Showing 114001 words to 115393 words out of 115393 words
na, shine na sayo maganin domin in saka masa yaci, to kwata² na manta sai na aje shi a sarari, shine Ayaan 'din ya 'dauka batare da sanina ba yaci har ya baiwa Yaya (Ta na nufin Naseer).".
Gaba 'daya wajan aka 'dau salati banda Hajiya Jummai da ta ke share hawaye a fakaice, da Naseer da ya 'kafeta da idanu domin yasan lokacin da Ayaan ya kawo masa pie 'din daga 'dakin mummy ya fito. Ita kuwa Mufeeda 'kin yarda tai su ha'da idanu da Naseer 'din.
Nan dai Alhaji Mudassir yai wa Mufeeda fa'da akan ajiye irin wa'dannan abubuwa a fili tare da fatan Allah ya kiyaye nagaba. Kana kowa ya watse.
Mufeeda na shiga 'daki Naseer ya biyo ta tare da fa'din,
"Abunda kika fa'da ba gaskiya bane. Bake kika saka maganin 'beran nan ba, ki fa'damin wa ya saka".
'Bata rai Mufeeda tayi tare da fa'din,
"Ni kuma iya gaskiya ta na fa'da, ni ce na saka".
Cikin tsawa ya ce, "karya kike yi ki fa'damin yanzun nan". Sosai Mufeeda ta razana, domin bai ta'ba mata makamancin wannan tsawan ba.
Hajiya Jummai ce ta turo 'kofar ta shigo, tare da du'kawa bisa guiwowin ta ta ce,
"Ni ce na saka Naseer. Son zuciya ta ya saka ba saka maganin 'bera a cikin pie 'din don Ayaan ya ci. Amma wallahi nayi nadama. Da sauri na fito domin na 'dauke na zubar Sai na tadda babu komai cikin fridge 'din shine ba fito ba taras har yaci kai ma ya baka".
Ido, hanci, da baki Naseer ya bu'de yana kallon Hajiya Jummai tare da fa'din,
"Yanzu mummy har 'kiyayyar ya kai ki iya yin kisan kai? To da yanzu Allah bai kare ba? Da kin rasa 'dan ki kema. Mummy wani irin rayuwace wannan?". Yana gama fa'din haka ya juya a fusace tare da fa'din,
"Dole su inna su san wannan batu. Saboda kin tsani yarinya har zaki iya yun'kurin kashe mata 'da. Gashi baki kashe NATA na kin zubar da 'dana ko 'ya ta dake cikin ta".
Saurin shan gaban sa Mufeeda tayi tare da fa'din,
"Wallahi wallahi idan har wani yasan da batun nan bayan mu uku, aure na da kai ya 'kare".
Cak ya tsaya yana kallon ta cike da mamaki. Wani irin 'kimar ta da darajarta na 'kara nunkuwa cikin zuciyar sa tare da wutar 'kaunar ta cikin zuciyar sa. Kawai Sai ya saka duka hannun shi ya rungume ta tare da sakin kuka.
Mummy ma kukan takeyi tare da ro'kar gafarar Mufeeda. Mufeeda ta kwace jikin ta tare da kamo mummyn tace
"Wallahi babu komai Allah ya yafe mana baki 'daya".
Tun daga wannan rana mummy ta canza gaba 'daya. Hatta Hajiya Zulfah Sai da mummy take ta ro'ki gafarar ta. Yanzu zaman su suke gwanin ban sha'awa tamkar 'yan uwan juna.
Baby kuwa ta shiga watan haihuwar ta kuma Lukman ya cika al'kawari ya dawo da ita. Kwanan su shidda da dawowa ta sunkuto 'yarta mace kyakkyawa mai kama da ita taci suna Asma'u, takwara akai wa Hajiya Jummai ana kiran yarinyar da Samha.
*KADUNA*
A kaduna garin gwamna kuwa, Ummu nah wani ha'di tai na ban mamaki, domin tuni ta ha'da Aaeedah da Naseer soyayya, da da farko kamar abun bazai yi 'karko ba, har ta watsar da zancan, Sai Gashi daga baya da kan su suka shirya kan su domin dai Naseer Sai yake gani kamar wata Mufeedan aka bashi don Aaeedah babu inda ta baro Mufeeda. Lokaci guda akai bikin da su Zaheeda da Zaleeha don suma sun sami mazajan aure.
Gaba 'daya Naseer ya susuce akan Aaeedah, don ta iya koyawa mutun 'kaunar ta a zuciya. Duk wani gurbi na yarta Sai da ta bi ta cike shi tsaf a zuciyar Naseer. Sosai yake son abunsa tare da tarairayar ta.
