Showing 111001 words to 114000 words out of 115393 words
ke wajan su, Naseer ya bar musu ita har su aurar da ita, hakan kuma ba 'karamin da'di ya masu ba.
...........Biki saura kwana uku aka kawo lefe nagani na fa'da. Kowa sai sanbarka yake yi. Kasancewar Naseer kano ya ce Dinner kawai za'ayi shi said an kai amaraya acan kano za'ayi, sai Mommah ta ha'da mother's day anan gidan su na SMC kasancewar 'katotan gida ne. Ana gobe 'saurin aure akai mother's day 'dinnan. Ranar Mufeeda tayi kuka kamar ranta zai fita, da kyar aka sa mu ta zo ta zauna a mazaunin ta, sai da Mommah take da kanta ta taho da'ita. Ranar gaba 'daya ji tai kamar an fizgo 'kaunar tsohon mijinta an dasa mata cikin zuciyar ta, soyayyar su da sha'kuwar su ta dawo mata fil a ranta.
Shikuwa Naseer ji yai kamar an dasa masa wani irin juriya da ha'kuri cikin ransa. Domin har wanka yai ya shirya cikin shadda maroon wacce ta amshi jikin sa tare da fiddo asalin kyawun sa da kuma 'yar ramar da yayi. Direct babu inda ya nufa sai can gidan iyayan shi inda ake mother's day. Kamar ha'din baki Ayaan da Abid suma kalan kayan da ke jikin mahaifin su, shike jinin su harda 'dinkin. Ba 'karamin kyau su kai ba.
Ita kuwa Mufeeda wani wani rantsatstsan maroon lace ne a jikin ta, ku'din sa kimamin dunu arba'in da biyar, sai ba'kar alkyabbar dake jikin ta da ya sha stones.
Tuni aka soma shagalin biki, Mufeeda kuwa ko motsi tak'i yadda tai a wajan da take. Anyi ² ta tashi ta 'dan taka tak'i.
Lokacin da Naseer ya shigo gidan hannun shi ri'ke da Abid da Ayaan, gaba 'daya kallo ya koma kan shi. Aikuwa suna ha'da idanu da Mufeeda tai wani irin mi'kewa ta na tahowa a hankali har ta iso tsakiyar filin inda Naseer ke tsaye a wajan shi da 'ya'yan shi, duk mutanan wajan sai duka zuba masu idanuwa. DJ kuma kamar yasan mai ke faruwa said ya saki wakar Nazifi asnanic *SAI WATA RANA*.
Wasu hawayene suka soma gudu a idanun Mufeeda, take amshe wa'kar tare da fa'din,
🎻 *_SAI WATA RANA MASOYI ZAN BARKA, SAI WATA RANA RABUWA BA MUTUWAA BA_. _NI DA KAI A YAU MUYI BANKWANA, SAI WATA RAAANA RABUWA BA MUTUWA BA, 'DAN UWA RABIN RAI NA BAN SO MUYO RABUWA_*🎻
🎻
🎻 *_ASHEE SABO YANADA DA'DI, AMMA IN ZA AI RABO DA ZAFI. GASHI ZA MIYO RABO DA JUNA, AMMA NA SANI NI BANDA LAIFI, KA TAUSAYA IN NAIMA LAIFI, KACEE KAYAFE IN KAMA GABANA_*🎻
Tuni shima Naseer ya cafke tare da fa'din,
🎻 *_NI DA KE A YAU MUYI BAN KWANA, SAI WATA RANA RABUWA BA MUTUWA BA, 'YAR UWA RABIN RAI NA BANSO MUYO RABUWA_*
sosai suke kuka kamar ran su zai fita, kuma basu daina wa'kar ba. Hatta Abid da Ayaan da basu san meke faruwa ba, suma kukan suke yi. Hatta mutanan wajan ma kuka suke yi da wa'danda suka san ko mai da ma wa'danda basu sani ba.
