Showing 3001 words to 6000 words out of 115393 words

Chapter 2 - NI DA SHI ABU 'DAYA NE HAUSA NOVEL

11 Aug 2024

22940

a wajan wasu na zagin kallamu sabida kwata kwata bai ri'ke zumunci ba, bai ri'ke 'yar 'Dan uwan shi a mana ba. Wa'danda ko suka San tantagaryar halin sa, sai dai su yi wa Mufeeda addu'a tare da tausaya Mata a zuciyar su suyi gaba. Dan Kallamu ko 'dan sanda bai Kai shi makirci da sharri ba. Shiyasa kwata kwata ba Mai shiga sabgarshi a unguwan.
Ba ruwan shi da 'dirkeken cikin dake gaban Mufeeda. Haka ya dauki sanda ya bi ta ya na kwa'da Mata tana tafiya da kyar jini na bin ta, ta na kuma masa magiyar ya rufa Mata asiri ya bar ta ta zauna a gidan sa. Sai da suka fita daga layin har bakin babban titi sannan ya Mata kashe di akan ka da ta Saki ko kyeyar ta ya 'kara gani a gidan sa sannan ya juya.


Rana ta fito irin Mai shegen zafin nan. Gashi dama rabon ta da abinci tun daran jiya, ga uban jinin da take zubarwa, wani jiri ne ya kwashe ta yuuuu ta fa'di timm bisa cikin ta, dai dai lokacin wata dalleliyar mota Fara Sol ta ja wani dogon birkii ki ka ke kiiiii daf fa ita.






More comment
More typing.



*MAMAN UMMU CE✍️*
[7/17, 3:09 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*


🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* (Maman Ummee)


ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ ).


