Showing 15001 words to 18000 words out of 115393 words
wani ra'da'di a zuciyar ta.
*KADUNA*
Karfe 3:12 ya isa Kaduna, kai tsaye *MANAAL HOSPITAL* ya wuce tare da jin wani nisha'di a zuciyar sa.
Parking yai ya fito, kai tsaye office 'din Dr Haroon ya wuce kasancewar tun ya na kan hanya su kai waya ya shaida masa ya na asibiti.
Kwankwasa office 'din ya yi tare da turawa 'dauke da sallama a baking shi. Zaune ya ke ya na ta faman rubuce rubuce a laptop ya 'dago tare da ams masa sallamar tare da fa'din,
"Ahh'a mutumina har ka iso? Gaskiya ka yi sauri" ya fa'di hakn ne tare da mi'ka mass hannu su kai musabahaa.
"Ni kuma sai nake ganin ma ban yi Saudi ba, don ban yi gudu ba, a normal speed na ke tafiya" Architect Naseer ya fa'di hakan tare da jawo kujera ya zauna.
"Ka fa'dawa Wanda bai San ka ba, akwai uban da ta kai ka gudu ne a mota". Fa'din Dr Haroon.
"Ni dai duk mu aje wannan a gyefe, ya patient 'din ta ka da babies 'din ta". Architect ya fa'da.
"Alhamdulillah wallahi, son 'Dan kwanakin nan ma da haka nan baka ga yadda su da uwar suka murmure ba, wannan dogon wuyar da uwar su ta yi har ya soma cike wa, sai dai fa yaran akwai 'diba, hana ta bacci suke, do ma na sayo mata madara ba bai was baaba Habiba anq ha'da musu dashi, don idan ba haka ba, wallahi ba 'karamin wuya uwar zata sha ba". Dr Naseer y fa'da.
"Ai 'ya'ya biyar ba wasa ba". Fa'din architect.
"Yauwa Naseer, ka fara shaida min a waya yadda ku ka yi da daddy. Wai da gaske ya amince ka tafi da wannan baiwar Allah da 'ya'yan ta?" Dr ya tambayi architect cike da mamaki a fuskar shi.
"Wallahi abokina ya amince, yanzu saura Abu 'daya, gobe ko jibi na ke so mu wuce *KANO*, sai dai wani hanzari ba gudu ba, shin ita zata yadda ta bi ni".
"To idan ba ta bika ba Ina za ta da 'ya'yq har biyar?" Fa'din dr.
"Ga shawarar da na kawo, yanzu idan ka rubuta mana sallama, zan kwashe ta ita da 'ya'yan ta a mota, sai muje can wajan 'kanin mahaifin na ta, idan ya hakura to, idan kuma ya na nan a kan bakar shi, sai in lalla'bata muyi *KANO*". Naseer ya fa'din hakan.
"To shikenan yadda ka CE, hakan za'ayi, yanzu bari na rubuta sallamar sai mu tafi, Dan ni ma zan biku don na zama shaida" dr ya fa'da tare da zaro wata pepar ya soma rubutu.
"Ni bari na Shiga na duba su". Fa'din architect Naseer tare da mi'kewa ya fita
*_____________________________________*
"Gaskiya baaba ni dai na gaji da tsotsan Ayaan, duk ya fisu ci wallahi, duk sai 'karar da ni ya ke"
"Kai *MUFEEDA* kowa ya kalle ki ya San kin ciko kin yi dumurmur dake, 'ya'yan nan basu saki rama ba. Ke ba ki ganin irin cin da kike yi ne yanzu"
Turo baki rai tare da fa'din,
"Yoo ai suke kwashe duk abincin da nashi, da naci da sun tsotse, shiyasa ko wani bayan awa biyu na ke jin kamar an min yasar cikin"
"Gaskiya kam dole kiji kamar ana miki yasar cikin, ai 'ya'ya biyar ba wasa ba" fa'din Naseer da shigowar shi ke nan ya iske ta na korafi.
