Showing 111001 words to 114000 words out of 132946 words

Chapter 38 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1146

Salamatun da kuma yaron dake kiran kansa da Jawad suka tanadar ta kowanne bangare, musamman babban al'amarin da ya ?ara girgiza kowa na cewar Jawad Win ya tashi ne a gidan Alhaji Bashir wanda yake ?anin mahaifinsa.

Komai ya faru ne kamar almara, kamar mafarki ko kuma wani labari da ba zai zama gaskiya ba, shi yasa a cikin lokaci kadan zancen ke ta tawo kusufa-kusufa a cikin danginsu har ma da waje, wadanda ke zaune a garin Kanon ma har sun fara zuwa don ganewa idanunsu, don Salamatu kiran kowa take yi, kowa ya kira ta zata ce yazo gidan saboda murnar dake cike fala ranta.

Ko ta zancen ?awar tata Kilishin da kuma matakin da ya kamata su dauka akanta na irin wannan zaluncin da ta haifar bata yi, sai yayyensu maza uku da suka gama shawara tare da Nasir ne sannan? suka yanke shawarar Waukan yansanda a tafi har inda Kilishin take, don wanda yake Babba a cikinsu ya Wauki zafi da yawa ta yadda ya rantse da Allah babu abinda zai hana su zama akan shari'ar.

Wayar da Aunty Bilkin take tare da wata ?awarta dake can wajen aikinsu ta kare daidai lokacin da? Hajiya Salamatun ta bude kofar dakin ta shigo hannunta Wauke da wata katuwar leda fara.

"Aunty Bilki Yaya Nura zai wuce yanzu."

Ta fada tana kallonta a cikin mutanen dake dakin, da mamaki a fuskarta tace.

"A'a, tafiya kuma ba dauka zasu bari ko zuwa gobe idan komai ya natsa, naji suna zancen za'a je a taho da Kilishin."

Sunan Kilishin da ta ambata ya rage fara'a a fuskarta kafin tace.

"Shi kaWai zai tafi, su suna nan anjima zasu je tare da Nasir, yace shi yana da meeting din wani contaract da zaiyi a yau."

Ta gyada kanta tana kallon ledar hannunta sai tace.

"Kaya ne nasa aka kawo masa Aunty Bilki, daga Kaduna yake kuma ashe bai zo da kaya ba."

Ta fada tana fito da set Win kaya guda goma Winkakku da wani yaronta ya bata lambar irin wajajen Winkin nan na yanzu masu sunan 'Wardrobe' da suke da kaya dinkakku nasu kyau da zaka je ka siya.

Yadikan dukkaninsu plane masu tsananin kyau da kalolinsu mabanbanta, kowanne anyi masa Winki mai kyau irin sealed din nan da maza ke yayi.

"Zai daWe ne kafin ya koma?"

Aunty Bilkin ta tambaya, sai ta girgiza kanta.

"Babu inda zai koma Aunty Bilki, tare zamu je kuma tare zamu dawo na gaya masa ne dai kawai ya kira Bashir din ya gaya masa komai."

Ta faWa da dukkan ya?inin da zai iya fitowa daga cikin zuciyarta, sannan ta mayar da kayan cikin ledar da cewar zata same shi ta bashi, caraf? sai Amira ta mi?e ta karSa da niyyar kai masa, don haka sai ta samu waje a kusa da Aunty Bilkin ta zauna, tana gaya mata mutanen da suka kira ta a waya suna cewa ayi mata barka.

Sai dai sam ba fahimtar ta sosai take yi ba, ba komai take ganewa a cikin bayanin ba, zuciyarta zagaye kawai take yi taba komawa daren jiya, daren jiya da suka zauna tare da Jawad suka fayyace komai game da al'amarin, tarin bayanin da yayi nusu na yadda yaji labarin komai a cikin kankanin lokaci da ma dukkan abunda ya faru bayan nan,sai dai ba komai ne yafi tsaya mata a rai ba illa sunan Bashir da ya kira a matsayin mutumin da ya rayu a gidansa kuma yake masa kallon mahaifi tsawon shekarun nan.

