Showing 51001 words to 54000 words out of 115393 words
abunda Musa ya fa'da.
Ita kuwa Mufeeda murmushi ta 'ka'karo tare da fa'din,
"Ina wuni? Ya hanya?".
Kallon ya ke fuskan shi 'dauke da murmushin jin da'din ganin fuskan ta. Ya ce,
"Alhamdulillah. Na same ki lafiya? Na tafi can ina ta 'kewar ki. Duk na 'kosa na dawo na ganki".
"To ai ga ni ka ganni yanzu".
"Au haka ma zaki ce, wato ke ba ki ke wa ta na ke nan?".
Dariya ta yi sai fararan ha'korin ta su ka bayya na. Ta ce,
"Na yi mana".
"Ba wanin nan, gashi nan ma ko irin zumu'din ganin nawa ma ban ga ni a tattare da ke ba".
"Lallai, haka dai na ce". Fa'din Mufeeda.
Ledar hannun sa ya mi'ka mata tare da fa'din,
"Ga 'yar tsarabar ki nan, ki ha'kuri ba yawa".
No'kewa ta yi tare da 'kin kar'ban ledar.
Fuskan shi ya 'dan tamke tare da fa'din,
"Za ki fara ko? Kin fi kowa Sanin abunda na tsana ke nan. Ni da ke ai mun zama 'daya. Ba na son wannan abu da ki ke min. Ko ni da ke ba 'daya ba ne?".
" *NI DA KAI ABU 'DAYA NE*". Mufeeda ta ba shi amsa kan ta na 'kasa ta na wasa da 'kasan hijabin ta".
"Yauwa to idan dai haka ne, amshi nan". Ya fa'di hakan ne ta re da mi'ka mata 'katuwar ledan.
Amsa ta yi tare da fa'din,
"Nagode Allah ya saka da alkhairi, ya kuma 'kara bu'di".
"Ameen gimbiya ta. Meye labari?"
"Labari na wajan ka". Mufeeda ta ba shi amsa.
Nan suka cigaba da soyayya cikin nisha'di.
Karfe tara ya mata sayyama ita kuma ta shigo cikin gida.
Karaf *MAI ZOGALE* ta warce 'katuwar ledan da ke hannun ta tare da fa'din,
"Munahika, da wucewa 'daki za ki yi da wannan 'katuwar Leda 'daki? Wato ki ce ke ka'dai ko?".
" *MAI ZOGALE*, bu'de mana ledar muga abunda ke ciki". Marwanatu ta fa'da.
Hayaniyar su ne ya fito da KALLAH daga cikin 'daki da har bacci ya soma 'daukar sa.
"Wai me ke faruwa ne *MAI ZOGALE?*". KALLAH ya fa'da.
"Wannan 'yar iskan yarinyar nan ne wannan yaro ya kawo mata 'katuwar leda. Ka gan ta nan (ta nuna masa ledar). Shine ta ke son shigewa 'daki ta ci ita ka'dai". Fa'din *MAI ZOGALE*.
'Karasowa ya yi tare da 'kafa mata rankwashi a kai ka na ya ce,
"Shegiya mai mugun hali irin na uwale da ubale". Sai ya mai da duban shi ga *MAI ZOGALE* tare da fa'din,
"Zazzage ledar muga me ke ciki".
*MAI ZOGALE* ta shiga zazzage ledar kasancewar akwai wutar lantarki a tsakar gidan. Akwai wadataccan haske .
Wasu dogayen riguna ne guda uku 'yan kanti masu matu'kar kyawu. Sai mayukan shampoo da conditional da kumakumai. Sai kuma roban ice-cream irin manya² roban nan da chocolate da biscuits kala². Ga turaruka designers masu 'dan karan 'kamshi ko ba'a fesa a jiki ba. Da su kayan kwalliya.
Shasshe'kar kukan Marwanatu ke tashi a tsakar gidan.
Da sauri KALLAH ya kalle ta tare da fa'din,
" *SHALELE* lafiya? Mai ya same ki?".