Da Sauri ta 'dago ta kalle shi, son ba ta tsammaci zuwan shi a yai ba, wani irin da'di taji da ganin shi. Sunkuyar da kai ta yi tare da fa'din,
"Sannu da zuwa, ina yi ni ya hanya?"
'Karasawa yai ya 'dauki Ayaan dake kan cinyar ta tare da fa'din
"Lafiya qalau alhamdulillah. Ya qarfin jiki?"
Kai a sunkuye kamar wani sirikin ta ta bashi amsa da lafiya 'kalau.
"Baaba Habiba ina yi ni, mun same Ku lafiya???"
"Lafiya 'kalau Nasuru, ya wajan iyayan ba ka, ya ka baro su??"
"Lafiya 'kalau muka bari su, sunce a gaishe ku. Ya kuma hidima da jikoki??"
" 'yan jikoki ga sunan tubarkallah sai 'kiba suke abun su".
Dr Haroon ne ya shigo tare da fa'din,
"My petient, yau dai dai gida" sai ya mai da kallon shi izuwa ga Baaba Habiba ya CE,
"Baaba yau dai zaman asibiti ya 'kare, an sallame ku sai gida yau".
"To to alhamdulillah, ai jikin yai sauki, yara kuma ga sunan Masha Allah". Fa'din baaba Habiba.
"Gaskiya kam, yanzu baaba sai a fara harha'da kaya, ni ma bari na taya ku da 'daukar wasu cikin mota".
" To 'dan albarka" fa'din baaba Habiba.
*MUFEEDA* kuwa tunda akai maganar sallama ta dai na fahimtar ko mai, don gaba 'daya hankalin ta ya tashi, tunani ta fara yi ina zata nufa da 'ya'ya har biyar. Ba tai aune ba ta fara jin saukar zafafan hawaye a fuskan ta.
'Dagowar da architect Naseer yai ya sauka akan fuskar ta, har yanzu dai fuskar cike ta ke da 'kuraje. Kallon ta yai na wasu 'yan da'ki'kai sannan yai ajiyar zuciya tare da fa'din,
"*MUFEESA* ki ba ni dama in taimaki rayuwar ki, na San ki na fama da 'kunci da ba'kin cikin a zuciyar ki, ban San labarin ki kamar yadda na fa'da miki a baya, amma haka kawai na ji ina bu'katar taimakon ki dai dai gwargwadon iya ka ta".
Sosai ta fashe da kuma mai yin rai. Cikin kuka ta ke fa'din,
" yaya na kowa ya guje ni, ban da uwa ban da uba, ba ni da bngon jingina, Wanda na dogara dashi, ya wulakantani ya Kore ni, 'kanin mahaifina shi ma y kyamace ni, gwara kowa akan irin tsanan da dangin mahaifiya ta su ke min. Meye laifi na, mai na musu, mai yasa kowa ke kyamatata.*YA ALLAH*" Sai ta kuma rushewa da wani tsumamman kuma da ya firgita 'yan biyar suma a lokaci 'daya suka saki kuka.
Idanwan shi ne sukaa ka'da su kai jajir, jijiyoyi kan shi duk su kai ru'du ru'du.
"Idan har cikin zuciyar ki kin 'dauke ni matsayin yaya to ina so ki share hawayan ki, kamar yadda na mi ki al'kawari zan taimaki rayuwar ki da izinin ubangiji. Yanzu ki kimtsa, za muje can gidan 'kanin mahaifin na ki, idan ya saduda ya amshe ki, to idan kuma bai amshe ki ba, ni zan tafi dake" ya na gama fa'din haka ya fice saboda zuciyar shi da ke wani irin tafarfasa. Wannan zuwan da zai yi wajan 'kanin mahaifin ta ma, don dai ya na son kafa hujja ne, amma da babu abunda za suje su yi a can, daga nan *KANO* kawai zasu wuce.