Mukaminsa da ya ambata na matsayin minister shine abinda kai tsaye ya tabbatar mata da cewar Bashir din da ta sani a rayuwarta ne, kanin mijinta Ibrahim wanda yake kamar yayansa, don tun kafin mijinta yayi aure shi yake da mata uku, tana tare da Ibrahim din kuma ya kara ta uku mai suna Mardiyya, ta san shi ta san matansa sarai! Don sun yi shiri da matarsa ta biyu Yagana. Bayan abubuwa sun lalace a tsakaninsu ne sai itama ta juya mata baya kamar sauran duka danginsa.

Ibrahim yana son haihuwa, sun fara samun matsala ne tun daga lokacin da ta haifi dan da akace musu ya rasu, sannan sai abubuwa suka lalace a tsakaninsu bayan an tabbatar da matsalar da ta samu a mahaifarta, matsalolin da suka kai ga rabuwar aurensu tun a wancan lokacin, kuma cikin wani ikon Allah sai daga ita har shi babu wanda ya sake haihuwa a dukkan aurarrakin da suka yi bayan nan har zuwa lokacin da Allah ya karbi rayuwarsa.

Tana tuna lokacin da aka gaya mata rasuwarsa, shekaru kusan ashirin da wani abu a baya, tana tuna iya zafin hakan da taji tun a wancan lokacin, zafin da bai kai wanda take ji a kirjinta yanzu ba, wanda take ji idan ta tuna cewa Ibrahim ya rasu ne yana tare da Wansa ba tare da ya sani ba, don a bakun Jawad take ji cewa anan gidan Bashir Win akayi jinyarsa kafin ya rasu...

"Kukan me kike yi kuma Salamatu? Idan na murna ne ai ya isa haka, idan kuma wani tunanin ne a ranki ki kauda shi gefe dan Allah, ki godewa Allah da ya nuna hakan tun da ranki kafin ki bar duniyar, ki sa a ranki cewa ya so ki da rahama ne tunda har ya baki wannan damar... Ga ki da ranki da lafiyarki da dukiyarki har da kwarinki, ba sai a lokacin da ba lallai ki iya komai ba... Gidewa Allah zaki yi ki kara gode masa Salamatu, ba kullum ne al'amari irin wannan ke faruwa a duniyar ba."

Sai ta sa hannunta tayi saurin goge gawayen fuskarta sannan ta daga kai alamun ta yarda hakan ne... Sannan ta dago daidai lokacin da jikokin Aunty Bilkin yayan wata yarta Muniba da itama ta karaso a lokacin suka taho da gudu suka rungume su... Ta ri?e yarinyar a jikinta tana kallon Muniban data shigo rike da karamin dan ta a hannu yayin da sauran ?anmatan dakin suka juya suna yi mata magana, kowanne fuskarsa dauke da fara'a...

Sai kawai ta furta kalmar Alhmdlilah a fili tana kara godewa Ubangiji ya daya azurta ta da wannan damar a rayuwa.

*

Jawad yana tsaye daga cikin Wakin, daga jikin windon Wakin inda aka saki farar liner dake jikin labulayen ta yadda daga yadda yake a tsaye yana hango wasu motoci biyu da suka shigo gidan mutanen cikinsu na ?o?arin fitowa. Hannunsa Waya na kare da waya yayin da guda Waya ke rike da labulen yace.

"Wallahi mutane take ta kira Haro, daga safiya zuwa yanzu gidan ya kusa cika... They are making me feel uncomfortable, yanzu muka rabu da shi kanin nata Nasir, yana gaya min cewa idan yansandan sun iso tare zamu fita zuwa gidan ita Waya matar, tsakanin jiya da yau Haro na rasa ma lokacin da zan zauna inyi tunanin cikin kaina..."

Daga cikin wayar Haro yayi dariya kafin yace.

"Kace ka zama wata sabuwar amarya kawai, but I'm really happy for you man! Wallahi kayi sa'a ba kowa ne ke gane irin wannan abun game da rayuwarsa kuma ya samu mafita cikin kankanin lokaci ba... You solved everything out kafin ma mu sani, don ni sai jiya da daddare ne da muna waya da Bello na office dinku yake ce min wai ka dauki hutu a lokaci guda yana fata dai lafiya sannan na san cewar ashe baka gari ma."