Sai da wa'kar gaba 'daya ta 'kare kana Mufeeda ta zube a gaban Naseer idanunta na tsiyayar da hawaye tare da fa'din,
"Yallab'ai na yafe maka duk abunda ka min ko da kuwa kana cikin hayyacin ka ne. Wallahi yalla'bai tun ranar da naji ainahin abunda ya faru nake jin tausayin kanmu. Abunda yasa nake avoiding 'dinka shine nasan babu wani sauran igiya tsakanina da kai, kuma kusancina a gareka masiface, domin zuciyoyin mu ne zasu 'kara dun'kukewa wajena 'daya alhalin bamuda damar 'kara kasancewa da juna. Yalla'bai tabbas Mashkura ta ci amanata, na cutar dani iya cutarwa, domin ta raba miji da matar sa da kuma uwa da 'ya'yanta. Na 'dauki hakan a matsayin 'kaddarata, kuma kai ma ina son ka 'dauki haka a matsayin rubutaccan 'kaddarar ka, sannan dan Allah yallab'ai kai aure kai ma ka samu wacce zata kula da kai da kuma baka soyayya fiye dani ma. Tabbas zaka sa mu yalla'bai. Dan Allah idan har dagaske kana 'kaunata haka, kada ka sake ciwo a kai na, ka da ma 'kara bari damuwa tai maka illa ko dan ka rayu da 'ya'yan da na haifa maka". Ta na kaiwa nan kuka yaci 'karfin ta sosai. Da gudu Irfana dake ri'ke a hannun mama Fatima ta fizge tayo kan Mufeeda ta ru'kun'kume tare da fashewa da kuka. Mommah ma kukan take yi a fakaice tana share hawaye. Ummu Nah ko hai'kan take kukan ta. Daga can gyefe cikin taron mutane kuwa, Mashkura ce da dungulmin hannun ta tana wani irin kukan nadama, tare da kaico wa rayuwar ta. Domin da badun shiga rayuwar wannan masoya da suka shimfi'da rayuwar auran su cikin soyayya da 'kaunar juna, da yanzu haka bata faruwa, gashi ita bataci ribar komai ba, sai na wuya da kuma 'kare rayuwarta da za ta yi da hannun 'daya da rabi. Cikin sauri tai suf³ ta fece batare da kowa ya ankare da ita ba, domin ta San a yadda tsumin soyayyar Mufeeda ya tasowa Naseer yanzu, babu shakka idan yai ido biyu da ita babu tantamam gawarta za'a tsinta.
Mother's day dai ranar haka ya watse saboda koke² da Mufeeda da 'ya'yanta su kai ta yi harda kakannin su kamar gidan mutuwa. Shikuwa Naseer ji yai kamar wani abu da ya tokare wuyarshi ya sauko ya wuce. Yaci kuka idanunshi kamar yai shaye², KB ne ya kamashi su ka bar gidan.
Mufeeda kuwa wani zazzafan zazza'bi ya saukar mata da SAI da aka kira wata nurse ta zo tai mata allura. Baaba Habiba ke kula da ita, kasancewar tun biki saura sati suka dura a 'kasar, abunda ya tsayar dasu ma, ordern kayan 'daki suka tsaya yiwa Mufeeda. Don komai a china aka je aka sayo mata. Kayan gadon ta kawai abun kallone. Alhaji Aliyu kashe ku'di yai ta yi kamar bai son ciwon ku'din ba, don cewa yai idan bai yiwa tilon 'Yar shi ba, wa zai wa. Aiko ya sha fa'da wajan alhaji Mudassir, domin cewa yai shi ba ubanta bane da zai kama ya mata komai ba tare da ya bari shi ya mata ba. Ha'kuri sosai ya ba shi, kana ya sauko.
..........Rana dai bata 'karya sai dai uwar 'diya taji kunya. Yau dai dubban jama'a suka shaida 'daurin auran architect Naseer Mudassir da amaryan sa Mufeeda Aliyu a kan sadaki dubu dari. Da kuma Lukman Mudassir da amaryan sa Jalila (Baby) ita ma akan sadaki dubu 'darin. Kunnuwa da bakunan wa'dannan anguna sun'ki rufuwa musamman architect Naseer Mudassir kano.
Gyefe guda kuma amarya sai rusar kuka take yi tare da fara kewan iyayan ru'konta da kuma 'ya'yan ta kasancewar ba dasu zata tafi ba suna wajan mahaifin su.