*PAGE 4*


Da saurin ya fito dan ko iya rufe motar bai yi ba ya na fa'din
"subhanallah! Baiwar Allah lafiya???
Dishi-dishi take ganin shi, can kuma komai ya 'dauke mata difff kunnuwan ta suka do'de, jikin ta ya sake gaba daya.
A matu'kar ru'de ya cicci'be ta tare da bude motar ya aje ta a back seat, kasancewar fararan shadda ne a jikin sa, sai ya ri'ne da jinin dake zuba a jikin ta, amma shi hankalin shi a tashe, KO lura da hakan ma bai yi ba. Da wani mugun speed ya ke tafiya har ya 'karaso MANAAL SPECIALIST HOSPITAL.
Cicci'bota ya yi ya na kwala kiran "NURSE! NURSE!! NURSE!!! Where the hell are you???
Da gudu wata nurse ta 'karaso wasu biyu na bin ta a baya da gadon gungura marasa lafiya. Kwantar da ita suka yi suka gungura ta zuwa wani da'ki, kasancewar shi sananne a wajan shiyasa basu bukaci katin awo ba, amma da badun haka ba ma bazasu kar'be ta ba.
Kasancewar ya San babu yadda za'ayi su barshi ya shiga, sai bai yi yun'kurin shigan ba, Amman sai Kai wa da komowa ya me yi.
Doctors har uku ne akan ta, ka na kallon fuskokin su za ka ga tsantsan 'bacin rai a fuskokin su. Daya daga ciki ne ya fito, Kai tsaye ya nufi in da bawan Allah nan ya ke, kamin ma ya 'karasa wajan shi har shi ya iso inda ya ke.
"Ka biyo no office". Abun da ya ce masa ke nan yai hanyar office 'din shi da sauri.
A ki'dime ya bi sa, tare ma suka saka 'kafa a office 'din. Zama doctor ya yi sannan ya nuna masa wajan zama shi ma ya zauna.
Doctor ya kalle shi ranshi a matu'kar 'bace ya ce,
"Haba architect! Da ilimin ka zaku bari har sai yarinya ta jiga ta haka sannan Ku kawo ta asibiti? Kasan irin jinin da ta zubar kuwa?.
Gaban shi ya buga daamm bai sai lokacin da bakin shi ya su'buce wajan fa'din,
"I'm sorry doc ba laifi na ba ne, ita din 'yar gudun hijira ce."
Doc yai saurin mi'kewa tare da fa'din,
"Subhanallah! Gaskiya to ta na bukatar taimakon gaggawa domain CS za ai mata, kuma ta na bu'katat jini leda uku, sannan muna bu'katar sa hannun ka a nan."
Warce takardan ya yi ba tare da wani tunani ba yai signing sannan ya ce,
"Ba matsala doc a dibi jini na, ai jini na O ne,".
"To shikenan muje LAB sai a 'diba'.
A tare suka fit a, cikin 'kan'kanin lokaci aka 'dibi jinin sa. Ita kuwa Mufeeda har an sauya Mata kaya zuwa na tiyata an gungura ta zuwa 'dakin tiyata.
Da yake kwararrun likitoci ne a kan ta, cikin abinda bai fi awa guda ba aka gama tiyatar.
Doctor Haroon ne ya fito jikin shi sharkaf da zufa, amma fuskan shi kamar gonar auduga ya 'karaso kusa da architect ya mi'ka masa hannu.
Shiko Architect da sauri ya kama hannun doc ya ce,
" doc ya ya ta ke, kun ciro 'dan KO 'yar?"
Murmushi doc ya yi tare da fa'din,
"Architect Naseer tunda muke kar'bar haihuwa KO tiyata a asibitin nan, ba'a ta'ba haihuwa irin na baiwar Allah nan ba, wannan matar 'ya'ya biyar muka Ciro a cikin ta, biyu maza uku mata ".
Wani irin zaro idanu Architect ya yi tare da fa'din
"Kai Dan Allah doctor? Inaa take ita? Ta na cikin 'koshin lafiya??"
Doc ya dafa shi tare da fa'din,
"Ka kwantar da hankalin ka Architect, alhamdulillah ta fita daga hatsari, yanzu haka ma ta na 'dakin hutu an saka mata jini, babies 'din kuma ana gyarasu ne, yanzu ma nazo na fa'da maka ana bu'katar kaya ne."
Architect Naseer ya ce,
"Alhamdulillah, Bari ka ga nai sauri na sayo kayan". Bai jira abunda doctor zai ce ba yai hanyar waje da sauri, kwata kwata shi bai ma kalli rigar jikin shi ba, balle ya ga jinin da ya bushe a jiki.