Jawad ya saki labulen ya taho cikin dakin yana kare wa kayan cikinsa kallo, a tunanin Haro komai ya faru ne cikin sauki, a lokaci guda ba tare da wani bata lokaci ba, amma shi ya sani halin da ya shiga da kuma wuyar da ya sha a iya wannan Wan tsukin,? idan za'a rarraba ta a zuciyar wani zai Wauki watanni kafin ya iya kai ?arshensa.

Shi kadai ya san abinda yaji shi kuma shi kadai ya san abinda ya fuskanta a cikin zuciyarsa da ma jikinsa, sannan ga tasirin dukkan abinda ya faru jiya, na yadda ya samu abinda baiyi zato ba bayan sun bashi tabbacin da shi kansa ba zai iya musantawa ba. kusan hotuna goma Hajiya Kilishi ta dauko masa na mahaifin nasa da takira da sunan Ibrahim Shanawa, kuma tun a hoton farko yaga kamar ya san fuskar kamar ya gane shi duk da cewa suna ta zuzuta kammaninsa dashi.

Sai da ya fara yi mata bayanin inda ya taso sannan komai ya fito fili, wani ikon Allah da kuma wata sabuwar isharar ta fahimtar dashi cewa a tsawon rayuwar da yake tunanin ya shafe a hannun wasu mutane, ashe ba wasu bane, a cikin danginsa yake, a tsakiyarsu ma tunda tun kafin hawan Alhaji Bashir matsayin minista gidansa yake a matsayin centre guda ta family dinsu, kusan kowa yazo zai samu wajen zama babu takura, shi yasa a yanzu da yake matsayin ministan ?an aikin dake tafiyar da al'amarin gidan su kansu wajensu daban.

Bai kira kowa ba, bai kira su Hajiya Mardiyya ko kuma wani a gidan ba har yanzu, yafi son sai ya gama tara hankalinsa waje guda tukunna, yafi son sai ya saita iya abinda ke gabansa a yanzu, don ya sani gaggawa ba zata haifar masa da komai ba.

Ya ajiye wayar hannunsa a gefen gadon dakin sannan ya nufi ?ofar toilet ya buWe... wanka yake so yayi ya canja kayan jikinsa shi yasa yake ta jinkirtawa don ta gaya masa cewa zata sa a kawo masa wasu, hoton fuskar Zainab ya gifta a ransa a lokacin, ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha wanke masa toilet, ta haka ya fara gane ta, ta haka ya fara gane cewa an canja masa mai gyara masa daki kafin ma ya fahimci wacece ita.

Ya cije lebbensa kadan yana ?o?arin tuno Waya zagayen halin da yake ciki, sai dai hakan baiyi nisa ba lokacin da aka kwankwasa kofar Wakin, sai ya saki ta toilet Win da yake ri?e da ita sannan ya matsa gaba ya buWe.

Wata yarinya ce, tun safe ya ganta a gidan bayan ya tashi daga bacci, don bayan an kawo masa breakfast ma ta zo daga baya ta kawo masa lemo da kuma Pringles tace ya kara, bai ma san wacece ita ba, bai san matsayinta ba,yaji dai kawai suna koran sunanta da Ameera.

Bakinta ya tale da murmushin da yayi daidai a fuskarta.

"Yaya J, hope dai ban katse ka kana wani abun ba?"

Ya zura wayarsa dake hannu a aljihu sannan ya girgiza kansa yana kallonta.

"Kar ki damu I'm fine."

Sai ta sake wani murmushin sannan ta gyada kanta.

"Toh Alhmdlilah... Kaya ne Aunty tace in kawo maka."

Ta fada tana nuna ledar hannunta da yatsanta daya mai dauke da wani zobe dake kyalli a cikin fitilar wajen.

"Nagode." Ya fada yana mika hannunsa fon ?arba amma bata miko din ba sai tace.

"Can I choose a colour for u? Wanda zaka sa yanzu?" (Zan iya zaSar maka kala?)

Jawad ya ?ara kallonta, zuciyarsa na kokarin gaya masa wani abu da ba shine ransa ba yanzu, sai kawai ya sake mi?e hannunsa yace.

"Kar ki damu zan Wauki duk wanda yake a sama ne kawai."

