Showing 42001 words to 45000 words out of 132946 words

Chapter 15 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1131

kan ?irjinta kafin kalaman Amma su fito da tasirin da yasa komai tsaya cak a cikin kanta.

"Idan ya dawo, ki san ta hanyar da zaki gaya masa cewa su nemi mutumin da suke nema har a cikin Prison!"

***

_Na gaya muku Kilishi ta fara ganin ta kanta!_

_Kun fahimci cewa Amma ta mayar da Kilishi ne kamar boyi-boyinsu?..._=??

_Hausawa sunce idan baka iya kama Sarawo ba, shi barawon sai ya kama ka..._>?#?>?#?

*Muje zuwa dai, an fara kunno wutar!*

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*09*

~~~~~~

_There was love and then there was your love, and that was entirely different._ _-Unknown._


**

*Shekarar 1997*

"Ga kanun labaran bi da bi....

A jiya laraba ne mai girma shugaban ?asa General Sani Abacha ya ?addamar da taron karSar sababbin kayan ayyuka na aikin wutar lantarki a yun?urinsa na samar da Worewar wutar lantarki a faWin Nijeriya bakiWaya...."

Rediyon dake yashe a tsakar gidan ke fitar da labaran yayin da mace Waya tal don dake tsajar gidan ke tsugunne daga can gefe tana wanke-wanke. Da misalin karfe goma sha boyu ne na rana, ranar kuwa ta hasja a sama kwal alamun lokacin na rani ne. Daga gefe guda na tsakar gidan akwai wutar itace daje ci bal- bal yayin da tukunya ke tafasa akanta.

"Assalamu alaikum."

Muryar Amma ta wancan lokacin tayi sallama daga bakin kofar tana shigowa, hannunta daya dauke da wata ?ar karamar yarinya mai kama da ita sak! Kuma sautin muryarta da ya fito tare da sallamar, yasa wannan matar juyowa ri?e da kwanon silbar dake hannunta, fuskarta ta haska da tsananin murna da kuma farin cikin ganin nata.

"Maraba lale da Halima, marhaba bikum."

Amon muryar tata ya fito da labarin kan fuskarta yayin da ta mike da sauri tana kara yi mata sannu da zuwa.

"Shigo, shigo Halima, jiyan nan ai muke zance da Sani nace mun kwana biyu bamu ga juna ba zan sami lokaci inje in gano halin da kuke ciki, ashe kya ce ma kuna tafe."

"Wallahi Hajiya iya, muna hanya kam."

Amman ta fada da nata murmushin itama bayan shigarsu dakin.

Hajiya iya ta karbi yarinuar dake hannunta kafin Amman ta zauna kan tabarmar da aka shimfida a saman ledar dakin.

"Anya kuwa ba zan dawo da kishin nan ba, da nace na ha?ura muyi zaman salama amma wannan kyan da kike zubawa Aminatu zan yarda kuwa?"

Ta faWa tana kallon yarinyar data kira Aminar, wadda ke shirin Sangalewa da dariya kamar ta gane maganar da take mata, sai ta cigaba da cewa.

"Kodayake idanu ne kawai, wannan hancin ba tasowa zaiyi ba."

Amma tana ta dariya har lokacin da itama Hajiya iyan ta nemi waje ta zauna kan wani kushin dake fuskantar tabarmar ri?e da yarinyar.

Hajiya iya ?anwar mahaifinta ce, dattijuwa ce mai kirki da kuma sanin ya kamata, bata taSa haihuwa ba, amma akwai wani Wan mijinta guda Waya Sani da ita ta rike shi tun yana yaro, don haka kusan su ?anuwanta duka sun san shi, tana yawan zuwa dashi wajensu idan har zata je.

Amma a Nigeria ta tashi tare da sauran ?anuwanta, amma bayan rasuwar iyayenta? ita ta koma Niger yayin da sauran ?anuwanta biyu suka zauna a wajen yayarta Zahra'u (Tanti) wadda tayi aure a lokacin. Amma da Allah yayi dole bata da rabon zama a Niger Win dole aure ya sake dawo da ita Nigeria, kuma aka kawo ta unguwa guda da Hajiya iyan, don haka kusan kodayaushe suna cikin ziyarar juna tunda ita? kadai ce ?aruwar iyayenta mafi kusa.