Cikin 'kan'kanin lokacin suka gama parking kayan suka kai mota. Baaba Habiba goyi *SHAHIDA* *ABID* kuma a hannun ta. *MUFEEDA* ta dauki *AYAAN* wata nurse kuma ta dauki *IRFANA* ya yin da dr Haroon ya 'dauki *HUSNA*. Dama shi architect tuni ya na cikin mota. Nurse 'din nan ta aje *IRFANA* a cikin mota cikin 'Dan gadon jarirai ta koma cikin, kasancewar dacSEINNA ya zo. Bayan sun shisshiga, doc Haroon na gaba, architect Naseer yaja mota tare da nufan gidan 'kanin baban *MUFEEDA*
*HMMMMM NI KUWA MAMAN UMMEE NA CE ASHE ZA'A KWASHI 'YAN KALLO KENAN A GIDAN KALLAH*
*COMMENT DIN KU SHI ZAI BA NI DAMAN SUBURBU'DO MUKU NEXT PAGE, JIN SHURU YA NA NUFIN AJE TYPING*
*MAMAN UMMEEN KU CE*✍🏼
[7/17, 3:10 PM] Babyy: *بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahimm* ( _Maman Ummee_)
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
_Wannan page 'din tukuici ne a gare ki Hauwa saboda sharhin ki na 'karamin karsashi. Allah dai ya bar 'kauna_💕💝💓❤️😍💗.
*PAGE 11*
*___________________________________*
A 'Dan nesa da 'kofar gidan su kai parking. Architect Naseer ya juyo idanuwan nan nashi jazur ya kalli MUFEEDA ta re da fa'din,
"Ki aje yaran ki fito mu 'karasa".
Gaban ta dukan uku-uku ta aje AYAAN dake kan cinyar ta a inda ta ta shi sannan ta fito daga cikin motar. Dr Haroon ma ya fito kasancewar shi architect tuni har ya kai kofar gidan ya tsaya. Baaba Habiba kawai a ka bari da yara.
"Shiga ciki". Shine abunda Naseer ya fa'di tare da tsuke fuska kamar ba shi yai maganar ba. Da sauri kuwa ta 'dago ta kalle sa idanuwan ta Na zubda kwalla, jikin ta har wani rawa yake yi.
"Ki Shiga na ce, babu abunda zai faru". Kamin ma MUFEEDA tai yun'kurin shiga ciki, kamar an turo Kallah said gashi ya fito, ya ci kwalliya da 'daya daga cikin shaddojin shi da yake matu'kar ji da shi, don occasionally yake amfani da kayan. Kuma daga dukkan alama Sauri ya ke yi. Wani wawan burki yaja tare da furta,
"Kan uwar nan! Ke dan kafatanin dangin uwar ki ba Na CE ka da ba 'kara ganin mai kama dake a kwar gida Na ba? Wato kin rai Na ni ko?" Sai kuma ya juya ya kalli Naseer, wani kallon yau zaka ci uwar ka ya watsa masa tare da kyasta na uku da na babban yatsa a saitin fuskan architect ya ce,
"Yau zaka san cewa ni ma kwallon shege ne, wato kai ga 'dan iska, kuma wuyar ka ya isa yanka. Shi ne har zaka 'kara zuwa min kwar gida wato in yi duk abun da na ga dama koh? To kuwa zaka ga abunda zan yi yanzun nan". Da Sauri ya koma gida ya na kwa'da kiran mai zogale.
MUFEEDA ba ta san sanda ta kama hannun arc Naseer ba ta re da fa'din,
"Dan Allah ya ya mu gudu ka da ya fito ya same mu ana wajan, dan Allah". Ta na maganar ne ta na kuka kasancewar ta san wanene 'kanin mahaifin na ta, ba 'karamin aikin shi ba ne ya tara masu jama'a a nan wajan, ko ma ya jefi Naseer 'din da mummunan sharri a cikin jerin sherurrukan na sa.