"Wallahi idan har ba za ku min abunda na ke so ba a gidan nan, za ku ne me ni ku rasa". Ta na gama fa'din hakan ta zu'ba 'dakin ta da gudu tare da kullo 'kofa.
Da gudu KALLAH ya bi ta ya na bubbuga kofar tare da magiyar ta bu'de. Amma fir ta'ki bu'dewa. Sai gunjin kukan ta ya ke ji hankalin shi na tashi.
Tattare kayan *MAI ZOGALE* ta yi ta re da kallon Mufeeda ta ce,
"Kin wani zuba min idanu, ai sai ki wuce ki ba ni waje. Don na yi rantsuwa ba ki cin ko mai a cikin kayan nan. Zan dai iya daurewa in ba ki riga 'daya. Shi ma sai Marwa ta za'ba ta darje".
"Yi ha'kuri *MAI ZOGALE*, je fa ta da minti ko kwaya 'daya ne". Fa'din KALLAH ta re da 'karisowa wajan.
Harara *MAI ZOGALE* ta maka masa tare da fa'din,
"Sittin ta ubangiji bazan bata ba, idan ka na da 'karfi kwata ka bata".
"Aah haba wane ni. Kawai da ma tausayi ta ba ni shiyasa na ce a bata minti guda 'daya". Fa'din KALLAH.
"To ban bayarwa". Fa'din *MAI ZOGALE* ta re da nufar 'dakin ta. KALLAH ya rufa mata baya.
Mufeeda kuwa ta na nan tsaye kamar icce, wasu zafafan hawaye na kwaranyowa daga idanuwan ta. Da kyar ta iya Jan 'kafa ta shige 'dakin ta tare da fa'dawa kan 'yar yaloluwar katifar ta, ta saki kuka mai ta'ba zuciya.
***************
"Wallahi idan har ka ce bazaka tuna baya akan tilon 'yar ka ba, zamu tattara ni da Marwanatu mu bar maka gidan tun da ba ka son farin cikin mu. Ka fi 'kaunar 'diyar wanka akan mu". Fa'din *MAI ZOGALE* tare da matsar hawaye.
"Haba², menene kuma haka *MAI ZOGALE?*, Meye na kukan? Kin fa san akan ku babu abunda bazan iya ba. Kawai dai tsoro na 'daya, shine yadda naga mutuwar mahaifi na. Shine kawai ke tayar min da hankali". Fa'din KALLAH.
"To ai se ka je kai ta tsoron, abunda za kai so 'daya kawai. Idan ya so daga baya ka ro'ki Allah ya gafarta maka. Ai Allah ya ce, duk abunda kai na laifi, idan na ro'ke shi zai yafe maka".
"Au haka ne *MAI ZOGALE?*".
"Yo hakane mana".
"To idan dai haka ne, ki shaidawa Marwanatu damuwar ta ya kau. Musa ya gama zama na ta. Shi da kan shi zai zo ne man auren Marwa gidan nan. Ku ba ni kwana uku kacal".
Wani da'di ne ya mamaye zuciyar *MAI ZOGALE* ta ce,
" Yauwa ko kai fa KALLAH " tare da mi'ka mata hannun suka karshe kamar tsoffin 'yan bariki.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 28_*
Washa gari da safe, Mufeeda ta tashi tai ayyukan gida as usual. Sannan ta 'daurawa Marwanatu ruwan wanka bayan ta yi na ta.
Mashkura ce tai sallama ta re da shigowa cikin gidan. Cikin sauri Mufeeda ta 'karisa gare ta tare da rufe mata ba ki ta na kuma yi mata alama da hannu ka da ta 'daga muryan ta don ka da ta tashi mutanan gidan duk da ba yanzu garin ya waye ba. Don kusan karfe goma ne na safiya.