"Kuna lafiya Halima?"

Amma ta gyaWa kanta a hankali har yanzu da ragowar murmushin a fuskarta.

"Maigidan naki da nasa ?an uwan suma duk kalau?"

Ta sake gyada kanta.

"Lafiya lau Hajiya Iya. Alhmdlilah."

Sai ta gyada kai itama tana sake kallon Aminan dake hannunta.

"Wannan kuma ba sai na tambaye ta ba, daga wannan kumatun nata ma na san kalau take."

Dukkaninsu suka yi wani murmushin yayin da Amina ta bangale da dariya alamun ta fahimci da ita ake. Kuma karar tafasar tukunyar nan daga waje ya katse Hajiya ita daga maganar da zata yi, ta mike da sauri tana fadin bari tazo, Amma ta karbi Amina yayin da ita kuma ta fita.

A wannan lokacin ne kuma tayi bakuwa, wata kawarta ce mai suna Inna Hajara tazo, a tsakar gidan suka gaisa kafin ta dauro alwalarta sannan ta shigo dakin, suka gaisa da Amman dake shayar da Amina dake kokarin bacci sannan ta tayar da sallarta a gefen tabarmar.

Ta shara-sharan labulen? Amina na kallon yadda take kai kawo a tsakar gidan har ta kammala tuka tuwon masararta ta kwashe, tana yi tana kiran suyi mata hakuri.

"Yawwa, na san idan nazo na zauna ne, aikin tsayawa zai yi, amma kinga yanzu ai komai ya kammala sai ci kuma."

Ta fada bayan ta dawo dakin rike da kwanukan data zubo musu abincin, ta ajiyewa Amina a gefenta tana zaunawa a inda ta tashi, Amina tayi bacci a jikin Amman lokacin, tayi lamo sai numfashi kawai take fitarwa a hankali yayin da bakuwar tata ta idar da sallarta.

Tana jin yadda hirarsu ta cigaba bsyan sun gyara suna cin abincin wanda tun ba'ayi nisa ba Amma ta gane tsaf akan abinda suke maganar don hira ce da ta riga ta zagaye fadin arewa a wannan lokacin kaf, kasancewar labarin wani abu ne da babu wanda ya taSa jin makamancinsa, wata mata ce da aka kama da laifin hayar wasu mutane da sula je har gida suka kashe ywar mijinta saboda irin takurwar da? matar tayi mata.

Ita kanta taji, kuma ko da ta tambayi mijinta ce mata kawai yayi su bar zancen don baya ko son ambatarsa.

"Ai sai jiya aka koma shari'ar, sai jiya suka sake zama."

Cewar Inna Hajarar tana kai lomar tuwo bakinta kafin ta cigaba.

"Da yake ta kwana biyu a wajen hukumar tana jin matsa shi yasa ba'a je koina ba ta amsa laifinta kuma ta fadi inda ta samo mutanen da ta saka suka yi mata aikin."

Hajiya iya ta dauko salati tun farko har ?arshe ta dire sannan tace.

"Su kuwa wadannan mara sa imanin daga ina suke."

"Wai a Prison tasa aka samo mata su..."

Amsar Inna Hajaran ta fito daidai lokacin da Amma ke shirin shimfide Amina don ta tashi tayi tata sallar itama.

"... Hajiya Ladi ta gaya min haksma suke yi dama, duk mai son Soye aikinsa gidan yari yake zuwa yayi cuku-cukun da za'a bashi wanda zasu yi masa, da sunyi sun koma shikenan babu mai sake ganinsu. A sallami iyayen gudansu suma a siyo musu ?an kayan bu?ata shikenan, aikin ka ya rufo kamar yadda na kwance a kabari yake rufe."

Hajiya iya ta jinjina kanta.

"Ita da tayi rashin sa'a aka kama guda a cikinsu shi yasa komsi ya caSe mata kenan..."

Maganganun Hajiya iyan, suka zama na ?arshe da suka taho tun daga wancan lokacin zuwa a yanzu da take tsaye ri?e da wayarta a hannu.

Kwakwalarta ta sake tariyo wannan ranar a cikin kanta tana sake biya kowacce kalma daga bakin Inna Hajara cikin nutsuwar da take jeranta su da kalaman da Amina ta gaya mata a yanzu cewar abinda su Ma'atuf ke nema da sun daina wahalar da kansu abinda suke nema yana wajen da ba zai taba fitowa ba.