Hannun shi ya zame a cikin na ta tare da fa'din,
"MUFEEY ki kwantar da hankalin ki, ni ma da nawa shirin nazo. Ka da ki damu da duk abunda zan fa'di, dai dai na ke da shi".
"A'aah ba za ai haka ba architect, mu bi mutumin nan a hankali". Fa'din Dr Haroon.
"An'ki a bishi a hankalin, kai ni fa ban zo nan ba don ne man sulhu, na zo ne na 'kafa hujja ko da zuwa nan gaba. Kuma ina son in maka wani kashe di, ko da wasa ban san ya san abunda MUFEEY ta Haifa".
Kamin Dr Haroon ya ce wani abu, sai ga mai zogala da wani uban gudu, saura ka'dan ta zame tai saurin dafe bango tare da kurma wani uban ashar.
"Yi a hankali mai zogale, kin san dai ba 'kaunar ki ake a unguwar nan ba, magauta na nan na kallon ki". Kallah ya fa'da tare da saurin zuwa Kusa da ita.
"Ai kuwa wallahi dai dai na ke da ko wani Dan kutunar bura uba". Zanin jikin ta saura ka'dan ya idasa kwancewa, tai azamar ru'kowa ta fito gidan gaba daya ta na wani zazzaro idanu. Da sauri MUFEEDA ta 'buya a bayan Naseer.
"Dan uwar ki dole ki 'boye ai, shegiya mai 'kama da jimina. 'Yar iskan yarinya wato kwaratan na ki har biyu ne kenan, lallai MUFEEDA wuyar ki ya isa yan ka, wato kin kawo su ki gwada mana uwar ki ta yi zama a 'kasan gada ko? To wallahi ba anan gidan ba, kin gama zama a gidan nan, zaku 'bace ko sai na muku yekuwa jama'a".
Dr Haroon yai saurin cewa,
"Wallahi baaba ba abunda kuke zato ba ne, wannan baiwar Allah ba........"
"Dan gyatumar ka ne mi baabar ka can in da ma fito wajan watsattsu, ka da ma 'kara kira na baabar ka idan ba haka ba inyi hajijiya da kai wallahi". Mai zogale ta fa'da.
Naseer da ran shi ya kai 'kololuwa wajan 'ba ci ya CE,
" Dallah malama mu ba wajan ki muka zo ba, don ni ba na magana da masu kwakwalan kifi, ki jaye ki bamu waje da mai gidan ki zamu yi magana. Kuma shi ma ba doguwar magana CE ta kawo mu ba, tambaya daya tak zan mashi, tabayar kuam ita CE, shin zai ri'ke MUFEEDA awajan shi amana kamar yadda 'Dan uwan shi ya bar masa, ko kuwa zai yi watsi da amanar? Ma'anan bazai ri'ke ta ba". Naseer ya fa'da a matukar fusace jijiyoyin wuyan shi duk sun fito sun yi bur'dun bur'dun.
"To *AKU* sarkin magana, bazan ri'ke ba 'din, ka saka ni a wuta ko idan Nazo Shiga ALJANNAN ka tare hanya saboda na'ki ri'ke zumunci. Ka ga min 'Dan iskan yaro". Fa'din Kallah tare da hayayya'ko masa.
" Fine, dama abunda na ke son ji ke nan, kuma ka sa ni, wallahi ko da wasa ka nuna cewa ka na da wata 'yar 'Dan uwa mai sunan *MUFEEDA* wallahi! wallahi!! wallahi!!! Hukuma ce za ta raba mu".
Ya na gama fa'din haka ya ja hannun MUFEEDA a matu'kar fusace su ka fara tafiya.
