Showing 102001 words to 105000 words out of 132946 words

Chapter 35 - FARAR WUTA 2 Hausa novel

Unknown   

31 Aug 2025

1129

har karshe sannan ya gyada kansa da sauri.

"Kar ka damu, just carry on yanzu zai ?araso insha Allah."

Ya faWi hakan sannan ya juya gefe, daga can barndar katon ofishin da suke ciki inda Faruk ke tsaye yana faman magana a cikin waya, maganar da bata komai bace illa bayani da kuma kwatance wa wani mai online shop guda Waya da suka samu da suke da Fre-dat Win da Abdurrahim yake nema, wani abu da su basu taSa saninsa ba don haka a yanzu Faruk Win na waya dasu ne don su san yadda? za'ayi a kawo.

A safiyar yau ?an sandan da suke aiki tare dasu suka kira Faruq da cewar basa tunanin akwai wani abu a cikin wannan tarin jakar cd's din da suka samu a gidan Awwalu, suka gaya masa cewar sun yi iya bincikensu amma basu iya ganin komai a cikin kowanne CD ba, don haka ba tare da Sata lokaci ba ya aika a aka dauko masa jakar don shi ya riga ya yarda cewa ba zai taSa yiwuwa ace an tara Cd's fal a cikin jaka guda ba tare da wani amfani ba, don haka suka bar wa yan sandan sauran aikin na nemo mai motar da ya Wauki Awwalun kamar yadda mutumin nan da suka samu a unguwar ya shaida musu cewa ya gane lambar motar.

Faruk yasa an dawo da Cd's Win office ne da tunanin idan komai ya natsa zasu nemo wajen da zasu iya kaiwa a buWe musu ko a wacce kasa ne, sai gashi tun ba'a je ko'ina ba, tun ranar da akayi hakan bata kai ga faduwa ba, tun shi kansa bai kai ga zuwa ma yaji me ake ciki ba, Allah ya kawo Abdurrahim cikin wajen, kuma kamar da wasa Faruk yace hannunsa ya kai kan jakar ya buWe ta yana zaro guda Waya a lokacin da suke hira game da kamfanin da kuma dawowarsa.

Yace kallo Waya kawai yayi wa Cdn ya rubuta masa sunansa da kuma abin da ake yi dashi, sannan ya tambaye shi me suke boyewa a cikinsa... Kuma dogon bayanin da yayi masa shi ya kaisu ga? kokarin da Abdurrahim din ya fara yi da Computersa wajen kokarin bude cikinsa.

Kuma kafin karasowar Ma'aruf, kafin zuwansa wajen yayi nasarar bude guda daya da ya fara dauka har sun ji muryar dake ciki, sai dai sakanni goma sha biyar ne kawai a cikinsa inda shiru ya cike fiye da sakanni goma sha biyu, sai a cikin sakanni ukun karshe ne kawai suka ji wata murya daga can nesa tana magana da wasu kalmomi da ba wanda ya iya fahimta a cikinsu balle ma su tantance sautin.

A yanzu yana kokarin buWe na biyun ne wanda a cikinsa har ya gano cewar anyi amfani da kusan minti talatin na sauti, don haka a yanzu yana kokarin buWe kowannensu ne yadda da ya samu Free-dat Win da suke nema, za'a karasa bude su nan take.

"A Kaduna suke ashe mutanen nan, flight nake dubawa daga Kadunan zuwa nan, sun ce zasu aiko da wani yaron su ya kawo..."

"Ba lallai ne a samu flight da wuri kafin yamma ba, mu duba wani wajen kawai..."

Ma'aruf ya fara fada amma Abdurrahim yayi saurin katse shi ta hanyar riko hannunsa sannan ya rubuta masa a cikin Tab dinsa cewar.

_"Nasu original ne, ba'a ko'ina ake samun abin nan ba, wasu zasu iya faking Winsa."_

Sai kawai Ma'aruf ya zura hannauensa gabaWaya cikin gashin kansa sannan ya gyada kai kafin yace da Faruq.

"Shikenan kayi musu booking Flight din zamu jira..."