Yayi zaton zai ga canji a fuskarta, amma sai jawai ta ?ara yin murmushi mai fadi tace.

"Shikenan, muna jiranka."

Da haka ta mi?a masa kayan sannan ta tsaya tana cigaba da kallonsa da murmushin a fuskarta ba tare da ta juya ba. Wani abu da ya ratsa zuciyarsa kenan yasa duk yadda ya kai ga jinsa wani iri sai da wani guntun murmushin ya sauka a lebbensa.

"Nagode."

Ya faWa yana rufe ?ofar, ta kaWa masa yatsu biyu a gefen fuskarta tana cigaba da murmushin kafin ya rufe ?ofar a fuskarta.

Ya rufe kofar daidai lokacin da wayarsa dake cikin aljihu ta shiga kara, hannunsa ya jawo ta da sauri ya duba, sunan Nura ya baiya na tar a jiki don haka ba shiri ya daga ya kara a kunnensa tare da sallama.

Daga cikin wayar Nuran ya amsa da sautin muryar da ya sanya zuciyarsa tsalle tun kafin Nuran ya kai ga faWin abinda ke bakinsa.

"Yallabai an samu matsala, wallahi yau da safe da muka tashi ba mu ga yarinyar nan ba, tun safe ake nemanta har yanzu babu labari....!"


***

_A cikin shafi biyu masu zuwa a gaba, labarin Farar wuta zai kai ga tsayawa insha Allah..._

_Nagode da tarin ha?urin ku, Allah ya sani na fiku damuwa ganin yadda lokaci ke ta jan mu, da kuma yadda nake ta yawo da nauyi a ka._

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
#fikrawriters
#FararWuta.
#fikrawriters
#FararWuta.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*24*