"Dalla ni sakar min baki, su tashi mana. Sai ka ce wasu kasa, tun baccin jiya. Wallahi ko rantsuwa na yi bazan yi kaffara ba, nasan babu Wanda yai sallar asubha a cikin su. Mtsw! Aikin banza. Ke KI ke nuna ki na jin tsoran su shiyasa su ke juya ki yadda su ke so. Wallahi da ni ne ke da tuni na yi aljanun 'karya na karya 'kasusuwan wancan shagi'da'd'diyar yayar ta ki". Fa'din Mashkura tare da ture hannun Mufeeda a bakin ta.
"Dan girman Allah *KURA* ki rufa min asiri, ka da ki ja fitar ma a hana ni". Mufeeda ta fa'da a marairaice.
Harara Mashkura ta watsa mata tare da fa'din,
"Na ji dan Allah, ka da ki min kuka, *MOTHER INDIA*".
"Eh na ji 'din" fa'din Mufeeda.
"Wani munahincin ake 'kullawa a wajan?". Fa'din *MAI ZOGALE* da fitowar ta ke nan daga 'baki baki duk miyan bacci.
"Ba da ku na ke ba, ko wacce ta tsatstsare ni da shegun idanuwa kamar za'a cinye ni 'danya". Fa'din *MAI ZOGALE* a hassale.
"Ayya Inna ba gulma muke ba, *KURA* ce ta biyo ma ni domin muje mu dubo result 'din mu, jiya network ya hana". Fa'din Mufeeda bakin ta har wani cracking ya ke yi.
Harara *MAI ZOGALE* ta jefi Mashkura da shi tare da fa'din,
"Ke wallahi *KURA* ki ke ko *DAMUSA*".
" *KURA* na ke". Mashkura tai saurin ba ta amsa.
Saurin kallon ta Mufeeda ta yi tare da marairaice wa. Ita kuma tai kamar ba ta ga ni ba.
*MAI ZOGALE* ta cigaba,
"Da ma na da'de da sanin ke ce ke nuna mata hanyar 'dai'daicewa. To wallahi idan ba ki fita daga idanuwan nan nawa na kulle ba, za ki ga abun da zan miki. Shegiyar yarinya, sai kafi'diri ke ba wani kyawu ba. Babu na huska bare na jiki. Zan zo har wajan uwarki, idan ba ta ja maki kunne akan hurewa Muheeda kunne ba, ni zan yi maganin ki da kai na, Sittin ta ubangiji idan kuma kin 'karya ta, ki cigaba ki ga ni".
Kamar Mashkura za ta ba ta amsa dai dai da ita, sai kuma tai wani tunani, idan har ta ba ta amsa, ita barin gidan za ta yi, bala'in akan Mufeeda zai 'kare. Sai tai shuru ta kyale ta, amma zuciyar ta tafarfasa ya ke yi.
"Ke kuma". *MAI ZOGALE* ta nuna Mufeeda,
"Ba za ki bar gidan nan ba sai kin gama komai wallahi, har kewaye sai kin wanke".
Da "To" Mufeeda ta amsa. Da ma ta gama komai, kewayen ne kawai ba ta wanke ba.
Ruwa ta ja a bokiti ta nufi kewayen ta wanke taaas tare da 'daurayo jikin ta sannan ta dawo 'daki ta shirya. Mashkura na waje na jiran ta don ta'ki shiga 'dakin, ta ce ita waje za ta tsaya.
Sauri sauri ta gama shiryawa. Doguwar riga ta saka ba'ka irin na larabawa da yaji stones jaa, sai tai rolling da gyalan abayan. Ba 'karamin kyawu ta yi ba kasancewar ta farar mace a cikin ba'ka'ken kaya. Flat shoe jaa ta saka tare da 'daukar purse jaa ta fito.
Mashkura na ganin ta tai hanyar waje, Mufeeda ta mara mata baya.
"Feedy kin ga yadda ki kai kyau kuwa. Anya bazan dai na jerawa da ke ba kuwa? Gaskiya idan na cigaba da jerawa da ke kasuwa za ki kashe min".
Hararar wasa Mufeeda ta jefe ta da shi tare da fa'din,
"Dalla matsa can, ke dai ki na da abun haushi wallahi. Yanzu ina zamu je? Kasuwan Sati ko bus stop?".
