Showing 48001 words to 51000 words out of 115393 words
HU'DU NE KAWAI KE YIN SHARHI. SAURAN KUMA DAGA MASU TURA STICKER, SAI MA SU CEWA THANKS. TO NI BA THANKS 'DIN KU KO STICKERN KU NAKE BU'KATA BA, SHARHI NAKE BU'KATA. KUMA BILLAHIL AZEEM WANNAN SHINE MAGANA TA TA KARSHE, IDAN KUN GYARA, SHIKENAN. IDAN KUMA BA KU GYARA BA, WALLAHI ZAN SHARE GROUP 'DIN TAAAS, NA GWAMMA CE NA TURA A SAURAN GROUPS 'DIN DA SUKE MIN COMMENT*
*BAASSS🤷🏼♀️🤷🏼♀️🤷🏼♀️🤷🏼♀️*
*_PAGE 25_*
A dai² 'kofar gidan *KURA* ta jaa birki ta re furta,
"To ni dai nan zan barki Feedy. Kin San halin baabar ta ki. Kuma ni ba ha'kuri gare ni ba wallahi".
Mufeda ta zame hannun ta a cikin na Mashkura ta re da fa'din,
"To shikenan *KURA*, sai mun ha'du gobe".
"A gaida min da Musan idan ya zo". Fa'din Mashkura ta na tafiya.
"Zai ji in sha Allah". Fa'din Mufeeda ta re da shigewa cikin gida.
" *UBAN DA YA HAIFI UWAR KI*". *MAI ZOGALE* ta fa'da ta re da sha'ko wuyar hijjabin Mufeeda ta kifa mata mari tare da fa'din,
"Uban wa kika mayar 'yar iska? Shegiya mai kama da aljana. Ni wallahi tsoro ma wannan shegen jaan fuska take kamar kosai take bani. Wa ni aiki Marwa ta saka k kamin ta bar gidan nan?".
Idanuwa Mufeeda sun ka'da sun yi jazur saboda shakan da *MAI ZOGALE* ta mata. Dakyar ta iya fuzgo magana ta ce,
"Dan Allah Inna ki yi ha'kuri, wallahi result 'din mu aka ce ya fito na neco, shine muka je dubo wa ni da *KURA*, kuma wallahi na tambayi baba, shi ya ba ni izini lokacin kin fita unguwa. Yanzu ma saurin da na ke yi kenan don na wanke mata kayan".
"Na ce bura uban kil ke da *KURAN*, ai dama na san ita ke hure miki kunne akan ki dai na mana aiki a gidan nan. Kuma zan je har gidan uban ta na ci mutuncin ta. Ke kuma wallahi ki ka ce za ki biye mata ba'kar wahala za ki sha a gidan nan. Shegiya mai hali irin na uwar ta". Tura ta tai yi sai da ta kifa a 'kasa.
Mi'kewa Mufeeda ta yi ta na dafe guiwar ta da ke mata zugi sanadiyar fa'duwar da ta yi. Wajan tumulin kayan da Marwa ta jibge a 'kofar 'dakin ta tayi. Kwaso su ta yi ta kai su bakin rijiya ta aje, sai ta koma 'kofar 'dakin *MAI ZOGALE* ta re da fa'din,
"Inna ga kayan can amma ba ta saka sabulu da omon wanki ba".
Wani irin 'daga labule *MAI ZOGALE* ta yi ta re da fa'din,
"Kan uwar ki na ce, kin ji ko? Omon ne bazaki iya saka ku'din ki ki saya ki wanke mata kaya ba sai na ba ki ku'di? To ki zauna ka da ki wanke kayan ki ga abunda zai faru da ke. Shegiya mai mugun hali". Ta na gama fa'din hakan ta saki labulan.
Mufeeda kuwa 'dakin ta nufa, idan da sabo ta saba da siyan sabulu da ku'din ta, ta wanke kayan Marwanatu.
Wata tsohuwar jakar ta da ta ke ajiyar ku'di ta 'dauko ta ciro 'dari biyu, ta mai da jakar sannan ta saka hajjab ta fito daga 'dakin. Dai dai lokacin Marwanatu ta shigo gidan. Turus ta yi ta tsaya ta na wa Mufeeda wani irin kallo idanuwan ta har wani 'kan'kancewa su kai. Ta ce tare da nuna uban tumulin kayan da ke aje gindin rijiya,
"Dan uban ki da ma wankin da na ba ki ba ki wanke min ba? To wata uwar ki ke yi da ba ki min wankin ba? Kuma na fa'da miki ba ni da sauran wankakken kayan da zan saka gobe, duk sun yi datti. Shine dan mugun hali ki ka 'ki wanke wa ko?".