_There are no happy endings, endings are the saddest part, so just give me a happy middle and a very happy start..._


~~~~~~

"Sai gyada Hajiya, sai gyada ci ko tsaraba.."

Wata yarinya dake Wauke da bokitin tallan gyadanta ta faWa tsaye daga bakin wata hayis dake dauke da fasonjoji wanda mafi akasarinsu mata ne dsuke da yara da kuma wasu a goye, banda hayaniyar cikin tashar akwai ta cikin motar ma da baka jin komai sai sautin muryoyin matan kawai dake ta kacaniya suna kuma ciye-ciyensu kala-kala.

Wani dattijo ya taso ya tsaya daga bakin ?ofar hannunsa ri?e da littafi zai fara karSar kuWin mota da kuma rubuta sunaye, wata mata dake Wurawa yaronta wani farin kunu? a leda tace.

"Motar fa bata cika ba..."

Ya gyada kansa.

"Na sani ai Hajiya ba saura mutum Waya ba, kowa ya fito da kuWin motarsa... Ke ya sunanki?"

Ya faWa yana ?o?arin rubuta sunan mace ta farko dake bakin ?ofar yayin da kowa a motar ya shiga ?o?arin binciko kuWi daga jakarsa, mutumin ya gama rubuta sunan ya dago da kansa daidai lokacin da idonsa ya sauka akan wata yarinya da ta karaso jikin motar sanye da wani farin hijabi dogo.

"?an mata ina zaki je? Jaji ko kuma Kawo?"

"Sameru zanje..." Muryarta ta faWa kusan a shake sautin na fitowa a hankali, sai ya girgiza kansa.

"Ga motocin Sameru can a wancan layin... Kudinki dari takwas ne, amma zan miki ragi, kawo dari bakwai a rubuta sunanki tun daga nan kafin mu isa."

Zainab dake tsaye tana kallonsa ta haWiye a wani abu a makogwaronta kafin ta girgiza kanta a hankali.

"Bani da kudi malam, dan Allah..."

"Baki da kudi?"

Ya tambaya sautin muryarsa na juyewa zuwa wani abu kamar izgili.

"To rawa zaki yi su kai ki Samerun ko kuma ya za'ayi?"

"Haba bawan Allah, kace mata babu mota kawai mana, sai ka bi ta da bakar magana."

Wannan matar ta faWa daga cikin motar, vai saurari daya daga cikinsu ba ya juya kawai ya cigaba da neman sunayen mutanen dake cikin motar.

Wani abu ya sake wucewa ta makogwaron Zainab a lokaci guda da ta shiga murza yatsun hannunta daga cikin hijabin, ?walla ta sake cika idanunta a lokaci guda, kafafunta sun gaji, tayi tafiya mai nisa kafin ta kawo tashar, tayi tafiya tun daga cikin kauyensu inda ta fito ta baya har zuwa wannan ?auyen dake gabansu inda anan babbar tashar da ake samun mota zuwa ?auyuka daban -daban a wannan hanyar take.

Kuma bayan isowarta kai tsaye aka nuna mata wajen da ake hawa motocin inda take son zuwa, Sameru... ?auyen da ?an uwan mahaifiyarta suke... Wajen da ta san cewa duk duniya bata da inda yafi shi a yanzu, babu wani waje ko kuma wani masaukin da wani zai bata da matsayinsa a idanun al'umma dama nata gabaWaya zai kai can.

Hadiza, wata yarinya da tayi kusan sa'arta a cikin gidan mijin nahaifiyarta da ta baro ita ke shaida mata dukkan abinda ya faru a lokacin rasuwar mahaifiyar tata, yadda yan uwansu kowa da kowa ya hallara a gidan da kuma tarin rigimar da aka sha da mijin mahsifiyar tata skan aikin da tmya tura ta.

Wani abu da lokacin da tana Abuja babu abinda take tunawa kamar hakan, yadda yanuwan mahaifiyar tata suka yi iya kokarinsu wajen ganin ta basu ita sun rike a lokacin da zata yi aure, amma ta ?i haksn,tace ta san zsi tike ta da amana kamar mahaifinta tunda amininsa ne, sannan ta kafa hujjar cewa duk duniya ita kadai take da ita a matsayin ?a kuma bata tunanin sake samun wata haihuwar a yanzu duba da shekarunta, don haka babu yadda suka iya suka bar ta a wajenta.

Kuna tun daga farko zaman gidan baiyi dadi ba sam! Sun sha wahalar da duk da karancin tunaninta tasha lissafa musu mafita ta hanyar mahaifiyar tata ta rabu dashi, amma bata yi hakan ba har karayar arziki tazo ta same shi inda babu bata lokaci ya shiga tura ?a?an sa aikatau, wanda daga baya ya hada har da ita da tarin hujjojin da mahaifiyar tata bata iya ?arewa ba.

Tana tuna ranar da ta tafi, ranar da ta tafi ta barta, tana tsaye daga kofar dakinta tans share hawaye da bakin zaninta, kwana suka yi tana bata hakuri da kuma shawarwarin da zata kare kanta yayin da itama ta shafe daren tana sa?e-sa?e cike da tunanin ha?uri irin na mahaifiyar tata da kuma taraddadin inda zata je da abinda zata tarar.

Ashe dukkan tarin abinda zata tarar din bai kai wanda zata dawo kuma ta iske ba, ?ofar dakin mahaifiyarta a ?ulle da wani ?aton jwado a daidai lokacin da ta taka kafarta cikin tsakar gidan, da kuma idanun mutanen gidan da yadda suke kallonta da mamaki da kuma wani abu da bata iya fassara shi ba sai a lokacin da mutumin nan yake gaya mata cewa babu mahaifiyarta...

Ta rasu, babu ita a duniyar nan, ta rasu sati biyu da suka wuce... Ta rasu babu wanda ya gaya mata, babu wanda yabi ta inda aka tura ta ya gaya mata. Mahaifiyarta ita kadai take da ita a duniya, guda daya ce babu wata... Amma ta rasa ta babu wanda ya iya zuwa ya gaya mata sai da ?addara ta dawo da ita da ?afafunta sannan ta samu labari, fuskar Jawad ta haska cikin idanunta a sannan, lokacin da ya riko hannunta kafin ta kai ga fita daga motar ya gaya mata cewa yana jiranta, zai jira ta a wajen har ta gama abinda zata yi ta dawo...

_"Ba zan iya tafiya babu ke ba, amma nayi alkawarin zan dawo dake insha Allah Zainab..._

Haka ya faWa da sautin muryarsa da duk da ba ta shi take yi a lokacin ba sai da ya ratsa har cikin zuciyarta, bata san me suka fito nema a lokacin ba, bata san me ya kawo shi har cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login