"Muje bus stop, zai fi sau'ki". Mashkura ta ba ta amsa.
Kiiii Mufeeda ta ja ta tsaya jikin wata akori kura.
Sauri kallon ta Mashkura ta yi tare da fa'din,
"Lafiya Feedy? Ya na ga kin tsaya?".
Saurara ki ji, wallahi ina bala'in son wa'kar nan, *Salman khan* ne ya yi ta a cikin film 'din *HERO*, kin manta, a gidan ku ma na kalla lokacin su na haskawa a tashar *BOLLYWOOD*.
Wawan tsaki Mashkura ta yi tare da saurarawa, don ita Sam ba ta ma ga ne wani film Mufeeda ke magana a kai ba. Don ita Indian film Sam bai dame ta ba, da dai Korean film ne ko Philippines.
*_Aankhon ke panno pe_*
*_Maine likha that say dafaa_*
*_lafzon mein Jo ishq tha_*
*_Huya naa hothon se bayaan_*
*_Khud se naraaz hoon_*
*_Kyun be-aawaaz hoon_*
*Meri khamoshiyan gain sazaa*
*Dil hai yeah sochta*
*_Phir bhi nahi pataa_*
*_Kis haq se kahin bataa_*
*_Ke Main Hoon Hero Tera_*
*_Ke Main Hoon Hero Tera_*
*Ke Main Hoon Hero Tera*
*Ke Main Hoon Hero Tera*
*_Main Hoon Hero Hero Tera_*
"Don son Allah ki zo mu wuce hakanan, ai kin ji". Fa'din Mashkura.
"Ai da kin bar ta, kin san halin 'dan 'kauye". Fa'din wannan kyakkyawan saurayin da ya gitta su yanzu.
"Kam bala'i! Na rantse da ubangiji, *KURA* zan yi wa wannan yaron mummunar wula'kanci. Ni ina wasa da shi ne?".
Dariya ne ke cin *KURA*, amma ta San muddin ta sake shi, ta shiga uku. Gumtse dariyar ta ta yi tare da fa'din,
" ki yi ha'kuri ki kyale shi, idan Naseer ne, haka ya ke da nai man fa'da wallahi ".
"Aikuwa zan yi maganin shi wallahi". Fa'din Mufeeda tare da yin gaba.
*__________________*
"Hello Ummu na, ki na ji na?". Naseer da ke kwance samar rantsattsan 3sitter king set ne ya fa'di hakan waya 'kirar CAMON16 'kare a kunnan shi.
"Abie ina jin ka". Wata kamilalliyar murya ta ba shi amsa daga 'daya 'bangaren.
Turo baki ya yi kamar ta na ganin shi, tare da fa'din,
"Ayya Ummu na, shi ne ki ka min shuru bayan ki na ji na".
Sanyayyiyar dariya ta saki tare da fa'din,
"To Abie, abun na ka ne da mamaki, ka na son yarinya, amma ka kasa ka gabatar da kan wajan. Zauna kallon ruwa kwa'do ya maka 'kafa".
"Ummu na please stop saying that. Ki na sakawa gabana ya na fa'duwa Wallahi. Wai ummu kinga yarinyar kuwa? Very beautiful wallahi".
"Ooh Abie ya fetse, ko kunya ta ma bai ji yanzu".
"Ummu idan ban fa'da miki abundape zuciya ta ba wa zan fa'dawa? Kin san dai Mom ba damuwa ta yi da ni ba. Kamar ba 'dan ta ba. Imaging! Wai first born ne ake wa haka. Ni wallahi ba NA son wannan habit na hausawa. Ummu ke ce kawai ki ke so na, sai dad".
"Ita ma mummyn na ka ta na son ka, kawaici ne ta ke yi da ake wa 'dan fari".
"I hate that". Naseer ya fa'da". Naseer ya fa'da. Tare da saurin 'kara fa'din,
"Yauwa Ummu, back to our topic, yanzu ya zan yi na shawo kan ta?".
