinda yazo ya faru a gaba, duk abinda yazo ya same shi zata karbi alhakin hakan ne ko da kuwa duniyar gabaWaya zasu goya mata baya don kare ta.

Watanni hudu kenan da dawowarsu garin Abuja, bayan watanni biyu na zaman jinyar Ma'aruf a asibiti da kuma faruwar wasu tarin al'amura masu Waga hankalin da babu wani a cikinsu da ya taSa sanin irinsa.

Ciwon Ma'aruf yayi tasirin da a karon farko likitocin ke zaton cewa ya rasa hankalinsa bakiWaya, don kusan mutum uku ne suka sa hannu akan cewar Bipolar diorder dake damunsa ta kai mataki na ?arshe wato 'Mania'.

Sai da aka samu banbancin ra'ayi a wajen mutune guda biyu sannan Baffa ya bada umarni aka fita dashi zuwa asibitin da yake ganin likita acan London, da Ishaq da kuma Baba Usman su suka kai shi, don har a lokacin hankalin Baffa ya kasu gidaje da yawa, wajen fuskantar tarin shari'ar da ake yi akan Hajiya Kilishi sakamakon wasu laifukan nata da ake ?ara ganowa a hankali ciki har da aminiyarta da take zarginta da raba ta da Wan cikinta da tayi tsawon shekaru.

Zancen ya sake ta da hankalin kowa a sanda suka ji shi... Don yanuwan nata da ?arfinsu suka zo da kuma tarin hujjojin da suka sa dole aka hada dasu a cikin shari'ar... Wanda bayan hakan ne, likitocin dake kula da Ma'aruf acan suka yi nasu ?o?arin wajen dawo dashi cikin hayyacinsa, sai dai da sharadin cewa dole ne ya samu a?alla watanni uku a wani waje da hankalinsa zai kwanta ba tare da tashin hankali da kuma yawan ganin mutane ba... Wani waje da zai bashi nutsuwar zuciya da kuma kwanciyar hankalin da zai manta da dukkan matsalolin da ya fuskanta yaji sunyi masa nisa har zuwa lokacin da kwakwalwarsa zata daidaita.

Don haka tun kafin su dawo Ishaq yasa suka kama hayar wannan gidan a cikin garin Abuja, wata kawatacciyar unguwa da kusan tsarinta da komai na kasar turai ne, don tun daga ranar da suka zo Amina ta sani cewa ba kowa ne a duniya yake samun damar rayuwar a irin waWannan wajajen ba.

Da farko ta sha wahala wajen fuskantar tarin abubuwa daga sabon Ma'aruf Win da a kullum take ganinsa a haka, baya magana baya cin abinci, baya komai sai sallah shima sai idan lokacinta yayi kenan, kuma tsakaninta dashi abu biyu ne kawai zai amsa maganarta da Eh ko A'a, sannan idan zasu kwanta zai rungume ta a jikinsa zuwa safe.

Baya cewa komai baya bata labari, baya mata ?orafi, baya tambayar kowa baya tambayar aikinsa, ko Hamida bai taba tambaya ba, ita kaWai Win kawai da ya gani tare dashi ita kadai yake kallo yana binta da eh ko a'a idan tayi masa magana, daga baya har tunani tayi itama din kamar bata da amfani a tare dashi, don haka sai ta samu rana guda ta gwada tafiya daya dakin tayi kwanciyarta don ta gani idan har zai kula bata nan ya neme ta.

Fatanta kuwa ya karbu don bata ko kai ga yin bacci ba taji motsin bude kofar dakin, da murmushi a bakinta lokacin da ya hawo gadon ya rufe ta a jikinsa ba tare da yace komai ba, ta dago da kanta tana kallonsa ta cikin dan siririn hasken Wakin dake shigowa daga windo na fitilar waje, idanunsa a lumshe suke yana kallonta dasu kamar a rufe.

_"I'm sorry BabyDoll..."_

Muryarsa ta fito a hankali da sautinsa wanda a lokacin idan zata kirga, bai fi cikin hannunta taji shi ba tun bayan zuwansu gidan, ta kalle shi kusa na wucewar minti guda tana auna daWi da zuciyarta ta shiga kafin a hankali bakinta ya sake talewa da wank murmushin sannan ba tare da ta sake cewa wani abu ba ta kwantar da kanta a saman kirjinsa kawai yana kara rungume ta.

Kuma tun daga wannan ranar, sai abubuwa suka fara yin sauki, ya zama yana magana daya biyu har ma ya tambaye ta wani abu, idan ta kunna T.v baya kashewa, sannan sau biyu a ranakun da yaga bata jin dadi kuma an kwana biyu likitar dake zuwa duba ta bata ba zo yace mata ta dauki wayarsa ta kira ta kasancewar duk lambobin mutanen da zasu nema idan suna bukatar wani abu a wayar tasa Ishaq ya ajiye lambarsu.