mota ya bu'de ya shiga ya tada tare da yin reverse ya fice daga asibitin. Bai tsaya KO Ina ba sai a wani 'katoton supermarket. Fitowa ya yi yai ciki, bai damu da kallon da mutane ke bin sa da shi ba domin ba ta su ya ke ba.
Kai tsaye wajan wataa ma'aikaciya ya nufa tare da Mata magana akan ta taimaka masa wajan za'ban kayan babies quintuplet biyu maza uku Mata.
Aikuwa matar nan ta dage ta za'bar masa kaya masu uban kyau da tsada. Wajan biya ATM 'din shi ya mika suka zari kudin su, wasu daga cikin ma'aikatan suka taya shi da kai kaya mota.
Kaya ne masu uban yawa, domin sun cika both, haka ma back seat hatta front seat ma sai da aka zuba wasu. Juya steering motar ya yi zuwa asibitin. Su kan su nurses 'din ba 'karamin mamakin uban kayan da architect ya siyo su Kai ba, bayan kuma sun San cewa ba shi da wata ala'ka da ita.
Tuni har sun gyara yaran sun saka ma matan uku pink din kaya, mazan kuma blue. Ba 'karamin kyau 'ya'yan nan su Kai ba. Labari tuni ya baza cikin asibitin cewa wata 'yar gudun hijira ta haifi 'ya'ya biyar uku mata biyu maza.
Architect Naseer kuwa farin ciki ya cika zuciyar sa, ji ya ke kamar shi aka wa wannan haihuwar, ji ya ke Ina ma 'ya'yan sa ne na cikin sa. Kiran sallar la'asar ne ya ya dawo da shi daga tunanin shi, sai a lokacin ya kalli kayan dake jikin shi, gaba daya ya lalace DA jini har ya bushe.
Da sauri sauri ya juya ya shiga office din doctor Haroon, minti takwas ya fito yai hanyar motar shi ya fice daga asibitin zuwa masaukin da ya sauka domin yai wanka ya sauya kaya ya rama sallar azahar da la'asar 'din da ya wuce shi.
6:35PM
A matu'kar firgice ta farka ta na fizge fizge ta re da fa'din,
"Na tsaneka Naseer, bazan yafe maka ba, sai ka yi nadama mafi muni a rayuwar ka. Wayyoo Allah na! Wayyooo ciki na, Baba ka da ka Kore ni dan Allah, wallahi babu in da na ke dashi da ya wuce nan".
Da gudu nurses suka yo wajan gadon suna danne ta, amma still ba ta dai na sambatu ba. Doctor Haroon ne ya shigo, dai dai da lokacin da Architect yai parking 'din motar sa. Doctor ya shiga duba ta, a hankali kuma sai ta dai na fizge fizgen amma ba ta dai na sambatu ba.
Architect Naseer ne ya shigo 'dakin hannun shi ni'ki ni'ki da ka ya, da wani 'katotan flask, dai dai lokacin kuma Mufeeda na fa'din,
"Wallahi cikin na ka ne 'yalla'bai, jinin ka ne. Naseer ka da ka Kore ni, ka da kamin haka."
Waro idanu Naseer ya yi, musamman yadda ya ga doctor Haroon na mashi wani irin kallo. Tabbas idan ba kunnuwan shi ba ne suka jiyo masa ba dai dai ba, ji ya yi wannan matar da ya taimaka ta Kira sunan shi. To a ina ta San shi? Shi dai ko mai Kama da ita bai ta'ba gani ba idan ba yau da Allah ga kawo shi ta layin ya gan ta yashe a kan titi ga jini na bin jikin kuma ita ka'dai wajan. Wannan shine dalilin da ya sa ya taimake ta.
'Karaso wa ya yi ya aje kayan da ke hannun shi, Nurses 'din nan suka gaishe shi, ya amsa musu tare da mi'kawa doctor Haroon hannu. Amsa ya yi but still ya na bin shi da kallon zargi.
Dan tsaki Architect ya yi tare da kauda Kai, kasa-kasa ya furta, "Wannan shegen kallon zargin da kake min fa ya fara isa ta, idan ka na da magana kawai ka yi".
Harara doc ya watsa masa tare da mishi kallon zamu ha'du sai ka warware min komai.
Jan kujera yai ya zauna ya na 'karewa jariran kallo da suka yi matukar kyau a cikin shigan da aka musu na kayan sanyi.
Doctor Haroon ya kalli Architect ta re da fa'din
"ka sa me ni a office". Bai jira yi mai zai ce ba, ya saka Kai ya fice. Nurses 'din ma tuni sun rufa masa baya. Dan tuni Mufeeda ta koma bacci don alluran bai gama sakin ta gaba daya ba. Sam jinin ta bai da 'karfi.




