Showing 90001 words to 93000 words out of 115393 words
Rumtse idanu ta yi tare da fa'din,
"Mai ya sa na saka turare ma?".
Nuna mata kusa da shi yai tare da fa'din,
"Seat I wanna talk to you".
Zama tai 'dan nesa da shi ka'dan tare da fa'din,
"I'm all ears".
Kallon ta yai na kusan 30seconds ka na ya ce,
"Mufeeda".
Kallon shi ta yi, gaban ta ya fa'di, domin idanuwan shi sun riga sun fa'da mata abinda zai ce.
Ha'diye miyau ya yi tare da fa'din,
"Mufeeda, I love you, ina son in aure ki, idan har zaki amince".
Kallon shi Mufeeda ta yi with out blinking, zuciyar ta na harbawa kamar ya fa'do 'kasa. Tsoro ya mamaye ta, duk da ta da'de ta na jirar hakan daga gare shi, amma yau da ya furta, sai ta ji tsoro ya mamaye mata zuciyar ta.
"Will you marry me?".
Maganar shi ta 'kara dukan dodon kunnan ta.
Kau da idanun ta tayi daga gare sa, haka nan kuma taji ta na son ta yi kuka. Cikin second biyu zafafan hawaye suka fara gudu a idanun ta.
Tashi Naseer yai ya tsugunna a gaban ta ya na kallon cikin idanun ta, tare da fa'din,
"Bazan takura miki ba, amma zan ba ki lokaci ki yi tunani da zuciyar ki. Amma dan girman Allah ka da ki ce min a'ah".
Tsam ta mi'ke da sauri ta soma tafiya. Naseer bai tsayar da ita ba, sai dai ya mi'ke ya tare da saak hannun shi cikin aljihu ya na kallon ta har ta fice daga garden 'din.
Fafiya ta ke yi ta na har'de 'kafafu, ta rasa farin ciki ta ke yi ko menene. Cak ta tsaye tare da jingina da 'kofar da zata sadaka da cikin garden 'din hannun ta dafe da saitin zuciyar ta. Babu abunda ya fa'do mata a rai sau Naseer tsohon mijin ta da kuma irin soyayyar da su kai, amma a karshe ya wula'kan ta ta. Ji ta yi wani irin tsanar shi na tasowa tun daga can cikin zuciyar ta, wani zuciyar ta ce mata,
"Mufeeda ba ki da hankali ne? Shi wannan 'din ki na da tabbacin ba zai iya wula'kanta ki ba ne. Ka da KI man ta shi ma Naseer daga tausayin ki ya soma, ki rufama kan ki asiri ki zauna a matsayin ki".
Ji ta yi an fizgi hannun ta sai da ta fa'da jikin wanda ya fizgo ta.
Zaro idanuwa tai ta na kallon shi a matu'kar tsora ce.
'Dage mata gira ya yi tare da fa'din,
"Ya mu kai da ke? Yauwa sati 'daya da na ce miki ina son muyi magana, ki ka ce min ummin ki na jiran ki za muyi magana anjima, shine har yanzu anjimar ba ta yi na?". Lukman ya fa'di hakan ya na kallon cikin idanun ta.
Jikin ta rawa ya ke yi, sai kalle² ta ke yi, still shi kuma bai sake ta ba, domin har numfashin juna su na ji.
"Maganar da zan fa'da ba mai tsawo ba ce, just 3 words. I love you". I rarrabe Lukman ya fa'di I love you 'din. Dai² lokacin Naseer ya fito daga garden 'din.
Wani wawan burgi yaja tare da fa'din
"What is this? What is happening here? I you kissing each other?". Naseer ya fa'da out of anger.
Wani irin zabura Mufeeda ta yi tare da zubawa da guru side 'din haj Zulfah.
Wani kallo Naseer ke bin Lukman da shi cike da tsantsar kishi, bakin shi har rawa ya ke yi wajan fa'din,
"Are flirting with her?".
"Stop thinking negative, it's not what you're thinking. I'm just telling her that I'm in love with her". Fa'din Lukman tare da 'ko'karin dafa kafa'dar Naseer 'din,
Wani irin kaucewa Naseer 'din ya yi tare da fad'in,
"You're in what?". Ya fa'di hakan ne ya na karka'de kunnuwan shi.
"I said I'm in love with her, do you have problem with that?".