Naseer kuwa yayi iya dauriyar sa domin kada auran tsohuwar matar ta shi ya dame sa amma ya 'kasa, suna dawowa daga 'daurin aure ciwo ya dawo sabo. Mal Ahmadu aka baiwa auran, shiyasa ma a nan Kaduna aka 'daura auran, na su Lukman be aka 'daura a kano. Hankalin Ummu Nah wannan karan yafi na kowani lokaci ta shi don Naseer aman jini yake yi guda².
Mufeeda kuwa da kyar aka dannata cikin mota domin ru'kun'kume mama Fatima tai tana kukan da SAI da ya saka mutane dayawa kuka a wajan.
Karfe hu'du a kano ta musu, 'dakin Hajiya jummai mahaifiyar Naseer aka fara kai Mufeeda. 'Kin fitowa tai ta tarbe su, sai wasu daga cikin 'yan uwanta ne suka kar'bi Amarya. Yayyin Naseer kuwa, musamman aunty Saudat, tunda suka ji labarin Mufeeda jinin su ce, 'kaunar ta ya shiga ransu. Cike da fara'a da kuma mutunci suka kar'be su. Daga baya su kai masu rakiya har 'dakin Hajiya Zulfah ita ma ta kar'be su cikin mutunci. Mufeeda kuwa tanajin sun shigo 'dakin Hajiya Zulfah sai ta kwakwuneta tare da sakin kuka. Sosai ta shiga lallashinta, ita ta kai ta har 'kofar 'dakin ta tare da cema ta tai bismillah ta shiga da 'kafar dama.
Masha Allah, domin tsayawa zayyane maku tsaruwar 'dakin Mufeeda 'bata baki ne, kawai Ku hasaso da kan Ku. Don dai 'dakunar bacci ukune a 'dakin kuma kowanne akwai setin gado a ciki. 'Daya mahaifin ta alhaji Aliyu ya mata order daga China, 'daya kuma alhaji Mudassir ya saya mata. Dayan kuma mal Ahmadu ya mata su dai dai 'karfin sa kuma sun ha'du don MBF mai kyau kalar coffee brown. Kuma duk ciki sunfi burge Mufeeda.
............Bayan isha'i aunty Saudat ta shirya Mufeeda cikin wedding gown kalar purple da ya amshi jikin ta, farar fatan ta ya kuma haska kyawun kayan. Fuskan yaci makeup light amma tai 'dan karan kyau. Ango ko farar shadda ce jikin sa da tasha aiki da purple 'din zare, ba'kin fatar shi wai she'ki take. Hall cike da jama'a, haka aka sha dinner aka rabarbashe domin ango Naseer ya ti'ki rawa doctor Haroon sai tsiya yake masa. Sai sha biyu aka ta shi, ango ya tarkato matar shi suka dawo gida, don rashin kunya hawa abikai akan babu Wanda zai maka shi, kuma haka akai, said dai yasha zagi da tsiya.
Tunda suka dawo gida, Mufeeda ke jin wani nauyayyan bacci, amma Naseer ya yahata kwanciya said da tai Wanka kana taci kazar da ya kawo ka'dan sannan ta kwantar. A tunanin Mufeeda shima Naseer kano ba zai mata komai ba kamar yadda Naseer bai mata komai ba ranar da aka kai masa ita. Sosai Mufeeda ta sha mamaki da taji lokacin da Naseer ya 'kusanceta taji kamar ranar zata fara domin harda kukan ta. Ba ita ka'dai ba hatta Naseer 'din ma cike yake da mamaki domin shi shaida ne akan Mufeeda 'din ba budurwa bace ta ta'ba aure harda 'ya'ya biyar. Ba komai ya kawo hakan ba, wai gyaran da tasha wajan Mommah da mama Fatima. Naseer kuwa harda kukan da'di tare da fa'din da ASN haka aure yake da tuntuni ya yi nai tsaya ya kai wannan lokacin ba. Tarairaya kam Mufeeda tana shan sa kamar zai matar da ita cikin sa. Sai wai abunda Mufeeda ta zo ta lura da shi, shine Naseer Nada matu'kar bu'kata ba kamar tsohon mijin ta, said dai bata ta'ba nuna NASA gazawarta baa, don nasan bai da wani wajan bayan wajan ta.