"Ki yi hakuri Marwa, yanzu nadawo daga dubo result 'din neco 'din mu, yanzu haka ma kin ga ku'din na 'dauko zan sayo sabulu na wanke miki kayan". Fa'din Mufeeda jikin ta na rawa.
"Maza.... Zo ki wuce ki sayo ki wanke su taaass, ko ran ki ya 'baci".
Sum sum Mufeeda ta bi ta gyefan ta ta wuce.
Minti biyar ta dawo 'dauke da sabulu da oma ta hau wanki. Ta na cikin yin wanki ta yi rabi, *MAI ZOGALE* ta kwalo mata Kira. Da sauri ta mi'ke ta isa 'dakin.
"Uban wa ki ke so ya 'daura miki girkin dare? Ga kayan miya can ki jajjaga ki 'daura mana dafadukar shinkafa da wake na manja". Fa'din *MAI ZOGALE*
Mufeeda mai da kallon ta tai wajan da Marwa ke kwance ta na daddanna waya ta na taunar cingam kamar wata karuwa.
"Kallon uwa me ki ke ma ta kamar za ki cinye ta?". *MAI ZOGALE* ta hayayya'ko wa Mufeeda.
*NA FA'DA, BARI NA 'KARA MAI MAI TAWA. WALLAHI IDAN BAN GA RUWAN COMMENT BA, IN SHARE GIDA TAAAS, IN KOMA TURAWA SAURAN GROUPS, KUMA SU MA IDAN BAN GANIN COMMENT YADDA YA KAMA TA, WALLAHI UPDATE SAI SATI SATI* 🙅🏼♀️🙅🏼♀️🙅🏼♀️
*DAGA AL'KALAMIN MATAR SAYYADEE✍🏼*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 26_*
"Kin sa fa kallon sa'ar ta ta ke min. Ta ga ina kwance shine ta ke kallo na, irin ga ni mai ya sa za ki saka ta girki bayan ita ta na wanki". Fa'din Marwa.
"Lallai kam, biri ya yi kama da mutum. To wallahi duk sai kin yi su. Za ki tashi ki soma aikin da na saka ki, ko sai na ci uban ki Ahmadu yanzu!?".
Saurin mi'kewa Mufeeda ta yi tare da fita daga 'dakin ta na share hawaye. Kitchen 'din da ke tsakar gidan ta nufa. Gawayi ta fara hurawa, sannan ta soma gyarawa kayan miyan ta re da jajjagawa.
Kamin ta gama jajjagen ma har wutan ta ruru, sai ta 'daura tukunya ta zuba manja. Da yai zafi sai ta zuba kayan miya. Da ya soyu sai ta tsaida ruwan sanwan, ka na ta wanke wake ta zuba ta koma kan wanki ta cigaba da yi kamin waken ya dahu ta wanke shinkafa ta saka da su maggi da gishiri.
Cikin 'kan'kanin lokaci waken ya dahu ta wanke shinkafa ta saka tare da sauran kayan girki. Da ma ta gama wanki shanya kawai ya rage. Sai ta shanya kayan ta wanke bakin rijiyar da tai wanki a wajan tare da 'dauraye bokitai ta aje su a ma'adanar su.
Bayan ta gama girkin ta sauke, sai ta 'daura ruwan wanka. Allah ya so ta ma ta na fashin sallah, don a na kiran magriba ta gama wankin da ta fara tun biyu na rana.
Ruwan wankan da ta saka ya na tafasa ta juye a cikin bokitin Wanka tare da Jan ruwa a rigiya ta surka ruwan.
Ta 'dauka kenan zata nufi ba yi Mashkura da fitowar ta ke nan daga 'daki ta ce,
"Ke! Ina za ki da ruwan nan, bayan kin san banyi Wanka ba? Kin ma rai na kan ki wayau wallahi. Sallah malama ki je ki kai min ba yi, yanzu zana zo nai wanka. Idan kin ga dama kya iya ficewa ki bani waje". Ta na gama fa'din haka ta juya 'daki.
'Kasake Mufeeda ta yi, tsabar ba'kin ciki ji ta yi wasu zafafan hawaye na bin kuncin ta. Ta na nan tsaye har Marwanatu ta iske ta ba ta ma san ta zo ba. Sai jin wani zazzafan maruka hagu da dama ta yi a kumatukan ta tare da fa'din,
"Ke dan uwar ki ni sa'ar ki ce ko? In ce ki kai min ruwa ga ni nan zuwa in yi wanka shine dan tsabar iskan ci ki ka tsaya a wajan 'ki'kam kamar wata soja, ke ga 'yar iska ko?".
"Hayaniyar mi na ke ji haka Marwa? Me ke faruwa ne?". Fa'din KALLAH da shigowar shi gidan ke nan.