*AFTER 7YEARS*
Wata farar mace nagani wacce a 'kalla zata kai 32years zaune akan kujera, tana danna laptop. Gyefan ta kuma wasu kyawawan yarane maza 'yan shekaru shidda masu kamanni da juna, kana ganin su kaga mahaifin su hatta ba'kin fatan su mai shinnin na mahaifin su ne suna home work. Daga gyefe kuma Abid, Ayaan da kuma Naseer kano na hango suna buka ludo a wayan Naseer 'din. Sunyi girma domin shekarunsu Tara yanzu.
"Koma gida daddy, wallahi na mai da ka". Naseer ne ke dariya tare da fa'din,
"Ni ma zan rama son".
Mufeeda ta kashe system 'din tare da fa'din,
"Nureen ka biyewa yara bayan kasan Mummyn su na hanya don tace wai aron da ta tayi kawaicin ya isa haka. Kuma ko kimtsa kayan su basu yi ba kuma naji tace ba kwana za suyi ba don suna zuwa ko 1hour bazasu yi ba za su juya".
'Dan tsaki Naseer yai tare da fa'din,
"Wallahi Aaeedah akwai naci, nan fa jiya da mukai waya nai ta bata baki akan zan kawo su jibi da kai na, amma 'kememe ta 'kiya".
"Hmm Aaeedah ce fa". Fa'din Mufeeda.
Ko kamin ta rufe baki Sai ga knocking. Naufal dake homework ya ta shi tare da bu'de kofar, aikuwa yai tsalle tare da 'dane Aaeedah dake bakin 'kofar yana fa'din oyoyo aunty.
'Karasowa tai cikin 'dakin tare da fa'din,
"Ina baban naku yake da ya 'da'd'dagoni, aikuwa Sai ka biyani mai na da na 'kona".
"Ina dai wannan ne baki da damuwa".
Dariya Aaeedah tai tare da fa'din,
"Tare muke da Qalby, yana waje".
"Shikuma kamar ba'ko, ya shigo mana".
"Suna gaisawane da Abba (alhaji Mudassir)".
Kamin ta ida rufe baki Sai ga Naseer 'din yana sallama.
Amsa sallama su kai gaba yayin da yaran gaba 'daya suka nufe shi tare da rungume shi.
"Doctor! Doctor!! Doctor!!! Kune allura". Naseer Kaduna ya fa'da yana dariya.
Ita Mufeeda dariyar take yi tare da fa'din,
"Ku kuma kune ku'di ba". Ta fa'di hakane tare da 'daukar kyakkyawar yarinyar dake sa'be a kafa'dar shi ta na bacci. Yarinya da Aaeedah ta Haifa ne, takwara akai wa Mufeeda, kuma kamar su 'daya da Aaeedah.
Naseer ya ta so tare mi'kawa naseer Kaduna hannu suka gaisa tare da zaulayan junan su.
Tuni Mufeeda ta shiga kitchen ita da su Irfana da shigowar su kenan daga 'dakin Hajiya Zulfah suka ha'da lafiyayyan abinci suka jera a dining.
Sai da suka cika cikin su kana suka shiga cafta cike da nisha'di.
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!
Nan ma kawo karshan littafin nan mai suna NI DA SHI ABU 'DAYA NE. Ya Allah ina ro'kon ka kuskuren da na aikata a ciki ka gafarar mu.
Ina matu'kar gaisuwa gareke ku, Darma, Haleematou, Farida Haruna, Queen Zara da duk sauran da ban ambata ba. Domin kuna 'daya daga cikin wa'dan'da suke matu'kar 'ko'kari wajan yi mani comments. Da bazarku nake takawa.🥰❤️🥰
Da wannan damar nakeso nai amfani wajan ro'kon ku gafara, duk wanda na 'batawa rai yayin rubuta wannan book don Allah ya yafe min, ni na yafe maku duniya da lahira domin idan yau mune, gobe ba mu bane. Sannan nagode kwarai naga sa'konnin gaisuwar ku da fatan samun lafiya da kuka min. Nagode kwarai da kulawar ku a gare ni. Kuma Alhamdulillah jiki nata improving.
Ku cigaba da bina a littafin *ZINA* in sha Allah zai fa'dakar tare da ilimantar da kuma nisha'dantar wa. Duk wanda bai karanta littafin *ZINA* ba an bar shi a baya wallahi, littafi ne da yazo da wani salo da kuma abubuwan dake faruwa a cikin wannan zamanin.
❤️❤️❤️❤️❤️❤️