.........Amarya Baby kuma, bayan biki da kwana biyar suka Lula Germany. Domin a can mijin ta Lukman ke aikin sa. Sosai ita ma take shan soyayya wajan mijin NATA Lukman musamman da ya sa mu abarsa cikakkiyar budurwa, ranar ya godewa Allada ya tsare NASA matar yasa daga fa'dawa halakar *ZINA*. Sosai yake tarairayar abunsa.
'Bangaren Hajiya Jummai kuwa, har gobe bata sakewa Mufeeda fuska, duk da Mufeeda ta na iya 'ko'karinta wajan kyautata mata, haka zata girka 'dan abun marmari ta kai mata ita da hakiya Zulfah, amma da ta kai mata zata ce ta kwashi abunda ta yafi da shi bata bbu'kata, kuma ko da wasa Mufeeda bata ta'ba fa'dawa Naseer ba.
Agurguje please.
Watan Mufeeda biyar a gidan Naseer, sosai ake zuba love tsakanin ta da Naseer, kowa na 'ko'karin nunawa 'dan uwan sa 'kauna da kulawa. Tunda aka kawo ta kano sai dai suyi ta waya da quintuple, sosai tai biyumissing 'din su. Naseer ya mata al'kawari insha Allah 'karshan watan nan shi da kan shi zai je har kadunar ya 'dauko mata su suyi mata sati biyu.
'Bangaran Naseer Kaduna kuwa, ko ma'kiyi idan ya ganshi yanzu sai ya tausaya masa. Ya mugun ramewa. Sai dai kuma ya fawwalawa Allah lamuransa, ya bar komai wajan Allah tare da kar'ban 'kaddaransa. Sai dai batun aure kam ya jinginesa a gyefe, ko kallan mace bai yi da niyyar so balle aure.
.............Mufeeda yanzu kam ta 'kara kyau tai haske jikinta yai lukui², mijinta ya naima mata gurbin karatu a Bayero tana karantar medicine don ita daman burinta ta zama doctorn mata. Tana da kuma shigar 'karamin ciki na wata 'daya da sati biyu. Baby kam ita ta kusa juyewa, domin tana shiga taci karo da shi. Mummy ce ma ta matsawa Lukman 'din akan ya dawo da ita wankan gida. Shi kuma yace in sha Allah tana shiga watanta zai dawo da ita.
Mufeeda sosai take samun matsi daga Hajiya Jummai, amma bata ta'ba bari hakan ya dameta ba, Naseer yasan da hakan, amma ita bata ta'ba masa 'korafi ko ta gaya masa wasu abubuwan da Mummyn ke mata ba. Haka zai zaunar da ita yai ta bata ha'kuri, ita kuma ta nuna nasa babu komai ai itama uwace a gare ta.
Kamar yadda Naseer yai mata al'kawari har Kaduna yake ya 'dauko mata su. Naseer kuwa ya kar'be shi cikin mutunci harda 'Yar hirar su, don da zai komo kamin ma har wajan mota ya rakoshi tare da ce masa a gaida iyali.
Mummy kuwa kamar zata ari baki saboda fa'da akan don me zaije ya 'dauko agola ya kawo gidan shi. Ta kuma masa kyakkyawar warning akan dole su koma wajan ubansu don ba zai yi ya ri'ke agola ba. Shi dai Naseer ha'kuri kawai yai ta bata.
Su Ayaan an girma kyawunsu da wayan su SAI da'da fitowa yake. Gadu da shiga ran mutane.
Hajiya Zulfah kuwa tafi kowa farin ciki da zuwan su Ayaan 'din, don a 'dakin ta suke wuni. Ayaan ne kawai da shegen ciye² yake zuwa 'dakin Hajiya Jummai kasancewar ta na ha'da snacks ta aje cikin fridge a kitchen. Shikuna tunda ya kyallara idanuwa ya ga ni ya maida 'dakin ta WAJAN zuwa domin kwa'dayi. Ita kuma tana ajewane saboda bata cin bredi, da safe dasu take ha'dawa ta sha tea.