"Ka ga Baba, 'yar iskan yarinyar nan ta saka ta kai min ruwa ba yi in zo in yi Wanka, shi ne ta tsaya a nan kamar wata soja salan ruwan ya huce". Fa'din Marwa ta na wani zazzarewa Mufeeda idanu.
A fusace KALLAH ya 'karaso wajan kamar zai make Mufeeda, sai wani huci ya ke yi tare da fa'din,
"Wai ke wata iriyar da'ki'kiyar yarinya ce mara tunani? Wannan ba yar ki ba ce?". Fa'din KALLAH ya na nuna Marwanatu.
"To wallahi ki ka bari *SHALELE* ta 'kara kawo 'karar ki waje na, na lahira sai ya fikii jin da'di. Shashashar yarinya kawai. Maza 'dau ruwan ki kai mata bayi".
Saurin 'daukar bokitin Mufeeda ta yi tare da nufar bayi.
*MAI ZOGALE* ce ta fito hannun ta ri'ke da shinfi'de'diyar bulala ta mi'kawa KALLAH ta re da fa'din,
"Amshi nan. Wallahi idan ba 'dumama mata jiki ka yi da yamman nan ba, ba dawowa cikin hankalin ta za ta yi ba. Tuntuni na ke lura da ita, saboda Marwa ta ba ta 'yan kala biyar ta wanke mata, shine ta ke wani cika ta na batsewa. 'Dazun ma daga na saka ta girki, harda nai man zagi na ta yi". Sai ta soma sharar 'kallar munafurci.
"Haba! Haba!! Haba *MAI ZOGALE*, wannan yarinya ki ke wa kuka? Za fa ki saka na karairaya ta". Fa'din KALLAH.
"Ai abun ne akwai ban haushi wallahi. Kamar wannan yarinya da na raine ta za ta ri'ka zuba min rashin kunya, ai abun da haushi wallahi". Fa'din *MAI ZOGALE*.
"Dan uban ki zonan, idan ki ka bari na 'karaso wajan wallahi sai na 'balla maki 'kashin ha'kar'karin ki na hagu. Hegiya 'yar dangin mai ta". KALLAH ne ya fa'di hakan ya na kallon Mufeeda da ke raku'be da gini.
Da sauri ta 'karaso wajan da KALLAH su ke. Ai kuwa bai yi wata wata ba ya shiga lafta mata wannan zabgegiyar bulalar ta ko ina a jikin ta.
Mufeeda kuwa sai zabga ihu ta ke yi ba bu mai taimako. Don duk ma'kotan su ma ba sa shigowa gidan, don sun san bala'i da makirci irin na KALLAH da matar shi *MAI ZOGALE*.
Sai da KALLAH ya da ke ta yadda ran sa ke so sannan yai wurgi da bulalar kuma ya ce minti biyar ya ba ta ta zubo masa abinci ta kawo masa 'dakin *MAI ZOGALE*.
Fuskan *MAI ZOGALE* fal murna ta du'ka ta 'dauki bulalar ta re da 'kara tsulawa Mufeeda a gadon bayan ta SAI da ta gantsare.
"Za ki tashi ki je ki zubo masa abincin ko sai na 'kara shimfi'da maki a jikin ki?".
Da sauri Mufeeda ta mi'ke ta na sosa bayan ta, hawaye na shatata a idanun ta ta nufi kitchen. Plate ta 'dauka ta zuba shinkafa da waken da ta dafa ta saka cokali tare da 'daukar copi ta 'deba ruwa ta fito ta nufi 'dakin *MAI ZOGALE* kai wa KALLAH abincin.
Sallama ta yi. Babu Wanda ya amsa mata, dama ta San ba amsawar za su yi ba. Kutsawa ta yi. Zaune ta same mu su na hira. Aje abinci ta yi kusa da KALLAH ta re da fa'din,
"Baba ga abincin nan".
Harara ya watsa mata tare da fa'din,
"Wallahi idan bakya shiga hankalin ki a nan gidan sai na sabarta ki. Kuma da ki ka kawo min abincin ni 'daya, ita Innar ta ki na ta kai ki kawo mata ba kenan?".
"Yanzu na ke so na kawo mata na ta, dama na fara kawo ma ka ne sannan na koma na zubo mata". Mufeeda ta fa'da hawaye na zubo mata.
"To ai sai ki tashi ki je ki kawo mata". KALLAH ya fa'da. Ya yin da *MAI ZOGALE* ke antaya mata harara da tsantsar tsana.
Fita Mufeeda ta yi. Kici'bus su ka yi ita da Marwanatu ta fito daga wanka za ta shiga 'dakin *MAI ZOGALE*. Rankwashi ta zuba mata a tsakiyar kai tare da shigewa 'dakin mamar tata.