So take yi ta haWa abubuwa guda biyun waje guda sai dai kuma kwakwalarta na ayyano mata tazarar shekarun dake tsakanin zamani biyun da cewar tabbas abubuwa na iya canjawa, amma kuma a lokaci guda sai tunaninta ya cilli kan watarana da yamma lokacin da ta hau adaidaita sahu don zuwa gidan ?aruwarta Tanti, a cikin adaidaita sahun aka Wauki wani mutumi da suka shiga hira shi smda Wan adaidaita sahun kan halin da ?asa ke ciki a yanzu, kuma ba zata manta ba ya rantse fiye da kirgen da zata iya tunawa cewa fiye da rabi na masifar da ake ciki da sa hannun shuwagabanni.

"... Wai kana ina za'a shiga gidan yari a debo masu laifi duk a basu bindiga Wan kare, to rabin masu garkuwa da mutanen nan da kuma wadannan ?an bindigar duk waye ya sansu, wani ya shekara homa a gidan yari za'a dauko shi ya fito yayi wani aikin, da sun ga al'umma sun natsa an fara gano su shikenan sai a maida du inda suka fito, wa ya isa ya gano su a inda ba zasu taba fitowa ba?..."

Kalaman suka kai ?arshe tare da tabbatarwa da kuma yakinin kowanne abu dake cikin kanta, ya?inin da take jin sa har ?asan zuciyarta don haka ba bata sake bata wani lokaci ba hannunta ya sake lalubo nambar Amina a take.

"Idan ya dawo, ki san ta hanyar da zaki gaya masa cewa su nemi mutumin da suke nema har a cikin Prison!"

***

"Ban gane ba, kin ga yarinyar bayan tsawon kwanaki da Sacewarta, har a gaban alkali an baki ita kuma kice min kin dauke ta kin sake mayar da ita hannunsa? To meye hikimar Rukayya?

Na zata shi kike so, shi kike so ya dawo rayuwarki, kuma Allah ya mallaka miki ?ar da ta dalilinta zaki hillace shi ya dawo gareki, amma sai ki Wauke ta ki mika masa ita ke ki koma gefe?

Wane irin tunani ne wannan Rukyy? Wane jahilin ne yace miki..."

"Mahaifiyata ce."

Ksi tsaye Rukayyan ta katse kawarta mai suna Hanan dake wannan zancen ta cikin wayar.

"Kin san ni ba shashasha bace Hanan, tunda kika ga nayi hakan,kin san da dalili,kuma shi ya kamata ki fara tambaya ba ki shiga ?o?arin aibata ni ba."

Ba ganinta take yi ba, amma zata rantse Hanan Win ta taSe baki wani abu da yake al'adarta kafin tace.

"Ni ba aibata ki nake yi ba,amma koma meye shirin naku ina tabbatar miki wannan shirme ne,da kin tambaye ni tun farko da ba haka..."

"Ke na tambaya ai tun farko Hanan..." Ta katse ta muryarta na dagawa.

"Ke na tambaya tun kafin in gama iddar auren Ma'aruf, zuciyata tayi nadama tun a sannan, amma ke kika ce kar in bashi hakuri don in koma Hanan, kuma ke na tambaya kika bani shawarar auren Alhaji Ahmad, kuma ke na tambya lokacin da su Maamah suka hada ni da Jawad, ke kika nuna min cewa in biye masa muyi wannan rayuwar zan manta komai, amma na manta din Hanan? Sannan ke na tambaya kika hada ni da Mary ?ar aikin Hamida... Hanan ki gaya min a cikin tarin wannan shawarwarin naki wanne ne ya juye zuwa alkhairi? Wanne ne ya juye zuwa alkhairin da har yanzu nake mora?"

"Ban gane ba Rukayya, me kike nufi? Me kike nufi dani?"

Muryarta ta fito ne da harzukin dake keto wayar yana dukan kunnen Rukayya.

"Ina nufin ke ba ?awar arziki bace Hanan, na fahimci babu wani abu mai kyau da ya taba faruwa dani a tsawon zama na dake."

Kuma daga haka, bata jira komai ba ta katse wayar, ta rike ta a hannunta tana kallon adadin mintinan da suka Wauka a wayar.