Aikuwa kwatsan watarana ta shiga kitchen ta iske Ayaan yai mata kaca² da snacks. Haushi ya ka mata ta bubbuge shi tare da mur'de masa kunne ya fita yana kuka. Tun daga ranar bai kuma komawa ba. To abunka da yaro ba hankali, bayan kwana biyu ya koma, SAI dai Hajiya Jummai kamashi, SAI ya gama 'barnar ya fita take zuwa ta iske WULA'KANCIn da ya mata. Aikuwa ranta ya 'baci ainun kuma ta 'kudurci maganin shi. Wata rana ta fita kasuwa da kanta, SAI ta sayi abincin 'bera dawo gida ta ha'da lafiyayyan meat pie tare da wannan maganin 'beran ta saka a fridge kamar yadda ta saba. Aikuwa kamar Ayaan ya sa ni ya shiga kitchen 'dinnan yaga pie 'dinnan ya 'dauko da sauri ya fito tare da barin fridge 'din a bu'de. SAI da ya gutsira kana ya five daga 'dakin da gudu ya na taunawa. Ita kuma haijya Jummai SAI hankalin ta ya ta shi, ta ji har cikin zuciyar ta abunda tayi bata kyauta ba, yanzu idan yarin mutane yaci ya muku shikenan tayi kisa fa, to tacewa Allah me. Da gudu ta fito daga 'daki ta sauko 'kasa, kai tsaye kitchen ta nufa taga fridge a bu'de kuma ba meat pie. Jikin ta har wani rawa yake YI ta fito da gudu, dai² lokacin da Ayaan ya saka Naseer ya bu'de baki tare da saka masa wannan pie 'din ya gutsira tare da taunawa. Wani irin ihuu Hajiya Jummai ta kurma tare da fa'din,
"Naseer kar ku ci, a kai maganin 'bera a ciki". Ta na fa'din hakane tare da nufosu da gudu.
Ko kafin ta iso tuni Ayaan ya soma aman wani irin farin kumfa. A rikice Naseer ya shiga wani irin jijjigashi , SAI dai shima tuni idanuwan shi suka soma kakkafewa bakin shi na fidda kumfa. Ai tuni Hajiya Jummai ta gigice tare da sakin fitsari ana tsaye. Ihunta ne ya fiddo mutanan gida dama alhaji mudassir na gida akai asibiti dasu.
Gaba 'daya asibitin nan kowa tayi cirko cirko, Mufeeda kuwa da ta sa mu LABARIN sumewa tayi
[10-31 3:24 PM] Mai Daddawa: wanda hakan ya jawo mata zubewar cikin ta. Da 'kyar da si'din goshi doctor ya ceto ran Ayaan da yasha dakyar. Naseer kuwa shuru har yanzu yana theater room. Sai bayan kwana hu'du har an fidda rai sannan Allah yai ikonsa ya farfa'do. Lokacin tuni Ayaan ma ta gyare. Hajiya Jummai kuwa sai hamdala takeyi tare da tur da halin ta. Wani nadama ya lullu'beta. Ta kuma ji zuciyar ta tai mata sanyi. Duk da babu Wanda yasan ita ce ta saka maganin 'bera, kuma ikon Allah babu Wanda ya bi ta kan hakan don duk hankula a tashe yake.
Gaba 'daya mutanan Kaduna sunzo don duba masu jiki, da za su koma Naseer da daga baya shima ya biyosu ya tattara 'ya'yan sa suka koma kuma har a sannan ba'a sallami Naseer ba. Don iya jigata ya jigata, kuma shi bai kai Ayaan cin pie 'din bama.
Bayan an sallamoshi ne, alhaji Mudassir da Inna Huwaila suka tsare kowa a parlour tare da tambayan su yadda akai maganin 'bera ya shiga pie 'din da Ayaan da Naseer suka ci. Inna Huwaila ta ce kuma dole a fito da wanda yai wannan aika² ko tai la'ana. Hajiya Jummai sai zufa takeyi domin tasan yanzu 'karshan zamanta da alhaji Mudassir ne ya zo. Amma bisa matu'kar mamakinta sai ta ji muryan Mufeeda na fa'din,
"Daddy ka gafarceni, nice na saka wannan maganin 'beran".
Gaba 'daya kallo ya koma kan ta. Inna Huwaila ta ce,
"Ke zaki min shuru ko sai na la'ance ki? Karya kike ba ke bace. Idan kuma kece miye dalilin ki?".
Hajiya Jummai cike da matu'kar mamaki take kallon Mufeeda wani irin nadama na saukar mata. Mufeeda kuwa sunkuyar da kai tayi tare da fa'din,
"Wani 'bera ne ya buwaye ni a kitchen 'di