Saurin dafe tsakiyar kan ta ta yi sabida wani zafi da ta ji a tsakiyar kan ta, tare da fa'din,
"Allah ya isa wallahi. Sai Allah ya saka min". 'Kasa 'kasa ta fa'di hakan.
Kitchen 'din ta nufa ta zubowa *MAI ZOGALE* na ta. Sannan ta koma kitchen 'din ta kuma saka ruwan wanka.
Ta na nan kitchen 'din har ruwa ya tafasa, lokacin tuni har an shiga sallar isha'i, kuma ta tabbatar nan da wasu 'yan mintina Musa zai zo wajan ta.
Sauri sauri ta juye ruwan tare da surkawa ta nufi ba yi. Cikin minti takwas ta kammala wankan ta, ta fito tai 'daki tare da gyara jikin ta ta sauya pad wanda Mashkura ke taimaka mata dashi duk wata, don ba laifi su na da 'dan rufin asiri.
Ta na cikin saka kaya yaro yai sallama ta re da fa'din,
"Wai inji Musa ya ce, ana sallama da Mufeeda".
Saurin le'kowa Mufeeda ta yi ta re da fa'din,
"Ka je ka ce ta na zuwa".
Da "To" ya amsa tare da ficewa
mai kawai ta shafa da man le'be. Ko powder ba ta shafa ba. Dogon hijjbi ta saka har 'kasa da flat shoe ba'ki.
Fitowa ta yi, ta nufi 'dakin *MAI ZOGALE* tai sallama. Babu wanda ya amsa mata kamar yadda tai zato. Shiga 'dakin ta yi tare da dur'kusawa ta ce,
"Inna Musa ne ya aiko kira na".
Wani irin mi'kewa Marwanatu ta yi ta re da 'daukar gyalen ta, ta fice da sauri.
Da kallo Mufeeda ta bi ta, ya yin da *MAI ZOGALE* ta ce,
"Na ji, ta shi ki bar min 'daki".
Mi'kewa Mufeeda ta yi tare da fita daga 'dakin.
"Ahhhh Musa Musa, Musa mutanan Allah. Kai ne a gidan na mu?". Marwanatu ta fa'di hakan idon ta 'kuri akan ba'kar 'katuwar ledan da ke hannun sa.
Musa da ke jingine da jikin katangar gidan ya 'dan juyo ya kalle ta tare da 'dan sakin fuska ya ce,
"Eh wallahi ni ne, jiya na dawo da daddare, kin san bazan iya runtsawa ba yau idan har ban ga 'kanwar nan ta ki ba. Kin san fa ita ce rayuwa ta".
Wani malulun ba'kin ciki ya tokare wuyar Marwanatu. Cikin zuciyar ta ta ce,
"Wai shi wannan har yanzu ba zai fahimce ni son sa na ke yi ba. Wallahi sai na aure shi ko ya 'ki ko ya so". Kwafa tai ciki yadda ba zai ji ba. Amma a zahiri sai cewa ta yi,
"Allah sarki. Soyayya manya. To ya Abujan? Ko ba can ka je ba".
Murmushi ya yi sannna ya ce,
"A'a, ba Abuja na je ba, Cameron mu ka je ni da baba na".
"Camaru?" Marwanatu ta fa'da tare da zaro idanu.
Sosai Marwanatu ta bashi dariya. Duk da ya san private school ta yi, amma bai san me yasa ita 'din da'ki'kiya ba ce. Yanzu haka duk zaton ta 'kasar turawa ya je irin su England, ko America.
"Lallai ka ce Ka ta'ba shiga jirgi". Fa'din Marwanatu.
"Shige shige ma kuwa, domin har saudiya na je, kuma na ce Switzerland. A Hong Kong ma na ha'da degree 'di na".
Sosai mamaki ya cika Marwanatu. Ashe duk yadda ta zaci Musa su na da ku'di sun wuce haka. Lallai kam ko ya'kin duniya za a 'kara yi sai ta auri Musa.
Dai dai lokacin Mufeeda ta 'karaso wajan 'dauke da sallama a bakin ta.
Cike da 'doki tare da shau'ki ya amsa sallamar ta.
Wani harara Marwanatu ta jefe ta dashi 'kasa 'kasa, ka na ta mai da kallon ta izuwa ga Musa ta ce,
"To ni ba ri na shiga gida na barku ku zan ta".
"To yayar mu, Allah ya ta she mu lafiya". Fa'din Musa.
Harara ta 'kara maka wa Mufeedan, sannan ta wuce cikin gidan kamar za ta bangaje ta, tai saurin kauce mata.
*MATAR SAYYADEE*✍🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 27_*
"Hmmm!" shi ne