Da dukkan maganganun da ta furta a wayar nan ta kwana a ?irjinta, dasu ta kwana suna yawo a zuciyarta, don a cikin tarin tunanin dake yawo a cikin kanta ta iya nemo wannan kawai ta jera shi daya bayan daya ta fitar da karshensa, kuma abinda bata gama sani ba shine bayan Hanan, mutane nawa ne kuma bata yi sa'ar kasancewa dasu ba a cikin rayuwarta.

Hannunta ya fita daga bangaren kira na wayar tata, ta shiga wajen sakonni, bayan na banki, sunan Jawad ne a kasa, sakon sa na karshe daya tura mata kafin su yi wannan haduwar.

_I madly love you Barbie, me yasa kike hukunta ni? Pick my call please..._

Haka kurum taji a ranta cewa shirunsa a yanzu yana da nasaba da wani abu, Jawad mai naci ne, mai wani irin rufaffen nacin da baya ji kuma baya gani idan har ya dora ransa akan wani abu, ta san wannan ba tun akanta ba, tun akan aikinsa don hakan shine babban abun da yasa cikin ?an shekaru kadan matsayinsa ya kere kowa a wajen, to ta yaya don kawai tayi masa wannan bayanin zai ha?ura komai ya cigaba da tafiya daidai?

Wayarta tayi kara tun kafin tunaninta ya kai karshe, Mahaifiyarta ce Hajiya Nafisa, ta Wauka daga haka tasa a speaker.

"Ki sauko kasa, muna magana ne akan wadda zata je gidan."

Wadda zata je gidan, ba sai Maamahn ta fasa ba, wadda zata je gidan tana nufin gidan Ma'aruf, yarinyar da zata je ta kwance asirin nan, asirin da kamar yadda suka tsara komai a yau ba sai gobe ba aikinsa zai fara, Ma'aruf zai tsani koma wacece yarinyar dake cikin gidan nan a matsayin matarsa, tsanar da a cikin kankanin lokaci zai rabu da ita, don ta riga ta san ko waye Ma'aruf, idan baya son abu baya son sa har cikin ransa kuma babu wanda ya isa a duniyar nan ya canja ra'ayinsa game da hakan hatta Baffa kuwa, shi yasa shi kansa Baffan baya saka baki akan al'amarin wani hukunci da ya yanke.

Sai kawai tayi wani murmushi mai fadi tana hango yadda rayuwa zata maida ita bigiren da ta yarda babu kamarsa duk duniyarta.

Ta yi mu'amala da maza da yawa tun kafin aurenta, amma babu wanda ya kamo kafar Ma'aruf a cikinsu shi yasa ta dage har ta aure shi a sannan, kuma bayan zuciya ta ruWe ta ta fito, har yanzu bata ga wanda ya kama kafarsa a komai ba... Jawad yana ji da kansa wajen iya kulawa da kuna tarairayar mace, amma ta tabbata zai zubar da dukkan makamansa idan da zata hasko masa kwana Waya kawai a rayuwar aurenta da Ma'aruf kafin abubuwa su canja a tsakaninsu.

Wayarta ta sake ?ara, Maamah ce, sai kawai ta sake wani murmushi mai fadi tasa hannunta duka biyu tana gyara dogon gashinta zuwa baya.

Bata san wane irin zama Ma'aruf ke yi da sabuwar matarsa ba, amma koma wane iri ne, yau zata zama rana ta ?arshe da hakan zai zo ?arshe.


***

"Meye wannan?"

Ma'aruf ya faWa a hankali yana laluben gefen fuskar Amina dake tsaye a gabansa, a jikin wardrobe Win dakinta ya same ta, tana kokarin samowa Hamida kayan da zata saka sakamakon bata nan jikinta da tayi da hodar ta fasa gabadaya kuma ta zube a jikinta, duk yadda ta kai ga kwashe kayan kwalliyar nan bai hana Sata kayan nata da take gudu ba.

Dawowarsa kensn daga cikin gida, don can ya fara shiga baysn ya dawo, bata ssn wajen wa yaje ba amma tana tunanin wajen Baffa ne don yau ma yans gida. ?azu bayan gama wayarta da Amma, Ssmirah tazo sun shiga sun gaishe shi, har da Hamida da taki zuwa wajensa ta makale a hannunta, wani sbu da ya taba zuciyarta a lokscin yayi mata dadin da kuma yabawa kanta na cewar yarinyar ta fara sabawa da ita.