Wani kallon banza ya watsa ma Lukman 'din tare da nuna mass hannu ya na fa'din,
"Don't you ever dream of that, Mufeeda is mine. I mean mine alone. I'm the one who brought her here, and I'm warning you to stay away from her if you don't want to be hurt".
"Really? Let see what will happen". Lukman ya fa'da tare da jifan shi da kallon banza ka na ya wuce.
*SORRY FOR THE LATE UPDATE*
😍😍😍😍😍😍😍
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 43_*
A matu'kar fusace Naseer ya nufi side 'din haj Zulfah. Baby da ke gyefe la'be ta kuma gama jin duk bada'kalar da ya faru tsakanin Naseer da Lukman ta nufi side 'din haj Jummai da gudu har ta na zame wa bakin ta na buguwa da 'kofa. Ko takan fashewar da ba'kin ta yai ba ta bi ba ta shiga 'dakin da sauri ta na waige².
Matar yaya Abubakar da ke zaune a parlour ta na taimaka wa 'yara su na homework ta 'dago ta bi ta da idanuwa har ta haye step 'din. Girgiza kai matar yaya Abubakar ta yi tare da fa'din,
"Guntsi fesa, uwar gulma. Ji yadda bakin ta ke fidda jini, amma tsabar gulma ya hana ta jin zafin bakin. Kai Allah ka tsare min da gulma irin na baby.
Mur'da 'kofar ta yi ta tura ta shiga da sauri ta na fa'din,
"Mummy yau kin shiga uku wallahi, kamata yai ki zauna ki 'daura hannu akai ki ta rusa ihuuu saboda wannan bala'i da ya kunno miki".
Mummy da ke kishingi'de tai saurin mi'kewa zaune hankali tashe ta na fa'din,
"Ke baby ban san hauka, ki min baya ni mai ya faru".
Baby zama tai a bakin gadon ta zabga uban tagumi da hannu bibbiyu ta re da fa'din,
"Mun shiga uku! Wallahi ba 'karamin tashin hankali ba ne. Har 'ya'yan biyu. Wannan masifa da mai tai kama?".
"Ke dan uban ki zaki min baya ni ko Sai na ci uban ki". Fa'din haj Jummai hankali ta shi.
"Hmmmmm! Uhmmmm, hmm. To wallahi Mummy a gaskiya KI tashi tsaye. Domin wancan 'yarinyar mai 'ya'yan shegu har biyar za ta kai 'ya'yan ki ga halaka. Domin yanzu haka dai ba 'karamin zage² da tashin hankali Ya Naseer da Ya Lukman su kai ba akan ta yanzun nan, domin kuwa dukkan su sunce mata suna son ta. Wannan shi ya kawo hatsaniya da zage² ta uwa da ta uba tsakanin ya Lukman da ya Naseer. Ke mummy har kusan doke² su kai fa. Domin ya Naseer wani zabura yai ya ne mi cakumo wuyar rigar yaa Lukman, shi kuma ya Lukman yai wani irin kaucewa tare da 'ko'karin sha'ko wuyar shi tare da kai masa naushi". Baby ta fa'di hakan tare da kallon in da mummyn ta ke, Sai dai ta ga wayam. Saurin mi'kewa tai ta bi bayan haj Jummai da tun sadda baby ke cewa Naseer ya kai hannu zai cafko wuyar rigar Lukman ta fice daga 'dakin da wani irin sauri.
"Ahhh dole in bawa idanuwa abinci, bari na bita". Baby ta fa'di hakan tare da bin haj Jummai da har ta kai 'karshan staircase 'din.
Kai tsaye 'dakin Naseer ta nufa kamar a kumbure, kamar ka tsira mata allura ta fashe.
Ko da ta tura 'kofar, babu kowa a parlour. Baby tai saurin cewa,
"Mummy ai ya Naseer 'din ya na 'dakin wancan matar (haj Zulfah)".
Fuuu haj Jummai ta kwashi 'kafa tare da nufar side 'din haj Zulfah.
Ita ka 'dai ya sa mu a 'dakin jikin ta Sai rawa ya ke yi. Hankalin ta a tashe ta na tunanin abunda ya faru yanzu.
"Mai Lukman ya ce miki? Mai ku ke aikatawa?".