Ya fadi hakan wani abu na wucewa ta makogwaronsa da vai san meye ba,kuma a cikin wannan ofgice din suka shafe awanni suna cigaba da aikin tare da Abdurrahim din dake iya bakin kokarinsa wajen ganin yayi decrypting kowanne CD, har sai da ya zama kusan duka aikin tare suka yi shi su uku, wasu awanni da a cikinsu Ma'aruf ya kara fahimtar tarin abubuwa da yawa game da Abdurrahim din wanda ko a baya idan kowannensu yazo gida hutu bai sani ba kasancewar basu cika zama waje guda ba, a kullum shi yana tare da Hajiya Kilishi ne yayin da shi kuma Abdurrahim din ba zuwa nan yake ba.

Kuma a cikin awannin nan Ma'aruf ya kira wayar Baffa da kuma Ishaq wanda a yanzu su uku ne har da Baba Usman a wajen Hajiya Kilishi fiye da ?irgensa, hatta mutanen gida sunyi waya dasu yana shaida musu halin da ake ciki gane da Mamin kasancewar bayan zuwan wani likita an sake shiga da ita wata tiyatar tunda sunce ta farka amma still bata iya bude idanunta.

Sau Waya suka sake magana da Amina, bayan ta aiko musu da abincin da yaga banda tuwonsa har kuma da karin wasu girke-girken guda biyu duk da yace mata jar tayi, sai dai sunyi amfani mutuka don dasu Faruk da Abdurrahim suka cika cikinsu tunda ba inda suka fita, daga sallar la'asar har ta magriba anan cikin office din suka yi jam'insu, bayan haka bata kara kiransa ba, bata ?ara cewa komai ba tayi masa uzuri kamar yadda ta fahimci yana bu?ata wanda shi kaWai ya san daWin hakan da yaji a zuciyarsa.

Kuma bayan Sallar magaribar ne sa?on ya iso, wani matashi dashi aka aiko da Free-dat ya iso har cikin office din bayan Faruk ya tura anje an dauko shi daga airpot din.

Ya iso yana ta godiya da kuma murna kamar ya san su dama, a cikin drawer office fin Fatuk din Ma'aruf ya ?irgo dubu arba'in yace ya sake booking wani jirgin ya koma suma sun gode. Kuma bayan godiya har sai da yayi abinda yasa dukkaninsu yin murmushi kuwa duk da irin zagayen halin da suke ciki.

Bayan fitarsa ne Abdurrahim ya gama installing Free-dat Win nan a cikin labtop dinsa sannan ya shiga saite-saite da kuma taSe-taSe cikin kokarin bude CD na farko da suka saka a ciki.

Karfe takwas da rabi na dare a sannan, kuma a wannan lokacin tabbas ne da za'a auna jinin kowannensu zai yi sama fiye da zatonsu, idanunsu gabadaya yana kan labtop din yayin da koren layin ke tafiya a hankali zuwa inda zai kai karshe kafin sautin ciki ya buWe.

Idan ka Wauko hoton office din daga sama sai ka kalla sosai sannan zaka iya gane inda suke ma, don a hargitse yake gabadaya da tarin takardu da kuma wayoyin abubuwan da aka jojjona a cikin computer Abdurrahim, sannan ga kwanuka da flask din abincin da suka ci kowanne ya kalli hanyar garinsu.

Wannan koren layin na kan lamba ta 75 lokacin da wayar Ma'aruf tayi kara a aljihunsa, ya zaro ta hannunsa na wani abu kamar rawa ya kalli sunan da ya fito... Ishaq ne.

"Hello... Ya akayi?"

Bai ma san hakan ya faWa ba lokacin da ya kara ta a kunnensa.

Ishaq ya shafo nasa gashin daga can cikin asibitin da yake tsaye, idonsa ya kai kan Baffa da kuma Baba Usman dake kokarin shiga office din wani likita da yasa akayi kiransu kafin yace.

"An fito daga aikin Ma'aruf...."

"Alhmdlilah...."

Muryarsa ta faWa da karfin? da yasa daga Faruq har Abdurrahim din juyowa su kalle shi.

Ishaq ya girgiza kansa daga can kafin yace.

"Mami ta rasa idanunta B, bata gani...."