"Yauwa, firstly, ka dai na mai man fa'dan ta. Mace ba ta son a na kushe ta. Secondly, ka cire tsoro ka je gida kai sallama da iyayan ta ka mai mi zini, idan sun baka, sai kai fighting soyayya a wajan ta. It's very easy idan Ka bi shi a easiest way. Thirdly, ita ma ce ta na son a ri'ka ya bon ta. Sannun ka da Ka ri'ka zuwa wajan ta empty handed bayan ta amince".
Ga wanga ku 'kara da shi, dazun abubuwa ne su ka min yawa. Mu ja me gobe.
*MAMAN UMMEE✍🏼*
*MANAGE PLEASE, IDAN 'DAN WANI UZURI NE*
*MATAR SAYYADEE CE*✍🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
®🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*
*_Z• W• F•🏝_*
🌟NI DA SHI ABU DAYA NE🌟
('kiʀ'kiʀɑʀʀɑɳ ʆɑɓɑʀi)
ɓɑɳ yi ɗɑɳ wɑɳʝ kѳ wɑtɑ ɓɑ, iɗɑɳ yɑ yi รɦigɛ ɗɑ ʆɑɓɑʀiɳ ki/kɑ ɑkɑรi ɑkɑ รɑɱu.
laвarι ne мaι cιĸe da zazzaғan ѕoyayya, yaυdara, cιn aмana тare da 'dυмвιn nadaмa.
*Story and written by*
*Zulfa'u 'Saeed Ibrahim* ( _Maman Ummee_). @lso known @s
*MATAR SAYYADEE*
Dҽɖɩcatҽɖ tɷ mʏ 'kawaɭɭɩʏa ɾɷmaŋ ʝa'ɮa (ʍʏ ռaʍɛ saҡɛ )
*_PAGE 29_*
"Ummu na ki na ganin zata amince? Ni amincewar ta kawai na ke bu'kata. Idan har ta amince sauran sharu'd'dan duk masu sau'ki ne". Fa'din Naseer ya na wani marairaicewa kamar ya na gaban ummun.
"Abie in sha Allah zata amince maka. Haba kar ka ba ni kunya mana. Kai fa irin saurayin da mace ba ta iya rejecting ne". Fa'din Ummu na.
Wani sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da fa'din,
"Ummu na wallahi I'm deeply in love".
"Ahh naga alama kam. Tun da gashi dalilin hakan ko 'dan kunyar nan nawa ma baka ji". Fa'din Ummu na.
"Shafa kyeyar shi yai kamar ta na kallon sa, zai yi magana kenan ya jiyo muryan wata yarinya daga can 'bangaran Ummu na ta na fa'din,
"Ummu please in je in 'dauka?".
"To mayya, je ki 'dauka tun ka min ki cinye ni 'danya". Fa'din Ummu na.
"Halan Aeedah ce?". Fa'din Naseer.
"Ita ce mata, sarkin naci. Ni ina ga 'karshan shekaran nan ma zan turo ta Nigeria ta zo zumunci".
"Haba Ummu na, ke ba za ki zo ba kenan? Ni fa wallahi sai in ga kamar ba ki so na. Ban ta'ba ganin fuskan ki ba sai a hoto ko video call. Haka ni ma tun ina da 10year aka ce min kin koma saudiyya. Kawai uncle Sauban ya kwamushe mana ke. Gaskiya ku tattaro ku dawo Nigeria da zama". Fa'din Naseer ya na wani turo ba ki.
"Da zai yuwu da tun tuni mun dawo Abie, aikin sa na ya kai mu can, amma in sha Allah zan zo ka ji Abie na". Fa'din Ummu na cike da lallashi.
"Shikenan Ummu na, Allah ya kawo min ke lafiya". Naseer ya fa'da.
"Ameen my son. Za mu yi waya anjima, yanzu za muyi ba'ki. Bara na je na yi girki". Ummu na ta fa'da.
"Ok by Ummu".
"Bye". Dif