Lambobin mutum biyu ma kaWai tafi kira, daga mai canja musu ruwan dispenser sai mai zuwa ya siyo duk kayan abincin da take bukata, kuma a baya yawanci lokacin da zasu zo din, yana jinta dasu a ?ofa ba zai taSa tasowa ba... Sau Waya ya taba ido ya kalli mai yin cefenen da ya taya ta shigo da ledojin kayan da ya siyo ciki... Amma a yanzu shi da kansa yaje bude musu kofa ya karbi duk abinda suka kawo.

Bayan haka da ta fahimci ya fara sakewa, sai ta fara bashi labarai a hankali a hankali, yan kananan labaran da baza su ja hankalinsa da yawa ba wadanda ke magana akan? hakuri da kuma karbar kaddara, ba karara take fito da hakan ba, ko kadan ma bata amfani da kalaman da zasu fito da manufarta, labarin ne kawai zai zo a sigar dashi zai fahimci hakan, kuma da ta kula ya fara tunani na fahimtar abinda take nufi, sai ta kirkiro wani aikin ta tashi ta bashi waje don ya kara fahimtar abinda take nufi Win.

Sannan ta dinga kokarin binsa jam'in sallah, tana gani ya tayar zata yi saurin yin alwala tazo ta bi bayansa.... Tayi tarin abubuwan da ta san ko taya ya ne zasu iya tsayar da hankalinsa waje guda ya samu ya dawo wannan Ma'aruf din da ta sani, wannan Ma'aruf din da tazo ta tarar dashi cikin kyakkyawar rayuwarsa.

Jinya ce irin tata tayi ta, tayi da jikinta da kuma zuciyarta,tayi dukkan kokarin da zata yi da dabararta da kuma wasu daga cikin shawarwarin Amma har ma da Ishaq wanda a rashin Wanuwan nasa sai ya zama ita yake kira a kullum yaji cigaban lafiyarsa.

Har sai da ta kai Baffa da bakinsa watarana da suka yi waya ya bata shawarar cewa ta dinga saka lemon tsami a ruwan Wumi ta samu yasha kafin ya kwanta, yace mata hakan ba karamin abu bane dake wanke zuciyar Wan Adam...

Hajiya Maimuna kuwa tasa Munaya ta rubuto mata tarin addu'o'in wasu kuma tayi recording da muryarta tana tofawa a cikin ruwan shan sa, wani lokacin har ma da kayan da zai saka kafin ya fito daga wanka. Samirah ma ta sha kiran waya ta gaya mata abincin da ta san yana so tun asali wadanda idan anyi ransa ke jin dadi.

Kowa ya taimaka, kowa ya taimaka da iya abinda zai iya duk kuwa da halin da har yanzu zuciyioyinsu ke ciki, musamman su Samiran ?a?an Hajiya Kilishin da ko a idanunsu, ba?o zai shaida damuwar da suke cikinta har yanzu, amma har su Salma dake gudajensu suna kira su ji lafiyarsa????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? .

Don haka duk da ta sani cewa ba da iya taimakonta kadai suka karaso matakin da Ma'aruf din yake a yanzu ba, matakin da take ganin kusan bashi da maraba da warkewarsa gabaWaya, duk da haka tana jin zata Wauki alhakin duk abinda zai biyo baya idan har aka samu wani akasi ga me e da lafiyar tasa.

Kowa yayi kewarsa a gidan nan, tarin kewar da take ganin kamar shine ruhin gidan nasu gabaWaya, don irin murnar data ji daga kowa a gidan a ranar da shi da kansa ya dauki waya ya kira su, wani abu ne da mizaninta ya kasa aunawa.

Tana tsaye daga baya bata ko jin me suke cewa, da amsoshinsa kadai take ayyana tarin murnar da har ?walla sai da ta saka ta, sai ta juya masa baya tana sharewa da tafin hannunta yayin da zuciyarta da ma duk wani abu mai hankali a cikin kanta ke ?ara tasbihi ga jalla wata'ala da ya takaita wahalarsa da ma tasu bakiWaya, don ko daga gidansu Amma tace kowa yayi kwanan farin ciki musamman ma Baba wanda ya matsu ya ga dawowarta.

Bayan hakan Ma'aruf da kansa ya yanke ranar da zasu koma Kanon bayan tarin abubuwan da suka ?ara gamsar da ita warkewarsa, don a yanzu har da Faruk suna waya game da harkokin kamfaninsu, yana gaya masa iri tsarin sababbin securities dn da Abdurrahim ke sakawa a kowanne bangare na kamfanin ta yadda babu wani mai wayon da ya isa ko yaga kaya ma idan za'a fitar dasu daga kamfanin balle kuma kuWi.

A yanzu haka ma kusan sati guda baya yini a gidan yana can fafutukar rufe asibitinsa MMB-6?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login