Muryar Ishaq din ta fada a daidai lokaci guda da wannan koren layin ya kai karshe a jikin Computer Abdurrahim, kuma babu wani bata lokaci sautin dake kai ya shiga playing tar a cikin office, cikin murya guda da hatta Abdurrahim da ya debi shekaru baya gida kai tsaye zai shaida cewa Hajiya Kilishi ce, Mami... Mami dai! Mamin Ma'aruf!

_"...A banza na sa aka kashe min Jamal Awwalu? Ko kuwa a banza na rufe idon Ma'aruf daga ganin kowa hatta uwarsa kuwa? Ba duk akan wannan burin nawa bane ko kuwa ka manta kaima Win alfarmar burin nawa kake ci har yanzu... To ta yaya zaka ce min mu dakata tukunna?_

_Ka sanni bana jira Awwalu, bama ni da kwanakin dazan sake wani jiran.... Ishaq ya kira waya yace Ma'aruf ya farka, kuma Baffa ya gaya masa cewa duk yadda zasu yi likitoci su sallame su tsakanin gobe ko jibi su taho don haka bani da lokaci Awwalu, ka nemo duk mutanen nan dole ne kuWin kamfanin Bakori su shigo account dina a goben nan....!_

A daidai wannan lokacin ne daga can waje wani mai adaidaita sahu ya faka a gaban ginin kamfanin, Awwalu ya fito daga ciki idanunsa na kallon dogon ginin wajen da ya haska tar! da fitulu....

A wannan lokacin ne kuma daga can unguwar Nasarawa GRA, Ashraf ya buWe Wakin nahaifiyarsa Hajiya Nafisa, tana tsaye daga jikin mudubin dakin tana feshe jikinta da turare sakamakon shirin da take yi na zuwa wajen mijinta wanda ya dawo ?asar a wannan ranar.

BuWewar kofar tasa ta juyo ta kalle shi a lokaci guda kuma sakewar fuskarta na canjawa da yanayin mamaki sakamakon yadda ta ganshi kusan a birkice.

"Lafiya Ashraf daga ina?"

Ta tambaya, sanin cewar a dazu ya bar gidan bayan yazo yayi wa mahaifin nasa sannu da zuwa.

"Mamaah ina kika ce Ru?ayya ta tafi?"

Wani asibitin kawarta a Abuja, don a duba ta sakamakon ciwon kan da take yawan fama dashi.... Haka tace musu a Wazu bayn da kowa ya hallara a falon mahaifin nasu suna murnar tarbarsa, har Ahmad na cewa dole tayi ciwon kai tunda ta saka damuwa a ranta,mahaifin nasu kuma yace a kirawo ta a gaya mata ya dawo don haka itama ta dawo.

Fuskarta a Waure kaWan tace.

"Ba munyi zancen nan da ku Wazu ba? Me zata yi maka?"

Sai kawai ya Wago wayarsa dake hannunsa ya nuna mata.

"Abokina ne ya turo min hotunan wani hatsari da? ya haWa da kawunsa a Niger dazu... Mamaah har da Rukayya a ciki....!"

Ya fadi hakan a lokaci guda da idonta ya sauka akan hoton Rukayyan dake kwance a gefen titin tare da alamun mutane kwance a gefenta, taba sanye da wata doguwar rigarta da ta sani ta atamfa wadda ta yayyage ta kuma Saci gabaWaya da jini, idanunta a rufe suke yayin da fuskarta take a daddauje wajaje da yawa,yanayinta bashi da maraba da na sauran gawawwakin daje zube a wajen...!

***

_?arshen tika tika.......!_


Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.?????????