Kuma sai da numfashinta ya katse a yanzu daya zura hannun nasa gefen fuskarta, tana jin yadda yatsun nasa suka ratsa kunnenta, sanyin jikinsu na bi ta kan fatar ta.

"?an kunne ne, baka sanshi ba?"

Ta fada tana kallon cikin idanunsa hannunta rike da kayan da ta dauko, ya gyada kansa a hankali yana cije lebbensa kafin yace.

"Na sanshi, kawai bana son shi ne."

"Saboda me?"

"Saboda damuna zai dinga yi."

Sai da ta dan tsaya tana kallonsa kafin tace.

"Ta yaya zai dame ka?"

Bai ce komai ba ya fara kokrin zare shi a hankali, ya karkato da fuskarsa dab da tata yana kallon ta yadda zai cire kuma bata ce komai ba ta tsaya kawai jiran taga abinda zai yi, ya cire na bangaren dama, sannan ya karkato da kansa daya gefen ya cire na hagun shima, ya hada su a hannunsa sannan ya kamo nata daya a hankali, na hagun da bata rike kayan dasu ba, ya bude tafin hannun ya dora mata su a ciki.

"Please in dai saboda ni kike sawa ki daina, bana son su, takura min zasu yi 'Cox bayan kafafunki, I like this curve of your body best."

Numfashinta ya tsaya cak a ?irjinta yaki fita yaki shigactsawon wasu da?i?ai, dama kafafunta burge shi suke? Inalillahi! Ai bata taba tunani ba, ko lokacin da ta saka wannan yaluwar rigar sai da tayi ta ayyana yadda yake kallonsu a ranta amma bai ce komai ba, sai yau Allah ya budi bakinsa ya fada kenan.

Sai kawai ta rufe idanunta ta bude sannan tace.

"Insha Allah."

"Insha Allah me? Baki karasa ba..."

A hankali tana kallonsa tace.

"Me zan karasa?"

"Sunana..."

"Ma'aruf?"

Ya girgiza kansa.

"Wannan na kowa ne, though I like the way kike fadan 'R' din sunan, amma na fi so ki samo min wani daban, da ke kadai zaki dinga fada."

Ta danyi shiru tana cigaba da kallonsa, kwakwalarta na gaya mata cewa sun bar Hamida a can falo amma wani gefen na gaya mata cewa tunda kallo take yi vabu komai.

"Kamar me toh?"

Innocence din cikin muryarta ya fito tar, yayin da idanunta ke cigaba da kallon sa. Sai kawai yayi dariya yana zura hannunsa cikin gashinsa sannan ya girgiza kansa, kuma maimakon ya bata amsa sai kawai ya juyo da ita, tana fuskantar Wakin, ya tsaya daga bayanta sannan ya sunkuyo da fuskarsa cikin wuyanta, bakinsa daidai kunnenta ya rada a hankali yace.

"Call me the first thing you see..."

(Ki kira ni abu na farko da kika gani.)

Ta cije lebbenta tana murmushi, kuma a hankali idonta ya sauka akan robar sukarin da ta Wauko Wazu tayi amfani dashi a wani kayan gyaran fuska da akace mata sai an hada da sukarin.

"Sugar..."

Muryarta ta fito a hankali, sai yayi wani irin murmushi mai sauti a cikin wuyan nata yace.

"Yes! I know I'm that sweet Sunshine."

Sai kawai ta juya tana nata murmushin itama ta kalle shi, kuma a wannan lokacin ne kwakwalarta ta gaya mata cewa shine damarta na gaya masa sakon da take jin nauyinsa a cikin ?irjinta.

"Ina so ne in gaya maka wani abu."

Bakinta ya yanke shawarar fadar abinda ke zuciyarta kai tsaye tun kafin kwakwalarta ta canja tunani.

Sai ya gyada kansa yana kokarin rike ta a cikin hannunsa alamun yana saurarenta, ta haWiye wani abu a ma?ogwaronta a hankali tunaninta na ?ara gaya mata muhimmancin abinda zata fada.

"Ka yarda dani?"

A lokaci guda taga yanayin fuskar sa ya canja, ragowar murmushin na barin kan fuskar tasa, ya zama so serious Win da taji zata iya zagin kanta inda har da ba abu mai muhimmanci zata faWa ba. Ya ?ara gyada kansa sau daya yana kallonta kafin yace.

"With every cell

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login