"Yeeekuwa jama'a, JAMA'AAAH kuna ina? Ku fito ku gane was kan ku, MUFEEDA CE da kwarton ta har kofar gidan uban ta, ku firfito ku firfito kuga tsantsan karuwan ci a gabam idanuwan ku". Mai zogale CE ke wannan maganar da iya 'karfin ta. Aikuwa kan ka CE kwabo jama'a makwafta sun firfito,vya yin da shi kuma Naseer yai saki hannun Mufeeda ba, ita kuma gaba daya jikin ta a sake ya ke, shi ke controling din ta ma, ko juyowa ya hana ta yi, sai ma bu'de mota da ya yi ya saka tq a ciki. Baaba Habiba kuwa kuka ta ke domin ta na hango duk abun da ke faruwa daga cikin motar. Kallon 'yaran ta yi, ta kuma kallon Mufeeda da ita ma ta ha'da kai da guiwa ta na kuka, sai zuciyar ta ta 'kara karye wa ta saki kuka mara sauti, don ka da ta 'kara karya zuciyar Mufeedan.
Mutane kuwa wasu na mamakin dama haka Mufeeda ta ke, a fuskar Musa zuciyar kuma Fir'auna. Ya yin da wasu kuma su kai tur da hali irin na Kallah da Mai Zogale.
Reverse ya yi ta re da fizgar motar ya bar unguwar zuciyar sa na masa suya, al'kawari ya 'kara 'daukar wa kan sa akan zai taimaki Mufeeda da 'ya'yan ta har iya inda 'karfin sa ya 'kare.
Kai tsaye gidan Dr Haroon ya nufa, babu Wanda ya CE wa kowa 'kala a cikin su, don zuciyar kowa tafarfasa ya ke yi, ya yin da Mufeeda kuwa da ke kuka har yanzu kuma babu Wanda yai yun'kurin lallashin ta, domin kukan ne kawai zai rage mata ra'da'di. A 'kofar gidan yai parking. Sai a lokacin Naseer ya saki wani wawan ajiyar zuciya ta re da fa'din, baaba Habiba min gode kwarai da taimakon ki a gare mu, ha'ki'ka bazan man ta da hakan ba". Rafar Dari Dari ban dur daya ya mi'ka mata tare da fa'din,
"Baaba ga wannan, mu zamu wuce *KANO*.
Da sauri MUFEEDA ta 'dago don jin kanon da architect Naseer ya fa'da.
Baaba Habiba kuwa girgiza kai ta yi tare da fa'din,
" wallahi 'da na bazan kar'bi ku'din nan ba, zaman da na yi da Mufeeda don Allah na yi shi, don wallahi har cikin zuciya ta na ke jin ta tamkar 'diyar da na haifa, fata na a gare ta shi ne, Allah ya dubi maraicin ta ya kawo mata mafita". Da kuka ta 'karashe maganar. Mufeeda kuwa wani irin runguma ta mata tare da fashewa da kuka kamar ran ta zai fita. Dakyar baaba Habiba ta zare jikin ta ta fito, don cibaga da zama a motar zai iya FASA mata zuciya saboda tausayin Mufeesa. Ba ta iya juyowa ba ta kalli Mufeeda tai saurin shigewa ciki, don ji ta ke Ina ma ai ma ta tayin tafiya kanon tare da Mufeeda ta rin'ka kula dasu, tunda ita ma ba ta da kowa duk su na 'kauye. Allah yai ba ta haihuwa ba, kuma iyayan ta duk sun rasu, nai man na kai ta fito birni saboda zamani na yanzu kowa kan sa ya sani daga kwauri said guiwa. Shi yasa ita ma ta fito dai taimakon kan ta. Kuma ita 'din ma ba wata tsohuwa ba CE, don baza ta wuce irin arba'in da biyar 'din nan ba, kawai wahala CE ta mai da ta kamar 'yar shekara sittin.
"Aboki na kanon ka nufa ke nan??" Dr Haroon ya fa'da.
Gya'da masa kai kawai ya iya yi.
"Idan har ka na ganin ba damuwa, ga shawarar".
"Ina jin ka". Shi ne abunda architect ya fa'da.
"Kai tafi da baaba Habiba kano idan za ta amince, soboda kula da 'ya'ya har biyar ba abun mutun biyu