*FARAR WUTA 2.*

*?AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*22*

_People pay for what they do and for what they allowed themselves to become, simply by the lives they lead.- Edith Warthon._

~~~~~~

Haske ya ratso cikin Wakin, ta tsakanin labulen dake dagewa a hankali sakamakon iskar dake kada su kasancewar windon a bude yake.

Farko hasken rangwame ne kafin a hankali cikin abinda bai minti biyar ba ya shiga karuwa a hankali, yana yin yawan da ya fara damun fuskokin mutane biyun dake kwance akan doguwar kujerar falon, Amina da kuma Hameeda duka su biyun sun kudundune ne cikin sigar da a kallo daya zaka san cewa bacci ne ya dauke su a wajen ba tare da sun shirya masa ba.

Hasken yasa Amina ?ifta idanunta a hankali kusan sau hudu kafin ta bude su,ganinta na sauka akan Hamidan da kanta yake daf da tata fuskar ta yadda saman gashin kanta kawai take iya gani.

Idanunta suka tsaya a layukan dake tsakanin kalbar kanta tana ?o?arin saita tunaninta kafin ta tuna dukkanin halin da suka shiga a daren jiya.

Ma'aruf bai dawo ba, babu shi babu kuma su Baffa, da misalin karfe goma na daren jiya suka fara buga wayoyinsu ita da mutanen cikin Gida, ta Baffa da kuma Baba Usman basa shiga kwata-kwata, wayar Ishaq da kuma Ma'aruf Win kawai ake samu suna shiga suna katsewa har ?arshe amma babu wanda yake dauka.

Da farko suna kira ne don su ji halin da Hajiya Kilishi ke ciki amma ba'a fi minti goma ba sai ya koma suna kiran ne don su san halin da su Win ma suke ciki.

Hankalinsu ya tashi zuwa nisan da ba zai kwatantu ba, sai daga ?arshe da Munaya tayi tunanin a kira Malam Sani sannan suka? samu shi ya dauka a bugun farko da bai katse ba, kuma kai tsaye ya gaya musu cewa ai sun riga sun baro asibitin tare dasu Baffa, ya gaya musu cewa bai san dai me ya faru ba amma ya fahimci kamar wani ne ya kira su da cewar su taho kamfani don tare har da Ishaq suka taho kamfanin yana bin bayansu a motarsa.

Da magiya Hajiya Maimuna ta roke shi akan ya hau zuwa saman ya bawa Waya daga cikinsu wayar amma bayan yaje Win yace kofar koridon da take kaiwa ga ofishin da suke ciki ma gabaWaya a kulle take don haka ba zai iya shoga ba.

Wani abu da ya kara tsurar dasu kenan, suka yi firgi-firgi dukkaninsu mata kawai a cikin gida don hatta su Hamida dake harkokinsu tare dasu Sahla sai da suka sami waje suka nutsu... Hajiya Maimuna tace tafiya zata yi, tasa Munaya ta kira wani Wan yayarta da suke kira da Abdoul akan yazo ya dauke su su tafi.

Sai dai inda Allah ya taimaka, minti biyar bayan hakan kiran Baffa ya shigo cikin wayar Hajiyan, tana tuna idanun kowannensu a lokacin nan, da kuma sautin karar bugun zuciyarsu da bayan nata da ya cika kunnuwanta tana jin kamar tana jin na Surayya da kuma Samiran dakezaune a kowanne gefenta.

Kuma sai Allah ya taimaka suka ji abinda dukkaninsu suke fata, Baffa ya shaidawa Hajiya Maimuna cewa babu komai ba abinda ya faru gasu nan zuwa, a lokaci guda sai hankalinsu ya kwanta kowa ya shiga hamdala yana godewa ubangiji, amma tun a lokacin haka kurum taji cewa ita bata gamsu da hakan ba, jikinta bai sake ba kamar yadda na su Samira yayi a lokacin.

Tayi niyyar su zauna acan har ?arasowarsu amma sai Inna Danejo tace dare yayi, gwara Ma'aruf yazo ya same ta a gida bayan dukkan gajiyar da yasha, don haka su Munaya suka rako ta tare da Hamidan da tayi bacci a lokacin, kuma sai da suka shigo suka koma sannan ta tuna da wayarta da ta bari a cikin gidan.