Maganar Naseer ya katse Mufeeda cikin tunanin da ta tafi.
Saurin kallon shi ta yi tare da fa'din,
"Wallahi ba abunda ka ke tunani ba ne, babu wani abunda na ke yi mara kyau. Na fito daga garden ke nan naji ya ri'ke ni".
"Ba kuma ki da bakin da zaki iya ce masa ya sa ke ki ko?". Naseer ya jefe ta da tambaya.
Tuni idanuwan ta sun cicciko da hawaye suna shirin zubowa.
"Wallahi ka da kika sake wannan hawayan su zubo. Idan kuma ki ka bari su ka zubo zan baki mamaki".
Saurin mai da hawayan ta yi ta na kallon 'kasa.
"Ki saurare ni da kyau, wallahi ko da wasa ka da in sake in 'kara ganin ki da Lukman, idan ki ka bari na sake ganin ki da shi zan ba ki mamaki. Ke tawa ce ni ka 'dai, ko kin 'ki, ko kin so".
"Sannu uban ta". Fa'din Lukman da ya bugo 'kofar ya shigo yana wa Naseer kallon uku saura kwata.
"Ni ba uban ta ba ne, amma kuma ni future husband 'din ta ne nan ba da da'dewa ba. Mufeeda tawa ce". Fa'din Naseer ya na huci.
Mufeeda kuwa ta na tsaye jikin ta Sai rawa ya ke yi. Harga Allah ba ta son wannan cacar bakin da wa da 'kani su ke yi akan ta.
"Haba? Ta yaya ta zama takan?". Fa'din Lukman.
"Ka na so kasan hakan?". Fa'din Naseer. Ba tare da ya jira abunda Lukman zai ce ba, ya isa in da Mufeeda ta ke tare da jawo ta Sai da ta fa'da jikin sa, kana ya sa'kalo wuyan ta tare da ha'de bakin su ya shiga kissing 'din ta passionately. Dai dai lokacin haj Jummai ta turo 'kofar ta shigo baby na biye da ita a baya.
Wani irin zaro idanuwa baby da haj Jummai su ka yi tare da fa'din,
"What??".
~*KADUNA*~
Sosai mal Ahmadu ke kuka tare da ri'ke hannun daddy ya na fa'din,
"Nagode, Nagode, nagode alhaji, Allah ya 'kara girma. In sha Allah ni kuma zan cika maka al'kawarin ka, yanzu haka ma can gidan zan nufa, kuma a yau zan fara aikin tono wannan envelope 'din".
Dafa shi daddy yai tare da fa'din,
"A'ah, ko mai a hankali za muyi shi, yanzu tare da ni mu tafi can gida na, Sai bayan kwana biyu ka 'dan murmure sai kaje gidan ka fuskanci 'kanin ka, ka ga reaction 'din sa akan dawowar ka kwatsam".
"Shikenan alhaji, duk yadda ka ce haka za'ayi".
Shagon aski daddy ya fara kai mal Ahmadu aka aske masa gashin kan shi da yai buzu² tare da canza masa kamanni. Daga wajan aski, sukai supermarket ya saya masa kaya kana suka wuce gida.
Hannu bibbiyu Mommah ta kar'be shi, kasancewar daddy ya mata bayanin zai kawo ba'ko. Abinci aka ba shi mai rai da lafiya ka na yai sallar azahar. Daddy ya ce mata ya kwanta ya wuce gajiya zuwa nan da la'asar.
Washa gari, mal Ahmadu kasa ha'kurin zama yai ya cewa daddy yau zai je can gidan shi domin yaji in da 'Yar shi ta ke. Kasancewar daddy bai fa'dawa mal Ahmadu ko mai akan Mufeeda ba.
Daddy bai tsayar da shi ba, kasancewar a SMC su daddy su ke da zama, shi kuma can Fulani road a badarawa. A 'kafa ya taka, mutane da dama basu gane shi ba. Wasu kuma sai kallo tsoro da mamaki suke bin shi da shi. Shi kuwa mal Ahmadu duk Wanda ya ga ni a hanya zai tsaya ya ba shi hannu su gaisa sai yai gaba har ya isa gidan shi.
Abubuwan da ya faru a baya gaba 'daya ya dawo masa. Hawaye ke zubowa daga idanuwan sa, bayan hannun sa ya saka ya share hawaye ya na wani murmushi mai cin rai.