*More comment*
*More typing*


*MAMAN UMMEE CE*✍🏼
[7/17, 3:09 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*


®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


*_Z• W• F•🏝_*

🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.

laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story & Written by*
*Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* (Maman Ummee)


ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )


*PAGE 5*


Murmushi architect ya yi tare da mi'kewa ya bi bayan doc. Kwankwasa kofar ya yi sannan ya tura. Zaune ya samu doc ya na duba wasu files, sannan ya na kuma tattara wasu takaddu, alamu ya nuna ya tashi a aiki yana shirin komawa gida.
Jawo kujera ya yi ya zauna still murmushi kwance a fuskan shi. Gyaran murya ya yi tare fa fa'din
'Hey Mr man, ka Kira ni, kuma gashi nazo. Fa'di cutar ka''
Harara doctor Haroon ya watsa masa Tara DA fa'din,
"Wallahi sai kamin baya ni wacece wancan yarinya. Domin alamu ya nuna ka Santa. Allah dai ya sa wa'dancan 'ya'yan ba na ka ba ne'
"Aikuwa DA nafi kowa farin ciki wallahi, yadda Allah ya saka min 'kauna 'ya'ya ace wa'dancan kyawawan 'ya'yan nawa ne, hmmm Allah ka 'dai ya San irin sadakar DA Zan yi yau 'din nan." Naseer ya fa'di hakan.
Harara doc ya 'kara watsa masa tare DA fa'din,
"Look I'm serious Naseer, ka yi min ba ya ni, nasan ka, nasan halin ka, nasan Kai ba mazinaci ba ne, amma mai yasa take dangantaka da 'ya'yan ta? bayan kuma ka ce min ita 'din yar gudun hijira ce".
"Aboki na gaskiya akwai abunda na 'boye maka, magana ta gaskiya wannan yarinya ban San ta ba, ban San daga Ina ta fito ba, ni yau ma na me shirin komawa kano wallahi. Na fito daga company DA muke aiki ne ma Zan tafi masauki na, shine na gan ta kwance a akan titi a wannan halin DA nazo da ita. Su nana kuma DA take Kira ta na ala'kantawa DA cikin jikin ta, zai iya zamowa KO mijin ta shi sunan shi Naseer. KO ma dai menene idan ta farfa'do maji."
Sai a sannan doc Haroon ya Saki wani gwauron numfashi tare DA fa'din,
"Alhamdulillah. DA na zaci ko abokin nawa ya canza halin da na San shi da shi me."
Dariya duk suka fashe dashi tare da tafawa.
Mufeeda ba ta gama farfa'dowa daga alluran da aka Mata ba sai 'karfe takwas da minti goma. A hankali take bu'de idanun ta, duk a tsammanin ta zata farka ta Gan ta a cikin kabari, amma sai ta Gan ta a cikin wani daki, ga kuma 'kasan cikin ta dake mata wani azababban zugi.
Shiko Naseer bai lura ta ma farka ba, ya na nan kusa da quintuplet ya na masu wasa, jin 'ya'yan ya ke yi hat cikin 'bargon shi.
It's kuwa Mufeeda a hankali komai ya soma dawo mata, wani irin kuka ta kece dashi mail ta'ba zuciya.
A matu'kar firgice ya 'dago ya na kallon ta, da sauri ya 'karasa wajan ta ya na tambayar ta ko lafiya.
KO 'dagowa ba ta yi ba balle ta kalle shi ba. Fita ya yi da sauri ya kira doctor Mansur, domin doc Haroon ya da'de DA tafiya gida. Tare suka shigo shi da doctor. Doctor ya 'karasa wajan ta tare da fa'din,
"Sannu ko malama. Ya jikin naki? Mai ke damun ki yanzu?"
A hankali ta 'dago ta kalle shi fuska sharkaf da hawaye ta ce,
"Nan ke min ciwo" cikin ta ta nuna dai dai inda aka yanka.
Jinji na Kai doc ya yi, tare da yin rubutu a file din ta, sannan ya kalli architect tare da fa'din,
"Wannan ba wani damuwa ba ne, a hankali zai Bari in sha Allah."
Jinjina Kai ta yi. Fita doctor ya yi. Naseer kuwa gadon jariran ya yi ya 'dauko Namijin tare da nuna Mata fuskan shi cike da annuri. Kamar bazata kalla ba, said kuma ta juyo ta kalli babyn. Gaban ta ne ya bada daaam domin jaririn babu in da ya baro mahaifinshi, hatta wani 'Dan 'digon ba'ki a kumatun Naseer wannan 'da sai da ya 'dauko. A cikin zuciyar ta ta ce, Allah ya raya min Kai a tafarkin sunnan manzo SAW.
Mai da na hannun shi ya yi ya kwantar tare da 'dauko 'dayan ya 'Kara nuna Mata. Wannan Karon mamaki ne ya bayyana a idanun ta. Gya'da Mata Kai Naseer ya yi alamar kwarai shi ma 'Dan ki ne. Shima sak kamar na farkon harda 'digon bakin kumatun.
Wannan karan da Naseer ya aje 'dayan matan biyu ya 'dauko ya 'karaso wajan ta. Wani irin waro idanun ta ta yi ta na kallon 'ya'yan kamar a mafarki tare da girgiza kan ta, don't gani take kamar hakan bazai yu ba, Allah da ta tuna da ikon Allah said taji wasu zafafan hawaye na zubowa daga idanun ta.
Still Naseer ya kuma aje biyun ya 'dauko autar kasancewar duk an musu shaida. Wannan Karon da karfi ta fashe da kuka har da shasshe'kar kuka. Bai San dalilin kukan ta ba, amma haka man yaji zuciyar shi ta karye.
Mai da 'ya'yan ya yi duka akan gadon su, sannan ya jawo kujera ya zauna kusa da gadon ta, a sanyaye ya kalle ta ya ce,
"Baiwar Allah, ban sanki ba, ban kuma San daga Ina kike ba, sannan kuma ban San maye matsalar ki ba. Amma na San tabbas ki na cikin wani hali. Idan babu damuwa ki fa'damin matsalar ki ko Zan iya magance mini shi"
"Waye Kai?" Mai makon ta bashi amsa sai ta jeho masa tambaya.
"Ni ne wanda ya kawo ki asibitin nan". Ya ba ta amsa.
"Nagode da taimakon da Kai min, ha'ki'ka da ba dun Allah ya turo ka kai kuma ka taimake no ka kawo ni nan ba, da wani labarin ake yi yanzu. Nagode Allah ya saka maka da alkhairi"
"Babu komai ai wannan yi wa Kai ne. Ki fa'da min address 'din gidan Ku, sai inje in sanar dasu halin da ake ciki, domin nasan duk in da suke yanzu suna cikin tashin hankali".
Wannan tambaya da ya Mata sai ya 'Kara tado mata da miki. Ba ta bashi amsa ba sai kukan da take yi .

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login