Da tunanin dawowar Ma'aruf cikin abinda ba zai fi ?asa da minti talatin ba yasa bata yi niyyar komawa ba, ta canja kayan jikinta zuwa na bacci sannan ta canjawa Hamida ma, tun rana take jin wani abu kamar zazzabi na shirin kamata, ko abinci bata ci mai yawa ba don haka kurum taji bata son kamshin miyar da aka yi a cikin gidan, tana da ragowar abincin da tayi wa su Ma'aruf aka kai musu amma ta saka a fridge ta sani yayi sanyi yanzu.

A yadda take jin kowacce gaSa a jikinta tayi nauyi sai kawai taji gwara ta hakura da abincin don haka ta dawo falo ta kwanta, kuma tun tana kirga minti biyar da goma har ta koma sha biyar da ashirin, har idanunta suka fara rufewa babu alamun dawowar Ma'aruf, kuma a lissafin da take yi na komawa cikin gida ta dauko wayar bacci ya dauke ta, bata farka ba sai karfe biyu na dare da kukan Hamida ya tashe ta, kafafunta na sasarfa ta koma dakin inda ta same ta zaune akan gado tana kiran sunan 'Mammy'.

Sunan da tana ji ta san mahaifiyarta take nema tunda ba haka take gaya mata ba, da kyar ta lallaba ta ta koma baccin, wanda a lokacin ne kuma tashin hankali ya daki tsakiyar kanta da tunanin halin da ake ciki da yasa Ma'aruf bai dawo ba har a sannan.

Ta zura hijabinta sannan tayi hanyar kitchen da niyyar nufar cikin gidan, amma tana buWe ?ofar baya ta kitchen Win, da duhun daren lokacin ya shiga idanunta da kuma shirun dake waje, sai ta kasa fita, ta rufe ta sannan ta dawo zuciyarta na gaya mata cewa dukkan halin da ake ciki zata sani idan garin Allah ya waye.

Sai dai bayan ta dawo ta zauna din, ko da wasa bacci ya kasa daukarta, hankalinta ya kasa kwanciya, ta dinga zama tana canja waje, tayi sallah raka'a biyu kuma ta kasa kara wata daga hakan, tana zaune kawai akan sallayar zuciyarta da yatsunta cike fal da lissafin abinda zai iya faruwa, a haka Hamida ta sake farkawa tana kuka, wannan karon sai da ta Wauke ta suka dawo falo sannan ta sake komawa, kuma minti biyar bata yi ba ta sake tashi da wani kukan.

Wani abu da ya sake tsorata ta kenan don tun sanda tazo gidan ko sau Waya bata taba tashi cikin dare ba, hannayenta na rawa ta samu da kyar ta bata lemo sannan tayi shiru kwance a jikinta, abinda ya hana ta sake tashi kenan saboda tana tsoron idan ta yi motsin da zai tashe ta ba lallai ne ta sake komawa ba, kuma zaman waje Wayan yasa dukkan tarin bugun da zuciyarta ke yi da kuma saka da warwarar dake ranta bacci ya sace ta a cikinsu wanda bata farka ba sai yanzu.

Sai a yanzu da idanunta da kuma zuciyarta suka cika da wani irin nauyi da bata taSa jin sa ba a rayuwarta, ta mi?e da sauri wanda hakan ya farkar da Hamida da kanta ya sauka daga jikinta.

Karfe bakwai da minti uku na safe...

Lokacin da agogo ya nuna a ciki idanunta kenan, ta kalli ko'ina a falon, su kadai ne har yanzu babu Ma'aruf kuma babu alamun wani ya shigo, wani abu ya zarce ta makogwaronta yana ?o?arin zana kalar tashin hankalin da take shirin fuskanta a cikin kirjinta, wajen da ta bar wayarta ta tabbata su Samira zasu gani, idan komai lafiya kamar yadda Baffa yace ya kamata ace su Samira sun kawo mata wayar, ko ma wani ya shigo ya gaya mata dalilin rashin dawowar Ma'aruf din.

Wani tunanin ya daki kwakwalar ta a lokaci guda, me yake shirin faruwa ne? Ko ma me ya faru din? Sai yanzu take ganin me yasa Inna Danejo zata ce a rako su su dawo gida a jiya bayan su Baffan basu iso ba? Idan da gaske ne komai lafiya yake me yasa har yanzu Ma'aruf bai dawo ba? Ko kuma a kawo mata wayarta? Manta ta tayi ma ko kuma me ya faru?

Ba shiri bugun zuciyarta ya karu a lokaci guda, duk wata alama da zata tabbatar mata da cewar ranar yau daban ce ta shiga haskawa a idanunta, hatta yanayin hasken ranar ta ganshi daban da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login