'Daga 'kafar da zai yi suka ha'da idanu da KALLAH dai² ya fito daga cikin gida Marwanatu a bayan shi ta na masa 'korafin yunwa ta ke ji. Duk ta koma kamar wata mahaukaciya.
Wani irin zaro idanuwa KALLAH yai tare da nuna mal Ahmadu da hannu bakin shi na wani kakkarwa
*MANAGE PLEASE*
الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 44_*
Wani murmushi mai cin rai mal Ahmadu ya saki tare da 'kallon 'dan uwan shi KALLAH daga tsakiyar kai har yatsun kafafun shi. Sai ya ga ma yafi shi kyawun ga ni shi da ya fito daga prison.
"Ni ne nan 'dan uwan ka Ahmadu. Ba abun mamaki ba ne da Ka ganin an an baban ka a kuma raye. Allah bai nufi abunda ka so ba, domin a wannan ranar da kamin sharrin ni 'dan kidnapper ne har aka yanke min hukuncin rataya. To Allah bai nufi hakan ba, duk wa 'yan da aka yanke mana hukunci tare da su, an rataye su, ni kuma da yake Allah ya san ba ni da laifi ban aikata abunda ake tuhuma ta da shi ba, sai Allah ya ku'butar da NI ba su rataye ni ba. Yanzu Kallamu idan Ka kashe ni, mai hakan zai 'kare ka dashi? Saboda abun duniya da anan zamu bar shi, ka za'bi salwantar da rayuwa ta wajan bada shaidan 'karya akan ni ina shigo da Ghana must go 'din ku'di da makamai. Haba KALLAH, menene ban yi maka shi da zaka saka min da wannan abu? Ka nisanta ni da 'ya ta na kusan tsawon shekaru goma sha d'aya. Mai na maka?".
KALLAH da ke ta fama zufa, jikin shi gaba 'daya ya ji'ke da zuwa, sa hawayen munafurci ya ke yi, ya ce,
"Dan uwa na kar.........".
"Kul! Kar ka kuma kira na 'dan uwan ka, ni ba 'dan uwan ka ba ne. Azzalumi macuci, maha'inci wanda bai tsoran Allah". Mal Ahmadu ya katse shi tare da fa'din haka a tsawace.
Tuni mutane sun yi cincirundo su na kallon abunda ke faruwa tare da furta albarkacin bakin su wajan tsinewa KALLAH.
A nan wajan fa'din halayan KALLAH, wani ya ke shaidawa mal Ahmadu irin u'kuba da azabar da KALLAH yai wa Mufeeda shi da matar shi *MAI ZOGALE* da a yanzu ta ke halin rashin lafiyar shanyewar 'barin jiki.
Tuni malam Ahmadu ya zube a wajan sumamme. Mutane su kai kan shi tare da shigar da shi cikin gidan shi su ka yayyafa masa ruwa ya farfa'do.
Marwanatu da tuni ta shige 'dakin mahaifiyar ta ta shaida mata mahaifin Mufeeda ta dawo ta kuma 'kara mata da maganganun da mal Ahmadu yai wa baban na ta.
*MAI ZOGALE* da ke kwance sai uban zarnin fitsari da warin kashi ta ke, ta soma matsar kwallah, ta na so tai magana amma babu bakin maganan. Bakin nan ya karkace waje 'daya sai dalalar da miyau ta ke yi.
Marwanatu ta galla mata harara tare da fa'din,
"Ni fa matsala ta da ke shegen 'kazantar ki, ji yadda kike wani dalalo da miyau kamar wata 'karamar yarinya. Sai uban warin kashi ki ke yi da zarnin fitsari. Ni wallahi bazan iya da matsalar ki ba. Zuwa zan yi in bi 'kawa kursum can TAFA in ci duniya ta da tsinke".
A can tsakar gida kuma mal Ahmadu ya sa mu ya farfa'do, amma sai kuka ya ke yi wiwi ya na fa'din
"Ina 'ya ta? Ina Mufeeda ta ta ke. Dan Allah ku naimo min 'ya ta".
"Kwantar da hankalin ka, ina sha Allah duk in da Mufeeda ta ke, za mu ta ya ka nai man da dukiyar mu da 'karfin mu in sha Allah". Fa'din wani bawan Allah da ke ri'ke